Da yawa cikin masu lura da al'amuran yau da kullum kan harkokin
duniya musamman a bangaren siyasar kasashe da zaman lafiya kan yi mamakin yadda
kasar Amurka, ta hanyar Hukumar Tsaron Kasar (Department of Defence – DoD) ke
amfani da wasu jirage da na'urorin zamani na sadarwa ke sarrafa su daga wata uwa
duniya, don kashe ko darkake shahararrun abokan gabanta da suka yi fice wajen
adawa da yadda hukumomin kasashen Turai da Amurkan ke gudanar da manufofinsu na
siyasa, da kuma tasirin hakan ga kasashe musamman na Gabas-ta-Tsakiya. Galibin
hare-haren da kasar Amurka ke kaiwa a bakin iyakar kasashen Pakistan da
Afghanistan – inda ake kashe fararen hula, da ma sojojin kasar Pakistan – duk
da wadannan jirage masu sarrafa kasar take amfani.
Mabudin Kunnuwa
Cikin watan da ya gabata ne har wa yau Hukumar kasar Iran ta sanar
da cewa ta bugo wani jirgi mai sarrafa kansa na kasar Amurka, wanda ya shigo
iyakar kasarta da wajen tazarar Mil 44.
Bayan kwanaki biyu da wannan ikirari ne Gwamnatin kasar ta nuna wa
manema labaru wannan jirgi da ta kado, a yayin da yake shawagi a cikin kasarta
don leken asiri ko tattaro bayanan sirri, kamar yadda ta sanar. Haka kuma, mako guda bayan wannan lamari na
kasar Iran, sai ga sanarwa a kafafen yada labaru cewa wani jirgin kasar Amurka
mai sarrafa kansa ya fado ko yayi hadari a daya daga cikin kasashen da ke
Gabas-ta-Tsakiya. A halin yanzu da nake
wannan rubutu dai, kasar Amurka na da ire-iren wadannan jirage masu sarrafa
kansu da take girke a kasar Djibouti, wanda daga cikinsu ne daya ya fado kasar
Iran, har ta kado shi, duk da cewa ba a samu wata alamar karaya ko harbi ko
ballewa a jikin jirgin ba. Ba ma kasar
Amurka ba kadai, a yanzu akwai kasashe 44 da ke da irin wadannan jirage masu
sarrafa kansu na yaki, watau Drone ko Pilotless Aircraft. Daga cikinsu akwai kasar Ingila, da
Kanada, da Jamus, da Isra'ila, da Rasha da sauran kasashen nahiyar Turai. Akwai alamar fannin Kimiyya da Kere-kere (Science
and Technology) na taka rawa sosai wajen haddasa yaduwar ire-iren wadannan
sababbin kayayyakin fasaha.
Wannan ya tuna min da wata kasida da babban Malami Sheikh Yusuf
Al-Qardhaawi ya gabatar shekaru kusan bakwai da suka shige, kan mummunar tasirin
binciken kimiyya a duniya, da yadda hakan ke zama sanadiyyar halaka rayuka da
dukiyoyi a duniya baki daya. Babban
Malamin ya nuna cewa ba komai ya haddasa hakan ba sai karkatacciyar manufar da
masu wannan ilmi ko bincike suke da ita, na son duniya, da rashin yarda da
samuwar Allah a matsayin mahalicci abin bauta.
Wadannan munanan cututtukan zuci da Malamin ya zayyana, su ne suka samar
wa duniya tsarin Mulki da Kasuwanci da ake ta kokarin kakaba wa kasashen
Musulmi ko kasashe masu tasowa, cewa dole su yi riko da su a matsayin tafarkin
rayuwa. Wadannan tsare-tsare kuwa su ne tafarkin
kasuwanci da tattalin arzikin kasa na Jari-hujja, watau Capitalism. Wanda tsari ne da bai san talaka ba,
sannan ya ginu ne a kan manufar tara dukiya, da kokarin taskance su. Daya tsarin kuma, wanda ke kokarin mika
hakkin hukunci da tsarin gudanar da rayuwa ko shugabanci ga mutane kadai – duk
da nakasarsu wajen tunani da sanin maslahar kansu – shi ne tsarin Dimukiradiyya,
watau Democracy. Wanda duk abin
da jama'a ta raja'a akai shi za a bi, ko da ya saba wa mahalicci da maslahar
rayuwarsu wacce ba su iya hangowa a sadda suke yanke hukunci.
