Wednesday, November 2, 2011

Tallafin Hasken Leza Ga Fannin Likitanci

Matashiya

Watanni uku da suka gabata wani direba ya kamu da ciwon ido mai tsanani, inda har ya wayi gari ba ya iya tukin mota sai dai a tuka shi. Wannan abu ya ci masa tuwo a kwarya musamman lokacin da likita ya sanar da shi cewa sai an masa tiyata a saman giran idanunsa, don magance wannan matsala. Daga nan kuma wata sabuwar damuwa ta cika masa zuciya. "Yanzu wannan na nufin za a fasa kashin da ke goshi na kenan?" ya tambaye ni watarana muna cikin hira. Sai muka fashe da dariya. Muka ce masa ai ko za a fasa, to ba za ka sani ba. Wannan bawan Allah dai bai samu natsuwa ba. Da yaje ya kama tambaya kan irin wannan lalura, sai wasu suka ce masa ai wane da wane ma an musu irin wannan tiyata, amma basu kai labari ba; sun sheka barzahu.

Da muka ga dai damuwa ta kai masa ko ina, kasancewar abokinmu ne, a ma'aikata daya muke aiki, sai muka fara bashi shawaran cewa ya rage damuwa, idan kuwa ba haka ba, to, wata sabuwar cuta za ta kama shi. Haka aka yi. Cikin taimakon Ubangiji aka shirya masa takardun fita waje, aka masa biza zuwa kasar Indiya, muka masa addu'a, ya haye jirgi; sai kasar Hindu. Kwanaki biyu da masa tiyata aka sallame shi. Sai kwatsam ga Malam Sani ya dawo. Kowa na tunanin ya ji an ce sai bayan mako daya zai dawo. Yana zuwa sai ga shi garau, yana murmushi, babu ko bandeji a saman goshi ko idanunsa. Babban Magana! Ba a yi aikin bane? Ya ce an yi, "Ni kaina ban san da me suka yi ba. Kuma ko tsaga jiki na ba a yi ba." Daga nan na fahimci sabuwar fasahar tiyatar da suka yi amfani da ita. Wannan fasahar tiyata ita ake kira "Laser Surgery" a fannin likitancin zamani; watau tsarin amfani da hasken Laser wajen yin tiyata. Masu karatu, yau kuma ga mu dauke da bayani kan wata fasahar sadarwa a tsari da yanayin tururin haske ko iska mai dauke da sinadarai, mai kuma taimakawa wajen sawwake tsarin aiwatar da tiyata a wannan zamani namu.

Asali da Samuwa

Da farko dai, wannan fasaha ta hasken leza (watau Laser Light, ko Laser Beam, a turancin kimiyyar lantarki), tana samuwa ne ta amfani da tsarin kambama tururin haske ko iska zuwa yanayin haske mai kaifi, mai kuma tafiya a tafarki daya kacal. Ana amfani da wannan kambamammen haske ne ta hanyar na'urar da ake kira leza a halin yanzu. Na'ura ce mai dauke da kafofi guda biyu. Da kafar shigar sarrafaffen iska ko hasken, da kuma kafar da ke fitarwa. Wannan kafa da ke fitar da wannan sarrafaffen haske 'yar karama ce ainun, don haka hasken ke zama siriri. Na'urar na fitar da hasken ne a yanayi daban-daban; akwai nau'in haske mai dauke da iska, akwai haske zalla mai dauke da launuka daban-daban. Sannan na'urar tana da gejin kadadar zafi ko maimaituwar tsarin launi ko zafin da ake son wannan sarrafaffen iska ya fito da su don a aiwatar da irin aikin da ake son yi. Wannan ke nuna mana abubuwa guda hudu da ke tattare da wannan nau'in haske. Abu na farko, shi haske ne sarrafaffe daga sinadaran iska ko tururin haske (watau Radiation). Abu na biyu shi ne, hasken na taskance ne a na'urar leza (mai yanayin girma da daban-daban). Abu na uku shi ne, hasken na fita ne da karfi, da haske, da gwargwadon zafin da ake so, kuma hasken mai kaifi. Abu na hudu shi ne, hasken na tafiya ne a tafarki guda daya, ba ya barbazuwa. Bincike ya tabbatar da cewa nau'ukan hasken leza suna yanke abubuwa ne kamar yadda duk wani abu mai kaifi ke yankewa. Ba ma nan kadai ba, suna da tasirin hasko wuraren da hannu ko almakashin mai tiyata ba za su iya shiga ba.

