Mabudin Kunnuwa
Makonni uku kafin Nijeriya ta cika shekaru hamsin da samun ‘yancin siyasa daga kasar Burtaniya da ta mallake ta na tsawon shekaru kusan dari, Sashen Hausa na Rediyon BBC ya gayyace ni don wata hira ta musamman kan ci gaban da kasarmu ta samu tsawon shekaru hamsin tun samun ‘yancin kai, a fannin Kimiyyar Sadarwa, watau Information & Communications Technology (ICTs). Malam Ibrahim Isa, wanda ya jagoranci wannan hira a madadin gidan rediyon, yana son in sanar da al’ummar kasar nan ne irin halin da muka baro a baya a fannin sadarwar tarho, da kwamfuta, da kuma samuwar Intanet, da halin da ake ciki yanzu, da kuma cewa ko nan gaba kasar nan na iya jagorantar kasashen Afirka a fannin sadarwar wayar salula da kwamfuta da Intanet, da kuma amfani da Tauraron Dan Adam wajen ciyar da al’umma gaba a fannonin ilimi, da likitanci, da sadarwa, da shugabanci. A cikin wannan hira, wacce ta dauki tsawon mintuna goma a takaice, na tabbatar da halin da muke ciki iya gwargwado, da irin kokarin da gwamnati ta faro a baya, da kuma abin da take kan yi a yanzu. A karshe dai, kamar yadda na san da yawa cikin masu karatu suka ji (saboda sakonnin tes da kira da na samu), na tabbatar da cewa har yanzu Nijeriya bata kai ko ina ba a wannan fanni. Wannan hukunci zai tabbata ne idan muka gwama kasarmu da sauran kasashen Afirka, wadanda muke nahiya daya da su, ba wai da wasu kasashen da suke nesa ba.
To amma duk da haka, wannan ba ya nuna cewa bamu yi wani kokari ba, musamman idan muka dubi halin da a baya muka baro. Duk da cewa wannan kasa ba ta da wani tabbataccen tsarin samar da ci gaba a fannin kimiyar sadarwar zamani kafin shekarar 2000, amma da Shugaba Olusegun Obasanjo ya dare karagar mulki ya kafa wani kwamiti da yayi nazari ya kuma fitar da shawarwari masu kayatarwa na yadda za a mayar da kasar nan gagarabadau a fannin kimiyyar sadarwa ta zamani, ba a nahiyar Afirka ma kadai ba, har a sahun kasashen duniya baki daya; kafin shekarar 2010. Wadannan shawarwari sun hada da samar da hukuma mai zaman kanta wacce za ta lura da wannan aiki baki dayansa. Wannan hukuma ce za ta zama sila tsakanin tsare-tsaren gwamnatin tarayya a daya bangaren, da na jihohi da kuma na kananan hukumomi. Ta hanyar wannan hukuma, za a ilmantar da jama’ar kasa yadda za su iya amfani da hanyoyi da kayayyakin sadarwa na zamani, za a samar da runbunan adana bayanai a dukkan bangarorin uku, za a samar da gamammen tsarin sadarwa ta Intanet, wanda zai hada dukkan makarantun kasar nan – jami’o’i da sakandare da kuma firamare – da asibitoci, da cibiyoyin binciken kimiyya da kere-kere, da jami’an tsaro, da jami’an shigi-da-fici (kwastan da magireshon) da sauransu.
Bayan haka, shawarwarin, wadanda aka dabba’a su cikin wani kundi mai take: National Information Technology Policy, mai shafuka 52, sun wajabta wa Gwamnatin Tarayya aikin samar da kudaden shiga da kuma hanyoyin hadin gwiwa tsakanin Nijeriya da wasu kasashe da suka ci gaba a wannan fanni. A takaice dai, wannan kundi na dauke ne da shawarwari mafi kayatarwa, wadanda da zarar an dabbaka kashi sittin cikin dari, ba ma dukkansu ba, kasar nan za ta ci gaba a wannan fanni, har ma ta zama abin koyi. To amma kaico! In ka kebe hukuma guda daya da aka kafa mai suna National Information Technology Agency (NITDA), wacce har yanzu take fama da matsalolin kudaden gudanar da aiki, babu abin da aka yi. Sai cikin watan Mayun wannan shekara ne gwamnati mai ci ta sake kafa wani kwamiti da yayi bitar “ci gaban” da ake tsammanin an samu a baya, sannan ya sake fitar da wani kundi mai take: “ICT 4 Development”, watau “Ciyar da Nijieriya Gaba ta Hanyar Kimiyyar Sadarwa na Zamani”. Wadannan sababbin tsare-tsare dai ba su da bambanci da abin da wancan na baya ya kunsa, sai bambancin shekarun da aka haddade cewa kasarmu za ta ci gaba, har ta shallake wasu kasashen; zuwa shekara ta 2015.
Wannan hira na daga cikin dalilan da suka sa shafin Kimiyya da Kere-kere ganin dacewar gabatar da bicike na musamman kan ci gaban wannan kasa ba a fannin kimiyyar sadarwar zamani kadai ba, har da fannin kere-kere, wadanda su ne ginshiki wajen ci gaban kowace kasa a duniya. Domin ta hanyarsu ne kasa ke iya ciyar da al’ummarta har ma ta fitar da ragowar abin da ta noma zuwa wasu kasashe, ta hanyar ci gaba a fannin kimiyya da kere-kere ne kasa za ta iya hada kan al’ummarta a siyasance, ta koya musu tarbiyya ingantacciya; ta hanyar gamammiyar tafarkin sadarwa da ingantaccen rumbun bayanai na kasa. Har wa yau, ta hanyar inganta wadannan fannoni ne hukuma za ta iya samar da kyakkyawar hanyar bayar da ilmi – daga matakin farko har zuwa kololuwa – ga dukkan al’ummarta. Ta hanyar bunkasa wadannan fannoni guda biyu hukuma na iya samar wa al’ummar kasarta dukkan ababen da suke bukata a fannin kere-kere; daga kayayyakin amfanin gida, zuwa ababen hawa irinsu jiragen sama, da na ruwa, da motoci, da babura, da kuma kekuna. A daya bangaren kuma, tana iya amfani da wadannan fannoni wajen rage yawan sace-sace, da kashe-kashe, da dukkan wasu ayyukan assha a kasa. Samuwa da yiwuwar dukkan wadannan ababe a kasa irin Nijeriya ba wani abu bane mai wahala in Allah ya yarda.
