Monday, December 19, 2011

Janaral Mikhail Timoveyevich Kalashnikov (1919 – )

Mabudin Kunnuwa

"Duk sadda na ga Bin Laden rike da AK-47 sai in ji tsarguwa ta kama ni. To amma yaya na iya? Su kansu Mujahidai ai ba wawaye bane; su kansu suna neman bindigar da tafi inganci ne." - Janaral Mikhail Kalashnikov

Daga cikin nau'ukclip_image002an bindigogin zaman jiya har zuwa yau, ba a samu nau'in da ta shahara matuka, aka santa ko ina a duniya ba, ake amfani da ita ta kowace hanya da dalili ba, kuma sojoji, da 'yan sanda, da masu gwagwarmayar neman 'yanci ke amfani da ita dare da rana safe da yamma ba irin nau'in bindigar AK-47. Da jin sunan wannan bindiga na tabbata galibin masu karatu sun san ta, ko da kuwa basu taba ganinta ba. Idan ka taba ganin wannan dingida, da jin sunan na san take kwakwalwarka ta hararo maka ita. Ga wadanda basu taba ganinta ba, su yi hakuri, ya kamata a ce na sa hotonta don su gani. Sai dai kuma kaico, ba akanta bayanin wannan mako yake ba, sai dai makaginta, makerinta, masaninta, kuma mahaliccinta: Janar Mikhail Timovetevich Kalashnikov.

Haihuwa da Nasaba

Shi ne Mikhail, dan Timoveyevich, dan Kalashnikov, an haife shi ne a ranar 10 ga watan Nuwamba, shekarar 1919, a garin Kurya da ke Lardin Altai Krai na kasar Rasha na yanzu. Bayan gama karatunsa na matakin farko, ya shagaltar da kansa da rubutun wake (Poem), kuma a karshe ya rubuta littattafai har guda 6. A shekarar 1938 ya shiga aikin Soji, inda hukumar tsaron kasar Hadaddiyar Daular Sobiyet na wancan lokaci mai suna Red Army ta dauke shi aiki a matsayin Kwamandan tankokin yaki, watau Tank Commander.

Lokacin da yake soji ya halarci yake-yake da dama. Ya shugabanci tankokin yaki a lokacin yakin Brodi (Battle of Brody) a watan Yuni na shekarar 1941, inda a karshe da zafi yayi zafi ya janye rundunarsa. A yakin Bryansk (Battle of Bryansk) da aka yi cikin watan Oktoba na shekarar 1941 ya samu rauni mai muni. A karshe dai aka bashi hutun jinya na tsawon watanni 6. Yana kwance a gadon asibiti yana jinya ne sai yaji wasu daga cikin sojoji 'yan uwansa suna korafi kan irin makaman da hukumar sojin kasar ke basu a lokacin yaki. Cewa ba su gamsar da su, kuma suna shan wahala wajen aiki da su sanadiyyar rashin saukin mu'amala.

Fasahar Kere-keren Makamai

Kafin wannan lokaci, tuni ya halarci kwasa-kwasai masu dama kan yadda ake mu'amala da bindigogi da yadda ake sarrafa su. da yaji irin korafin da wadancan sojoji ke yi, sai ya fara tunanin yadda zai taimaka wajen samar da bindiga mai saukin mu'amala, mai gamsarwa, mai dadin sha'ani. Yana samun sauki, sai nan take ya fara kera wata nau'in bindiga mai sarrafa kanta, wacce ake iya rikewa a hannu ko a dora a kafada, watau Submachine Gun. Bayan ya gama kera wannan bindiga, sai ya gabatar da ita ga hukumar sojin Daular Sobiyet na wancan lokaci, to amma sai aka yi rashin sa'a suka ki amincewa da ita a matsayin makamin yaki. Duk da haka, wannan ya baiwa hukumar damar fahimtar irin kaifin basira da fasahar da Allah ya baiwa Kalashnikov. Daga cikin basirar da Allah ya bashi akwai lura da dabi'ar sauki wajen kera duk makamin da yake kerawa.

Don haka, a shekarar 1947 sai Kalashnikov ya fitar da shahararriyar bindigarsa da ya sanya wa suna "Automat Kalashnikova Model 1947" ko AK-47, kamar yadda aka santa a halin yanzu. Bayan ya gabatar wa hukuma wannan sabuwar bindiga da ya kera, sai tayi nazari kanta. Bai samu amincewar hukuma ba sai shekarar 1956, watau bayan shekaru tara kenan. Daga nan ne hukumar sojin kasar ta amince cewa lallai wannan nau'in bindiga ta AK-47 amintacciya ce abin amincewa wajen tsaro. Ba ma wannan kadai ba, hukumar ta danganta wannan bindiga da kasar Rasha baki daya.

Bayyanar wannan bindiga a kasar Rasha ya bata shahara a sauran kasashen duniya, inda aka wayi gari kusan duk wata kasa da ke duniya a yanzu ba a rasa sojojinta da wannan nau'in bindiga ta AK-47. Bindiga ce amintacciya. Daga shekarar da Kalashnikov ya kera wannan bindiga zuwa yau, an samu zubin AK-47 masu dinbin yawa. Kusan kasashe da dama sun caccanza mata tsari, da kintsi, da yanayin sarrafawa, da dai sauransu. A wasu kasashen ma an canza mata suna, da lamba da dai sauransu. A takaice dai, akwai nau'ukan bindigar AK-47 sama da guda goma, wadanda aka canza musu tsari ta wajen ingantawa, da kayatarwa, a shekaru daban-daban.

Kalashnikov dai kwararre ne kan ilmin kimiyyar kere-kere, inda ya samu digiri na biyu a kan haka, watau Advance Degree in Technical Sciences. A halin yanzu yana raye, akwai kuma dalibansa biyu 'yan kasar Jamus da ya karantar dasu ilmin kera makamai, kuma sun shahara sosai a kasar Jamus, inda kowannensu ya kera bindigogin da suka shahara su ma. A hirar da kamfanin dillacin labaru na Reuters ya yi da shi a shekarar 2009, lokacin bikin karramawa da kasar Rasha ta shirya masa, ya ce:

"Duk da cewa akwai nau'in bindigar AK-47 sama da miliyan dari a duniya a yau, amma babu ko sisi da nake samu wajen yaduwarsu a matsayina na wanda ya kera su; in ka kebe dan fansho da nake karba daga hukuma, da kuma ladar hakkin mallaka da wasu kamfanonin sayar da kayayyakin abinci suke bani, don amfani da sunan bindigar da suka yi a kan hajojinsu."

Babbar falsafarsa dai wajen kere-kere ita ce yin la'akari da dabi'ar sauki. Ya ce duk abin da aka ce yana da saukin sha'ani ko mu'amala, to za a yi amfani da shi sosai, kuma zai fa'idantar, fiye da abin da yake da wahalar sha'ani ko sarrafawa. Ga abin da yake cewa:

"Duk abin da yake da wahalar sarrafa, ba shi da wani amfani. Kuma duk wani abu mai amfani ga jama'a, to za ka samu yana da saukin sarrafawa."

Darasi

Babban darasin da za mu koya daga rayuwar wannan bawan Allah shi ne, a kullum mu zama masu la'akari da abin da zai zama gyara da sauki ga dukkan al'ummar da muke rayuwa a cikinta. Wannan shi zai sa kwakwalwarmu ta rika kawo wuta, har mu samu kwazon da basirar ciyar da al'umma gaba ta hanyar da ta sawwake gare mu.

………………………………………………………

Fadakarwa

"Assalaamu Alaikum, Baban Sadik don Allah ina son in ja hankalinka. Idan masu tambaya suka rubuto maka tambaya, tare da yi maka sallama, maimakon ka amsa sallamar, sau da yawa sai kace "Barka da warhaka…" Da fatan za a gyara don kwadayin samun lada." Daga CPL Mamman B. Abdul Dambatta, Police College, Kaduna.

Wa alaikumus salaam, hakika na yi farin ciki da wannan fadakarwa naka. Allah saka da alheri, ya kuma ba damar kara tunatar da ni a duk sa'adda aka hararo wani kuskure da na tafka ko nake tafkawa. Kamar yadda na sha sanarwa, ni dan Adam ne, ina gafala kamar yadda kowa ke rafkana. Hakika Allah ya bani ikon gyarawa daga yanzu. Allah mana jagora, amin.

