Monday, February 25, 2013

Binciken Malaman Kimiyya kan Yadda Bacci da Mafarki ke Samuwa (3)


Matakan Bacci

Baya bayani ya gabata cewa akwai nau'ukan bacci guda biyu; da bacci mai nauyi, da mara nauyi.  Mai nauyin, wanda Malaman Kimiyya ke kira Non-Rapid Eye Movement (NREM) Sleep, yana dauke ne da matakai guda hudu. Da gajeren bacci ko gyangyadi, kamar yadda na kira shi, da mataki na biyu wanda ke dauke da bacci na hakika.   Wannan shi ne matakin da malaman kimiyya ke kira True Sleep.  Har dai zuwa mataki na hudun.  Nau'i na biyu kuma shi ne madaidaicin bacci, wanda suka kira Rapid Eye Movement (REM) Sleep. A wannan mataki ne kwayan idanun mai bacci ke jujjuya a sadda yake bacci.  Sai dai kuma, sabanin yadda bayanai suka zo, idan dan adam ya shiga bacci, matakan da yake bi cikin baccin sun sha bamban.  Ba wai daga gyangyadi yake farawa, daga nan ya wuce matakan nau'i na farko, ya shiga na biyu, daga nan ya farka ba.  Abin ya wuce haka.

Da zarar mutum ya kwanta bacci zai bi matakin farko na bacci mai nauyi, zuwa matakin bacci na biyu, da mataki na uku, da mataki na hudu.  Wannan kan faru har na tsawon mintuna 90, kafin mai bacci ya shiga nau'in bacci na biyu, wato madaidaicin bacci kenan.  Idan ya shiga madaidaicin bacci, zai ci gaba da yin bacci, kafin wani lokaci sai kuma ya sake dawowa  matakin bacci mai nauyi na uku, wato Delta Sleep kenan, kamar yadda bayani ya gabata a baya. Daga nan ya sake gangarowa matakin bacci na biyu, wato True Sleep.  Da zarar ya kwashi mintuna 20 a wannan mataki na bacci, sai kuma ya sake komawa nau'in bacci na biyu, wato nau'in baccin da kwayar idanunsa za su rika jujjuyawa a ciki.  Bincike ya nuna cewa masu bacci kan maimaita wannan yanayi sau uku zuwa hudu a kowane lokacin baccinsu, daga nan kuma sai su farka.  Wannan ke nuna mana cewa, bayan mai bacci ya wuce mataki na farko har zuwa na hudu, zai shiga yanayin bacci madaidaici, daga nan sai baccinsa ya sake nauyaya, sanadiyyar komawa mataki ba uku, daga nan kuma ya saukaka, sanadiyyar shiga mataki ba biyu, sai ya sake komawa yanayi madaidaici.  Wannan zai maimaitu kamar sau uku ko hudu kafin farkawa.  To me ke haddasa bacci ne?

Me Ke Haddasa Bacci?

Wannan tambaya ce da galibin masana suka ta kokarin amsa ta tsawon shekaru, amma har zuwa wannan lokaci samun amsa gamsasshiya ya gagara.  Wani mai tambaya a yanar sadarwa ta duniya ya jera wasu tambayoyi kan asali da samuwar bacci ga dukkan masu binciken kimiyya a duniya, wanda a cawarsa har yanzu sun kasa amsawa.  Yace me yasa, duk kwarewarsu a fannin kimiyya, da samuwar hanyoyi da na'urorin sadarwa da binciken kimiyya a duniya, amma sun kasa gano abin da ke haddasa bacci?  Yace idan har da gaske suke yi a fanninsu na bincike wanda a kanshi suka kware kuma aka sansu, me yasa har yanzu suka kasa gano dalilin da yasa dan adam da sauran halittu ke bacci?  Ta yaya aka yi suka kera kumbo har suka je duniyar wata, suka jefa wasu kumbon nazari da bincike zuwa wasu duniyoyin, suka gano cututtuka da yadda ake tiyata har ma a cire zuciya a dasa wata, a cire koda a dasa wata, amma ga bacci, wanda dabi'a ce da dan adam ya sifatu da ita, kuma shi ne abin da dan adam yafi yi cikin kashi biyu na ukun rayuwarsa, amma sun kasa gano dalili da abin da ke haddasa shi?

A hakikanin gaskiya akwai alamar cewa lallai malaman kimiyya sun gaza a wannan janibi.  Farfesa Allan Rechtschaffin, babban malami a fannin bincike kan bacci da yadda yake samuwa, wanda farfesa ne a Jami'ar Chicago da ke kasar Amurka, ya kwashe shekaru 50 yana gudanar da bincike kan bacci yadda yake samuwa da dukkan alamunsa.  Amma da kansa ya sanar da mujallar New York Times cewa, sadda aka masa tambaya kan dalilin da ke sa dan adam ya shiga yanayin bacci, yace: "Wannan wani kalubale ne mai girma ga malaman ilmin halitta (Biologists)."  A wani wuri kuma da tambaya makamanciyar wannan ta sake maimaituwa, sai ya sake cewa: "A takaice dai, har yanzu babu wani bayani kan me yasa muke bacci; kawai muna yi ne a duk sadda baccin ya dauke mu."  Wannan kamar alamar gazawa ce, to amma akwai da yawa cikin malaman kimiyya da ke ganin har yanzu bincike ake yi, kuma ba a fid da rai ba.A hakikanin gaskiya dai gano hakikanin abin da ke haddasa bacci abu ne mai wahala, domin alakar da ke tsakanin bacci da ruhin dan adam.