Wadannan tsare-tsare biyu, watau tsarin Jari-hujja a bangaren
kasuwanci, da tsarin Dimukiradiyya a bangaren shugabanci, su ne manyan matsalolin
duniya a halin yanzu. Domin suna gadar da son duniya, da tsoron mutuwa, da
kwadayi, da son mulki, da danniya, da mamaya, da dai sauran abubuwan da a halin
yanzu muke gani. A bayyane yake cewa manyan
kasashen duniya suna fama da matsalar tattalin arziki, da basussukan da suka
musu katutu, wanda kuma hakan ya samo asali ne daga mummunar sakamakon tsarin
Jari-hujja, musamman dabi'ar son tarawa, da cin mummunar riba, da barin 'yan kasuwa
su yi yadda suka ga dama. Wanda wadannan kuma, kamar yadda masu karatu za su
shede ni, su ne manyan dirkokin tsarin Jari-hujja. A bangaren Dimukiradiyya
kuwa ba sai na fadi abin da ke faruwa ba.
Kasashen da ke gaba-gaba wajen tallata wannan tsari suna iya kokarin
kiyaye dokokinta a kasashensu, amma a wasu kasashen, sai wanda suka ga daman ya
zama shugaba yake zama. Akwai kasashen
da sunyi kokarin bin tsarin, amma saboda mahangarsu ta rayuwa ta sha bamban da
mahangar kasashen yamma da ke tallata tsarin, sai suka taimaka aka ruguza
su. Gajeren misali na cikin abin da ya
faru a kasar Aljeriya a shekarar 1994.
Muna neman tsarin Allah daga faruwar irinsa a kasar Misra. A takaice dai, hobbasa da ke haifar da
samuwar ire-iren makaman yaki da suka sha karfin tunanin dan adam a yau, ta
hanyar tallafin fannin Kimiyya da Fasahar Sadarwa da Kere-kere, na samun goyon
bayan tsarin jari-hujja ne da tsarin shugabancin mamaya da danniya. Ba ilmin bane aibu. Ba abin da ake kerawan bane aibu a sake, sai
dai manufar da ke karkashin hakan, wacce ke bayyana bayan tsawon zamani. Jama'a ku gafarce ni, na buge da wani abin
daban.
Ma'ana da Asali
Jirage masu sarrafa kansu, ko Drone, ko Unmanned Air
Vehicle, ko Pilotless Aircraft kamar yadda ake kiransu a harshen
Turanci, nau'ukan jirage ne marasa matuki, marasa direba, wadanda ake sarrafa
su daga cibiyar sadarwa da ke kasa.
Wadannan jirage sun sha bamban da makamin mizail ko makami mai
linzami. Duk da cewa makaman mizail su
ma ana harba su ne kamar yadda ake harba wadannan jirage masu sarrafa kansu,
amma sabanin mizail, su jirage masu sarrafa kansu na iya daukan makamai ne su
jefa a wuri, ko su dauki hoton wurin da abokan gaba suke, ko su dauko kaya, ko
su gano inda masu rauni suke daga filin daga.
Su mizail makamai ne gaba dayansu.
Da zarar an harba su sukan isa wurin da aka aika su ne kai tsaye,
shikenan sun gama aikinsu. Sannan ana
iya darkake makaman mizail kafin su isa inda aka jefa su ko a hanyar da suke
tafiya, amma jirage masu sarrafa kansu na iya kubuta daga wannan, domin akwai
wadanda ke iya bacewa cikin sararin samaniya, iya gwargwadon kwarewar makerinsu. Bayan haka, mizail kamar mutum-mutumi ne su,
inda aka tura su nan za su. Amma jirage
masu sarrafa kansu suna da dabi'un fahimtar abubuwa, da gani, da kuma kauciya
ko gociya kamar yadda bayanai za su nuna nan gaba.
Tunani kan sarrafa jirgi ba tare da matuki ba ya samo asali ne tun
shekarar 1898, a watan Mayu, lokacin bajekolin kayayyakin fasahar kere-kere da
aka yi a Dandalin Madison (watau Madison Square) da ke birnin New
York na kasar Amurka. A wannan biki na
bajekolin kayayyakin fasahar lantarki ne Nikolas Tesla, wani masanin kimiyyar
lantarki, ya gabatar da wani jirgin ruwa da ake sarrafa shi ta amfani da
siginar rediyo, daga waje. A wurin ne
yayi gwajin wannan jirgin ruwa, da yadda ake sarrafa shi ba tare da direba ba,
daga waje, ta amfani da siginar rediyo.
Wannan bikin bajekoli dai an shirya shi ne wata guda bayan sojojin yakin
kasar Andalus (Spain) sun nutsar da wani jirgin ruwan yakin kasar Amurka
a gabar tekun Havana (Havana Harbour).