Wannan fasaha dai ta samo asali ne cikin shekarar 1960, lokacin da aka gudanar da bincike, aka tsara yadda fasahar za ta yi aiki, a rubuce. A cikin shekarar 1974 ne aka kirkiri na'urar farko mai amfani da hasken leza. Wannan na'ura kuwa ita ce na'urar manna tambari a jikin hajojin kasuwanci, watau Bar Code Machine. A cikin 1978 kuma aka kirkiri na'urar faifan garmaho, watau Gramophone Player kenan. Na tabbata mai karatu ya san wannan na'ura. To, tana amfani ne da nau'in hasken leza wajen haska layukan bayanai masu dauke da kide-kiden da ke cikin faifan. Ana shiga shekarar 1982 kuma sai aka kirkiri na'urar CD, watau CD Player; wacce har yanzu muke amfani da ita wajen sauraro ko kallon fina-finan faifan CD. Dagan an kuma sai kamfanin kera kwamfuta suka cafke, inda aka kirkiri na'urar dabba'a bayanai mai amfani da hasken leza ita ma. Wannan na'ura ita ake kira Laser Printer, kuma har yanzu ana amfani da su wajen dabba'a bayanai.

Tun bayyanar wannan hikimar ta sarrafa haske don amfanin al'umma, an samu fannonin rayuwa da dama da suke amfani da ita wajen kere-kere, da yanke-yanke, da huje-huje, ko jone-jone. Wannan kafin samuwar haka a fannin likitanci kenan. Misali, manyan masana'antun kere-kere na amfani da wannan fasaha wajen yin waldan karafa. Bangaren soji kuma na amfani da shi wajen gano inda abokan gaba suke a lokacin yaki, da darkake abokan gaba. A fannin tsaro ma ana amfani da wannan tsari na fasahar leza. Da shi jami'an tsaro ke amfani wajen gano tambarin yatsun masu laifi, da tsarin gano masu laifi ta hanyoyin kimiyyar sadarwa na zamani. A fannin binciken kimiyyar sararin samaniya ma akwai tsarin fasahar leza. Galibin masu binciken kimiyya a halin yanzu na kan habbaka wannan fasaha ne don yin amfani da ita wajen tafasa sinadaran Yuraniyon, wanda makamashi ne mai muhimmanci wajen kera makamin nukiliya. Sannan malaman kimiyya a jami'o'i suna amfani da fasahar hasken leza wajen gudanar da bincike ta hanyoyi da dama. Idan muka koma bangaren bukukuwa da shakatawa, nan ma akwai hannun wannan fasaha wajen kayatar da jama'a. A kan yi amfani da wannan haske cikin yanayi mai ban sha'awa, a kawata wuraren biki da shi. A halin yanzu da masu bincike suka fara tunanin hanyoyin sawwake matsalolin da ake fuskantan cikin tsarin tiyata a asibitoci, sai tunannin wannan fasaha ta hasken leza ta fado musu.

Amfani da Hasken Leza a Fannin Likitanci

Kamar yadda bayanai suka gabata, akwai fannonin rayuwa da dama da ake amfani da wannan fasaha mai matukar tasiri. A dukkan fannonin nan kuwa, ana amfani da fasahar ne a irin yanayin da ya kamaci abin da ake son samarwa ko kawarwa ko gyattawa. A fannin likitanci ana amfani da wannan fasaha wajen yin tiyata a saman fatar fuska da sauran bangaren jiki, kan abin da ya shafi cututtukan fata ko wani abin da ke makale a jikin fatar. Wannan fanni shi ake kira Laser Skin Surgery. Bayan shi, akwai kwararru kan fannin likitanci masu lura yin wannan aiki (watau Dermatologists), tare da amfani da wannan fanni har wa yau wajen gyaran fatan jiki don ado, watau Cosmetic Laser Surgery kenan. A kan yi amfani kuma da wannan fasaha wajen gyaran hakora; masu kogo ne, ko masu girgidi, ko kuma namar da ke rike da hakora. Sannan akwai tiyatar koda da ake yi da wannan fasaha ta hasken leza, watau Laser Kidney Stone Surgery kenan. Wannan shi ake amfani da shi wajen narkar da tsakuwan da ke cikin koda, ko duk wani dunkulalle ko daskararren abin da ya toshe hanyoyinsa.