Agogon Dabi'a (Biological Clock)

Duk da cewa ba a gano hakikanin abin da ke haddasa dan adam bacci ba, cikin bincike da ake yi an gano lallai akwai wani yanayi na dabi'a da ke cikin jikin dan adam, wanda ke la'akari da yanayin mahalli, don tilasta wa jiki shiga yanayin bacci.  Wannan yanayin dabi'a kuwa shi ne abin da a turancin kimiyya suke kira Biological Clock, ko Circadian Rhythm.  Wannan yanayi tun cikin shekarar 1960 malaman kimiyya suka tabbatar da samuwarsa a jikin dan adam.  Wasu malamai kan kira shi Cibiyar Bacci, wato Sleep Center, amma babu wanda ya san a ina yake a jikin dan adam.  Wasu na ganin a kwakwalwa yake.  Sai dai wannan hasashe ne.  yanayi ne kawai gamamme, wanda ke amfani da mahallin da dan adam ke rayuwa a ciki.
Malaman kimiyya suka ce idan dan adam yana rayuwa a wuri, sai dare ko yamma ya shiga, nan take dabi'ar halittar jikinsa zai fahimci canjin yanayi a muhalli. Daga nan  sai wannan agogon dabi'a ya tilasta wa jikin dan adam samar da wani sinadari mai suna Melatonin wanda ke haddasa bacci nan take.  Da zarar gari ya fara wayewa kuma, jikin adam zai sinsini irin canjin da ke faruwa a lokacin da gari ya fara wayewa, sai wannan sinadari na Melatonin ya fara narkewa ko zagwanyewa, sai bacci ya kaura daga idanun mai bacci, ya farka. Da zarar rana ta fito, ko an shiga lokacin yini kuma, sai hasken rana ya hana wannan sinadari na Melatonin zuba. Wannan abu ne mai kamar saukin fahimta, amma yiwuwarsa ya sha bamban da yadda mai karatu ke karantawa ko hankaltarsa a zuciyarsa daga abin da yake karantawa a yanzu.  Domin na san yanzu haka wani zai ce ya aka yi wasu ke yin bacci da rana?  Wannan tambayar ma dai har yanzu tana jiran amsa.

Sabubban Samuwar Bacci

Duk da cewa malamai basu gano hakikanin abin da ke haddasa bacci ba, amma sun gano sabubba da dama, wadanda ke da alaka na kut-da-kut wajen jefa dan adam cikin yanayin bacci.  Daga cikinsu akwai yawan gajiya. Kamar yadda masu karatu suka sani, yawan gajiya kan sabbaba bacci.  Abu na biyu shi ne cin bashin bacci.  Ma'ana, a rashin kwanciya a lokacin da ya kamata mutum ya kwanta, wato lokacin da bacci ya bijiro masa kenan.  Galibi mukan sha shayin kahwa ko mu tauna goro don hana bacci zuwa, ko mu sha wasu kwayoyi ko a mana allura.  Duk wadannan kan hana bacci ne na wani dan gajeren lokaci, amma ba har abada ba.  Binciken malamai ya nuna cewa cin wani abu ko shan wani abu da manufar hana bacci zuwa a lokacin da ya kamata a yi shi, yana da cutarwa mai girma, sannan hakan kan canza dabi'ar jikinsa (ma'ana agogon dabi'arsa) wanda ke bayuwa zuwa ga canza masa lokacin bacci.

Cin bashin bacci, abin da malamai ke kira Sleep Debt, yana da illa sosai, kuma kwashe tsawon yini ana bacci ba ya sa mutum ya biya bashin baccin da ake binsa.  Domin kuwa lokacin baccinsa ya riga ya canza, dole sai ya sake tarbiyyar dabi'ar jikinsa wajen tilasta mata yin bacci a lokacin da ya kamata yayi.  Galibin masu gadi a lokutan dare kan samu matsalar bashin bacci, musamman idan aka sake canza musu lokacin aiki zuwa rana.

Daga cikin dalilan da ke haddasa bacci akwai yanayin mahalli, kamar yadda bayani ya gabata.  Da zarar yamma ya gabato, akan samu sauyin yanayin dabi'ar jiki (Biological Clock), wanda hakan ke haddasa samuwar sinadarin Melatonin, nan take sai jiki ya fara canza yanayinsa, daga farkawa zuwa kasalar da ke kai mutum ga bacci.  Daga cikin abin da ke canza yanayin zuban wannan sinadari dai akwai yawan zama cikin duhu a kullum, da yawan zama cikin haske a lokacin dare; duk suna canza yanayin zubansa. 