Watanni uku bayan wannan bikin bajekoli sai Nikolas Tesla ya rubuta
kasida ta musamman kan yadda za a iya sarrafa jirgin yaki mara direba, don
darkake abokan gaba a lokacin yaki, da yadda za a iya kai hari da irin wadannan
jirage. Daga nan sai ya tura wa mujallar
Electric Engineer don ta buga.
Amma sai suka ki karban kasidar, domin a cewarsu, wannan wani abu ne da
bazai taba iya faruwa ba, balle a yi tunanin shigar dashi cikin kundin ilmin
kimiyya. A takaice dai suka ce wannan
wani nau'in binciken ilmi ne da ba za a iya dabbaka shi a aikace ba.
Ana shiga karni na 20 (20th Century) sai fannin fasahar
kere-kere ya kara ci gaba wajen samar da nau'ukan bincike don samar da ire-iren
wadannan jirage da Nikolas Tesla ke hasashensu a bincikensa na shekarun baya. Babban abin da ya bayyana hakan kuwa shi ne jiregen
ruwan kasar Jamus masu suna U-Boats suka addabi kasar Amurka a lokacin
Yakin Duniya na daya, wanda nan take hukumar Amurka ta tara masana don gudanar
da bincike da zai kai ga samar da ire-iren wadannan jirage masu sarrafa kansu,
watau Drone. Hakan ya faru ne a
shekarar 1917, kafin kare yakin. A
lokacin yakin duniya na biyun ne har wa yau, Hukumar Nazi ta kasar Jamus a
karkashin Hitla ta yi wa kasar Burtaniya ruwan wasu irin bamabamai masu dauke
da na'urar da ke sarrafa su. Harba su
kawai ake yi zuwa kasar, su kuma suna sarrafa kansu. Wadannan na'ukan bamabamai su ake kira Pulse-Jet-Powered
Bombs. Bayan yakin duniya na biyu har wa yau, kasar Isra'ila ta mallaki
irin wadannan jirage masu sarrafa kansu – ta rigi kasar Amurka mallakarsu –
inda ta yi amfani da su a kan sojojin yakin kasar Siriya da ke Lebanon a
shekarar 1982. Daga shekarar 1990 zuwa yanzu kuma an samu sauyin tsari da
kintsin wadannan jirage, sanadiyyar ci gaba da aka samu a fannin kimiyyar
sadarwa da kwamfuta da kere-kere. Wasu
dalilan kuma su ne tunanin inganta tsaro, da yunkurin mamaya da kuma cika fuska
a siyasar duniya.
Tabbas kasar Amurka ta mallaki jiragen kafin shekarar 1990, domin
ta yi amfani da su a kasar yugosilabiya, lokacin da kungiyar NATO (wadda kasar
Amurka mamba ce) ta darkake kasar, a yunkurinta na hambarar da gwamnatinsa. Lokacin da ake ta gwambza wannan yaki dai
kasar Amurka ta kawo agajin, inda tad a jiragen yaki masu dauke da direbobin da
ke tuka su, da kuma nau'in jirgin da ke sarrafa kansa mai suna Predator, wanda
aikinsa a lokacin shi ne nuna inda sojojin Slobadan Mulosovich suke, sannan ya
sanar da matuka jiragen yakin Amurka a duk inda suke a kasar, ta hanyar siginar
rediyo, nan take su kuma sai su kai hari.
Ana cikin haka ne sai aka fara samun matsala wajen siginar da jirgin ke
bayarwa, inda har ya kusan gwara jiragen yakin kasar Amurka da juna, sanadiyyar
rashin ingancin tsarin sadarwar. Bayan
wannan yaki ne Janaral Jumper, wanda shi ne ya shugaban rundunar Amurka da wannan
yaki, yace basu ga ta zama ba. Nan take aka sake inganta jirgin Predator, inda
a karshe shi ma aka sa masa inda zai rika daukan bamabamai don aiwayar da
aikinsa.
Nau'ukan Jirage Masu Sarrafa Kansu
Akwai su kala-kala, kuma nau'i-nau'i. Da farko dai sun sha bambann wajen girman
jiki. Akwai kanana ainun, wadanda ake iya harba su da hannu, su tashi sama su
je su aiwatar da aikin da aka tura su.
Akwai matsakaita, wanda ake dora su a saman na'urar cilla jirage don
harba su. Sannan akwai manyan wanda
girmansu ya kai kananan jiragen yakin zamani.