Hakika ina sane da yadda galibin ‘yan Nijeriya suke yanke kauna a kullum dangane da yiwuwar ci gaba a wannan kasa tamu ta kowane bangare. Sai dai abin da nake gaya mana shi ne, kowace kasa da irin tafarki da kuma tsarin ci gabanta. Kamar mutane ne; tsarin jikinmu ba daya bane. Don haka yanayin girmanmu da ci gabanmu ba zai taba zama daya ba. Ana iya haifan jarirai guda biyu a rana daya, a lokaci daya, amma daya ya riga daya girma, ya riga shi yin arziki, ya kuma riga shi mutuwa in ta kama. To haka kasashe suke. Tarihinmu ya sha bamban da na sauran kasashen da suka ci gaba, hatta wadanda suke makwabtaka da mu a Nahiyar Afirka. Duk wanda ya je kasar Gana a misali, sai ya sha mamakin ganin yadda suke da tsari, suke girmama dan Nijeriya, kudinsu na da daraja, al’ummarsu na bin doka sau da kafa, jami’o’insu na da inganci fiye da namu, suna da kima a idon kasashen duniya fiye da mu, bayan haka, suna da wutar lantarki mai inganci, kuma Hukuma na girmama talakawanta, kamar yadda su ma suke girmama doka da oda iya gwargwado, da dai sauransu. Idan aka koma bangaren kimiyya da kere-kere ma, suna da kokari matuka, sannan Allah ya hore musu karfin zuciya da hazaka wajen sake-sake da kokarin sarrafa albarkatun kasa da Allah ya hore musu, duk da cewa kasarmu ta fi kasar Gana dukiya nesa ba kusa ba. A takaice dai, bunkasar Nijeriya da ci gabanta abu ne mai yiwuwa; ba dole bane ya zama yanzu-yanzu, domin gyara na daukan lokaci. Barna ce ake iya yinta cikin kankanin lokaci.
A cikin kasidun da ke tafe, za mu kawo bayanai ne kan tarihin ci gaban wannan kasa a fannin kimiyya da kere tun kafin samun ‘yancin siyasa a shekarar 1960. Sannan mu dubi halin da muke ciki yanzu; shin gaba muka ci ko baya? Idan baya muka ci (wanda shi ne galibin tunaninmu) to me ya haddasa hakan? Sannan a karshe za mu kawo jerin shawarwari daga bakin kwararrun masana kuma ‘yan Nijeriya, wadanda suka kware a fannin kimiyya da kere-kere; irin shawarwarin da muddin aka dabbaka su, to kasar nan za ta ci gaba in Allah Ya yarda. Amma kafin nan, ya kamata mu dubi dukiyar da Allah Ya hore mana na albarkatun kasa, sannan mu dora kasarmu kan wasu ka’idoji guda shida da masana harkar kimiyya da kere-kere a duniya suka yarda cewa sai kasa ko al’umma ko daula ta cika su sannan za a iya cewa ta ci gaba a wannan fanni.
Muna Da Arziki
Alal hakika duk wani dan Najeriya da ya san ciwon kanshi ya san cewa wannan kasa Allah ya hore mata tarin albarkatun kasa da na sararin samaniya. Ba wai tsabar kudade da muke samu daga cinikin danyen mai nake nufi ba; tsantsar arzikin kasa nake nufi. Bayan tarin albarkatu irinsu azurfa da zinare da tagulla da da nau’ukan karafa da Allah ya tara mana a karkashin wannan kasa tamu, ita kanta kasar da muke takawa a makare take da albarka irin ta noma. Kada mu mance, shekaru kusan sittin da suka gabata, lokacin da kasar Malesiya ta zo da kokon baranta neman irin shuka na kwakwar manja, bayan mun bata ta tafi da shi kasarta, ta shuka, wannan iri bai yi kai ba. Saboda yanayin kasarsu bai da sinadaran da wannan itaciya ke bukata. Sai da suka dawo Najeriya, suka debi kasarmu cikin jirgin ruwa, suka tafi da shi. A can ne suka gudanar da bincike mai kyau kan irin sinadaran da wannan kasa tamu ke dauke da su, sannan suka cakuda wannan kasar da suka debo daga Najeriya da nasu kasar, sannan suka fitar da wani irin kasa na musamman da zai iya baiwa wannan itaciya ta kwakwar manja sinadaran da take bukata don yin yabanya da yado. A yanzu duk duniya babu kasar da ta kai kasar Malesiya arzikin kwakwar manja. Daga tuwon siddin mota har zuwa tsantsar manjar miya, wannan kasa na sarrafawa – domin babu abin da wannan kasa ke watsarwa daga kwakwar manja. Idan har sai da kasar Malesiya ta wahala wajen tarbiyyantar da kasarta kafin kasar ta iya daukan wannan shuka, me za a ce ga kasarmu? Yanzu idan ka je Kudu, za ka samu gonakin kwakwar manja sun zama saura. Babu ruwan gwamnati da abin da ya shafi wannan sina’a. Idan mai gonar ya ga dama ya noma, ko kuma ya mayar da itaciyar zuwa tulun banmi, ya rika tatsa yana sha; ba ruwanta.
Dangane da abin da ya shafi yanayi kuma, watau Weather, Allah ya mana arziki har babu iyaka. Bayan sinadaran hasken rana da muka kasa sarrafa shi (sai dai mu shanya kayayyakinmu da abincinmu kawai), wani ma’aikacinmu ya sanar da ni cewa ya je ziyara kasar Amurka inda ya hadu da wani masanin yanayi, kwararre. Bayan sun tattauna, sai baturen ke tambayarsa daga wace kasa ya fito, ya ce shi dan Najeriya ne. Sai baturen yace masa, ai ya dade yana burin ya zo wannan kasa tamu, domin ya dade yana bincike (na karatu tsantsa) dangane da yanayin kasar. A karshe sai ya sanar da wannan aboki nawa cewa, duk wani yanayi na muhalli da ake da shi a sauran kasashen duniya, to, akwai irin shi a Najeriya. Kada mu mance cewa, a kasar nan ne kadai za ka iya shuka itaciyar tuffa (Apple) har ta fitar da ‘ya’ya sama da daya a kowane zangarniya. A sauran kasashe kwaya daya-daya take fitarwa. Wannan ke nuna tsabar albarkar da ke wannan kasa. Wani babban malamin musulunci ya bamu wani labari mai ban dariya da takaici, shekaru kusan shida da suka wuce, inda ya ce wani dan kasar Sin (Chinese) ya kama hanya zuwa kasar Abiya (Abia State) da ke Kudu maso gabashin kasar nan. Yana cikin wata tawaga ce ta ‘yan Najeriya, suna tafiya a cikin mota. Da suka fara shiga kurmi, sai wannan mutumin ya fara mamakin irin yadda Najeriya ke noma babu kakkautawa. Sai daya daga cikin ‘yan Najeriya da ke tawagar ya tambaye shi, me ya gani? Sai yace ai ya ga ko ina ya duba, sai ya ga shuki ne zalla; gaba daya kasa ta zama koriya! Bai san duk tarin ciyayi bane, wadanda ruwan sama ya tsirar da su. Daga nan sai aka sanar da shi cewa ai duk wannan tarin ciyayin Allah ne da yake ciyar da dabbobi da su, ba wai shuka su aka yi ba. Sai mamaki da bakin ciki ya kama shi nan take. Ya ce a kasarsu sai sun tarbiyyantar da kasa, sun cakuda ta da wasu dabarun kimiyya sannan take musu yadda suke so. Tare da haka, kasar Sin na cikin kasashe masu ciyar da duniya a bangaren noma. Labarai makamantan wannan ba za su kare ba. Abin da nake son kara tabbatar mana shi ne, muna da arzikin da zai iya juya wannan kasa tamu ta shallake kowace kasa ne wajen ci gaba a kowane fanni a duniya. To amma kaico, kamar yadda larabawa ke cewa: ga rakumi dauke da tulun ruwa a cikin sahara, kishirwa na gab da kashe shi, saboda bai samu wanda zai sauke masa wannan ruwa ba balle ya kwankwada. Bayan wadannan bayanai takaitattu da muka koro kan albarkatun kasarmu, shin, a wani matsayi muke yanzu?