Friday, November 11, 2011

Mazan Jiya a Fannin Kimiya: Abu Abdallah, Al-Khawaarizmi


Mabudin Kunnuwa

Da yawa cikinmu kan yi mamakin yadda fasahar kere-keren kwamfuta musamman, da yadda fannin lissafi ya zama wani makami mai karfin gaske wajen kimiyyar kere-kere, da gine-gine (na gidaje, da gadaje, da ma'aikatu), da yadda fannin lissafi har wa yau ya zama makami wajen kawo ci gaba a fannin likitanci da hada magunguna a duniyar jiya da yau.  Galibinmu idan wadannan al'amura suka birge mu, sai ka ji mutum ya ce: "Shege Bature!," ko yace: "Aikin Nasara…!", ko wani zance makamancin wannan da ke nuna gamsuwarsa da abin, da kuma mamaki kan yadda abin ya kayatar da shi.  Sai dai kadan daga cikinmu (al'ummar Musulmi) ne muka san cewa, fannin lissafi a yau, musamman bangaren da ya shafi kimiyya da fasahar kere-kere da likitanci, da kimiyyar gine-gine, wanda ya samar da asalinsa, ya kuma habaka shi, ya inganta shi, ya kuma samar da turbar da har zuwa yau ake amfani da shi, musulmi ne!  Wannan bawan Allah kuwa shi ne Abu Abdallah, Muhammad ibn Musa Al-Khawaarizmi, wanda ya assasa fannin lissafin da a Turancin yau ake kira Algebra, da Trigonometry,da kuma Algorithm.

An haifi Imam Al-Khawaarizmi ne cikin shekarar 780 miladiyya, a garin Khawaarizm (ko Khiva) da ke Lardin Khuraasan a wancan lokaci, watau Lardin Xorazm kenan da ke kasar Uzbekistan a yau.  Imam Abu Rayhaan al-Birooni, daya daga cikin manyan malaman tarihi da ilmin musulunci a wancan karni ya ce asalin zuriyarsu Al-Khawaarizmi 'yan kabilar Fasha ne.  Imam Abu Ja'afar Al-Tabari kuma ya ce dan asalin Lardin Qatrabbul ne, kusa da birnin Bagadaza na kasar Iraki a yau.  A takaice dai galibin marubuta sun nuna cewa ayyuka da hidimar da Imam Al-Khawaarizmi yayi wa ilmi sun fi nasabarsa shahara a duniya. A nashi bangaren, Imam Ibn Nadeem a cikin littafinsa mai suna Kitaabul Fihrisah, ya kawo takaitaccen tarihin Imam Al-Khawaarizmi, inda ya kididdige littattafan da ya rubuta, da kuma cewa ya rubuta su ne tsakanin shekarar 813 – 833 miladiyya. Ya yi hijira zuwa birnin Bagadaza, inda ya yi aiki a matsayin mai binciken ilmi a babbar cibiyar ilmi da ke daular musulunci ta Bagadaza a wancan lokaci da ake kira Daarul Hikmah, karkashin Khalifah Ma'amoon.  A nan ne ya yi bincike kan fannin kimiyya, da lissafi tsantsa, musamman kan rubuce-rubucen kimiyya da a baya aka rubuta cikin harshen Girka, da Sanskirit.

Babbar hidimar da Imam Al-Khawaarizmi ya yi wa fannin kimiyya shi ne kan lissafi (Mathematics & Arithmetics), da ilmin sararin samaniya (Astronomy). Dukkan masana fannin lissafi da ke kasashen Turai – na karnin baya da na yanzu – sun yi ikirari da cewa shi ne asalin wanda ya samar tare da inganta fannin ka'idar lissafi kan "ragewa da daidaito", ko Aljabru wal Muqaabala, a harshen Larabci, ko Algebra a Turance, da dukkan nau'ukanta – irinsu Trigonometry, da Linear Equation, da kuma Quadratic Equations.  Hakan na taskance ne cikin shahararren littafinsa mai suna Al-Kitaabul Mukhtasar fee Hisaabil Jabr wal Muqaabalah.  Khalifah Ma'amoon ne ya zaburar da shi wajen rubuta wannan littafi.  Robert da Gerard sun fassara littafin zuwa harshen Latin.  A halin yanzu akwai kwafin littafin, wanda ya rubuta da larabci, a Jami'ar Oxford.  Wannan fannin ilmin lissafi ne ya samar da asalin ilmin tsarin yadda kwamfuta ke lissafi, da yadda take iya kurumtar da bayanai (Cryptography) da kuma yadda ake tsara hanyoyin gina masarrafar kwamfuta, watau Computer Algorithm.  Ya kuma yi bayanin hanyoyin da fannin lissafi ke taimakawa wajen kasuwanci da kuma tsarin rabon gado, duk ta wannan fanni na "Ragewa da Daidaito", watau Algebra. 

Daga cikin hidimarsa har wa yau akwai littafin da ya rubuta mai dauke da lissafin tazarar da ke tsakanin halittun sararin samaniya, irin Rana, da Wata a yayin da suke juyawa ko shawagi. A cikin wannan littafi mai dauke da babuka talatin da bakwai har wa yau, ya kididdige jadawalolin da ke dauke da wannan lissafi watau Astronomical Tables.  Ya yi nazarin asalin wannan littafi ne daga nau'ukan ilmin sararin samaniya da aka rubuta cikin harshen Hindu na kasar Indiya. Masana sun fahimci hakan ne daga sunan da ya baiwa littafin bayan ya rubuta, watau: Zinjul Sindhind.  A cikin wannan littafi har wa yau ya yi bayanin yadda duniyoyi biyar da aka gano a wancan lokaci (watau The Five Planetary Bodies) suke juyawa. Bayan haka, akwai littafi da ya rubuta mai suna Kitaabu Sooratil Ard, a fannin ilmin kasa (Geography).  Wannan littafi yana dauke ne da yadda duniya take, da abubuwan da ke cikinta ko samanta na teku da rafuka da sauransu.  A cikin littafin ya yi bayanin tazarar nisar duniya a kwance (Latitude) da kuma tazarar nisanta a tsaye (Longitude), da yadda tsarin rani da damina ke kasancewa. Bayan haka, ya samar da babbar Taswirar Duniya, watau Global Map, wanda har yanzu ake amfani da shi (watau taswirar duniya mai kamar kwallo).  A ciki ya haddade fadi da tsawon manyan tekunan duniya, ya kuma gano wasu, ta hanyar ilmin gano bigiren kasa ta hanyar lissafi.  Har wa yau akwai kwamiti na musamman da Khalifah Ma'amoon ya kafa mai dauke da masana kimiyyar sararin samaniya guda 70, Imam Al-Kawaarizmi ne ya shugabanci wannan kwamiti.   

Wannan ke nuna kwarewarsa, da kuma tasirin ilminsa a zamanin da yake raye.  Allah ya karbi rayuwarsa a shekarar 850 miladiyya, shekaru kusan 1200 kenan; yana dan shekaru 70 a duniya.  Allah ya rahamshe shi, ya kuma sa aljanna makomarsa, amin.

