Mabudin Kunnuwa
Na tabbata masu karatu sun ji ko ma sun karanto daga kafafen yada labaran gida da na waje kan batun ambaliyan danyen mai da ya faru a tekun Meziko na kasar Amurka. Kamar yadda muka sha jin labarai, wannan ambaliya ko hadari ya fara ne tun cikin watan Afrailu, amma ba a samu dama da ikon tsayar da shi ba sai cikin watan Agusta. Wannan ambaliya na danyen mai ya haddasa barna mai yawa, da hasarar rayukar dan Adam da na dabbobi tudu da na teku, da kuma hasarar dukiya da na gurbatar yanayi wanda mummunan tasirinsa na iya daukan tsawon shekaru ana fama da shi.
Wasu cikin masu karatu sun nuna sha’awar jin kwakwaf kan yadda wannan lamari ya faru, da tasirinsa ga muhalli, da kuma cewa ko za a iya sarrafa gurbataccen man da aka yade daga saman tekun ko a a? Kafin wannan bukata ta masu karatu, shafin Kimiyya da Kere-kere ya yanke shawarar kawo bayanai masu nasaba da hakan tun sa’adda da wannan matsala ta fara aukuwa. To amma ganin cewa matsalar ta ci gaba babu kakkautawa, sai na dakata don ganin inda abin zai kai. Domin wannan ne zai bamu damar kawo bayanai ba ma kan wannan ambaliya na tekun Meziko ba kadai, a a, har da tarihin asali da kuma sau nawa aka samun irin ambaliya na danyen mai a cikin teku? Wannan, da ma sauran bayanai ne na debo mana daga rumbun bayanai na duniya, don mu amfana, tare da kara gejin ilminmu kan ire-iren wadannan ambaliyoyi da ke faruwa lokaci-lokaci a tekunan duniya. Sai a biyo mu sannu a hankali.
Tarihin Ambaliyan Danyen Mai a Duniya
Ambaliyan danyen mai a cikin teku, ko “Marine Oil Spill” a harshen Turanci, ya fara aukuwa ne sama da shekaru hamsin a tarihin duniya. Duk da cewa ambaliyan danyen mai a jumlace ya shafi cikin teku da kan tudu, za mu mayar da hankalinmu ne kan tarihin ambaliyansa a cikin teku kadai, don shi ya fi hadari da wuyan sha’ani, kuma shi ne wanda ya fi daukan hankali a duniya.
A tarihin duniya an samu aukuwar ambaliyar danyen mai a saman teku sau goma sha biyar, tare da hasarar dukiya mai dimbin yawa ga kasa ko kamfanin da abin ya shafa; bayan hasarar rayukan dan Adam da na dabbobin da ke karkashin da harabar tekun. Cikin wadannan ambaliya guda goma shabiyar, akwai biyar daga cikinsu wadanda suka shahara sanadiyyar yanayin aukuwarsu. Na farko shi ne ambaliyan daya auku a Tekun Meziko (watau The Gulf of Mexico) da ke Kudancin Amurka, karo na farko. Wannan ambaliya ya auku ne a ranar 3 ga watan Junin shekarar 1979, inda aka ya tuttudar da danyen mai (watau Crude Oil) kimanin Tan 480,000 (480,000 metric tonnes). Cikin jerin ambaliyan danyen mai masu hadari da aka yi a duniya, wannan shi ne na farko da ya dauki hankalin duniya, kamar yadda aukuwansa na biyu cikin watannin Afrailu zuwa Agusta ya yi a wannan shekara. Ambaliya na biyu da ya fi kowannen hadari shi ne wanda ya auku a Tekun Tsibirin Trinidad & Tobago, a ranar 19 ga watan Yulin shekarar 1979; wata guda kenan bayan aukuwar na Tekun Meziko, kamar yadda bayanai suka gabata a sama. Wannan ambaliya kuma ya tuttudar da danyen mai kimanin Tan 287,000 (287,000 metric tonnes) zuwa cikin tekun Atilantika da ke makwabtaka da tsibirin.
Sai karo na uku da ya fi kowanne shahara sanadiyyar dimbin hasarar da aka tafka. Wannan ambaliya ya auku ne a Tekun Fasha (Persian Gulf), sanadiyyar ambaliyar danyen mai da aka samu daga rijiyoyin mai na kasar Kuwaiti. Hakan ya faru ne a ranar 23 ga Janairun shekarar 1991, inda rijiyoyin man suka tuttudar da danyen mai da kimarsa ta kai Tan 1,500,000 (1,500,000 metric tonnes) zuwa cikin tekun. Dangane da yawan danyen man da aka rasa, wannan ambaliya ne na daya a duniya. Domin har yanzu ba a samu ambaliyan da ya haifar da hasarar danyen mai mai dimbin yawa irin wannan ba a duniya. Sai kuma ambaliya na gaba, wanda ya auku a tekun da ke makwabtaka da kasar Uzbekistan; can nahiyar Asiya ta Gabas kenan. Shi kuma ya auku ne a ranar 2 ga watan Maris din shekarar 1992, watau shekara guda kenan da aukuwar na kasar Kuwaiti. Kamar wadanda suka gabace shi, shi ma ya haifar da hasarar danyen mai zuwa cikin teku da muhallinsa wanda kimarsa ta kai Tan 285,000 (285,000 metric tonnes). Sai ambaliya na karshe da ya auku baya-bayan nan, watau daga watan Afrailu har zuwa watan Agustan wannan shekara. Kamar yadda masu karatu suka karanta ko ji a kafofin watsa labarai, wannan lamari ya auku ne a cikin Tekun Meziko (The Gulf of Mexico) da ke Kudancin Amurka, kuma a Tarihin kasar baki daya, shi ne ambaliyan da ya fi kowanne wajen hasara.
