Mabudin Kunnuwa
"Duk sadda na ga Bin Laden rike da AK-47 sai in ji tsarguwa ta kama ni. To amma yaya na iya? Su kansu Mujahidai ai ba wawaye bane; su kansu suna neman bindigar da tafi inganci ne." - Janaral Mikhail Kalashnikov
Daga cikin nau'ukan bindigogin zaman jiya har zuwa yau, ba a samu nau'in da ta shahara matuka, aka santa ko ina a duniya ba, ake amfani da ita ta kowace hanya da dalili ba, kuma sojoji, da 'yan sanda, da masu gwagwarmayar neman 'yanci ke amfani da ita dare da rana safe da yamma ba irin nau'in bindigar AK-47. Da jin sunan wannan bindiga na tabbata galibin masu karatu sun san ta, ko da kuwa basu taba ganinta ba. Idan ka taba ganin wannan dingida, da jin sunan na san take kwakwalwarka ta hararo maka ita. Ga wadanda basu taba ganinta ba, su yi hakuri, ya kamata a ce na sa hotonta don su gani. Sai dai kuma kaico, ba akanta bayanin wannan mako yake ba, sai dai makaginta, makerinta, masaninta, kuma mahaliccinta: Janar Mikhail Timovetevich Kalashnikov.
Haihuwa da Nasaba
Shi ne Mikhail, dan Timoveyevich, dan Kalashnikov, an haife shi ne a ranar 10 ga watan Nuwamba, shekarar 1919, a garin Kurya da ke Lardin Altai Krai na kasar Rasha na yanzu. Bayan gama karatunsa na matakin farko, ya shagaltar da kansa da rubutun wake (Poem), kuma a karshe ya rubuta littattafai har guda 6. A shekarar 1938 ya shiga aikin Soji, inda hukumar tsaron kasar Hadaddiyar Daular Sobiyet na wancan lokaci mai suna Red Army ta dauke shi aiki a matsayin Kwamandan tankokin yaki, watau Tank Commander.
Lokacin da yake soji ya halarci yake-yake da dama. Ya shugabanci tankokin yaki a lokacin yakin Brodi (Battle of Brody) a watan Yuni na shekarar 1941, inda a karshe da zafi yayi zafi ya janye rundunarsa. A yakin Bryansk (Battle of Bryansk) da aka yi cikin watan Oktoba na shekarar 1941 ya samu rauni mai muni. A karshe dai aka bashi hutun jinya na tsawon watanni 6. Yana kwance a gadon asibiti yana jinya ne sai yaji wasu daga cikin sojoji 'yan uwansa suna korafi kan irin makaman da hukumar sojin kasar ke basu a lokacin yaki. Cewa ba su gamsar da su, kuma suna shan wahala wajen aiki da su sanadiyyar rashin saukin mu'amala.
Fasahar Kere-keren Makamai
Kafin wannan lokaci, tuni ya halarci kwasa-kwasai masu dama kan yadda ake mu'amala da bindigogi da yadda ake sarrafa su. da yaji irin korafin da wadancan sojoji ke yi, sai ya fara tunanin yadda zai taimaka wajen samar da bindiga mai saukin mu'amala, mai gamsarwa, mai dadin sha'ani. Yana samun sauki, sai nan take ya fara kera wata nau'in bindiga mai sarrafa kanta, wacce ake iya rikewa a hannu ko a dora a kafada, watau Submachine Gun. Bayan ya gama kera wannan bindiga, sai ya gabatar da ita ga hukumar sojin Daular Sobiyet na wancan lokaci, to amma sai aka yi rashin sa'a suka ki amincewa da ita a matsayin makamin yaki. Duk da haka, wannan ya baiwa hukumar damar fahimtar irin kaifin basira da fasahar da Allah ya baiwa Kalashnikov. Daga cikin basirar da Allah ya bashi akwai lura da dabi'ar sauki wajen kera duk makamin da yake kerawa.