Thursday, November 10, 2011

Steve Jobs: Gwarzo Kan Kimiyyar Sadarwa ya Kwanta Dama


Laraba, Oktoba 5, 2011
 
Marigayi Steve Jobs
Ranar Laraba, 5 ga watan Oktoba ne dai tsohon shugaban kamfanin Apple Inc., watau Steve Jobs, ya kwanta dama, makonni shida da mika ragamar shugabancin kamfanin.  Jobs dai ya rasu ne bayan fama da yayi da mummunar cutar sankara da ake kira Pancreatic Cancer, na tsawon shekaru bakwai.  Kafin rasuwarsa dai ana kirga shi daga cikin mutanen da suka yi tasiri mafi girma a duniya wajen habbaka harkar sadarwa da kere-kere, musamman kan wayar salula, da kwamfuta, da na’urorin sadarwa nau’uka daban-daban, da allon shigar da bayanai na kwamfuta (Keyboard), da lasifika da dai sauransu.  An kiyasta cewa Jobs ya mallaki hakkin mallaka (Patents) kan kirkirarrun kayayyakin fasahar sadarwa har wajen 338.  Shi ne ya kafa kamfanin Appl Inc. da kamfanin NeXT Computer (kamfanin da ya kera kwamfutar da aka fara amfani da ita wajen kirkira da mu’amala da fasahar Intanet), da kuma kamfanin Pixar & Disney.  Jobs ya shahara a fannin sadarwa a duniya, don haka duniya ta dauka a ranar rasuwarsa – daga shugabannin kasashe zuwa ‘yan makaranta. Daga cikin shahararrun kirkire-kirkirensa, akwai na'urar sauraren wakoki mai suna iPod da dukkan nau'ukanta – irinsu iPod Classic, da iPod Nano, da kuma iPhod Touch – da kwamfutar Mac da dukkan nau'ukanta – irinsu Macbook Air, da Macbook Pro – da wayar salula nau'in iPhone da dukkan nau'ukanta – irinsu iPhone, da iPhone 3G, da iPhone 3GS, da iPhone 4G, da kuma iPhone 4S, wadda ake gab da fitarwa kafin mutuwarsasai kuma shahararriyar na'urar sarrafa bayanan nan mai suna iPad.  Kafin rasuwarsa, Jobs na da shekaru 56 a duniya, kuma ya mallaki tsaban kudi da kadara – dala na gugan dala – har wajen dalar Amurka biliyan takwas ($8billion), watau kusan Tiriliyon daya da biliyan dari uku da goma shabiyu kenan (N1.312 tr) a nairan Najeriya. A halin yanzu ga fassarar shahararriyar jawabin nan da ya taba yi wa daliban Jami’ar Stanford, daya daga cikin jami’o’i masu kima a duniya, ranar bikin yaye dalibai a shekarar 2005. A sha karatu lafiya:
.......................................................

“Rayuwarku ‘Yan Kwanaki Ne Takaitattu...”

“Ina matukar farin cikin kasancewa tare da ku a wannan rana da ake bikin yaye ku daga daya daga cikin Jami’o’i masu nagarta a duniya.  Ni kam ban samu damar gama Jami’a ba a rayuwata.  A hakikanin gaskiya ma dai, wannan shi ne lokacin da yafi kusantar da ni da bikin yaye dalibai a jami’a.  A yau zan baku wasu labarai ne guda uku daga tarihin rayuwata.  Su kenan.  Babu wani dogon bayani.  Labarai uku ne kacal.

Labarin farko dai waiwaye ne, abin da masu iya magana kan kira "Adon tafiya."

Na yanke shawarar gujewa daga Jami’ar Reeds ne watanni shida bayan fara karatu.  Amma sai na tsaya a makarantar ina rabe-rabe tsakanin darussa, har na tsawon watanni goma shatakwas, kafin a karshe dai na gudu.  To me yasa na kasa gama karatuna?

Dalilin dai ya samo asali ne tun kafin a haife ni.  Mahaifiyata wata budurwa ce dalibar Jami’a, wacce bayan ta dauki cikina, a karshe ta yanke shawarar bayar da ni ga wasu ma’aurata bayan ta haife ni.  Ita dai tana ganin lallai ya kamata a ce ta bayar da ni ne ga wadanda suka yi karatu, don haka, haihuwata ke da wuya sai ga wani Lauya da matarsa sun zo, don sa hannu kan takardar yarjejeniyar karba ta a matsayin dansu.  To amma da suka duba suka ga namiji ne, sai suka fasa, domin su mace suke so.  Daga nan sai aka mika ni ga iyaye na (na yanzu), wadanda a lokacin suke jira, tunda wadancan ba su son namiji.  Cikin tsakiyar dare aka bugo musu waya ana tambayarsu: "Mun samu da namiji, duk da cewa ba namiji muke tsammani ba; kuna bukatarsa?"  Sai nan take suka ce: "Sosai kuwa."   Sai bayan an mika ni ne daga baya asalin mahaifiyata ta gano cewa ashe wanda ya karbe ni bai gama Jami’a ba, matarsa ma ko sakandare bata gama ba.  Wannan yasa mahaifiyata ta ki sa hannu a kan takardar yarjejeniyar da aka rubuta.  Sai da aka yi ta mata magiya, da alkawarin cewa za a sa ni a makaranta har sai na gama, sannan ta sa hannu kan yarjejeniyar.

Haka kuwa aka yi.  Bayan na cika shekaru 17 aka sa ni a Jami’a.  To amma sai nayi ragon azanci na zabi Jami’a mai dan karen tsada, irin Jami’ar Stanford, inda aka wayi gari duk albashin iyayena yana karewa ne wajen biyan kudin makarantar.  Bayan tsawon watanni shida sai na ga wannan tsari bai da wata fa’ida.  Ni dai ban da wani tunani kan yadda zan tafiyar da rayuwata nan gaba, balle tunanin yadda karatun Jami’a zai iya taimaka mini cinma burina a rayuwa.  Amma ga shi duk dan abin da iyaye na ke samu na albashi na karewa wajen karatun.  Don haka na yanke shawarar fita daga makarantar, ina mai yakinin cewa lallai komai zai daidaita a karshe.  Wannan shawara da na dauka mai matukar hadari ce a lokacin, amma ta la'akari da abin da ya biyo baya, a halin yanzu ina iya cewa ita ce shawara mafi muhimmanci da na taba yankewa a rayuwata.  Da na yanke shawarar barin Jami'ar, sai na daina halartar dukkan darussa, sai wadanda nake da sha'awa a kai kadai.

Lamarin dai ba yadda aka so ba.  Domin ko dakin kwana ba ni da shi a Jami'ar; a kasa nake kwanciya a dakin abokai.  Sannan sai na je aike nake samun dan taro da kwabon da zan sayi abin da zan sa a bakin salati.  Kuma sai na yi tafiyar tazarar mil 7 a duk ranar lahadi nake samun abinci mai dadi a Hare Karishna.  Na ji dadin hakan.  Domin galibin abubuwan da na koya sanadiyyar kwazo da neman sani, a karshe sun fa'idantar da rayuwata baki daya.  Bari in baku wani misali:

A lokacin nan, Jami'ar Reeds ce kadai ke da kwararrun malamai masu karantar da darasi kan Fasahar Zane (Calligraphy) a duk fadin kasar nan (Amurka).  Duk wani hoto mai kayatarwa, duk wani taswira da zane da ka gani a manne a jikin kujerun dalibai ko a jikin gine-ginen Jami'ar, to, da hannu aka zana shi.  To, ganin cewa na yi niyyar barin Jami'ar gaba daya, kuma ba dole bane in halarci dukkan darussa, sai kawai na yanke shawarar lazimtar darasin koyon ilmin Fasahar Zane (Calligraphy) kadai, don samun kwarewa a wannan fanni.  Na koyi yadda ake zana haruffan Sans Seriff – daya daga cikin haruffan rubutu a kwamfuta - da dukkan nau'ukansa, da nau'ukan tazarar da ake so tsakanin hadakar haruffa a zane, da kuma dukkan hikimar da ake bukata wajen tsara rubutu ya kayatar.  Wannan abu yana da ban sha'awa ainun; cike da tarihi, da fasaha mai kyatarwa, irin kayatarwar da kimiyyar zamani ba ta iya bayarwa. Hatta ni kaina abin ya birge ni sosai.

Duk da wannan kwarewa da na samu, ban taba tunanin watarana zan kwatanta abin da na koya a aikace ba.  Amma shekaru goma da suka gabata, sadda muke tsara sabuwar kwamfutarmu ta farko nau'in Macintosh, sai wannan ilmin Fasahar Zane (Calligraphy) da na koya a Jami'ar Reeds ya halarto ni.  Kuma nan take muka yi amfani da wannan ilmin Fasahar Zanen haruffa muka shigar da haruffa masu kayatarwa cikin Mac.  Don haka, ita ce kwamfutar farko da ta zo da haruffa masu kayatarwa.  To, da a ce ban lazimci darussan koyon wannan fasahar ba a Jami'a, da wannan sabuwar kwamfuta ta Mac bata samu wadannan haruffa masu kayatarwa tare da tsarin tazara tsakanin haruffa ba, ko kadan.  Kuma musamman ganin cewa manhajar Windows ta kwaikwayi Mac ne wajen tsarin haruffa, kenan da ba don samuwarsu a cikin Mac ba, da babu wata kwamfuta a duniya da za ta mallake su.  Da a ce ban yanke shawarar barin Jami'a ba a lokacin, da ba zan taba tunanin barin sauran darussa ba balle har in lazimci darasin koyon Fasahar Zanen nan kadai.  Kuma da abin da wannan ke nufi shi ne: kwamfutoci ba za su samu wadannan haruffa masu kayatarwa ba kamar yadda suke da su a yau.  Tabbas, sadda nake Jami'a nake ta wannan bundun-dundun, ban taba zaton hakan zai iya faruwa nan gaba ba, ko kadan.  Amma a halin yanzu a bayyane yake, duk sadda na kalli rayuwata shekarun goma baya.