Wasu Ka’idoji Shida
Wannan ya kawo mu ga wasu ka’idoji ko ma’aunai guda shida da za mu yi amfani da su wajen gano iya gwargwadon ci gabanmu a kimiyya da kere-kere a halin yanzu. Malaman Kimiyya da Kere-kere suka ce akwai wasu sifofi guda shida da duk kasar da ta cika su, to ba za a iya cewa ta ci gaba ba a kowane fanni ne kuwa. Siffa ta farko, idan ta kasa kera manyan injinan sarrafa abubuwa; daga nona zuwa kere-kere, misali irin su katafilolin noma da na sharan hanya, da na hako abubuwa daga karkashin kasa, da jiragen kasa, da motoci, da wasu injinan zakulo abubuwa daga kasa ko dora su a sama, to ba a kirga ta cikin sahun kasashen da suka ci gaba. Idan muka dubi Najeriya za mu ga cewa haka muke. Ko keken dinki ba na tunanin muna kera shi a kasar nan, balle na hawa, balle babur, balle mota, har a kai ga katafilar nona (tractor). Sifa ta biyu, idan kasa ta kasa hako (ba sarrafawa ake nufi ba) albarkatun da Allah ya mata daga karkashin kasa, sai ta dogara ga wasu kasashe masu taimaka mata da kayayyakin aiki da kuma ma’aikatan da za su yi mata wannan aiki, to ita ma ba za a sanya ta cikin sahun kasashen da suka ci gaba ba. Idan muka dubi wannan sifa, sai mu ga cewa daram ta zauna a kanmu. Ga kamfanonin kasashen waje can a Kudu, suna ta cin karensu babu babbaka. Ba ma harkar mai kadai ba, hatta injinan hako albarkatun kasa irinsu su zinare da azurfa, duk ba mu da mu. Galibin masu aikin kuza a Najeriya da hannunsu suke yi. Kai, hatta injinan haka rijiya daga wasu kasashe muke sayowa. Sifa ta uku, idan aka wayi gari galibin manoma a kasa suna amfani ne da hannunsu (fartanya da garma) wajen nome kasar da suke shuka a kai, to ba za a ce ta ci gaba ba. Idan muka dubi wannan ita ma, sai mu ga daram ta zauna a kanmu. Watakila mai karatu ya ce ai akwai masu amfani da katafilun noma, watau tractor. Amma mutum nawa ne? Galibin manoman Najeriya da karfin tuwonsu suke noma abin da ake ci. Wannan har a babban birnin tarayya ma haka abin yake; duk daya ne, wai makaho ya yi dare a kasuwa.
Ma’auni na hudu, idan kasa tana dogaro ne da wasu kasashe wajen sayen bangarorin mashina ko injinan sarrafa kayayyaki ko albarkatu da take amfani da su, to nan ma ba za a ce ta ci gaba ba. Ai mun gama da wannan, tunda har ta kaimu ga sayen wadannan kayayyaki daga wasu kasashe, ai dole ne mu koma gare su idan sun lalace. A takaice dai, Najeriya ba ta iya kera bangarorin manyan injinan da take amfani da su wajen sarrafa arzikinta. Sifa ta biyar, idan ya zama galibin kayayyakin da kasa ke sayarwa a kasuwannin saye da sayarwa na duniya nau’in arzikin da ta ciro ne daga kasa kai tsaye, ko ta noma kadai, bai wai sarrafaffu ko kerarrun abubuwa ba, to nan ma za a ce bata ci gaba ba. Wannan a fili yake. Tabbas muna fitar da karafa, da alminiyon, amma danyensu; domin kamfanonin da ke sarrafa su sun kwanta dama. Don haka galibin kayayyakinmu basu wuce danyen mai ba, watau Crude Oil, sai albarkatun noma, da wasu abubuwa. Sifa ta karshe, suka ce idan kasa ta kasa kera makaman da za ta kare al’ummarta da su, sai dai ta siyo daga wasu kasashe, to, nan ma ba za a ce ta ci gaba ba. Wannan ke nuna mana cewa, hatta kayayyakin kare kasa, sai mun siyo. Kuma haka ne. Amma ba wannan bane aibun, aibun na farawa ne daga lokacin da muka kasa yin wani kokari wajen ganin mun samu ‘yancin kanmu dangane da abin da ya shafi kera abubuwa irin wannan. A karshe, a tabbace yake cewa lallai har yanzu da sauranmu. Domin cikin wadannan ka’idoji ko sifofi guda shida da muka zayyana, babu guda daya da kasarmu ta ketare shi; duk sun zauna daram a kanmu. To daga ina matsalar ta faro ne?