Rashin Bacci

Rashin bacci matsala ne mai girman gaske ga dan adam.  Domin yana rage kaifin fahimta.  Sannan dan adam kan shiga wani yanayi na rashin daidaituwar kwakwalwa da fahimtar abubuwa.  Rashin bacci kan taimaka wajen yawan zuban sinadaran insulin a jikin dan adam, wanda hakan ke taimakawa wajen haddasa yawan kiba a jiki  Rashin bacci na haddasa yawan mantuwa, domin kwakwalwa kan samu kanta ne cikin halin rudu.  Bincike ya nuna cewa rashin bacci na tsawon awanni 17 na iya haddasa nakasar darajar fahimta a kwakwalwar dan adam da kashi 0.05%, iya gwargwadon abin da zai iya sa mutum ya shiga halin maye idan ya sha barasa cikin moda biyu.  Rashin bacci na haddasa hauhawan jini ga dan adam, da kuma yawan kiba, kamar yadda bayani ya gabata.

Wednesday, February 13, 2013

Binciken Malaman Kimiyya kan Yadda Bacci da Mafarki ke Samuwa (2)Binciken Kimiyya a Karni na 20 (20th Century)

Har zuwa karshen karni na 19 malaman kimiyya sun hadu kan cewa a lokacin da dan adam ke bacci, da gangar jikinsa da kwakwalwarsa duk ba su aiki; a sake suke.  Wannan tunani da fahimta ta shahara sosai.  Abin da ya bambanta tsakanin masu bincike dai shi ne, me ke haddasa bacci?  Ko wani bangaren jikin dan adam ne ke da alhakin sa shi bacci?  Wanda kuma har aka shigo karni na 20 babu wani sakamako mai gamsarwa.
A farkon karni na 20 ne aka samu karuwar sanayya da budi wajen bincike, sanadiyyar bunkasar ci gaba a fannin kere-kere, inda aka samu na'urorin gudanar da binciken kimiyya da kiwon lafiya a duniya. A cikin kasidarsa na musamman cikin shekarar 1922, Curt Richter ya bayyana sakamakon binciken da ya gudanar kan wasu dabbobi da kuma shuke-shuke, inda ya kara tabbatar da cewa lallai muhalli na da tasiri na musamman wajen sabbaba bacci ga dabbobi da shuke-shuke. 

A shekarar 1929 kuma bincike ya tabbatar da cewa lallai kwakwalwar dan adam a farke take a sadda yake bacci, sabanin yadda bincikensu ya nuna musu a karnin baya.  Wannan na daga cikin sakamakon binciken da suka shahara matuka, musamman ganin yadda a karnin baya dukkan masana suka hadu kan cewa a sadda dan adam yake bacci, kwakwalwarsa a tsaye take cak; ba ta aiki.  Wannan na cikin sakamakon binciken masanin kimiyya Johannes Berger, inda yake bincike kan bambancin da ke tsakanin yanayin bacci da yanayin farke a rayuwar dan adam.  Sanadiyyar wannan bincike ne aka kirkiri na'urar nazarin kwakwalwa mai suna Electroencephalograph (EEG) a shekarar 1929 din dai.  Daga nan kuma wasu masana suka yi amfani da wannan na'ura wajen gudanar da bincike kan dan adam mai bacci, na tsawon wasu lokuta.  Wadannan masana dai su ne: Alfred Loomis, da Newton Harvey, da kuma Garret Hobart, wanda sanadiyyar binciken ne aka gano matakan bacci da dan adam ke bin cikinsu, a sadda yake bacci.  Sun gano matakai guda biyar ko nau'ukan bacci guda biyar, kamar yadda bayanai za su biyo baya nan ba da dadewa ba.

Bayan wannan hobbasa da aka yi, inda masana kimiyya da binciken dabi'ar dan adam suka fara ganin haske cikin sakamakon bincikensu, a shekarar 1936, masani Erwing Bunning ya sake gudanar da bincike kan dalilan da ke jefa dan adam wannan yanayi dai.  A sakamakon bincikensa ne ya gano cewa akwai wani agogo na dabi'a, wato Biological Clock ko kuma Internal Clock, da jikin dan adam ke amfani da shi wajen gano lokutan da suka kamace shi zuwa bacci.  Bayan wannan bincike sai ga wani masani mai suna Parlor.  Shi kuma ya gudanar da nashi bincike ne kan wasu karnuka, inda ya gano cewa lallai har yanzu dai kwakwalwa kan daina aiki a sadda dan adam ke bacci, sanadiyyar wasu sinadaran lantarki dake shigowa daga babbar kafar sadarwar jikin dan adam, wato Central Nervous System.  To amma da tafiya tayi nisa sakamakon wannan bincike nashi bai samu karbuwa ba, domin babu bayanai na sheda dake nuna haka a rubuce, ko a kimiyyance.