Don haka, a shekarar 1947 sai Kalashnikov ya fitar da shahararriyar bindigarsa da ya sanya wa suna "Automat Kalashnikova Model 1947" ko AK-47, kamar yadda aka santa a halin yanzu. Bayan ya gabatar wa hukuma wannan sabuwar bindiga da ya kera, sai tayi nazari kanta. Bai samu amincewar hukuma ba sai shekarar 1956, watau bayan shekaru tara kenan. Daga nan ne hukumar sojin kasar ta amince cewa lallai wannan nau'in bindiga ta AK-47 amintacciya ce abin amincewa wajen tsaro. Ba ma wannan kadai ba, hukumar ta danganta wannan bindiga da kasar Rasha baki daya.
Bayyanar wannan bindiga a kasar Rasha ya bata shahara a sauran kasashen duniya, inda aka wayi gari kusan duk wata kasa da ke duniya a yanzu ba a rasa sojojinta da wannan nau'in bindiga ta AK-47. Bindiga ce amintacciya. Daga shekarar da Kalashnikov ya kera wannan bindiga zuwa yau, an samu zubin AK-47 masu dinbin yawa. Kusan kasashe da dama sun caccanza mata tsari, da kintsi, da yanayin sarrafawa, da dai sauransu. A wasu kasashen ma an canza mata suna, da lamba da dai sauransu. A takaice dai, akwai nau'ukan bindigar AK-47 sama da guda goma, wadanda aka canza musu tsari ta wajen ingantawa, da kayatarwa, a shekaru daban-daban.
Kalashnikov dai kwararre ne kan ilmin kimiyyar kere-kere, inda ya samu digiri na biyu a kan haka, watau Advance Degree in Technical Sciences. A halin yanzu yana raye, akwai kuma dalibansa biyu 'yan kasar Jamus da ya karantar dasu ilmin kera makamai, kuma sun shahara sosai a kasar Jamus, inda kowannensu ya kera bindigogin da suka shahara su ma. A hirar da kamfanin dillacin labaru na Reuters ya yi da shi a shekarar 2009, lokacin bikin karramawa da kasar Rasha ta shirya masa, ya ce:
"Duk da cewa akwai nau'in bindigar AK-47 sama da miliyan dari a duniya a yau, amma babu ko sisi da nake samu wajen yaduwarsu a matsayina na wanda ya kera su; in ka kebe dan fansho da nake karba daga hukuma, da kuma ladar hakkin mallaka da wasu kamfanonin sayar da kayayyakin abinci suke bani, don amfani da sunan bindigar da suka yi a kan hajojinsu."
Babbar falsafarsa dai wajen kere-kere ita ce yin la'akari da dabi'ar sauki. Ya ce duk abin da aka ce yana da saukin sha'ani ko mu'amala, to za a yi amfani da shi sosai, kuma zai fa'idantar, fiye da abin da yake da wahalar sha'ani ko sarrafawa. Ga abin da yake cewa:
"Duk abin da yake da wahalar sarrafa, ba shi da wani amfani. Kuma duk wani abu mai amfani ga jama'a, to za ka samu yana da saukin sarrafawa."
Darasi
Babban darasin da za mu koya daga rayuwar wannan bawan Allah shi ne, a kullum mu zama masu la'akari da abin da zai zama gyara da sauki ga dukkan al'ummar da muke rayuwa a cikinta. Wannan shi zai sa kwakwalwarmu ta rika kawo wuta, har mu samu kwazon da basirar ciyar da al'umma gaba ta hanyar da ta sawwake gare mu.
………………………………………………………
Fadakarwa
"Assalaamu Alaikum, Baban Sadik don Allah ina son in ja hankalinka. Idan masu tambaya suka rubuto maka tambaya, tare da yi maka sallama, maimakon ka amsa sallamar, sau da yawa sai kace "Barka da warhaka…" Da fatan za a gyara don kwadayin samun lada." Daga CPL Mamman B. Abdul Dambatta, Police College, Kaduna.
Wa alaikumus salaam, hakika na yi farin ciki da wannan fadakarwa naka. Allah saka da alheri, ya kuma ba damar kara tunatar da ni a duk sa'adda aka hararo wani kuskure da na tafka ko nake tafkawa. Kamar yadda na sha sanarwa, ni dan Adam ne, ina gafala kamar yadda kowa ke rafkana. Hakika Allah ya bani ikon gyarawa daga yanzu. Allah mana jagora, amin.