Bayan haka, a kan yi amfani da hasken leza wajen aiwatar da tiyata a cikin idanu. Wannan ma shi ne fannin da ya fi shahara a bangaren likitanci. Shi yake sawwake aiwatar da tiyata cikin idanu ba tare da wasu matsaloli ba. Akwai kuma tallafin da wannan fasaha ta hasken leza ke bayarwa wajen goge zanen haihuwa da ake wa mutane (watau Birth marks), da zane-zanen jiki irin na zamani da galibin turawa ke yi a yanzu, watau Tattoos. A takaice dai, wanann fasaha ta hasken leza na taimakawa matuka wajen sawwake da yawa cikin matsalolin da ake fuskanta a bangaren tiyata a bangarorin jiki irinsu kunnuwa, da idanu, da fatan jiki, da koda, da dai sauransu. Duk wata kafa ta jiki da ke lungu sosai, wacce sai an wahala kafin a kai inda take, duk ana iya riskarta ta amfani da wannan haske na leza.

Wannan haske na leza ya sha bamban da sauran haske da muka saba mu'amala da su a rayuwarmu ta yau da kullum. Sauran nau'ukan haske sukan bazu ne da zarar sun fito daga muhallinsu. Wannan tsari shi ake kira Light Scattering. Kamar yadda hasken rana ke bazuwa, ta game dukkan ilahirin wurin da take haskawa. Amma hasken leza ya sha bamban. Wannan nau'in haske yana tafiya ne a tafarki guda daya tilo. Misali, idan kofar fitarsa kamar kofar allura ce, da zarar ya fito, a wannan yanayin na sirantaka da kaifi zai ci gaba da tafiya, har sai ya isa zuwa inda aka cilla shi, ba tare da karfin hasken, da kaifinsa, da sirantakarsa sun ragu ba. Bayan haka, kowane haske yana zuwa ne da iya karfin iska ko zafin da aka yi gejinsa kafin fitowarsa, kuma idan ya fito, duk iya nisan tafiyar da zai yi, wannan gwargwadon zafi ba zai ragu ba. Wannan ke bashi tasirin shiga lungu-lungu, sako-sako, don baiwa mai mu'amala da shi damar gani ko taba nama, ko jijiya, ko wani yadin da ke karkashin fatan jikin dan adam. Akwai yanayin da ke fitar da haske kai tsaye, don kona wata fata ko yanke ta. Akwai wanda ke fito da ballin haske (watau Light Pulses), akwai kuma mai fitowa a launuka daban-daban.

Tsarin Tiyata

Saboda saukin mu'amalar da ke tattare da hasken leza wajen tiyata, da zarar an hasko shi saman fatar jiki, sinadaran da ke cikin hasken kan narke cikin ruwan da ke cikin fatan, nan take. Kamar yadda muka sani, abin da yafi komai yawa a jikin dan adam shi ne ruwa. Wannan haske zai narkar da sinadaransa ne cikin ruwan da ke fatan jiki, daga nan kuma ya hade da sinadaran da ke samar da jinni, watau Hemoglobin, da Melanin.

Wannan haske na leza ne ke shiga cikin fata, ya kona duk kwayar cutar da ke cikinsa, ko ya bayar da damar rede matattaciyar yadin (watau Tissue) da ke tsakanin nama da fatar jiki. Da wannan haske har wa yau ake amfani wajen haska cikin kodar dan adam, don gano inda tsakuwa suke. Da zarar an hasko su, sai a cilla haske mai matukar zafi don narkar da wadannan duwatsu da ke cikin kodar ba tare da an keta kodar ko fatan jikin mara lafiya ba. Dangane da magance matsalolin hakora, akan yi amfani da wannan haske wajen haskawa ko leko inda matsala take a hakoran mara lafiya. Ana amfani da wannan haske har wa yau don cire gashin jiki, ko na kai, ko na wasu bangarorin jikin dan adam.