Ana cikin haka kuma sai ga wani sabon yanayi, wanda a cikinsa masana kimiyya suka mayar da hankulansu gaba daya kan kwakwalwa, wajen neman dalilin da ke jefa dan adam shiga bacci.  Basu daddara ba dai.  Wadannan masana dai sun hada da: Von Economo, da Nathaniel Kleitman, da Horace Mogoon, da kuma Ruth Rhines, inda suka gano cewa akwai alaka ta kut-da-kut tsakanin bacci a bangare daya, da kuma gajiya da fahimta (raguwa ko kari ko kyautatuwarsa) a daya bangaren.  Bayan su, a cikin binciken su Gustav Kramer, da Klans Hoffman, da kuma Colin Pittendrigh, sun tabbatar da cewa lallai akwai wata cibiya ta musamman da ke lura da halin da dan adam ke shiga a lokacin bacci.  A shekarar 1960 ne dai masana kimiyya gaba dayansu suka amince da wannan fahimta da bincike ya tabbatar da ita, cewa lallai akwai wata cibiya ta musamman da ke jefa dan adam cikin halin bacci, da zarar lokaci ko abin da ke haddasa shi ya yi.  Wannan cibiya kuwa, kamar yadda bayanai suka zo a baya, suna kiranta da suna: Biological Clock, ko Internal Clock ko kuma Circadian Rhythm.  Da wadannan ci gaba aka fita daga karni na 20 zuwa karni na 21.  Amma duk da haka, bayani kan hakikanin bacci da yadda yake samuwa dai, ba a kai gare su ba.

Binciken Kimiyya a Karni na 21 (21st Century)

Kafin karni na 21, masana sun mayar da hankulansu ne wajen yanayin mai bacci, da tsarin mafarki, da karin bincike kan nau'ukan bacci da dai sauransu.  Daga cikin sakamakon da suka samo, akwai bayanai kan: matakan bacci (Sleep Stages), da agogon dabi'a (Biological clock), da amfanin bacci, da cutarwar rashin bacci, da tasirin cin bashin bacci (Sleep Debt), da tasirin mahalli kan bacci, da kuma bayanai kan me ke haddasa bacci?  Bayan dukkan wadannan bayanai, za mu dubi mahangar addinin Musulunci kan bacci, da dukkan abubuwan da suka dandgance shi, a takaice.

Matakan Bacci

Sabanin yadda tunaninmu yake, ba da zarar mutum ya kwanta yake shiga bacci mai nauyi ba, sannan idan lokacin farkawa yayi, ba wai a hankali kawai baccin zai fara saukaka, sannan ya farka ba.  Wannan tunaninmu kenan na al'ada. Abin da ya tabbatar da kuskuren wannan fahimta tamu kuwa shi ne binciken malaman kimiyya kan yadda dan adam ke bacci.  Duk da cewa bacci wani yanayi ne, wanda ba wanda ya isa ya sanar da duniya halin da mai bacci yake ciki face shi.  In kuwa haka ne, to ta yaya masana kimiyya suka gano irin matakan da mai bacci ke bi ta cikinsu a sadda yake bacci?

Sun gano hakan ne ta hanyar bincike ta amfani da na'urorin kimiyya irin na zamani, kamar Electroencephalograph (EEG) da bayaninsa ya gabata.  Wannan ne kashin bayan sakamakon galibin binciken da ake ta yi kan bacci, musamman dangane da alakar dabi'a da gangar jikin dan adam a sadda yake bacci.  Abin da wannan na'ura take yi shi ne yin gejin jujjuyawa da kai-komon abubuwan da ke cikin kwakwalwa wajen karuwa ko raguwa, a sadda mai bacci yake bacci.  Malaman kimiyya sun zana alamomi nau'uka daban-daban, da irin abin da wadannan alamomi ke ishara zuwa gare su, wanda na'urar ke nunawa a sadda take daukan hoton kwakwalwar mai bacci.  Ta sanadiyyar gudanar da bincike da wannan na'ura ne aka gano nau'uka ko yanayin bacci guda biyu da kowane dan adam ke shiga cikinsu.

Bacci Mai Nauyi

Nau'in farko shi ne bacci mai nauyi, wanda malaman kimiyya suka kira da suna: Deep Sleep, ko kuma Non-Rapid Eye Movement (NREM) Sleep.  Sun kira wannan nau'in bacci da Non-Rapid Eye Movement ne saboda idanun mai bacci, bayan kasancewarsu a rufe sadda yake bacci, kwayar idanunsa a tsaye suke cik, ba su motsi.  Wannan shi ne nau'in bacci na farko, wanda ke dauke da yanayin bacci mai nauyi, wato Deep Sleep.  Wannan nau'in bacci yana da matakai guda hudu.

