Mabudin Kunnuwa
A wannan mako cikin yardar Allah za mu tabo wani fanni mai muhimmanci ga rayuwarmu baki daya, musamman kan abin da ya shafi safara, da sarrafa abubuwa, da kuma tafiyar da rayuwa gaba daya. Wannan fanni kuwa, kamar yadda mai karatu zai gani daga taken kasidar wannan mako, shi ne fannin yadda ake hako danyen mai, watau Crude Oil, ko kuma “Gurbataccen Mai”, kamar yadda wasu ke kiranshi. Za mu san wani abu kan haka, da yadda ake tace shi, da kuma yadda bayan an tace, ake fitar da sinadaran da rayuwarmu ke gudanuwa da su a yau, wajen tafiye-tafiye, da wanke-wanke, da tande-tande, da kuma samun abin sanyawa a aljihu. Amma kafin nan, ga yadda wannan kasida ta samo asali nan:
“Assalaamu Alaikum, ni dai a kullum ina sha’awar sanin yadda aka fara sanin danyen mai ne (Crude Oil), da yadda aka gano cewa yana da amfani a duniya, da inda aka fara tonowa, da wadanda suka fara tono shi, da shekarar da aka fara tonowa, da kuma amfanin da aka fara yi da shi. Na gode.”
Danyen Mai: Ma’ana da Asali
Danyen Mai, ko Crude Oil a harshen Turanci, shi ne garwayayyen ruwan sinadaran da ke makare a karkashin kasa ko duwatsu, wanda ya samo asali daga attakar matattun dabbobin ruwa da na kan tudu da suka rube sanadiyyar tsananin zafi da daskarewa, tun shekaru aru-aru. Daga daskararren jikin wadannan halittu ne wadannan sinadarai ke canza yanayi da kama, sai su narke sanadiyyar tsananin zafin da ke karkashin kasa da kuma tsawon zamani. Bayan sun canza yanayi, wannan sabon mai da ya samu daga jikinsu kan kunshi sinadaran kimiyya nau’uka uku. Nau’in sinadarin kimiyya na farko da ke ciki shi ne sinadarin Faraffin mai dauke da sinadarin hidarokabon. Nau’i na biyu kuma shi ne sinadarin Naften, shi ma mai dauke da sinadarin hidarokabon a cikinsa. Sai nau’i na karshe wanda hadaka ne na tagwayen sinadarai – tsakanin sinadarin Aroma da Asfalt. Wadannan sinadarai da ke samuwa a jikin kowane danyen mai da ake hakowa, su ne suka kawo samuwar rabe-raben nau’ukan danyen mai zuwa kashi uku.
Nau’in danyen mai na farko shi ne nau’in da ke dauke da galibin sinadarin Faraffin mai garwaye da hidarokabon. Wannan nau’i shi ake kira Paraffinic Crude a Turancin Kimiyyar Man Fetur na zamani. Sai nau’i na biyu da ke dauke da galibin sinadarin Naften mai garwaye da hidarokabon shi ma. Wannan nau’i shi ake kira Naphthenic Crude. Kashi na karshe shi ne wanda ake samunsa cakude da tagwayen sinadaran Aroma da Asfalt sama da kashi arba’in (40%). A turancin Kimiyyar Man Fetur a yau ana kiran irin wannan nau’i da suna Aromatic & Asphaltic Crude. Bayan wadannan rabe-rabe kuma, a yanzu masana kan kasa danyen mai zuwa kashi biyu, dangane da yanayin da aka debo shi. Idan yana da kauri, sanadiyyar bunkasar sinadaran da ke cikinsa sama da kashi arba’in da biyar, sai a kira shi “Daskararren Danyen Mai”, ko Heavy Crude, a Turance. Idan kuma sinadaran da ke dauke cikinsa ba su da armashi ta yadda suka sa ya zama tsala ko tsalalo, sai a kira shi “Narkakken Danyen Mai”, ko kuma Light Crude a turance.