Tarihin Ci Gaban Najeriya a Fannin Kere-kere
Hakika a bayyane yake cewa kowace al’umma na da hanyoyin da take bi wajen ciyar da kanta gaba a fannin kere-kere. Hakan kuma na samuwa ne ta hanyar fasaha da hazakar da Allah Ya hore wa dan adam. Kafin zuwan turawan mulkin mallaka kasar nan, al’ummar wannan kasa na amfani da ne da hanyoyi daban-daban da suka kirkira a fannin kere-kere. Muna kera kujerun da muke zama a kai daga bishiyoyin da Allah ya hore mana a dazuzzukanmu. Muna kera akushi, da masakai, da takalma, da zobba, da injinan saka, da na barza hatsi, da dai sauransu. Sannan muna da makera inda muke sana’anta abubuwan da muke bukata wajen noma da kiwo da zamantakewa. Makeran namu ma kala biyu ne; akwai “Farar Makera”, inda ake “Farar Kira”. A wannan makera ne ake kera tukwanen dalma, da farantan azurfa da zinare, da zabba, da dai sauran kayayyakin alatu da kyale-kyale. A daya bangaren kuma, akwai “Bakar Makera”, inda ake “Bakar Kira” don samar da ruwan garma, da fartanya, da sakatono, da magirbi, da sauran makamantansu. Dukkan wadannan abubuwa muna kera su ne ta amfani da fasaharmu da kuma itatuwa ko bishiyoyi ko duwatsun da Allah ya samar mana a muhallin da muke rayuwa. Wannan hanya ta ci gaban kere-kere, wacce turawa daga baya suke kira “Local Crafts”, ita ce hanyar da ta rike mu tun kaka da kakanni, kafin zuwan turawa. Kuma a haka muka ta rayuwa, cikin kwanciyar hankali da lumana, da kuma wadatuwar zuci.
Da Turawan mulkin mallaka suka shigo kasashenmu, sai suka zo da wasu sababbin kayayyakin kere-kere da aka kero daga kasashensu, kuma cikin karfi da yaji suka yi iya yinsu wajen ganin sun dakushe ci gaban hanyoyin da muke bi a baya don kera kayayyakin da suka same mu da su kafin zuwansu. Misali, a Arewacin kasar nan, Bature ya same mu da makera mai cike da tsari, da masaka mai cike da hikima da fasaha; ga kuma mutane masu hazaka da ke aiki a cikinsu. Kasancewar dukkan kasashe masu mulkin mallaka suna yin haka ne don amfanin kansu da kasashen da suke wakilta, nan take suka fara kokarin ganin sun kashe wadanann wuraren kere-kere da ke kasashenmu ta hanyoyi daban-daban, kamar yadda mai karatu zai karanta nan ba da dadewa ba.
Bayan sun karbi madafun iko a hannunsu, sai suka fara bullo da dokoki, suka sauya akalar ci gaban tattalin arziki, suka zo da sababbin tsare-tsaren shugabanci a kokarinsu na ganin sun tabbatar da rikonsu a kanmu. Daga nan suka gina tituna, da dogayen hanyar jirgin kasa don hade manyan biranen kasar da bakin bodar kasar. Sun yi hakan ne kuwa don amfanin kansu, kuma saboda samun saukin kwashe kayayyakin masarufi ta manyan jiragen ruwan da suka jibge a bakin gabar tekun Atilantika. A haka suka ci gaba da mulkin mallaka, suna dada fadada kasar, suna dada shuka tasirinsu, suna kuma dada debe abin da suke bukata na amfanin kasarmu don kaiwa kasashensu. Galibin wadannan ayyuka sun yi su ne da kudaden da kasar ta samar daga albarkatun noma – irinsu gyada da auduga da koko da katakai da sauransu. Bayan sun bamu ‘yancin kanmu (a siyasance), sai muka gano man fetur, daga nan sai kamfanonin hakon mai suka shigo, nan take sai kudaden shiga ya karu; musamman cikin shekarar 1973, sa’adda rikici yayi tsamari a tsakanin Falasdinawa da Kasar Isra’ila. Cikin wannan shekara kasar nan ta samu kudade masu dimbin yawa daga cinikin danyen mai, saboda kasashen Larabawa sun sanya takunkumin sayar da mai ga kasashen Yamma, don haka suka koma sayen danyen mai daga Najeriya da sauran kasashen da ke Kudancin Amurka. Da galibin kudaden da aka samu a wannan shekara ne aka gina tsofaffin Jami’o’in da ke kasar nan, da manyan gadojin da ke birnin Legas, da Kwalejin Fasaha da wasu daga cikin Cibiyoyin Binciken Kimiyya da dai sauransu. Sauran kudaden kuma aka yi gagarumin bikin al’adun nan mai taken Festac ’77, lokacin mulkin shugaba Obasanjo karo na farko. Daga wannan lokaci ne shugabannin Najeriya suka fara rasa alkibla a fannin ci gaban kasar nan, har a karshe muka samu kanmu cikin wannan halin da muke ciki. A halin yanzu ga wasu daga cikin dalilan da suka jefa kasarmu cikin ci baya ko ince rashin ci gaba a wannan fanni:
Mummunan Tasirin Mulkin Mallaka
Kamar yadda kowa ya sani daga baya, duk kasashen da suka shahara wajen mulkin mallaka a duniya sun yi hakan ne don amfanin kansu. Domin bayan kokarin da suka yi wajen kwashe kayayyakin masarufin da suka yi, sun kuma taimaka wa kamfanonin da ke kasashensu wajen tallata hajojin da suke kerawa. Hakan kuma bai yiwu musu ta dadi ba, sai da suka kirkiri dokokin da suka dakushe hanyoyin kere-keren da ke kasashen da suke mallaka. Hukumar Burtaniya ta taimaka wajen shigowa da bindigogi, da kayayyakin alatun daki, da kekunan hawa, da takalma, kai hatta ababen shaye-shaye na barasa ta taimaka wajen shigowa da su. A wasu bangarorin Najeriya – musamman kudanci – hukumar mulkin mallaka ta haramta sayarwa ko shan giyar “gwaggwaro” wacce ake tsimawa a kauyuka. Ba don komai ta yi haka ba sai don taimaka wa kasuwar barasar turai ta samu fadada. Wannan tsari na dakushe kokarin ‘yan kasa da kashe wa hajarsu kasuwa don ciyar da kasuwar hajojin kasashen turai gaba, ta yi mummunar tasiri wajen dakushe ci gaban kimiyya da kere-kere a kasar nan. A cikin littafinsa mai suna How Europe Underdeveloped Africa, Professor Walter Rodney, wani shahararren malamin tarihi da siyasar tattalin arzikin kasa na kasar Gayana, ya yi bayani filla-filla kan yadda turawan mulkin mallaka suka tsiyata al’ummar da suka mulkesu. Duk mai bukatar Karin bayani, to ya nemi wannan littafi.