Matakan Bacci Mai Nauyi

Matakin bacci mai nauyi na farko shi ne gyangyadi.  Shi gyangyadi wani yanayin bacci ne da ke tsakanin hakikanin bacci da farkawa. A halin gyangyadi, mai bacci na iya fahimtar mahallin da yake, tare da jin sautin da mutane ke fada, amma sama-sama.  Idan mutum na halin gyangyadi, jijiyoyin gabobin jikinsa kan fara sakewa, don karbar sabuwar yanayin da ke tafe.  Wannan shi ne matakin da masana kimiyya ke kira Light Sleep.  Da zarar an farkar da mutum daga wannan yanayi, yana ma iya cewa ba bacci yake yi ba.  Domin shi ne matakin da yafi kusa da yanayin farke.  Mai bacci kan kashe kamar minti 10 a wannan yanayi, daga nan kuma sai ya shiga mataki na biyu.

Mataki na biyu shi ne matakin baccin da numfashin mai bacci ke fara yin kasa, haka ma bugawar zuciyarsa.  Duk a wannan mataki suke fara yin kasa, suna lafawa.  Daga nan kuma sai yanayin zafi ko dumin jikinsa shi ma ya fara sauka.  Wannan shi ne matakin baccin da masana ke kira da suna True Sleep.  Wato bacci na hakika kenan.  Duk wanda ke yanayi irin wannan, da zarar ka ganshi ka san hakika bacci yake yi.  Idan ya kashe kamar minti 20 a wannan yanayi yana bacci, sai ya shiga mataki na uku.

Wannan mataki shi ne matakin da yanayin aikin kwakwalwarsa ke fara sauyawa.  Yanayin bugun kwakwalwarsa kan yi sama, sannan ya riga gangara kasa, a hankali.  Wannan tsarin bugawa shi ake kira Delta Waves, kuma shi yasa ma wasu masana kan kira wannan mataki da suna Delta Sleep.  A wannan yanayi ne bugun zuciyarsa da yanayin numfashinsa gaba daya suke yin kasa sosai.  Idan ba a kusa da shi kake ba, ba ka jin komai.  Wannan, kamar yadda malamai suka ce, shi ne zangon da ke tsakanin bacci na hakika da bacci mai zurfi ko nauyi.  Kuma shi ne galibin nau'in baccin mutane.  Mai bacci kan kashe minti 30 a wannan mataki kafin zuwa matakin gaba.

Mataki na karshe, wanda shi ne mataki na hudu, shi ne bacci mai nauyi; ma'ana hakikanin zangonsa kenan.  Wannan shi ne yanayin da tsarin numfashin mai bacci ke yin sama da kasa, kuma jijiyoyin gabobin jikinsa kan kara sakewa.  A wannan yanayi ne galibin kananan yara ke yin fitsarin kwance.  Idan aka farkar da mutum a wannan yanayi, yakan dauki 'yan mintuna yana cikin magagi bai wartsake ba.  Wadannan su ne matakan bacci mai nauyi guda hudu, wadanda a cikinsu ne kwakwalwar mai bacci kan shiga halin natsuwa, da kintsi, sannan bugun zuciyarsa yayi kasa da yadda ya saba bugawa a lokacin farke.  Da zarar mai bacci ya zarce na tsawon mintuna 25 zuwa 30, sai ya shiga nau'in bacci na biyu, wanda malaman kimiyyar dabi'ar dan adam ke kira Rapid Eye Movement (REM) Sleep.

Madaidaicin Bacci

Wannan shi ne nau'in bacci na biyu.  Na kira shi da suna "Madaidaicin Bacci" ne don bambance shi da "Bacci mara nauyi," wato matakin bacci na daya da na biyu a karkashin nau'in bacci mai nauyi.  Wannan nau'in bacci na dauke da mataki daya ne kacal.  Kuma shi ne matakin da mai bacci ke afkawa cikinsa, mintuna 70 zuwa 90 da fara baccinsa.  Idan mai karatu na tare da ni, na sanar da shi cewa matakin farko a bacci mai nauyi kan dauki mintuna 10 ne. Mataki na biyu kuma kan dauki mintuna 20.  Mataki na uku kuma kan dauki mintuna 30.  Sai kuma mataki na hudu, wanda ke daukan mintuna 25 zuwa 30.  Idan aka tara wadannan mintuna, za a samu 85 zuwa 90.  Da zarar mai bacci ya kai tsawon wannan lokaci, sai ya shiga yanayin bacci madaidaici.

A cikin wannan yanayi, kwayan idon mai bacci kan jujjuya, su rika motsawa daga nan zuwa can.  Wannan shi ake kira Rapid Eye Movement (REM).  Kuma shi ne abin da masu bincike suka hango tun cikin karni na 20, ta hanyar wancan na'ura mai suna Electroencephalograph (EEG).  A cikin wannan yanayi ne kwakwalwarsa ke zama kar, ta ci gaba da aiki sama da yanayin farko.  A cikin wannan yanayi ne jijiyoyin gabobin jikinsa ke sandarewa gaba daya, ya kasa motsi.  A cikin wannan yanayi ne har wa yau, mai bacci ke yin mafarke-mafarke nau'uka daban-daban. An kuma gano hakan ne ta hanyar tambayar masu baccin da aka sa a karkashin wannan na'ura ana lura da su a halin baccinsu.  Duk wanda yace ya yi mafarki, da zarar an duba sai a ga a sadda kwayan idanunsa ke jujjuyawa ne a halin baccinsa. 