Wannan ambaliya ya samo asali ne sanadiyyar rubewar da karafunan hako danyen mai na kamfanin British Petroleum (BP) suka yi. Wadannan karafunan hako danyen, watau Oil Drilling Rigs, suna can cikin rijiyoyin hako man ne da ke karkashin teku, wanda aka kiyasta nisan zurfinsa cewa ya kai kilomita 150. Cikin watan Maris ne kamfanin ya fara da lura da wani irin hayaki mai dauke da sinadaran Methane da ke fitowa ta hancin wadannan bututun hako mai. To amma bai dauki wani matakin gaggawa ba sai ji yayi bututun sun fashe, kuma nan take wuta ta kama ci ganga-ganga. Duk da cewa ‘yan kwana-kwana sun kawo dauki nan take, inda aka yi ta kokarin kashe wutan da tuni ya kama babbar injin da ke rike kuma take sarrafa wadannan bututun, ta yi ta ci da wuta ita ma. Da kyar dai aka kashe wannan gagarumar gobara da ta tashi. Kuma duk da cewa an samu kwashe ma’aikatan kamfanin da ke sarrafa wannan inji, amma akwai mutane goma sha bakwai da aka kasa gano inda suke. Ga dukkan alamu dai gobarar ta afka da su, ko kuma a kalla ta tilasta musu fadawa cikin teku ba tare da shiri ba.
Gama kashe wutan ke da wuya sai danyen mai ya fara tudadowa daga rijiyoyin mai da ke can karkashin teku, sanadiyyar fashewar bututun da ke zuko mai daga cikinsu. Wannan ta sa kallo ya koma kasa, bayan kashe gobarar da ta taso. Daga nan danyen mai ya ci gaba da tudadowa a kullum, inda a karshe ya tudado da danyen mai har Tan 574,000 (574,000 metric tonnes) zuwa cikin tekun. Kamfanin British Petroleum ya kashe sama da Dala Biliyan Hudu wajen yade wannan danye ko gurbataccen mai da ya yadu a saman teku, bayan lokaci da kuma danyen man da ya bata ko ya yi hasararsa.
Illolin Ambaliyan Danyen Mai
Wannan ambaliya da ke faruwa a lokuta daban-daban a tekunan duniya na da mummunar tasiri ga rayuwar jama’a da halittun da ke rayuwa cikin tekun, da kuma muhalli gaba daya. Da farko dai yana kyau mai karatu ya san cewa da mai da ruwa ba su haduwa. Duk lokacin da wani ya shiga wani, to dole ne a gane, domin ba su taba hadewa waje daya. Wannan shi ne abin da binciken Kimiyyan sinadarai ya tabbatar. A duk lokacin da aka samu cakuwarsu da juna, to mai ne ke kasancewa a saman ruwa. Bayan haka, tasirin mai a saman teku yana da gamewa sosai, saboda tasirin sinadaran da yake dauke da su.
Idan danyen mai ya game cikin ruwa, yakan haifar da maski – abin da a harshen Kimiyya ake kira “Mousse”. Wannan maski zai yi ta yawo ne a saman ruwa, tare da lakewa a jikin duk abin da ya ci karo da shi. Saboda tasirin gamewa da mai yake dauke das hi, an kiyasta cewa idan aka zuwa mai galan guda a cikin teku, yana iya game fadin eka uku zuwa biyar na saman tekun. Sannan idan ya kama shawagi, zai game jiki ko gashin dukkan dabbobin da yayi karo dasu ne, tare da lakewa a jiki ko fikafikansu. Wannan ke kara musu nauyi, har a karshe su kasa tashi, su yi ta nitsewa cikin tekun, har mutuwa ta cin musu. Bayan haka, idan kifaye suka hangi wannan maski na yawo a saman teku, nan take suna iya cafke shi har su hadiye, suna zaton abin ci ne. Idan kuwa suka hadiye shi, to nan take zai fara musu illa, ta hanyar haifar da wasu nau’ukan guba a cikinsu. Idan kuma ya gangara zuwa can karkashin tekun (watau Ocean Floor), sai ya bata dukkan abincin da suka tara.