Su ma nau'ukan zanen haihuwa ko zanen sha'awa da wasu ke yi a jikinsu, a yanzu an gano cewa da hasken leza duk ana iya goge su ko share su har abada. Idan muka koma bangaren gyaran fatan jiki ma haka abin yake. Da wannan haske ake amfani wajen baje dukkan kurajen da ke fuska (irinsu kyasbi da sauransu) ko kurajen baya ko kuma tamojin da ke bayan yatsun tsofaffi. Dukkan wadannan na karkashin tsarin amfani da hanyoyin tiyata don gyaran jiki, watau Laser Cosmetic Surgery. A karshe, a yanzu ma an gano cewa za a iya amfani da wannan haske na leza wajen kankare sinadaran da ke jikin wanda ya kamu da ciwon shan tabar sigari ko tabar wiwi a misali. Hakan na yiwuwa ne ta amfani da wannan haske don hasko muhallin da wadannan sinadarai suke, da kuma yin amfani da hasken wajen baje su ko narkar da su, su zama ba su da wani tasiri a jiki. Bincike ya nuna cewa ana samun nasara kashi 80 cikin 100 kan wannan matsala. Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba, hakan ya danganci yanayin jiki ne, da kuma zurfin jarabtuwa da tabar ga mara lafiya. Don haka, gwajin da za a yi wa mara lafiya kafin a fara aiwatar da wannan tiyata, shi zai tabbatar da cin nasara ko rashinsa.

Amfanin Hasken Leza

Masana fannin likitanci sun tabbatar da cewa wannan sabuwar fasahar tiyata ta hasken leza na da fa'idoji masu yawa wajen saukake tsarin tiyata, musamman tiyatar idanu, da na koda, da na fatan jiki, da cire gashi da dai sauran fannonin da wannan fasaha ta shafa. Amfani na farko ita ce saurin warkewa. Sun tabbatar da cewa lallai ana samun saurin waraka idan aka yi amfani da hasken leza wajen tiyata, idan aka kwatanta tsawon kwanaki ko lokacin da mara lafiya ke dauka kafin ya warke daga tiyatar da aka masa ta amfani da wukaken tiyata. Domin a bangaren fasahar hasken leza, akwai tiyatar da za a yi wa mara lafiya a rana guda, kuma ya mike a ranar ya ci gaba da harkokinsa. Illa dai za a bashi magunguna ne da zai rika sha.

Fa'ida ta biyu ita ce rage yawan kamuwa da wasu cututtuka a yayin tiyata. Kamar yadda muka sani, da yawa cikin wadanda ake wa tiyata ta amfani da wukaken tiyata kan kamu da wasu cututtuka, saboda fede fatan jiki ko cikinsu da ake yi da wukar tiyata. Wannan ke sa a dauki tsawon lokaci ana shan magani bayan an yi tiyatar. To amma idan aka yi tiyata da fasahar hasken leza, hakan kan rage yawan kamuwa da wasu cututtukan daban, watau Infection. Daga cikin fa'idojin amfani da fasahar hasken leza wajen tiyata har wa yau, akwai rashin zuban jini. A bangaren amfani da wukaken tiyata a kan samu zuban jini sanadiyyar fida da ake yi. Amma a tsarin amfani da fasahar hasken leza kuwa babu wannan matsalar. Domin akwai tiyatar da za a yi wa mutum, daga farko har karshe ba a zubar da jini ba. Saboda hasken na shiga cikin fata ne, yana iya yanke fatan ma ba tare da jini ya zuba ba ko kadan. Wannan na daga cikin fa'idoji masu muhimmanci.

Fa'ida ta gaba ita ce rage yawan rauni ga mara lafiya. Duk da cewa amfani da fasahar hasken leza wajen tiyata akwai zafi, amma kuma yana rage yawan raunuka da mara lafiya ka iya samu a yayin da ake ta fede shi ta amfani da tsarin aiwatar da tiyata da wukaken tiyata. Maimakon a yi ta yanke fatan ana kutsawa cikinsa don isa zuwa ga wata gaba da ake son aiwatar da aiki a cikinta ko a kanta, a tsarin fasahar hasken leza sai dai sinadaran haske su kutsa cikin fatan, har su isa zuwa ga gabar da ake son aiwatar da aikin a cikinta ba tare da an yi wa fatar rauni ba.

Fa'ida ta karshe ita ce, wannan fasahar haske ta leza tana da saukin sha'ani wajen aiwatar da tiyata ko samar da waraka a fannin likitanci, ta kowace fuska idan aka duba. Saukin sha'ani wajen yin tiyatar; saukin sha'ani wajen samar da waraka nan take (domin ana iya yi wa mutum tiyata da wannan sabuwar tsari, cikin awanni biyu ya mike ya kama harkokinsa). Sannan ga saukin sha'ani wajen mu'amala da gabobin jikin mara lafiya ba tare da an kutsa inda bai kamata ba a yayin tiyatar.