Rarraunan Tsarin Karantarwa
A tabbace yake cewa hanya mafi tasiri wajen samar da ingantaccen ilmin kimiyya da kere-kere na zamani, ita ce ta hanyar ilmin zamani. Sanin haka, tare da fahimtar hazakar da Allah ya yi wa mutumin Najeriya, ta hana turawa samar da ingantacciyar tsarin ilmin zamani a kasar nan. Domin sun san cewa muddin muka cafki wannan ilmi ta hanyar da ta dace, to ikonsu ya kare a kanmu. Duk wanda yayi la’akari da manhajar karatun da muka gada daga turawan mulkin mallaka zai fahimci haka cikin sauki. Bayan kashe tsarin karatun ajami da suka yi a shekarar 1913, sun tabbatar da cewa babu wani dan kasa da darajar karatunsa ta wuce sakandare ko elamentare. Amfanin hakan ma, kamar yadda shugabannin mulkin mallakar suka tabbatar da bakinsu, shi ne don samar da kananan ma’aikata masu musu hidima a ofisoshi, da kotuna, da kuma wadanda za su rika yi musu tafinta. Ga abin da Lord Lugard yake cewa cikin shekarar 1921: “Babban manufar gwamnatin (mulkin mallaka) wajen kafa makarantun firamare da sakandare a tsakanin ‘yan kasa shi ne don ilmantar da yara masu hazaka daga cikinsu don su zama malamai a wadannan makarantu, ko akawu a kananan kotuna da kuma samar da masu tafinta a tsakaninsu.” (Lord Lugard 1921). A nashi bangaren kuma, Rev. J. C. Taylor, daya daga cikin manyan shugabannin addini karkashin gwamnatin mulkin mallaka, ya kara da cewa sun karantar da yara a wadannan makarantu ne don taimaka musu wajen kira zuwa ga addini. Don haka suka dage wajen karantar da su “A B C D.” Ya fadi hakan ne a shekarar 1857. Wannan tasa a duk tsawon zaman gwamnatin mulkin mallaka a Najeriya, in ban da Kwalejin Fasaha ta Yaba da ke Legas da aka gina don samar da kwararru “masu matsakaicin ilmi” kan fasahar kere-kere, duk sauran makarantun sakandare ne da firamare da aka kirkiro don samar da ma’aikatan ofis da masu tafinta ko kananan ma’aikatan kotu. Ko kadan gwamnatin mulkin mallaka bata damu da inganta tsarin ilmi ba balle har a samu wasu kwararru da za su motsa ci gaban kimiyya da kere-kere a kasar nan.
Tsarin Habbaka Kamfanonin Kere-kere
Bayan samun ‘yancin siyasa gwamnatin Najeriya ta yi kokarin ciyar da kasar gaba a fannin kere-kere ta hanyar samar da kamfanonin kera-kere (na motoci, da mashina, da sauran kayayyakin aikace-aikace) a gida, tare da shigowa da kayan aikin don kera abubuwan da ake bukata ba tare da dogaro kan wasu kasashe ba. Wannan tsari na ci gaban tattalin arziki mai suna Import Substitution Industrialization Policy, ya fara aiki, inda har gwamnati ta kafa masana’antun kere-kere na motoci da bangarorinsu – kamar Fiat, da Leyland da Stear - da kuma kamfanonin sarrafa karafa – irin su Kamfanin Sarrafa Karafa na Delta, da Kamfanin Sarrafa Karafa na Ajaokuta – da aka samar don kera bangarorin mota (Automobile Spare Parts). Karkashin wannan tsari har wa yau, gwamnati ta tanadi masana’antar kera manyan bangarorin injina da mashinan masana’antu. To amma saboda rashin damuwa da ci gaban kasar, haka gwamnati ta bar wadannan kamfanoni ko masana’antu da ta fara kafawa don wannan gagarumin aiki mai muhimmanci, galala, har abin ya daidaice. Domin daga baya an daina shigowa da kayayyakin da wadannan masana’antu ke bukata don ci gaba da aiki, kuma a haka suka durkushe, aka sallami ma’aikatan da ke ciki; tsarin ya mutu. A daya bangaren, kasashe irinsu Brazil da Malesiya sun ci gaba nesa ba kusa ba a wannan fanni, alhali kuma cikin lokaci daya muka faro da su.
Rashin Dabbaka Sakamakon Binciken Ilmi
Duk da tabarbarewan ilmi a kasar nan, akwai cibiyoyin bincike masu kokarin kirkiro hanyoyin samar da sababbin kayayyakin kere-kere a kasar nan. To amma saboda shi bincike wani abu ne da ake fara shi a takarda, amma a kare shi da aiki, babu abin da ya damu hukuma da ire-iren sakamakon binciken ilmi da ke fitowa daga wadannan manyan cibiyoyin binciken kimiyya. A wasu kasashe, da ire-iren wadannan sakamakon bincike ake takama, su ake dabbakawa a aikace, har a karshe a samar da sababbin hanyoyin ciyar da rayuwa gaba. Bayan wadannan cibiyoyin bincike har wa yau, akwai sakamakon binciken ilmin kere-kere da ke fitowa daga manyan malamai masu hazaka a jami’o’inmu da kuma kwalejin fasaha da kere-kere, su ma ko kadan hukuma bata damu da su balle ta yi wani abu a kai. Ni kaina sheda na kan haka. Lokacin da nake sakandare, akwai malamin fannin Fiziya da ya kera jirgin saman mai saukar ungulu, watau Helicopter babba. Duk sa’adda muka shiga dakin bincikensa don daukan darasi, wannan abu da ya kera ya kan bamu sha’awa tare da kayatar da mu sosai. Sau tari mukan yi kwadayin ina ma ace gwamnati ko wani kamfanin kera jiragen sama ya dauke shi aiki, don karasa kera wannan jirgi. To amma kaico! Haka wannan hikima tasa ta kare tsakanin aji da dakin bincikensa, har ya bar makarantar.