Daga cikin illolin wannan danyen mai a saman teku har wa yau, akwai toshe hanyoyin shakar iska da halittun cikin ruwa ke amfani da su wajen numfasawa. Idan kuma maskin ya lake musu a jiki, yakan kashe musu garkuwan jikin (watau Immune System) da ke basu kariya daga cututtukan muhallin da suke rayuwa cikinsa. Sannan yana hargitsa musu tsarin hayayyafa, tare da gurbata dukkan kwayayen da suke jiran kyankyasa. A wasu lokuta a kan samu iska mai karfi ko kuma taguwar ruwa da ke hankada wannan maski na mai zuwa gabar teku, inda yake lakewa a jikin dukkan ciyayin da ke gabar, tare da gurbata abincin dabbobin wannan bigire. Idan kuma a gefen tsibiri ne ambaliyan ya auku, wannan maskin mai na iya daskarewa a karkashin tsibirin na lokaci mai tsawo, kuma dukkan kifayen da ke neman abinci a wannan bigire suna iya kamuwa da cuta sanadiyya cakuduwarsa da dukkan nau’ukan abincinsu da ke wajen. Idan kuwa haka ta faru, to, akwai jin tsoron wadannan kifaye suna iya harban dukkan sauran halittun da ke rayuwa tare da su cikin tekun, musamman ma manyan kifaye da zasu ci wadanda suka harbu, ko kuma manyan halittu irin su kada ko tsuntsayen da rayuwa a gaban tsibirin, masu cin kifaye. Wannan tsari na yaduwar cuta daga wata halitta zuwa wata halittar, shi ake kira “Cycle of Poisoning” a harshen Kimiyya.
A karshe, mummunan tasirin wannan maski da ke kwanciya a saman ruwa bai tsaya kan halaka dukkan dabbobin da ke rayuwa cikin tekun kadai ba, hatta dan Adam yana iya kamuwa da wasu cututtuka. Misali, bincike ya nuna cewa mata masu ciki na iya kamuwa da cuta idan suka shaki doyin wannan maski. Haka kuma masu ciwon da ke da alaka da numfashi su ma suna kamuwa da karuwar cututtuka. A karshe, bincike ya sake tabbatar da cewa sinadaran da ke cikin wannan maski da suka hadu da ruwa, suna iya hadda cutar kansa (Cancer) ga dan Adam muddin ya shake su.
Ina Amfanin Gurbataccen Man?
Da ma zasu so sanin shin, wannan gurbataccen mai da ake yadewa daga saman teku – ganin cewa asalinsa danyen mai ne mai dauke abubuwa da dama – ko za a iya sarrafa shi don yin abu ko tace shi don amfani da sinadaran da ke cikinsa kuwa? Wannan tambaya ce Malam Kimiyyar sinadara suka tabbatar da rashin yiwuwan hakan. Sun nuna cewa tunda har man ya riga ya cakudu da ruwa, to ya riga ya lalace kenan. Kuma ma bayan nan, sau tari ba a rasa tarkacen cikin teku da aka yado su tare da wannan gurbataccen mai, wanda kuma asalinsu ko dai ciyayi ne, ko ruwa, ko kuma tabo da kasar lakar da aka debo su tare. Bayan haka kuma, akwai sinadaran gishin ruwan teku da ke cakuduwa da man, wanda kumake rage masa karfi da karsashinsa. Wannan cakudadden danyen mai dauke da wasu ababe daban, shi ake kira “Chocolate Mousse”. In kuwa haka ne, ashe babu yadda za a yi a tace su. Domin dai mai ba zai taba yin aikinsa ba idan akwai ruwa a cikinsa, ko tabo, ko kuma duk wani abin da ba daga asali daya suka fito ba.
Wannan tasa a kasashen Turai misali, bayan an gama redo wannan maski na danyen mai daga saman teku, sai a tara shi waje daya, sannan a rika cike hanyoyi da su, ko kuma wasu bangarorin kasa da suka rifta. Hakan na da tasiri sosai wajen tabbatar da cikon da aka yi, domin wannan cakudadden danyen mai da ke dauke da ruwa da sauran karikitai, ba ya afkawa a duk inda aka yi ciko da shi. Domin haduwa yake yi da wadannan karikitai, ya sandare a karkashin kasa. Ya koma inda ya fito kenan.
Kammalawa
Kamar yadda bayanai suka gabata, ambaliyan danyen mai wani abu ne da wannan duniya ta fara jarabtuwa da shi tun ba yau ba, kuma aukuwansa na yin mummunan tasiri kan muhalli baki daya, da masu rayuwa a cikinsa. Duk da cewa ci gaban kere-kere a duniya ya samar da wasu sinadai da kuma hanyoyin narkar da wannan gurbataccen mai a saman teku, har yanzu ba a raja’a wajen amfani da wannan sinadari na musamman ba, domin bincike ya nuna cewa yana iya cutar da ma’aikatan da ke amfani da shi. Kuma cikin ambaliya goma shabiyar da aka taba yi a tekunan duniya, babu wanda ya haifar da hasara mai dimbin yawa irin na tekun Meziko da ya auku a watannin baya. Saboda an rasa rayukan mutane, da dabbobi, da hasarar danyen mai, da kudi, da kuma lokacin aiki mai dimbin yawa, irin wanda ba a taba yi a baya ba.
No comments:
Post a Comment