Masana sun kasa tantance dalilin da ke sa kwakwalwar dan adam zama a farke sosai, da yin aiki sama da yadda take yi a farko, da jujjuyawan kwayan idanunsa, da kuma yin mafarki.  Har yanzu babu wanda ya dace da wani amsa karbabbe ga kowa.  Sai dai hasashe.  Wasu sukan ce kwakwalwa kan kama aiki ne sosai a lokacin saboda taimaka wa sauraron gabobin jikin dan adam samun kuzari idan ya farka.  Wasu suka ce dan adam kan yi mafarki ne saboda kwakwalwarsa na tattauna al'amuran da suka faru ne a rayuwarsa sadda yake farke lokacin yini. Yana daga cikin dalilan da ke sa kwayan idanunsa ke jujjuyawa sadda yake bacci, don hangar abubuwa a cikin mafarkinsa.  Wasu kuma suka ce a a, kwayan idanun na jujjuyawa ne don gyatta mahallin zamansu, da kuma kara giris a wuraren da ba su samun giris sadda mai jikin yake farke.  Har yanzu dai lalube ne ake yi a cikin gaibu.   Kuma ya zuwa wannan lokaci da nake rubutu, bincike na ci gaba da gudanuwa don kokarin gano dalilan da ke haddasa wadannan al'amura.

Binciken Malaman Kimiyya kan Yadda Bacci da Mafarki ke Samuwa (1)
Gabatarwa
 
Idan akwai wani yanayin dabi'ar aiki da jikin dan adam ke yawan maimaita shi a dukkan lokuta da sa'o'in rayuwarmu, mai ban mamaki da al'ajabi, wanda kuma bamu cika damuwa da sanin hakikanin yadda yake ba, to, shi ne bacci da yadda mafarki ke aukuwa a yayin da dan adam ke halin yinsa a kan gado ko tabarmarsa.  Bacci wani yanayi ne mai ban al'ajabi; baka isa ka jawo shi yazo da karfi ba.  Idan kuwa har yazo ta sanadiyyar tilasta masa da kayi, to, a karshe za ka ji jiki.  Haka idan ya bijiro maka saboda lokacin yinsa yayi, amma ka ki amincewa ku tafi tare, to, nan ma za  ka ji jiki bayan wasu lokuta.  Shi ne dabi'a guda, wanda idan kayi shi a lokacinsa, za ka samu karin kuzari da gyaruwar fahimta, da kuma karin lafiya.  Shi ne dabi'a guda, wanda ke raba ka da wannan duniya ta gwagwarmaya, zuwa wata duniya mai kama da kawalwalniya, amma kuma a galibin lokuta hakika ce.  Shi ne dabi'ar jiki guda daya, wanda duk mulkinka, duk kudinka, duk ikonka, duk talaucinka, duk koshinka, duk yunwarka, duk malantarka, duk fushinka, duk farin cikinka, duk shagulgulanka, sai ka yi shi idan ya bijiro -  a tsaye ne, a jingine da bango ne, a kwance ne, ko kana tafiya ne.  Bacci, kamar yadda muka sanshi, wani tilasci ne na dabi'ar halittar dan adam da wasu cikin dabbobi; idan lokacinsa yayi, dole sai an dukufa.

To amma, me ke haddasa bacci ne?  Ta yaya jikin dan adam ke fahimtar lokacin da ya kamata yayi bacci?  Wani bangaren jikin dan adam ne ke da alhakin wannan aiki?  Shin, wai bacci ma nau'i nawa ne tukun?  Kuma meye bambancin da ke tsakanin nau'ukan baccin dan adam da wasu halittu?  Iya yawan kwanaki nawa ne dan adam zai iya jure wa kin bacci bayan alamun baccin sun bayayya a tare da shi?  Kuma meye sakamakon cin bashin bacci (Sleep Debt) ga lafiyar jikin dan adam?  A daya bangaren kuma, idan dan adam ya lazimci bacci a iya lokutan da suka kamata, wani alfanu zai samu wajen karin ingancin lafiyarsa?  Shin, tun yaushe malaman kimiyya suka fara bincike a kimiyyance kan yadda bacci yake?  Me suka gano?  Meye har yanzu ya bace musu wajen bincikensu?  Ta wani bangare Al-Kur'ani ya tallafa wa malaman kimiyya wajen hutar dasu ko kara musu kuzari don fadada bincike idan basu yarda ba?  Yaya mafarki yake? Shi ma me ke haddasa shi ne?  An gano hakan a  kimiyyance kuwa?  In eh, me aka gano? In a a, me ya gagari masu binciken ne? Mafarki nau'i nawa ne?  Me ya bambanta su?  Meye tallafin ilimin addinin musulunci wajen fahimtar hakikani da yanayi da kuma nau'ukan mafarki?  Sannan, a karshe mu ji tasirin mafarki a rayuwar dan adam a mahangar addinin musulunci.