Kamar yadda mai tambaya ke son sani, shi danyen mai a farkon zamani babu wanda ya san shi, balle ya san daga inda ya samo asali. A takaice dai a iya cewa shi ne ya fara bayyana kansa. Yadda lamarin ya kasance kuwa shi ne, wannan attakar matattun dabbobi da ya narke zuwa wannan sinadari na danyen mai cikin tsawon shekaru, a can karkashin kasa yake, a makare. Saboda tsananin zafin da ke can karkashin kasa, da wanda ke samuwa a tsakanin duwatsu, sai ya rika tilasta wa wannan daskararren ruwa na danyen mai rabuwa zuwa kashi biyu. Bangaren da ke tsakanin duwatsu sai ya gangara zuwa can kasa, ya ci gaba da taruwa har ya zama wata rijiya ta musamman. Wannan shi ake kira Oil Reserves, watau rijiyar danyen mai na karkashin kasa. Kuma shi ne nau’in mai da ake iya hakowa a yau, ta hanyoyi daban-daban. Kasancewar wannan lamari ya samo asali ne daga daular Girka, watau Greece ta da, shi yasa a wancan lokaci suke kiran wannan nau’in danyen mai da suna “Petroleum”, kuma abin da wannan kalma ke nufi shi ne, “Man Dutse”; watau man da aka samo shi a tsakanin duwatsun karkashin kasa. Asalin Kalmar “Petro”, a harshen Girkanci shi ne “Dutse”. Kalmar “Leum” kuma yana nufin “Mai” ne. Don haka suke kiranshi “Petroleum”, watau “Man Dutse”.
Sauran man da ke saman dutsen kuma sai tsananin zafin da ke cikin kasa ya tilasta musu haurowa, tunda ba za su iya komawa kasa ba saboda samuwar duwatsu a kasansu. A haka za su ci gaba da haurowa har sai sun riski kasar da muke takawa, su ci gaba da malala kamar yadda idaniyar ruwa ke yi a samansa. Wannan nau’i da ke malala a saman kasa da kansa, shi masana ke kira Surface Oil. Kuma a tarihin alakar dan adam da danyen man fetur, shi ne abin da ya fara nuna samuwar mai a karkashin kasa. Sanin hakikanin lokacin da wannan nau’in mai ya fara samuwa a tarihin duniya ba abu bane mai yiwuwa a rubutacciyar tarihi. Saboda wadanda suka gano shi, ba su da tabbacin cewa su ne na farko, balle su yi alfahari da hakan. Ko da sun san hakan, ba lallai bane ya zama a lokacin akwai hanyar rubutu kamar yadda muke da ita a yanzu. Idan ma akwai, to babu tabbacin an taskance sunan wanda ya gano wannan lamari. Da an taskance sunansa kuwa, to lallai da an sani.
Amfanin Danyen Mai a Zamanin Da
Kamar yadda bayanai suka gabata, an gano danyen mai ne sanadiyyar tunbatsa da yayi zuwa saman kasar da muke takawa, saboda masifaffen zafin da ya koro wani bangarensa daga can karkashin kasa, ko tsakanin duwatsu. Amma bangaren da ya gangara kasan dutsen shi yake zama rijiyar mai, kamar yadda muka sani a yau, kuma shi ne ake hakowa a sauran kasashen da suka gano wannan arziki. Dangane da haka, wadanda suka fara gano wannan bangaren mai da ke malala mai suna Surface Oil, ko kadan ba su zaci wani arziki bane na a-zo-a-gani. Don haka a zamanin baya babu abin da suke yi da shi sai zuba wa fitilunsu don ganin haske, ko cuccura shi don yin ciko a jikin jiragen ruwa (watau Caulking kenan a turance), da shafa shi a jikin karafa ko wasu abubuwa masu tsauri don mayar da su masu taushi, da yin rigunan shiga ruwa da su – don an gano cewa suna da tasiri wajen hana ruwa shiga cikinsu, don mai ne. A karshe kuma an yi amfani da su ne wajen yin magunguna ko hada magunguna da su. Dukkan wadannan nau’ukan amfani da aka yi da wannan danyen mai a zamanin baya, babu wani bincike na musamman da mutane suka gudanar kafin hakan, sai dai gwaji kawai. Da zarar sun ga ya musu abin da suke so, sai su ci gaba da amfani da shi a haka. Masana sun nuna cewa dukkan wadannan al’amura sun fara samo asali ne daga Karni na goma sha hudu miladiyya, watau 14th Century – wajen shekaru dari takwas kenan yanzu.