Wasu 'Yan Matsaloli

Kamar dai duk wani abin amfani ne, wannan fasaha ta hasken leza na da nata fa'idoji da kuma 'yan matsaloli wadanda ba za a rasa ba. Daga cikin 'yan matsalolin da ke tattare da wannan fasahar tiyata ta amfani da hasken leza akwai dan Karen tsada. Aiwatar da tiyata ta amfani da wannan sabuwar fasaha na bukatar kudi mai dimbin yawa, da kuma kwarewa. Saboda ba kowane likita bane zai iya aiwatar da tiyata ta amfani da wannan fasaha ta hasken leza. Abu na biyu kuma shi ne rashin yaduwa. Ba ka safai ake samun wannan fasaha a kasashe masu tasowa ba. Galibi sai kasashen Turai. Wannan yasa abin yayi tsada. Idan an samu a kasashe masu tasowa ma sai ka ga a asibitoci masu zaman kansu ne, kuma dole ya yi tsada. Har wa yau, duk da cewa amfani da wannan fasaha ta hasken leza na rage kamuwa da wasu cututtuka sababbi, a daya bangaren kuma akan kamu da wasu cututtuka masu alaka da sinadaran hasken, idan ba a dace ba.

Nau'ukan Fasahar Hasken Leza

Akwai nau'ukan hasken leza kala-kala. Na farko shi ne nau'in hasken leza mai dauke da sinadaran iska wanda ake kira Carbondioxide Laser (CO2 Laser). Kamar yadda bayanai suka gabata a baya, wannan fasaha ta hasken leza na dauke ne da haske da kuma iska, watau Gas. Wannan nau'in hasken leza mai suna CO2 Laser yana taimakawa ne wajen yanke fatar jiki ba tare da jini ya zuba ba. Kuma da shi ne ake yin tiyata don cire kwayoyin cutar da ke haddasa kuraje a cikin fatan jiki. Har wa yau ana amfani da shi wajen cire kwayoyin cutar sankara ko kansa (watau Cancerous Diseases). Saboda nau'in haske ne mai karfi, mai kaifi, kuma mai dauke da sinadaran haske masu zafi.

Nau'in hasken leza na biyu shi ne wanda ake kira ERBIUM Laser. Wani irin haske ne mai fitowa a hankali, ya shiga fatar jiki a hankali cikin natsuwa, sannan ya narke cikin ruwan jiki nan take, yana barbazuwa babu kakkautawa. Da wannan nau'in hasken leza ne ake iya rede matacciyar yadin fatar jiki (watau Skin Tissue), da irin fatar da zafin hasken rana ta kashe, daga jikin tsofaffi. Har wa yau akan yi amfani da wannan nau'in haske wajen cire rubabbiyar yadin fatar jiki (watau Dead Tissue) sanadiyyar kamuwa da kwayoyin cuta. Bayan haka, akan yi amfani da wannan nau'in haske don share kurajen fuska, irinsu kyasbi da sauransu.

Nau'in hasken leza na gaba shi ne wanda ke fitar da haske launin rawaya ko ruwan kwai, watau Yellow Light Laser. Wannan nau'in haske yana fitar da gajerun ballin haske ne launin rawaya, ko Short Pulses of Yellow-Color. Wannan launin hasken leza yana shiga cikin ruwan jiki ne, ya saje da launin sinadaran da ke samar da jini; ko Hemoglobin ko Melanin. Ana amfani da wannan launin hasken leza ne wajen magance matsalolin jijiyoyin bangarorin jiki. Ana kuma amfani da shi don goge jajayen tsagar jiki, watau Red Birth Marks.

Launin hasken leza na gaba shi ne launin hasken leza ja, watau Red Light Laser. Wannan nau'in hasken leza shi ne wanda ake amfani da shi wajen share ko goge tamojin yatsun hannu masu bayyana sanadiyyar tsufa ko yanayin zamantakewa a wani muhalli. Launin hasken leza ja shi ma yana fitowa ne da gajerun ballin haske, amma masu dauke da dimbin sinadaran haske masu yawa, don aiwatar da aikin cikin sauki. Hakan kuma na samuwa ne ta hanyar wani tsarin amfani da haske mai suna Q-Swtiching, a turancin kimiyyar lantarki.

No comments:

Post a Comment