Wannan kasida za ta tsawaita iya gwargwado, sannan za ta kunshi sakamakon binciken malaman kimiyya na karni na 19 zuwa 21 (19th to 21st Century), da irin kokarin da suka yi wajen neman gano hakikanin yadda bacci da mafarki ke samuwa a rayuwar dan adam.  Wannan bayani zai zo ne a mahangar tarihi ko a sigar tarihi.  Sannan za mu ta cin karo da zantukan manyan malaman musulunci da na kimiyya, da kuma nassoshin Kur'ani da hadisai ingantattu da suka shafi wannan maudu'i. Dalilin da yasa nake yawan yin wannan shi ne don mu rika fahimtar cewa duk abin da Kur'ani ya tabbatar da shi a kimiyyance, to  haka yake.  Idan malaman kimiyya sun gano haka, fa ni'ima, idan sun kasa ganowa, wannan ba ya nuna cewa abin ba haka yake ba; tsawon lokaci zai kaisu gare shi.  Idan kuma Kur'ani ya kore samuwar wani abu, to, ko an ce akwai shi, a karshe za ka ga ba hakikanin abin bane, wani abu ne daban.  Abin da wannan dogon zance ke nuna mana shi ne, in dai kimiyya ya kama hanyar daidai, babu yadda za a yi ya saba wa Kur'ani, sam ko kadan.  Sannan kuskure ne musulmi yaji wani sakamakon binciken kimiyya, mai ban al'ajabi, haka kawai ba tare da ya san ilmin Kur'ani da Shari'a ba, ya karyata samuwarsa don kawai kwakwalwarsa na inkarin yiwuwar abin a dabi'ance.    

Malam Bacci, Yaya Kake?

Bacci wani yanayi ne na dabi'ar jiki, wanda ke da cikakkiyar alaka da ruhin dan adam a lokacin samuwarsa.  Idan mutum ya shiga halin bacci, dukkan gabobin jikinsa da sauran hanyoyin sadarwa na gani, da zance, da shaka, duk suna kullewa; su daina aiki, face hanyar sadarwa guda daya.  Nan gaba mai karatu zai san dalili kan haka. A sadda dan adam ke halin bacci, yana numfashi, amma kuma babu hakikanin zatinsa.  Rashin samuwar hakikanin zatin adan adam a halin bacci ne ke sa ya rasa wadancan hanyoyin sadarwa na jikinsa face guda daya.  A takaice ma iya cewa lallai bacci wani yanayin dabi'ar jiki ne da ke tsakanin yanayin suma, da yanayin farke.  Ma'ana, wanda ke bacci ba a farke yake ba, domin ba shi da cikakkiyar tsarin hankaltar yanayin da yake ciki, sannan kuma ba a sume yake ba, domin yana numfashi ana ji.  Wannan wani al'amari ne mai matukar ban mamaki da al'ajabi. 

Duk da cewa zai yi wahala ace tun halittar duniya babu wanda ya taba bincike kan wannan yanayi na dabi'ar jiki, amma abin da tarihi ya taskance mana a yau shi ne kokarin da malaman falsafa, da malaman kimiyyar zamani suka yi tun cikin karni na 19.  Wannan kokari ya haifar da bunkasar bincike kan hakikanin yadda bacci ke samuwa a mahangar kimiyya ta amfani da tsarin binciken kimiyya na zamani, da kuma nassoshin Kur'ani kan yadda wannan lamari ke samuwa.  A halin yanzu ba wai a Jami'o'in kasashen yamma kadai ba, hatta a wasu jami'o'in kasashen musulunci a yau, akwai Cibiyar Bincike na musamman kan bacci (Sleep Research Center), a bangaren Fannin Ilmin Dabi'a (Psychology).   Wannan shi ne babban dalilin da ke nuna mana cewa lallai bacci, hatta a mahangar binciken ilmi na zamani, an yarda cewa wani abu ne da ke da alaka ta kut-da-kut da ruhin dan adam.  Amma ta yaya abin ya faro?

Binciken Kimiyya a Karni na 19 (19th Century)

Karni na 19 shi ne tsawon shekaru dari da suka faro daga shekarar 1800 zuwa 1900.  A wannan lokaci ko karni an samu nau'ukan bincike na ilmi da wasu malamai na kimiyya suka gudanar kan bacci da abubuwan da suka shafe shi.  A cikin wannan karni, abin da suka fi damuwa da shi kuwa shi ne: meye hakikanin abin da ke haddasa bacci a jikin dan adam?  Wasu daga cikin masana suka ce ai cikowar jini ne a kwakwalwar dan adam ke haddasa bacci.  Wasu kuma a sakamakon bincikensu suka ce a a, karfin bugawar jini ne a kwakwalwa.  A nasu bangaren, wasu kuma suka ce rashin samuwar jinin ne ma ke jawo wa dan adam bacci.  Ma'ana da zarar jini ya janye daga kwakwalwa nan take sai bacci ya kama mutum.  To amma wadannan sakamakon bincike basu dore ba, kamar yadda mai karatu zai gani nan gaba.