Har wa yau, ya kamata ku san cewa ba za ku taba iya fahimtar ci gaban rayuwarku ba idan kuna kallon me za ku yi nan gaba.  Za ku fahimci hakan ne kawai idan kuka kalli rayuwar da kuka yi a baya.  Don haka, dole ne ku tabbatar wa zuciyarku cewa nan gaba rayuwa za ta yi kyau.  Ya kamata ku zama masu yakini kan wani abu – kwazonku ne, ko kaddara, ko rayuwa, kai ko ma mene ne.  Wannan tsarin tafiyar da rayuwa da na dauka bai taba kai ni ya baro ba, kuma shi ne abin da yayi tasiri mafi girma a rayuwata.

Labarina na biyu kan soyayya ne da rashi.

Na ci sa'a – don na koyi abin da na fi sha'awar yi tun da kuruciyata. Ni da Woz mun kafa kamfanin Apple ne a garejin gidanmu, lokacin ina dan shekaru 20 a duniya.  Mun yi aiki tukuru ta yadda bayan shekaru 10, kamfanin Apple da ya faro da mutum biyu kacal a gareji, sai ga shi ya kasaita zuwa kamfanin da kimarsa ta kai dalar Amurka biliyan biyu ($2billion), da ma'aikata sama da mutum 4000!  Daidai wannan lokaci muka fitar da hajarmu ta farko mai kayatarwa, watau kwamfutar Macintosh, kuma daidai lokacin ne har wa wa yau na cika shekaru 30 a duniya.  Ana cikin haka sai aka kore ni daga kamfanin! Babban magana! Ta yaya za a yi a kore ka daga kamfanin da kai ka kafa shi?  Watau abin da ya faru shi ne, lokacin da kamfanin Apple ya fara habaka, sai muka yi hayan wani bawan Allah da nake da yakinin yana da kwarewar da zai iya taimaka mini wajen tafiyar da kamfanin.  Shekara daya bayan zuwansa komai ya tafi daidai.  Amma daga lokacin da mahangarmu kan tafiyar da kamfanin ta fara shan bamban da juna, sai sabani ya shigo.  Da haka ta faru, sai manyan daraktocin kamfanin suka goyi bayan ra'ayoyinsa.  Don haka ina cika shekaru 30 na fice daga kamfanin.  Kuma ficewa ce wacce ta yadu ko ina.  Nan take na rasa duk alkiblar rayuwar kuruciyata baki daya.  Wannan abu ya dagula mini lissafi matuka.

Har aka samu wasu watanni ban san me ya kamata in fuskanta ba.  Sai naji na fara zargin kaina kan rashin karfin halin rike nauyin shugabancin da aka dora mini, wanda kuma sa'o'ina suka damka a hannu na (sadda nake kamfanin Apple).  Nan take na hadu da David Packard da Bob Noyce, inda na yi kokarin basu hakuri kan wannan abin da nayi (na barin kamfanin Apple).  Na gaza matuka, inda har a karshe na yi tunanin barin kasar ma baki daya. To amma sai wani tunani ya fara shigo mini – ai har yanzu ina sha'awar abin da nayi (a baya).  Abin da ya faru a kamfanin Apple (na korar da aka mini) bai canza son da nake wa sana'ata ba.  Tabbas an kore ni, amma har yanzu ina sha'awar sana'ata.  Don haka na sake gwada wani kokarin.

Duk da cewa ban ji dadin abin da aka mini ba, amma daga baya na gano cewa, korar da aka mini daga kamfanin Apple alheri ne ga rayuwata.  Domin dawainiyar da ke kaina a wancan lokaci na shugabanci, yanzu ya sauka.  Na kuma samu sauki, inda na faro komai daga farko – cikin rashin tabbacin zan dace ko bazan dace ba.  Wannan ne ya bani damar shiga wata sabuwar marhala a rayuwata da ke cike da kwazo da hikimar kirkire-kirkire; babu nauyin kowa a kaina.

Bayan shekaru biyar da wannan kora ne na kafa kamfani mai suna NeXT, da wani kamfanin mai suna Pixar, kuma ana cikin haka na hadu da wata baiwar Allah mai ban al'ajabi da a karshe muka yi zaman aure da tare.  Ta hanyar kamfanin Pixar ne aka fitar da wani fim da aka yi, ta amfani da Fasahar Zanen Kwamfuta (Computer Animation) mai take: Toy Story, wanda shi ne na farkon irinsa a duniya.  Kuma wannan kamfani na Pixar ne ya tsere sa'o'insa wajen shahara da cin nasara a wannan fanni a duniya.  Abin mamaki, ana cikin haka kuma sai kamfanin Apple ya sayi wannan kamfani na NeXT da na kafa.  Wannan shi ne abin da ya dawo da ni kamfanin a karo na biyu, kuma fasahar da muka samar a kamfanin NeXT ta zama ita ce kashin bayan ci gaban kamfanin Apple kamar yadda kuke gani a yau.  Daga nan kuma na auri Laurene, muka ci gaba da rayuwa mai armashi.

Na tabbata da ba a kore ni daga kamfanin Apple ba a farkon lamari, da babu ko daya daga cikin wadannan ci gaba da za su riske ni.  Dandanon magani bai da dadi ko kadan, amma na tabbata shi ne abin da mara lafiya ya fi bukata.  Wasu lokuta rayuwa kan dake ka da guduma. Idan haka ya faru, duk kada ka yanke kauna da rayuwa.  Na gamsu cewa lallai abin da ya taimaka mini wajen tafiyar da rayuwa shi ne, ina sha'awar abin da nake yi (na aiki).  Don haka, wajibi ne ku lazimci abin da kuka fi sha'awan yi a rayuwa.  Kuma wannan shi ne abin da ya kamata ta bangaren aikin yi, da alakarku da masoyanku. Domin aiki shi ne abin da zai ci kaso mafi yawa na rayuwarku, kuma hanyar da za ku bi kadai don samun gamsuwa a rayuwa ita ce ta yin abin da kuka fi sha'awa.  In har baku samu abin da kuka fi sha'awan yi ba a rayuwarku yanzu, to, ku ci gaba da nema.  Kuma, kamar alaka ce tsakanin masoya, duk sadda shekaru suka yi nisa, tana kara armashi ne. Don haka ku ci gaba da bincike har sai kun samu abin da kuka fi sha'awan yi.  Kada ku yarda da wani abin da ba wannan ba.
Labarina na uku a kan mutuwa ne.

Lokacin da nake dan shekaru 17, na taba karanta wani zance mai kamar haka: "In har a kullum kana riya cewa ba za ka kai karshen yinin da  ka samu kanka a ciki ba, to, da sannu watarana tunaninka zai zama gaskiya." Wannan zance yayi tasiri matuka a ruhi na, kuma sama da shekaru 33 da suka shige, duk safiya idan na kalli fuskata a madubi nakan tambayi kaina: "A kaddara wannan shi ne yinina na karshe a duniya, shin, zan so in ci gaba da yin abin da na kuduri aniyar yi a yau?" Daga sadda na ci gaba da baiwa kaina amsar wannan tambaya da cewa, "A a," iya tsawon kwanakin da na yi ta yi wa kaina tambayar, daga nan na fahimci lallai ya kamata in canja wani abu a rayuwata.