Rashin Damuwa a Bangaren Gwamnati
Dabi’un gwamnatin tarayya da na jihohi wajen rashin damuwa da habbaka fannin kimiyya da kere-kere a Najeriya ya dada taimakawa wajen durkeshewar wannan fanni. Ba abin mamaki bane a yanzu ka samu kowace irin mota ce a kasar nan. Duk irin wanda kake so akwai, an shigo da ita. A wasu lokuta ma, mako biyu ko uku da kera wata sabuwar mota, ka sa idonka a kan titunan kasar nan, za ka ganta tana tafiya. Wasu masu alfarmar ma aka ce kamfanin kera motocin suke zuwa don zaban irin wacce suke so a kera musu. Amma har yanzu babu wanda ya damu – daga gwamnatin tarayya har zuwa jihohi - don ganin an farfado da tsarin samar da kamfanoni da masana’antun kere-kere a kasar nan. An wayi gari galibin tsare-tsaren gwamnati wadanda suka shafi fannin kimiyya da kere-kere, da ka ake shirya su, ba tare da shawartar kwararru a wannan fanni ba. A inda aka shawarce su wajen shirya tsare-tsaren kuwa, za ka samu ba a nemansu idan aka tashi aiwatar da shirin. Wannan ke sa ka ga an kashe kudade makudai a fannin, amma sai ka nemi aikin da aka yi ka rasa. Siyasanci, da tumasanci, da ‘yangaranci, da cin hanci, da rashawa sun bata tsare-tsarenmu baki daya. Wannan ba zai haifar mana da mai ido ba ko kadan.
Kangon Makarantu
A kasa irin Najeriya ne kadai za ka samu jami’o’i a kowace jiha, da kwalejin fasaha bila-adadin, amma ka nemi tasirin ilmin ka rasa. Hakan ya samo asali ne daga irin tsarin da ake tafiyar da karatun. Domin kowace jami’a tana bukatar tallafin kudi da zai tamaka mata wajen aiwatar da bincike mai inganci, ya samar da yanayin karatu mai kyau, ya kuma taimaka wajen tabbatar da kimar ilmi. Idan ka dubi kasarmu za ka ga kusan dukkan wadannan abubuwa guda uku babu su. Bayan haka, galibin makarantunmu suna fama da matsalar wutar lantarki, da hanyoyi marasa inganci, da rashin kayayyakin aiki masu taimakawa wajen samar da ilmi mai inganci; duk babu wadannan abubuwa. In kuwa haka ne, mai karatu ya gaya min yadda za a samu dalibai masu inganci da za su yi wani abin kirki! Wani malamin jami’a a kudancin kasar nan ya taba cewa, ba abin mamaki bane ka samu dalibi mai karatun fannin fasahar kere-kere (Mechanical Engineering) a jami’armu ya kasa bambance maka tsakanin sandar noti, watau bolt, da kuma noti, watau nut.
A duniya karankaf, kasar Indiya ce ta uku a fannin ci gaban kere-kere da kimiyyar lantarki, inda take biye da kasar Amurka da Rasha. A kididdigar shekarar 2003, kasar Indiya ta mallaki kwararru kan harkar kimiyyar kere-kere da lantarki sama da miliyan hudu. A shekarar 1985 kadai ta yi rajistan Injiniyoyi 750,000. Tana da manyan cibiyoyin koyar da ilmin kimiyya da fasahar kere-kere guda biyar da take kira India Institutes of Technology, wadanda take basu tallafi mai tsoka, don karantar da ingantaccen ilmi ga ‘yan kasarta da masu shigowa daga wasu kasashe. Kasar Indiya na fitar da galibin hajojinta ne zuwa kasar Amurka da sauran kasashen Turai. A shekarar 2008 kasar Indiya ta samu dalar Amurka dala na gugar dala har sama da biliyan goma sha daya wajen sayar da manhajojin kwamfuta da ‘yan asalin kasarta suka gina kadai. Duk wannan bai samu ba sai don sadaukar da kanta da tayi wajen ganin ta inganta ilmin kimiyya da kere-kere. Wannan ne kuma yasa jami’o’in kasarta da na kasashe irinsu Malesiya da Singafo ke samun dalibai daga dukkan sasannin duniya, ciki har da ‘yan Najeriya!
Hanyoyin Ci Gaba
Hanyoyin ci gaba a fannin kimiyya da fasahar kere-kere ga kowace kasa ce, a fili suke, musamman a wannan zamani da ke cike da hanyoyin mallakar ilmi masu yawa kuma cikin sauki. Duk da cewa ba wai hanyoyin bane muka jahilta, a a, sadaukar da kai ne kawai muka rasa da kishin kai. Amma duk da haka, kogi ba zai ki dadi ba. Ga wasu daga cikin hanyoyin nan:
Nazarin Kerarrun Fasahohi Daga Waje
Akwai kayayyakin kere-kere da hanyoyin ci gaba a fannin kimiyya da suka shigo mana har muke amfani da su. Me zai hana gwamnati ta kafa cibiyoyi na musamman don yin nazari da “dubiya” kan tsari da kimtsin yadda aka kera wadannan kayayyaki? Galibin kasashen da suka ci gaba basu mallaki kwarewar da suke takama da ita ba sai ta ire-iren wadannan hanyoyi. Wannan zai taimaka mana a hanyoyi biyu; na farko shi ne za mu rika kera wadannan kayayyaki cikin sauki kuma a kasarmu, sannan kuma ‘yan kasa za su mallaki fasahar kera su ba tare da sai sun je asalin kasashen da aka kero su ba. A wasu lokuta ma idan zuwa kasar ta kama, ana iya zuwa. Ga motoci nan bila-adadin, ga kerarrun mashinan zamani, ga injinan kera abubuwa da yawa – daga na tatse lemun tsami, da gyada, da na markade da dai sauransu – duk muna iya bibiyar asalin fasahar da aka yi amfani da ita wajen kera su. Wannan ba ya nufin a yanzu ba mu da wannan fasaha ko hanyar kere-kere, muna da fasahar. Amma babu tsari, sannan hatta hukuma bata ma san mutum nawa ne ke da kuduri wajen yin hakan a kowane fanni ba, balle har a amfana da fasaharsu. Idan har aka kafa cibiyoyin da za su rika lura da ire-iren wadannan ayyuka, to za a samu fa’ida mai dimbin yawa.
“Satar Fasaha” (Industrial Espionage)
A fannin ilmin ci gaban kasuwanci da kere-kere, “Satar Fasaha”, wanda a turance ake kira “Industrial Espionage”, shi ne leken asiri kan asalin ilmin fasahar yadda ake kera wasu kayayyaki – kamar injina, da mashina, da motoci, da sauran hajojin kasuwanci – ta hanyar karkashin kasa. Wannan hanya, duk da cewa a zahiri haramtacciyar hanya ce, amma a aikace babu wani kamfani ko kasa da ta tsira daga aikata shi a duniya baki daya. Da wannan tsari ne galibin kamfanoni ke amfani wajen satar fasahar yadda wasu kamfanonin ke kera hajojinsu. A aikace dai, a iya cewa wannan tsari ne halastacce; domin duk kasa ko kamfanin da ya ce haram ne, to za ka samu shi ma ya taba aikata shi a baya. Da wannan tsari, muna iya mallakar hanyoyin ci gaba mai dimbin yawa. Hakan kuwa na samuwa ne ta hanyar bincike a Intanet, da littattafai, da nemo bayanai ta karkashin kasa daga ma’aikatan wasu kasashe ko kamfanin da ke kera irin fasahar da ake bukatar habbakawa. Duk wannan, idan za mu yi da gaske, ba wani bane mai wahal ko kadan. Sadaukar da kai kadai muke bukata da kishin kasa.