Da shekaru suka karu sai wani sakamako ya sake fitowa mai nuna cewa dan adam na shiga halin bacci ne sanadiyyar wata iska da ke samuwa a kwakwalwarsa. Ko gundarin kitse (Cholesterol) da ke haifuwa a kwakwalwar dan adam.  Ko kuma sanadiyyar wata sarrafaffiyar iska (Carbon dioxide) da ke taruwa a kwakwalwar dan adam a lokacin yini, wajen kujuba-kujubarsa na rayuwar yau da kullum.  Suka ce idan wannan kitse ta taru, sai bacci ya rinjayeshi, nan take sai ya kama bacci.  Da zarar ya shiga halin bacci, a hankali wannan kitse tana narkewa, har sai an rasa ta, daga nan sai ya farka.  Babban magana!  Wannan sakamakon bincike shi ma bai dore ba.  Sai wani sabon sakamako ya bayyana, wanda ke nuna cewa wayoyin sinadarar lantarkin sadarwar jikin dan adam (wato: Nervous System) ke haddasa bacci, sanadiyyar sandarewarsu a lokacin da dan adam ke bacci.

Ana cikin haka sai wasu masu bincike suka ce sun gano bakin zaren.  A sakamakon bincikensu sun nuna cewa lallai ba kwakwalwa bane ke da alhaki dari bisa dari, akwai wani yanayi ne a jikin dan adam wanda ke haddasa masa bacci.  Wannan yanayi malaman sun kira da suna Inhibitory Reflex, ma'ana wani yanayi da ke samar da kansa, a wani lokaci na musamman.  Da tafiya tayi nisa sai masu wannan fahimta suka fadada bincike, inda suka sake gano cewa wannan yanayi na kai-komo ne tsakanin bacci da farkawa.  Ma'ana, idan lokacin bacci yazo, sai yanayin farkawa ya gudu.  Idan lokacin farkawa yayi, sai yanayin bacci ya gudu, don samar da yanayin farkawa.  Wannan canji na yanayi, a cewarsu, yana samuwa ne a kwakwalwa.  Amma bayan wasu 'yan shekaru sai aka karyata wannan tsarin tunani da bincike, shi ma.  Hakan kuwa ya faru ne daidai lokacin da aka gano matsayin Sandar jijiyar kwakwalwa (Brain Stem) wajen haddasa bacci da farkawa, ba wai a cikin kwakwalwar ba.  A shekarar 1836 kuma sai ga Charles Dickens da nashi sakamakon bincike, inda ya gano cewa lallai gwarti ko minshari a lokacin bacci, na daga cikin matsalolin da wasu ke samu  a bangaren lafiya.  Ma'ana, yin minshari ba wai dabi'a ce ta musamman ga mai bacci ba, rashin lafiya ce ta musamman wacce ke bayyana kanta a lokacin baccin.

Haka dai lamarin ya ci gaba, malaman basu yi kasa a gwiwa ba.  Tsakanin shekarun 1845 – 1866 sai aka gano tasirin mahalli wajen haddasa bacci.  Masu wannan tsarin fahimta suka ce lallai akwai alaka mai karfi tsakanin yanayin mahalli (hasken yini da duhun dare) wajen haddasa bacci ga dan adam, da dabbobi, kai hatta shuke-shuke.  Wannan sakamakon bincike shi ya samar da wani fanni na musamman kan ilmin bacci mai suna Chronobiology.  Ana kara shekaru biyu gaba (wato a shekarar 1868), sai wasu daga cikin malaman Daular Girka suka kunno kai da nasu sakamakon binciken.  Wadannan galibinsu malaman falsafa ne (Philosophers).  Wanda yayi hobbasa na farko shi ne Williams Griensinger, wanda ya gano yadda kwayar idon dan adam ke jujjuyawa a lokacin da yake bacci, duk da cewa fatar idon a rufe take.  Wannan yanayin bacci shi ake kira Rapid Eye Movement, ko REM a gajarce.  Wannan sakamakon bincike kam ya tabbata gaskiya ne, bayan samuwar na'urorin binciken kimiyya na zamani, musamman Electroencephalogram (EEG).  Daga nan kuma sai binciken shahararren malamin fannin Falsafa mai suna Sigmund Freud, wanda ya rubuta littafi na musamman kan fassarar mafarki mai suna Dream Interpretation.  A bangaren bacci, Freud ya gano cewa lallai jijiyoyin jikin dan adam kan sandare ya kasa motsi. Wannan yanayi shi ake kira Muscle Paralysis. 

Har zuwa karshen karni na 19, malaman kimiyya da ilmin dabi'a sun kasa fahimtar tsarin da mai bacci yake ciki, da abin da ke haddasa shi bacci, a hakika.  A yayin da kowannensu ya saba wa dan uwansa wajen sakamakon bincikensa, a daya bangaren kuma, duk sun dace a kan cewa a yayin da mutum ke bacci, kwakwalwarsa tana daina aiki ne gaba daba daya.  Kuskuren da ke cikin wannan zance da fahimta nasu bai bayyana a fili ba sai da duniya ta shiga karni na 20.