Tunanin cewa lallai nan ba da dadewa ba zan iya mutuwa, shi ne muhimmin abin da na taba cin karo da shi, wanda kuma ya taimaka mini wajen tantace duk wani abin da zan yi a rayuwata.  Duk wani abu mara kima a rayuwa – kamar burace-buracen zuci, da girman kai, da tsoron abin kunya, ko tsoron rashin cin nasara – da zarar an ambaci mutuwa, nan take duk sai su gushe. Ba abin da zai saura sai muhimman al'amuran rayuwa.  Yawan tuna cewa nan gaba za ka mutu, a iya tunanina, shi ne kadai abin da zai sa ka kauce daga fadawa tarkon yawan damuwa da wata hasara ta dukiya da kake tsoro. Ba ka da wata mafaka.  In kuwa haka ne, ba ka da wani dalilin da zai hana ka bin shawara kan abin da zai fisshe ka.

Kimanin shekara daya da ta wuce (2004) aka tabbatar mini cewa na kamu da cutar sankara mafi muni (Pancreatic Cancer). Da misalin karfe 7:30 na safiya aka dauki hoton ciki na, inda a karshe aka gano ina da wannan cuta ta sankara.  Ban ma taba sanin me ake nufi da wannan bangaren ciki da ake kira Pancreas ba. Nan take likitoci suka sanar da ni cewa, wata irin nau'in cutar sankara ce wacce ba ta da magani, kuma nan gaba ba zan wuce tsawon watanni shida ba a duniya. Daga nan dai likita ya shawarce ni da in koma gida "in gyatta al'amura na."  Wanda hakan, a kaikaice, hannunka mai sanda ne da likitoci ke yi wa mara lafiya cewa, ka je ka shirya wa zuwan mutuwa kawai. Abin da wannan ke nufi shi ne ka je ka sanar da iyalinka duk abin da ka san ya kamata su sani daga nan zuwa shekaru 10, a tsawon 'yan watannin da ke tafe.  Hakan na nufi ne har wa yau, cewa ka tabbatar da cewa komai ka gama kintsa shi, don sawwake wa iyalinki duk wata matsala da ka iya tasowa bayan mutuwa. A takaice dai, ka je ka musu wasiyya da bankwana!

Da tunanin wannan cuta dai na yini tsawon wannan rana. Can dai zuwa yamma, sai aka zo aka tsakuro samfurin wannan cuta daga ciki na. An yi hakan ne kuwa ta hanyar tsofa na'urar hango cuta a ciki (Endoscope) wacce ke dauke da wani dan karamin allura, ta bi ta makogwaro da ciki da hanji, har ta karasa inda mikin ciki yake (Pancreas), ta tsukuro kwayoyin halitta (Cells) daga cutar da ta tsiro a jiki.  A lokacin an mini allurar bacci, amma mai dakina tana wurin, kuma tace daidai lokacin da aka fito da wannan samfurin cuta, da aka sa shi karkashin na'urar hangen nesa, sai duk likitocin suka kama kwalla saboda murna.  Domin ya bayyana musu cewa wannan nau'in cutar sankara ce ta musamman da ake iya warkar da ita ta hanyar tiyata. 
Tuni har an mini tiyatan, kuma a halin yanzu na samu sauki.

Wannan shi ne lokacin da na samu kaina mafi kusanci da mutuwa, kuma ina fatan wannan lamari ya kusantar da ni zuwa wasu shekaru masu yawa nan gaba.  Bayan na wuce wannan marhala ta rayuwa, a yanzu ne zan iya sanar da ku wani zancen da a baya ba zan iya gaya muku shi ba, saboda rashin fahimtar mutuwa hakikatan. (Ga sako na gare ku):

Babu mai son ya mutu.  Hatta wadanda ke ganin sun yi aikin kwarai ba su cikan son su mutu ba, sai dole.  Amma kuma babu makawa, mutuwa ce masaukin da za ta tattaro mu duka.  Babu wanda ya taba guje wa mutuwa a baya.  Kuma haka lamarin ya kamata ya zama. Domin mutuwa ce abin da har zuwa yau duniya bata taba samar da irinta ba.  Ita ce abin da ke kawo canji a rayuwa.  Ita ce ke share tsohuwar al'umma don kawo sabuwa.  A halin yanzu da nake muku wannan jawabi, ku ne sabuwar al'umma, amma nan ba da dadewa ba, watarana za ku zama tsohuwar al'umma, a share ku don kawo wata sabuwar.  Ku mini afuwa idan wannan zance nawa ya firgita ku, amma wannan ita ce hakikanin gaskiya.

Rayuwarku 'yan kwanaki ne takaitattu, don haka kada ku shagala wajen kwaikwayon rayuwar wani.  Kada ku zama 'yan abi yarima a sha kidi.  Kada ku yarda surutan wasu su hana ku bin shawarar da za ta fisshe ku a rayuwa.  Abu mafi muhimmanci shi ne, ku zama masu juriya wajen bin abin da zai zama maslaha a rayuwarku da fahimtarku.  Domin su ne kadai suka fi kowa sanin abin da kuke son ku zama.  Duk wani abin da ba wannan ba, to, ya zo a bayanshi.
Lokacin da nake dan karami akwai wata mujalla mai kayatarwa da ake kira: Whole Earth Catalog, wadda mujalla ce da kusan kowa yayi amanna da ita.  Wanda ya fara buga wannan mujalla kuwa wani bawan Allah me mai suna Stewart Brand, wanda ke unguwar Menlo Park da ke nan kusa da ku.  Ya kuma kayatar da mujallar ne ta hanyar kwarewarsa ta adabin turanci da yake da ita.  Wannan lamari ya faru ne tun wajajen shekarun 1960, kafin bayyanar kwamfutoci da tsarin buga mujallu na zamani kenan. Don haka mujallar gaba dayanta ana buga ta ne ta hanyar amfani da keken rubutu (Typewriter) na wancan zamani, da almakashi (wajen rage tsawon shafukan), da kuma na'urar daukan hoto irin ta da (Polaroid Camera).  Wannan mujalla dai kamar wata shafin gidan yanar sadarwar Google ce da aka buga a shafukan takarda, saboda fa'idojin da take dauke dasu.  Duk da cewa shekaru 35 kenan kafin bayyanar Google, amma mujallar a cike take da nau'ukan ilmi da fadakarwa, kwatankwacin yadda gidan yanar sadarwar Google take a yau.

Stewart, tare da abokan aikinsa dai sun buga wannan mujalla na tsawon lokaci, bayan wasu 'yan lokuta kuma sai aka neme ta aka rasa.  Amma kafin nan, sun yi bugu na karshe daidai shekarar 1974 – sannan ina matashi kamarku.  A shafin karshe daga baya, akwai wani hoto mai kayatarwa na wani titi da aka dauki hotonsa da safe – irin yanayin da wasunku za su so su taka a cikinsa don watayawa. A karkashin wannan hoto akwai wani karin zance da ke cewa: "Ka zama mai yunwar ilmi. Ka zama mai budaddiyar zuciya." Wannan shi ne sakon bankwana da suka sa a shafin karshe na mujallar, kafin su daina buga ta gaba daya.  Ka zama mai yunwar ilmi. Ka zama mai budaddiyar zuciya.  Kuma a kullum nakan yi wa kaina wannan fata.  Don haka na ga dacewar yi muku wannan fata ku ma, a daidai wannan lokaci da kuke kokarin fara wata sabuwar rayuwa, bayan barin Jami'a, cewa:

Ku zama masu yunwar ilmi a kullum. Ku zama masu budaddiyar zuciya wajen karbar fahimta.

Na gode matuka

Wednesday, November 9, 2011

Tauraron Binciken Sararin Samaniyan Kasar Amurka ya Kwanta Dama

Ranar Jumu'a, 23 ga watan Satunba ne babban tauraron dan adam din nan na kasar Amurka mai suna Upper Atmosphere Research Satellite (UARS) ya ruso cikin wannan duniya tamu, bayan kwashe shekaru ashirin yana shawagi a cikin falaki. Tauraron, wanda hukumarclip_image002[7] Binciken Sararin Samaniya na Kasar Amurka mai suna NASA ta cilla zuwa sararin samaniya tun shekarar 1991, ya fara konewa ne sannan ya tarwatse, kafin ya shigo cikin wannan duniya, a yammacin Jumu'ar da ta gabata. Hukumar NASA dai ta bayar da sanarwar shigowar wannan tauraro nata ne kasa da mako guda kafin shigowarsa. Inda ta ce tana sa ran shigowarsa ne tsakanin ranar Jumu'a ko Asabar da ta gabata.