Samar da Yanayin Karatu Mai Kyau a Makarantu
A tabbace yake cewa ilmi ba ya samuwa ta sauki, amma hakan ba ya nufin a yi ta yinshi ne cikin wahala da kunci. Akwai irin yanayin da karatu ke bukata kafin ya tabbata a zuciya ko kwakwaklwar wanda ke daukansa. Idan ba a samu wannan yanayi ba, to babu yadda za a yi ya zauna, balle har a iya amfana da shi. Hakan ya hada da samar da malamai masu nagarta, da samar da tarbiyya ta hanyar lura da doka da oda a ko ina ne cikin kasa, da samar da kayan daukan darasi da karatu masu inganci, irin su littattafai, da azuzuwa masu dauke da wutar lantarki, da ruwan sha, da dakunan dalibai masu inganci, da kayayyakin binciken ilmi masu inganci, da kuma saukaka farashin karatu, ba mu ce dole sai an baiwa ‘yan kasa ilmi kyauta ba – tunda gwamnati ta dade tana kururuwar cewa bata da kudi. A gaskiya galibin makarantunmu ba a cikin yanayi mai kyau suke ba. Bayan rashin tarbiyya, wanda ke dakushe karshashi da kaifin basira da ilmi, akwai matsalar rashin muhallin karatu mai kyau. Maimakon karatu ya amfani dalibai, sai cutar da su ma yake yi. Abin da nake nufi da cutar da su kuwa shi ne, maimakon a samu sauki lokacin karatu, tsanani ake samu, ko dai daga wajen malaman ko kuma sauran dalibai ‘yan uwansu. Bayan haka, galibin tsarin karatarwa a makarantunmu sun koma da baki kawai ake yi kamar karatun Aku (theoretical), babu bangaren kwatance (practical), in ka kebe wasu daga cikin fannonin ilmi da suka shafi likitanci da bangaren lafiya. Dangane da haka, ga abin da Farfesa Otubanso, wani kwararren farfesa a fannin kimiyyar sinadarai (Chemistry), yake cewa: “…a yanzu dalibai sun daina koyon karatu a aikace (saboda rashin kayan aiki a makarantu), sai dai a rubuce kadai.” Da wannan tsari kuwa, babu yadda za a yi a ce makarantunmu sun yaye dalibai kwararru kan harkar kere-kere. In kuwa haka ta kasance, ban san inda muka dosa ba, duk kudi da dogayen gidajenmu. Wannan ya tuna min da zancen Martin Luther King, inda yake cewa: “Ci gaban kowace kasa bai tsaya a yawan dukiyar da ta mallaka ba, ko yawan kudaden shiganta ba, ko tsauraran ganuwar tsaronta ba, ko kuma dogayen gine-gine da ta mallaka masu ban sha’awa ba, a a, ya ta’allaka ne da iya adadin kwararrun da ta mallaka, masu ilmi, wayayyu, kuma mutanen kwarai.” Ya kamata mu sake lale.
Tallafi Ga Cibiyoyin Bincike Ilmi
Cibiyoyin bincike su ne kashin bayan ci gaban kowace kasa wajen kimiyya da kere-kere. Daga kasar Amurka zuwa Ingila, da Sin, da Malesiya, da Singafo, har zuwa kasar Indiya da Jafan, duk da cibiyoyin binciken ilmi suke takama. A wasu kasashe ma ba wai gwamnati kadai ke mallakar cibiyoyin ilmi ba, hatta kamfanonin kere-kere na da su. Tabbas tafiyar da cibiyar binciken ilmi abu ne mai wahala, domin yana bukatar makudan kudi da kwarewa da kuma tallafin wasu kasashe, amma duk da haka, wannan ba ya nufin ba za mu iya ba, tunda ga kasashe masu yawa, wadanda ma ake ganin ba kowa bane su, sun rike ire-iren wadannan cibiyoyi. Muna da cibiyoyin binciken ilmi, tsakanin fannin hada magungunan cututtukan jikin dan adam zuwa na dabbobi, har zuwa na binciken kananan kwari, amma idan ka shiga cikinsu sai ka tausaya musu. Cikin farko-farkon wannan shekara ne ministan Kimiyya da Fasahar Kere-kere yayi ta kira ga gwamnatin tarayya wajen samar da wani tsari da zai tabbatar da tallafi ga cibiyoyin binciken ilmi a kasar nan, amma har yanzu shiru kake ji, wai Malam ya ci shirwa. Galibinsu da kyar suke dogaro da kansu. Kudaden da ake tura musu na biyan albashi ne kadai, ba wai na gudanar da binciken ilmi ba. Akwai hukumomi da yawa a sauran kasashen duniya da ke bayar da tallafi a fannonin binciken ilmi da yawa, wajibi ne ga gwamnatin tarayya ko na jihohi su samar da wani tsari da zai tabbatar da yiwuwar hakan, don ciyar kasarmu gaba. Bayan haka, dole ne gwamnatin tarayya da na jihohi har wa yau, su rika ware wasu kudade na musamman a matsayin tallafi don gudanar da binciken ilmi a wasu fannonin da muke da nakasu a cikinsu. Alkaluman bayanai daga wasu kasashen za su tabbatar da cewa tallafin da gwamnatin tarayya ke bayarwa a wannan fanni, in ma tana bayarwa, ba komai bane idan ka gwama shi da na wasu kasashe. Misali, mujallar The Nigerian Engineer, bugu na 35, lamba ta 4, wacce ta fito cikin Disamba na shekarar 2003, ta tabbatar da cewa a shekarar 1985, kasar Indiya ta ciyar da dalar Amurka biliyan uku wajen tallafi ga wasu cibiyoyin binciken ilimi guda dubu daya da dari uku da ta mallaka. Mujallar kuma ta kara da cewa a duk shekara, hukumar Indiya na ciyar da kashi 1.5% na arzikin da take samu daga sauran kasashe don habbaka fannonin kimiyyar lantarki da bincike kan sararin samaniya, a yayin da kasar Amurka take ciyar da kashi 2.5% a wannan fanni ita ma. Amma tunda aka samar da Najeriya, a cewar wannan mujalla, mafi girman abin da ta bayar a matsayin tallafi a bangaren binciken ilmi bai wuce kashi 0.43% ba. Misali, a shekarar 1983 ta bayar da kashi 0.43%, a shekarar 1992 ta bayar da kashi 0.05%, a shekarar 2003 kuma ta dan haura zuwa kashi 0.23%. In har wannan shi ne abin da gwamnatin tarayya ke ciyarwa, duk da kudaden shiga da muke samu daga danyen mai da kudin fito, a fili yake cewa babu wata kima da hukumar tarayya ta baiwa wadannan cibiyoyin bincike a aikace, balle a yi maganar manufar gwamnati wajen habbaka kimiyya da kere-kere a kasar baki daya.