Bincike kan Danyen Mai, da Yadda aka Fara Hako Shi
Mutane sun dade suna amfani da wannan bangaren danyen mai da suke samu a saman kasa yana malala, kamar yadda bayanai suka nuna a baya, amma ba a fara gudanar da bincike na kimiyya mai tushe a kansa ba sai bayan shekaru dari biyar, watau cikin karni na shatara kenan. Wannan shi ne lokacin da kasashen turai suka fara juyin juya hali kan kere-kere da kimiyya, watau Industrial Revolution. Lokacin ne aka fara kera injina masu bukatar makamashin da za a sarrafa su da shi, da kuma sababbin hanyoyin samar da makamashin amfanin gida, irin su fitilu, da injinan amfanin gida da dai sauransu. Bayan shekaru hamsin da shiga wannan karni ne wani masanin fannin Fiziya mai suna Abraham Gesseur, dan kasar Kanada, ya nemi hukuma ta bashi lasisin sakamakon bincike na musamman da yayi kan danyen mai, inda a karshen bincikensa ya gano cewa idan aka tace danyen mai, ana iya samun man kananzir, watau Paraffin kenan. Ya yi haka ne a shekarar 1852. Kenan, a wannan shekara ne aka gano kananzir a tarihin duniya.
Ana cikin haka, sai wani kamfani ya gano rijiyar danyen mai a kasar Poland, cikin shekarar 1853, watau shekara daya kenan bayan wancan bincike. A tarihin duniya, wannan ita ce rijiyar danyen mai ta farko da aka fara ganowa, wacce kuma aka hako mai, da tace shi, don sayarwa a duniya. Kada mu mance shekarar, ita ce 1853. Bayan shekaru biyu kuma sai ga wani masanin kimiyya mai suna Benjamin Sillimon, wani dan kasar Amurka, dauke da rahoto na musamman kan binciken da ya gudanar cikin danyen mai. A cikin rahoton ne ya sanar wa duniya cewa lallai akwai nau’ukan makamashi da yawa a cikin wannan danyen mai, kuma masu amfani ne kwarai ga rayuwar dan adam. Benjamin ya yi wannan bincike ne cikin shekarar 1855. Da aka kara samun wasu shekaru biyu kuma, sai wani kamfanin mai ya gano rijiyoyin mai a kasar Jamus, ta hanyar amfani da na’urorin hako mai na zamani a wancan lokaci. Wannan kamfani ya yi wannan aiki ne daga shekarar 1857 zuwa shekarar 1859. Daga nan dai sanayya kan danyen mai da kuma amfaninsa ya ci gaba da yaduwa a duniya a hankali har zuwa wannan zamani da muke ciki.
Yadda ake Tace Danyen Mai da Sarrafa Shi
Duk da cewa mai tambaya bai bukaci sanin yadda ake tace wannan sinadari na danyen mai ba, na ga dacewar sanar damu wannan, don samun karuwar ilmi da fahimta. Shi ilmi, kamar yadda muka sani, ba kaya bane da zai iya karya maka wuya don ka dauke shi da yawa. Sai in ka sani, amma ka take – a fannin addini da hakkokin mutane.