Wannan tauraron dan adam mai suna Upper Atmosphere Research Satellite dai an cilla shi zuwa sararin samaniya ne ranar 12 ga watan Satumba, 1991, inda ya fara shawagi cikin falaki a ranar 15 ga watan, watau kwanaki uku bayan cilla shi kenan. An kuma harba shi ne cikin kumbon sararin samaniya mai suna STS-48, daga babbar tashar harba tauraron dan adam mai suna Kennedy Space Center Launch Complex a kasar Amurka. Babbar manufar da tasa kasar Amurka kerawa tare da cilla wannan tauraron dan adam zuwa cikin falakin sararin samaniya dai ba ta wuce manufar bincike kan wasu sinadaran kimiyya da ke samuwa a saman sararin samaniyan wannan duniya tamu, watau Upper Atmosphere kenan, kamar yadda sunan tauraron ya nuna. Bayan gano sinadaran kimiyya (watau Photochemical Research), har wa yau daga cikin aikinsa akwai auna mizanin zafin rana da ke cillowa zuwa cikin wannan duniya tamu, watau Ultraviolet Rays kenan. Wannan tauraro dai yana dauke ne da na'urorin daukar hoto daga sararin samaniya, da na'urar da ke sinsino sinadaran kimiyya a sararin samaniya, da na'urar da ke taskance sinadaran hasken rana don karfafa batiran da tauraron ke amfani da su don samar da wutar lantarki, watau Solar Panels kenan.

Hukumar NASA ta tanada wa wannan tauraro tsawon shekaru goma shabiyar ne a sararin samaniya don gudanar da ayyukansa, kuma ya gama ayyukansa ne cikin shekarar 2005, daga nan ya ci gaba da shawagi a cikin falaki a matsayin sharar sararin samaniya, watau Space Junk. Bayan shekaru biyar sai ya nufato wannan duniya tamu, don kwanta dama. A iya tsawon shekarun da tayi tana lura da shawagin wannan tauraro na UARS, Cibiyar Lura da Tauraron dan Adam na kasar Amurka mai suna Joint Functional Component Command (JFCC) a cibiyar sojojin sama da ke Vandenberg a jihar Kalfoniya, tace sadda ya shigo cikin sararin wannan duniyar ta mu, wannan tauraro ya yi shawagi ne daga Gabar Afirka, ya kewaya ta Tekun Maliya, ya hauro Tekun Pacific, ya gangara Arewacin Kanada, ya karaso Arewacin Tekun Atlantika, sannan ya kutso Yammacin Afirka, kafin ya wargaje a wani muhallin da har ya yanzu ba a sani ba.

Kafin kutsowa cikin wannan duniyar tamu, tauraron UARS ya fara konewa ne daga sararin samaniya, kamar yadda taurarin dan adam ke yi idan suka zama shara a sararin samaniya, sannan ya daidaice, dukkan bangarorinsa ashirin da shida suka wargaje. A halin yanzu dai hukumar NASA na gudanar da bincike ne don gano inda buraguzan wannan tauraron dan adam suka fadi. Amma ta nuna cewa akwai tabbacin cewa bai fado kan wani gari ko al'umma ba, musamman ganin cewa galibin lokacin shawaginsa bayan shigowarsa duniya duk ta saman teku ne ya gudana.

Wednesday, November 2, 2011

Tallafin Hasken Leza Ga Fannin Likitanci

Matashiya

Watanni uku da suka gabata wani direba ya kamu da ciwon ido mai tsanani, inda har ya wayi gari ba ya iya tukin mota sai dai a tuka shi. Wannan abu ya ci masa tuwo a kwarya musamman lokacin da likita ya sanar da shi cewa sai an masa tiyata a saman giran idanunsa, don magance wannan matsala. Daga nan kuma wata sabuwar damuwa ta cika masa zuciya. "Yanzu wannan na nufin za a fasa kashin da ke goshi na kenan?" ya tambaye ni watarana muna cikin hira. Sai muka fashe da dariya. Muka ce masa ai ko za a fasa, to ba za ka sani ba. Wannan bawan Allah dai bai samu natsuwa ba. Da yaje ya kama tambaya kan irin wannan lalura, sai wasu suka ce masa ai wane da wane ma an musu irin wannan tiyata, amma basu kai labari ba; sun sheka barzahu.

Da muka ga dai damuwa ta kai masa ko ina, kasancewar abokinmu ne, a ma'aikata daya muke aiki, sai muka fara bashi shawaran cewa ya rage damuwa, idan kuwa ba haka ba, to, wata sabuwar cuta za ta kama shi. Haka aka yi. Cikin taimakon Ubangiji aka shirya masa takardun fita waje, aka masa biza zuwa kasar Indiya, muka masa addu'a, ya haye jirgi; sai kasar Hindu. Kwanaki biyu da masa tiyata aka sallame shi. Sai kwatsam ga Malam Sani ya dawo. Kowa na tunanin ya ji an ce sai bayan mako daya zai dawo. Yana zuwa sai ga shi garau, yana murmushi, babu ko bandeji a saman goshi ko idanunsa. Babban Magana! Ba a yi aikin bane? Ya ce an yi, "Ni kaina ban san da me suka yi ba. Kuma ko tsaga jiki na ba a yi ba." Daga nan na fahimci sabuwar fasahar tiyatar da suka yi amfani da ita. Wannan fasahar tiyata ita ake kira "Laser Surgery" a fannin likitancin zamani; watau tsarin amfani da hasken Laser wajen yin tiyata. Masu karatu, yau kuma ga mu dauke da bayani kan wata fasahar sadarwa a tsari da yanayin tururin haske ko iska mai dauke da sinadarai, mai kuma taimakawa wajen sawwake tsarin aiwatar da tiyata a wannan zamani namu.

Asali da Samuwa

Da farko dai, wannan fasaha ta hasken leza (watau Laser Light, ko Laser Beam, a turancin kimiyyar lantarki), tana samuwa ne ta amfani da tsarin kambama tururin haske ko iska zuwa yanayin haske mai kaifi, mai kuma tafiya a tafarki daya kacal. Ana amfani da wannan kambamammen haske ne ta hanyar na'urar da ake kira leza a halin yanzu. Na'ura ce mai dauke da kafofi guda biyu. Da kafar shigar sarrafaffen iska ko hasken, da kuma kafar da ke fitarwa. Wannan kafa da ke fitar da wannan sarrafaffen haske 'yar karama ce ainun, don haka hasken ke zama siriri. Na'urar na fitar da hasken ne a yanayi daban-daban; akwai nau'in haske mai dauke da iska, akwai haske zalla mai dauke da launuka daban-daban. Sannan na'urar tana da gejin kadadar zafi ko maimaituwar tsarin launi ko zafin da ake son wannan sarrafaffen iska ya fito da su don a aiwatar da irin aikin da ake son yi. Wannan ke nuna mana abubuwa guda hudu da ke tattare da wannan nau'in haske. Abu na farko, shi haske ne sarrafaffe daga sinadaran iska ko tururin haske (watau Radiation). Abu na biyu shi ne, hasken na taskance ne a na'urar leza (mai yanayin girma da daban-daban). Abu na uku shi ne, hasken na fita ne da karfi, da haske, da gwargwadon zafin da ake so, kuma hasken mai kaifi. Abu na hudu shi ne, hasken na tafiya ne a tafarki guda daya, ba ya barbazuwa. Bincike ya tabbatar da cewa nau'ukan hasken leza suna yanke abubuwa ne kamar yadda duk wani abu mai kaifi ke yankewa. Ba ma nan kadai ba, suna da tasirin hasko wuraren da hannu ko almakashin mai tiyata ba za su iya shiga ba.

Wannan fasaha dai ta samo asali ne cikin shekarar 1960, lokacin da aka gudanar da bincike, aka tsara yadda fasahar za ta yi aiki, a rubuce. A cikin shekarar 1974 ne aka kirkiri na'urar farko mai amfani da hasken leza. Wannan na'ura kuwa ita ce na'urar manna tambari a jikin hajojin kasuwanci, watau Bar Code Machine. A cikin 1978 kuma aka kirkiri na'urar faifan garmaho, watau Gramophone Player kenan. Na tabbata mai karatu ya san wannan na'ura. To, tana amfani ne da nau'in hasken leza wajen haska layukan bayanai masu dauke da kide-kiden da ke cikin faifan. Ana shiga shekarar 1982 kuma sai aka kirkiri na'urar CD, watau CD Player; wacce har yanzu muke amfani da ita wajen sauraro ko kallon fina-finan faifan CD. Dagan an kuma sai kamfanin kera kwamfuta suka cafke, inda aka kirkiri na'urar dabba'a bayanai mai amfani da hasken leza ita ma. Wannan na'ura ita ake kira Laser Printer, kuma har yanzu ana amfani da su wajen dabba'a bayanai.