Samar da Makamashi na Hakika
Gwamnatin tarayya ta dade tana ta bikon masu zuba jari a wannan kasa tamu a kowane fanni ne kuwa, musamman fannin kimiyyar sadarwa. Lokacin da kamfanonin wayar salula irin su MTN da Econet (Zain) da Glomobile suka yanki lasisi kan wannan harka, babu irin wahalar da talakan Najeriya bai sha dasu ba, wajen yawan cajin kudin kira, da rashin yanayin sadarwa mai kyau, da kuma tsadar wayar salula. Duk da cewa an samu saukin wasu daga cikin wadannan matsaloli, a bayyane yake cewa lallai farashin da muke biya wajen kiran waya yana daga cikin masu tsada a duniya. Ba komai bane ya haddasa mana hakan sai tsadar rayuwa, wanda rashin makamashi na hakika ke jawo shi – daga kan kamfanoni ko masana’antu, zuwa kan talaka da ke sayan kayayyaki ko hajojin da suke fitarwa. Ba mu da ingantacciyar wutar lantarki. A kasar Gana har yanzu, sai an yi sanarwa a gidan rediyo ko talabijin idan za a dauke wuta a wata unguwa ko gari, tare da sanar da mutanen wannan bigire tsawon lokacin da hakan zai dauka, da ranar, da kuma lokacin. Galibin lokuta, idan hukumar lantarki ta sanar cewa za a dauke wutan na tsawon mintina biyar ne, a karshe cikin mintina uku da daukewa, za ka ga an dawo da wutar. Cikin watan da ya gabata ne daya daga cikin jihohin Najeriya da ke makwabtaka da kasar Kamaru ya fara tunanin jawo wutar lantarki daga kasar Kamaru zuwa jiharsa, don samun ingantacciyar wutar lantarki ga al’ummar jihar. Kada mai karatu ya mance, har yanzu Najeriya ce ke baiwa kasar Kamaru, da Nijar da sauran makwatanta wutar lantarki. Me yasa ba za mu iya alkinta abin da muke da shi ba? Akwai kamfanoni da yawa masu son zuwa Najeriya don zuba jari, amma babbar matsalar da suke dubawa bayan cin hanci da rashawa, ita ce matsalar wutar lantarki. Domin ko ba a samar da hanyoyi ba, in dai akwai ingantacciyar wutar lantarki, hatta karamin ma’aikacin gwamnati na iya tsara rayuwarsa, duk karancin albashinsa kuwa. Idan muka yi la’akari da kasashen da suka ci gaba a fannin kimiyya da kere-kere, za mu ga basu samu wannan matsayi ba sai da suka yaki zuciyarsu wajen tabbatar da samuwar ingantacciyar wutar lantarki a kasarsu. Wannan zai sa makarantu su samu ilmi mai inganci, sanadiyyar ingantacciyar karantarwa daga malamai. Shi zai sa kamfanonin kere-kere su samu kwanciyar hankali, ya zama damuwarsu kan bincike ne kawai da abin da za a kera, amma ba a kan makamashi ba. Wannan zai sa har wa yau, a samu karkon kayayyakin kere-kere da ake amfani da su. Idan kuwa gwamnati ba ta yi haka ba, to da sauran rina a kaba.
Lura da Bukatun Kasa/Al’umma
Abu na kusa da karshe da hukuma za ta yi shi ne ta lura da bukatar ‘yan Najeriya. Me ye muke da tsananin bukatuwa zuwa gare shi? Kuma yaya za a tabbatar da samuwarsa? Wannan shi ne abin da ya kamata mu lura da shi, ba wai mu zama “’yan abi Yarima a sha kidi” ba – don kasar Amurka ta je duniyar wata, wannan ba shi zai sa mu ma dole mu je ba. Don kasar Sin ta harba kumbo, ba shi zai sa mu ma dole mu harba ba. Don kasar Indiya ta kera makamin Nukiliya, har wa yau, ba wannan bane zai zama mana dalili dole mu ma sai mun kera ba. Don me? Bukatunmu kadai ya kamata mu duba. Idan muka dubi kasa irin Malesiya misali, za mu ga cewa duk da ci gabanta, ba ta damu da kera makamin Nukiliya ba, balle har ta kama cuku-cukun zuwa duniyar wata. Abin da kasar ta sadaukar da kanta wajen samarwa shi ne ingantaccen ilmi, da bunkasa fannin kere-kere da fasahar sadarwa, da kuma samarwa tare da tabbatar da doka da oda a kasarta. Duk wanda ya ziyarci wannan kasa zai fahimci haka. To amma ta yaya muka yanke shawarar harba tauraron dan adam, alhali ba mu da cikakken tsarin doka da oda, ba mu kawar da ci hanci da rashawa ba iya gwargwado, ba mu samar da ingantaccen ilmi ba, balle har mu tabbatar da samuwar ingantacciyar wutar lantarki? Idan mun ce ai ba a Najeriya bane tauraron ke da asali, amma ai muna da cibiyar da ke lura da shawagi ko bayanan da yake tarkatowa daga sararin samaniya a nan kasar, wadda kuma dole ne sai da janareto take dogaro. Anya, wannan ba tufka bane da warwara?
Shugabanci na Gari
Dukkan shawarwarin da muka kawo a sama, samuwarsu ta dogara ne kacokan kan shugabanci na gari; wani abu mai tsada da kasar nan ta rasa, tun shekaru kusan arba’in da suka gabata. Da shugabanci na gari ne kadai gwamnatin tarayya za ta iya sadaukar da kanta wajen ganin wannan kasa ta gyaru, ta kimtsu, ta zama ‘yantacciya daga kangin talauci, da kaskanci, da cin hanci, da rashawa, da dukkan abin da yake mata tarnaki wajen ci gaba. Don haka, dole ne mu tabbatar da cewa mun zabi shugabanni na gari. Allah mana gamo da katar!
No comments:
Post a Comment