Tace danyen mai, wanda a turancin Kimiyyar Man Fetur ake kira Fractional Distillation, wani tsari ne na ilmi da kuma amfani da na’urorin sarrafawa tare da tace danyen mai, don fitar da nau’ukan makamashi daga cikinsa. Hakan kuma na samuwa ne ta hanyar amfani da manyan injinan toya mai, da sarrafa shi, a wasu mizanin zafi na ma’aunin Santigireti. Wadannan injina na dauke ne da wasu manyan fanfunan karfe masu daukan zafi, wadanda ake kira “Gas-heated Furnace.” Kuma suna aikin rarrabe nau’ukan man da ke cikin danyen mai ne a mizanin zafi na Santigireti daga “00C” har zuwa sama da ma’aunin zafi “4000C.” Akwai matakai shida da ake bi wajen tace wannan danyen mai, kuma a kowane mataki akwai nau’in man da ake fitarwa, wanda ya dace da irin zafin tuyan da danyen man ya ji. A haka ake fitar da nau’ukan makamashin da ke cikin danyen mai, irinsu daskararren man kwalta, watau Bitumen, da man kananzir, watau Paraffin, da nau’ukan mai marasa nauyi, irin su man fetur, da man dizel, da gas, da kuma man jirgin sama. Dukkan wannan aiki ana yinshi ne a Matatar Mai, watai Oil Refinery.
Matakin farko shi ne matakin zafin da ya wuce “400” a ma’aunin zafi na Santigireti. A wannan mataki ne ake tace nau’in mai mai matukar kauri, wanda ake amfani da shi wajen shafe tituna, watau Bitumen kenan, ko kwalta, kamar yadda mai karatu zai fi fahimta da wuri. A Makati na biyu kuma, wanda ya faro daga ma’aunin zafi na “330” zuwa “400” a ma’aunin zafi na Santigireti. A wannan zango ne ake tace mai da ake amfani dasu wajen rage kaushin karafa da sauran abubuwa masu tsatsa – kamar su man giris, a misali. Sai mataki na uku da yake farowa daga ma’aunin zafi na “260” zuwa “330”. A wannan zango ne ake tace nau’in mai mai nauyi, wanda injina masu karfi ke amfani dashi, irinsu man dizel kenan. Sai mataki na hudu, wanda ya faro daga ma’aunin zafi na “190” zuwa “260”. A wannan zango ne ake tace man kananzir da ire-irensa. Sai mataki na biyar wanda ke farawa da ma’aunin zafi na “40” zuwa “190”. A wannan zango ne kuma ake samun taco man fetur da muke amfani dashi a ababen hawanmu – motoci da mashina da injina ko wasu nau’ukan janareto kanana. Daga nan kuma sai mataki na karshe, wanda ke farawa daga ma’aunin zafi na “0” har zuwa “40” a ma’aunin zafi na Santigireti. Wannan shi ne zangon tace mai na karshe, kuma a wannan zango ne ake fitar da nau’ukan mai marasa kauri, masu cakude da iska, irinsu man gas, da man gas na dafa abinci (Cooking Gas), da kuma sinadaran da ake yin sabulu da su don amfanin gida da ma’aikatu.
Kammalawa
Wannan a takaice, shi ne dan abin da ya samu. Kamar yadda mai karatu ya sani, bincike kan wannan fanni abu ne mai fadi, wanda ke bukatar lokaci da kwazo. Dan abin da muka kawo a nan ya zo ne don gamsar da tambayar mai tambaya. Sannu a hankali za mu rika dauko wasu bangarorin da bamu tabo su ba a yau, don basu hakkinsa gwargwadon hali. Da fatan an gamsu.
Gaskiyane! ALLAH yabaka ladan yada ilmi ameen
ReplyDeleteGaskiya haka yayi Allah yabada ladan yada ilimi
ReplyDelete