Tun bayyanar wannan hikimar ta sarrafa haske don amfanin al'umma, an samu fannonin rayuwa da dama da suke amfani da ita wajen kere-kere, da yanke-yanke, da huje-huje, ko jone-jone. Wannan kafin samuwar haka a fannin likitanci kenan. Misali, manyan masana'antun kere-kere na amfani da wannan fasaha wajen yin waldan karafa. Bangaren soji kuma na amfani da shi wajen gano inda abokan gaba suke a lokacin yaki, da darkake abokan gaba. A fannin tsaro ma ana amfani da wannan tsari na fasahar leza. Da shi jami'an tsaro ke amfani wajen gano tambarin yatsun masu laifi, da tsarin gano masu laifi ta hanyoyin kimiyyar sadarwa na zamani. A fannin binciken kimiyyar sararin samaniya ma akwai tsarin fasahar leza. Galibin masu binciken kimiyya a halin yanzu na kan habbaka wannan fasaha ne don yin amfani da ita wajen tafasa sinadaran Yuraniyon, wanda makamashi ne mai muhimmanci wajen kera makamin nukiliya. Sannan malaman kimiyya a jami'o'i suna amfani da fasahar hasken leza wajen gudanar da bincike ta hanyoyi da dama. Idan muka koma bangaren bukukuwa da shakatawa, nan ma akwai hannun wannan fasaha wajen kayatar da jama'a. A kan yi amfani da wannan haske cikin yanayi mai ban sha'awa, a kawata wuraren biki da shi. A halin yanzu da masu bincike suka fara tunanin hanyoyin sawwake matsalolin da ake fuskantan cikin tsarin tiyata a asibitoci, sai tunannin wannan fasaha ta hasken leza ta fado musu.

Amfani da Hasken Leza a Fannin Likitanci

Kamar yadda bayanai suka gabata, akwai fannonin rayuwa da dama da ake amfani da wannan fasaha mai matukar tasiri. A dukkan fannonin nan kuwa, ana amfani da fasahar ne a irin yanayin da ya kamaci abin da ake son samarwa ko kawarwa ko gyattawa. A fannin likitanci ana amfani da wannan fasaha wajen yin tiyata a saman fatar fuska da sauran bangaren jiki, kan abin da ya shafi cututtukan fata ko wani abin da ke makale a jikin fatar. Wannan fanni shi ake kira Laser Skin Surgery. Bayan shi, akwai kwararru kan fannin likitanci masu lura yin wannan aiki (watau Dermatologists), tare da amfani da wannan fanni har wa yau wajen gyaran fatan jiki don ado, watau Cosmetic Laser Surgery kenan. A kan yi amfani kuma da wannan fasaha wajen gyaran hakora; masu kogo ne, ko masu girgidi, ko kuma namar da ke rike da hakora. Sannan akwai tiyatar koda da ake yi da wannan fasaha ta hasken leza, watau Laser Kidney Stone Surgery kenan. Wannan shi ake amfani da shi wajen narkar da tsakuwan da ke cikin koda, ko duk wani dunkulalle ko daskararren abin da ya toshe hanyoyinsa.

Bayan haka, a kan yi amfani da hasken leza wajen aiwatar da tiyata a cikin idanu. Wannan ma shi ne fannin da ya fi shahara a bangaren likitanci. Shi yake sawwake aiwatar da tiyata cikin idanu ba tare da wasu matsaloli ba. Akwai kuma tallafin da wannan fasaha ta hasken leza ke bayarwa wajen goge zanen haihuwa da ake wa mutane (watau Birth marks), da zane-zanen jiki irin na zamani da galibin turawa ke yi a yanzu, watau Tattoos. A takaice dai, wanann fasaha ta hasken leza na taimakawa matuka wajen sawwake da yawa cikin matsalolin da ake fuskanta a bangaren tiyata a bangarorin jiki irinsu kunnuwa, da idanu, da fatan jiki, da koda, da dai sauransu. Duk wata kafa ta jiki da ke lungu sosai, wacce sai an wahala kafin a kai inda take, duk ana iya riskarta ta amfani da wannan haske na leza.

Wannan haske na leza ya sha bamban da sauran haske da muka saba mu'amala da su a rayuwarmu ta yau da kullum. Sauran nau'ukan haske sukan bazu ne da zarar sun fito daga muhallinsu. Wannan tsari shi ake kira Light Scattering. Kamar yadda hasken rana ke bazuwa, ta game dukkan ilahirin wurin da take haskawa. Amma hasken leza ya sha bamban. Wannan nau'in haske yana tafiya ne a tafarki guda daya tilo. Misali, idan kofar fitarsa kamar kofar allura ce, da zarar ya fito, a wannan yanayin na sirantaka da kaifi zai ci gaba da tafiya, har sai ya isa zuwa inda aka cilla shi, ba tare da karfin hasken, da kaifinsa, da sirantakarsa sun ragu ba. Bayan haka, kowane haske yana zuwa ne da iya karfin iska ko zafin da aka yi gejinsa kafin fitowarsa, kuma idan ya fito, duk iya nisan tafiyar da zai yi, wannan gwargwadon zafi ba zai ragu ba. Wannan ke bashi tasirin shiga lungu-lungu, sako-sako, don baiwa mai mu'amala da shi damar gani ko taba nama, ko jijiya, ko wani yadin da ke karkashin fatan jikin dan adam. Akwai yanayin da ke fitar da haske kai tsaye, don kona wata fata ko yanke ta. Akwai wanda ke fito da ballin haske (watau Light Pulses), akwai kuma mai fitowa a launuka daban-daban.

Tsarin Tiyata

Saboda saukin mu'amalar da ke tattare da hasken leza wajen tiyata, da zarar an hasko shi saman fatar jiki, sinadaran da ke cikin hasken kan narke cikin ruwan da ke cikin fatan, nan take. Kamar yadda muka sani, abin da yafi komai yawa a jikin dan adam shi ne ruwa. Wannan haske zai narkar da sinadaransa ne cikin ruwan da ke fatan jiki, daga nan kuma ya hade da sinadaran da ke samar da jinni, watau Hemoglobin, da Melanin.

Wannan haske na leza ne ke shiga cikin fata, ya kona duk kwayar cutar da ke cikinsa, ko ya bayar da damar rede matattaciyar yadin (watau Tissue) da ke tsakanin nama da fatar jiki. Da wannan haske har wa yau ake amfani wajen haska cikin kodar dan adam, don gano inda tsakuwa suke. Da zarar an hasko su, sai a cilla haske mai matukar zafi don narkar da wadannan duwatsu da ke cikin kodar ba tare da an keta kodar ko fatan jikin mara lafiya ba. Dangane da magance matsalolin hakora, akan yi amfani da wannan haske wajen haskawa ko leko inda matsala take a hakoran mara lafiya. Ana amfani da wannan haske har wa yau don cire gashin jiki, ko na kai, ko na wasu bangarorin jikin dan adam.

Su ma nau'ukan zanen haihuwa ko zanen sha'awa da wasu ke yi a jikinsu, a yanzu an gano cewa da hasken leza duk ana iya goge su ko share su har abada. Idan muka koma bangaren gyaran fatan jiki ma haka abin yake. Da wannan haske ake amfani wajen baje dukkan kurajen da ke fuska (irinsu kyasbi da sauransu) ko kurajen baya ko kuma tamojin da ke bayan yatsun tsofaffi. Dukkan wadannan na karkashin tsarin amfani da hanyoyin tiyata don gyaran jiki, watau Laser Cosmetic Surgery. A karshe, a yanzu ma an gano cewa za a iya amfani da wannan haske na leza wajen kankare sinadaran da ke jikin wanda ya kamu da ciwon shan tabar sigari ko tabar wiwi a misali. Hakan na yiwuwa ne ta amfani da wannan haske don hasko muhallin da wadannan sinadarai suke, da kuma yin amfani da hasken wajen baje su ko narkar da su, su zama ba su da wani tasiri a jiki. Bincike ya nuna cewa ana samun nasara kashi 80 cikin 100 kan wannan matsala. Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba, hakan ya danganci yanayin jiki ne, da kuma zurfin jarabtuwa da tabar ga mara lafiya. Don haka, gwajin da za a yi wa mara lafiya kafin a fara aiwatar da wannan tiyata, shi zai tabbatar da cin nasara ko rashinsa.

Amfanin Hasken Leza

Masana fannin likitanci sun tabbatar da cewa wannan sabuwar fasahar tiyata ta hasken leza na da fa'idoji masu yawa wajen saukake tsarin tiyata, musamman tiyatar idanu, da na koda, da na fatan jiki, da cire gashi da dai sauran fannonin da wannan fasaha ta shafa. Amfani na farko ita ce saurin warkewa. Sun tabbatar da cewa lallai ana samun saurin waraka idan aka yi amfani da hasken leza wajen tiyata, idan aka kwatanta tsawon kwanaki ko lokacin da mara lafiya ke dauka kafin ya warke daga tiyatar da aka masa ta amfani da wukaken tiyata. Domin a bangaren fasahar hasken leza, akwai tiyatar da za a yi wa mara lafiya a rana guda, kuma ya mike a ranar ya ci gaba da harkokinsa. Illa dai za a bashi magunguna ne da zai rika sha.

Fa'ida ta biyu ita ce rage yawan kamuwa da wasu cututtuka a yayin tiyata. Kamar yadda muka sani, da yawa cikin wadanda ake wa tiyata ta amfani da wukaken tiyata kan kamu da wasu cututtuka, saboda fede fatan jiki ko cikinsu da ake yi da wukar tiyata. Wannan ke sa a dauki tsawon lokaci ana shan magani bayan an yi tiyatar. To amma idan aka yi tiyata da fasahar hasken leza, hakan kan rage yawan kamuwa da wasu cututtukan daban, watau Infection. Daga cikin fa'idojin amfani da fasahar hasken leza wajen tiyata har wa yau, akwai rashin zuban jini. A bangaren amfani da wukaken tiyata a kan samu zuban jini sanadiyyar fida da ake yi. Amma a tsarin amfani da fasahar hasken leza kuwa babu wannan matsalar. Domin akwai tiyatar da za a yi wa mutum, daga farko har karshe ba a zubar da jini ba. Saboda hasken na shiga cikin fata ne, yana iya yanke fatan ma ba tare da jini ya zuba ba ko kadan. Wannan na daga cikin fa'idoji masu muhimmanci.

Fa'ida ta gaba ita ce rage yawan rauni ga mara lafiya. Duk da cewa amfani da fasahar hasken leza wajen tiyata akwai zafi, amma kuma yana rage yawan raunuka da mara lafiya ka iya samu a yayin da ake ta fede shi ta amfani da tsarin aiwatar da tiyata da wukaken tiyata. Maimakon a yi ta yanke fatan ana kutsawa cikinsa don isa zuwa ga wata gaba da ake son aiwatar da aiki a cikinta ko a kanta, a tsarin fasahar hasken leza sai dai sinadaran haske su kutsa cikin fatan, har su isa zuwa ga gabar da ake son aiwatar da aikin a cikinta ba tare da an yi wa fatar rauni ba.

Fa'ida ta karshe ita ce, wannan fasahar haske ta leza tana da saukin sha'ani wajen aiwatar da tiyata ko samar da waraka a fannin likitanci, ta kowace fuska idan aka duba. Saukin sha'ani wajen yin tiyatar; saukin sha'ani wajen samar da waraka nan take (domin ana iya yi wa mutum tiyata da wannan sabuwar tsari, cikin awanni biyu ya mike ya kama harkokinsa). Sannan ga saukin sha'ani wajen mu'amala da gabobin jikin mara lafiya ba tare da an kutsa inda bai kamata ba a yayin tiyatar.

Wasu 'Yan Matsaloli

Kamar dai duk wani abin amfani ne, wannan fasaha ta hasken leza na da nata fa'idoji da kuma 'yan matsaloli wadanda ba za a rasa ba. Daga cikin 'yan matsalolin da ke tattare da wannan fasahar tiyata ta amfani da hasken leza akwai dan Karen tsada. Aiwatar da tiyata ta amfani da wannan sabuwar fasaha na bukatar kudi mai dimbin yawa, da kuma kwarewa. Saboda ba kowane likita bane zai iya aiwatar da tiyata ta amfani da wannan fasaha ta hasken leza. Abu na biyu kuma shi ne rashin yaduwa. Ba ka safai ake samun wannan fasaha a kasashe masu tasowa ba. Galibi sai kasashen Turai. Wannan yasa abin yayi tsada. Idan an samu a kasashe masu tasowa ma sai ka ga a asibitoci masu zaman kansu ne, kuma dole ya yi tsada. Har wa yau, duk da cewa amfani da wannan fasaha ta hasken leza na rage kamuwa da wasu cututtuka sababbi, a daya bangaren kuma akan kamu da wasu cututtuka masu alaka da sinadaran hasken, idan ba a dace ba.

Nau'ukan Fasahar Hasken Leza

Akwai nau'ukan hasken leza kala-kala. Na farko shi ne nau'in hasken leza mai dauke da sinadaran iska wanda ake kira Carbondioxide Laser (CO2 Laser). Kamar yadda bayanai suka gabata a baya, wannan fasaha ta hasken leza na dauke ne da haske da kuma iska, watau Gas. Wannan nau'in hasken leza mai suna CO2 Laser yana taimakawa ne wajen yanke fatar jiki ba tare da jini ya zuba ba. Kuma da shi ne ake yin tiyata don cire kwayoyin cutar da ke haddasa kuraje a cikin fatan jiki. Har wa yau ana amfani da shi wajen cire kwayoyin cutar sankara ko kansa (watau Cancerous Diseases). Saboda nau'in haske ne mai karfi, mai kaifi, kuma mai dauke da sinadaran haske masu zafi.

Nau'in hasken leza na biyu shi ne wanda ake kira ERBIUM Laser. Wani irin haske ne mai fitowa a hankali, ya shiga fatar jiki a hankali cikin natsuwa, sannan ya narke cikin ruwan jiki nan take, yana barbazuwa babu kakkautawa. Da wannan nau'in hasken leza ne ake iya rede matacciyar yadin fatar jiki (watau Skin Tissue), da irin fatar da zafin hasken rana ta kashe, daga jikin tsofaffi. Har wa yau akan yi amfani da wannan nau'in haske wajen cire rubabbiyar yadin fatar jiki (watau Dead Tissue) sanadiyyar kamuwa da kwayoyin cuta. Bayan haka, akan yi amfani da wannan nau'in haske don share kurajen fuska, irinsu kyasbi da sauransu.

Nau'in hasken leza na gaba shi ne wanda ke fitar da haske launin rawaya ko ruwan kwai, watau Yellow Light Laser. Wannan nau'in haske yana fitar da gajerun ballin haske ne launin rawaya, ko Short Pulses of Yellow-Color. Wannan launin hasken leza yana shiga cikin ruwan jiki ne, ya saje da launin sinadaran da ke samar da jini; ko Hemoglobin ko Melanin. Ana amfani da wannan launin hasken leza ne wajen magance matsalolin jijiyoyin bangarorin jiki. Ana kuma amfani da shi don goge jajayen tsagar jiki, watau Red Birth Marks.

Launin hasken leza na gaba shi ne launin hasken leza ja, watau Red Light Laser. Wannan nau'in hasken leza shi ne wanda ake amfani da shi wajen share ko goge tamojin yatsun hannu masu bayyana sanadiyyar tsufa ko yanayin zamantakewa a wani muhalli. Launin hasken leza ja shi ma yana fitowa ne da gajerun ballin haske, amma masu dauke da dimbin sinadaran haske masu yawa, don aiwatar da aikin cikin sauki. Hakan kuma na samuwa ne ta hanyar wani tsarin amfani da haske mai suna Q-Swtiching, a turancin kimiyyar lantarki.