Bayan haka kuma, akwai masu saukar ungulu, su ma masu sarrafa
kansu. A daya bangaren kuma, akwai
wadanda ake aika su musamman don jefa bamabamai a inda abokan gaba suke. Akwai wadanda kuma su aikinsu tattaro bayanai
ne kadai, ba su kashe kowa. Sannan akwai
wadanda ke zuwa leken asiri a inda abokan gaba suke. Ire-iren wadannan ba a cika ganinsu ta dadi
ba a inda suke a sararin samaniya. Bayan haka, akwai wadanda ke aikin gano inda
abokan gaba suka zuba makamai don kai hari, musamman inda aka zuba nakiya da
wasu kananan bamabamai da Majalisar Dinkin Duniya ta haramta amfani dasu. A kasa ake watsa su, kanana ne, kuma suna iya
tsawon shekaru basu tashi ba sai an taka su tukun. Duk akwai jiragen da ke aikin gano inda aka
watsa ire-iren wadannan bamabamai. Ta
bangaren nisan tafiya da juriyar aiki a sama kuma, akwai masu cin gajeren zango
wajen tafiya; wadanda ba su iya wuce minti talatin a sararin samaniya suna
shawagi. Akwai masu cin matsakaicin zango, wadanda ke iya cin awa guda ko
awanni ashirin da hudu a sararin samaniya suna shawagi. Sannan akwai masu iya
kwanaki suna shawagi a sararin samaniya don tattaro bayanan sirri ko kuma lura
da abokan gaba da inda suka sa gaba. Nan
gaba ana sa ran kera masu cin dogon zango a sararin samaniya.
Tsari da Kintsin Jirage Masu Sarrafa Kansu
Wadannan jirage sun sha bamban da sauran jiragen da ke amfani da
direba ko matuki. Da farko dai, akwai
babbar cibiyar sadarwa a kasa (Ground Station) inda "matukin
jirgin" ke zaune, a gaban kwamfuta da sauran na'urorin sadarwa da
bidiyo. Daga nan ne yake baiwa jirgin
umarnin tashi, da nisan tafiyar da zai yi, da nisan bigirensa a sama, da
nahiyar da zai dosa, da kuma aikin da zai je ya aiwatar. Idan zai kai hari ne kan abokan gaba, akwai
lokacin da matukin zai bashi umarni, sai ya saki ko ya harba bam din da yake
dauke dashi, zuwa jiha ko nahiya ko bangaren da ake son ya jefa. Duk wannan aiki jirgin na yinsa ne a kan idon
matukin da ke wannan cibiyar sadarwa, yana kallon tafiya da jujjuyawarsa a sama
ta kwamfuta.
A yadda aka kera shi, ba holoko bane cikinsa; duk da cewa babu
matuki a ciki. Yana dauke ne da inji,
wanda ke taimaka masa mikewa zuwa sama.
Wannan inji dai an tsara gudanuwarsa ne musamman kan abin da ya shafi
shan mansa, ta amfani da wata ka'ida ta binciken kimiyya da Brequet ya samar,
daya daga cikin malaman kimiyyar kere-kere. Wannan ka'ida ita ce ake kira The
Brequet Endurance Equation. Ka'ida
ce ta lissafi da ke tantance iya adadin yawan mai da ke cikin jirgin, don tsara
iya nisan tafiya da jirgin zai yi. Bayan inji, wannan jirgi yana dauke ne da tangaran
din da ke taskance masa makamashin hasken rana (Solar Panel), wanda da
shi ne yake aiwatar da ayyukan da suka shafi sinadaran lantarki; irinsu
sadarwa, da haska kasa don hango bigiren da yake nema, da dai sauransu.
Bayan wannan, jirgin na dauke da batir mai tara makamashi wanda ke
amfani da sinadaran Lithium-ion wajen taskance makamashin lantarki, kuma
a duk sadda yayi kasa, wannan tangaran da ke taskance makamashi daga hasken
rana na kara masa tagomashi, watau Rechargin kenan. An tsara tsarin gudanarwar wannan batir ne ta
amfani da ka'idar lissafin makamashi ta Helios, watau Helios Prototype kenan. Sannan akwai na'urorin haskakawa masu amfani
da sinadaran haske nau'in Laser da na hasken Infra-red. Wannan ne ke taimaka wa jirgin haska duk
inda ya dosa, musamman wurin da yake son samun bayanai. Daga cikin abubuwan al'ajabin da wannan jirgi
ke dauke da su shi ne, yana iya gani ko hasko duk abin da yake son gani ta
amfani da wannan na'ura na hasken leza da infrared; ko da a cikin duhu ne mafi
tsanani ko a karkashin ruwa, duk inda ya haska zai gani. Ta amfani da wannan haske ne yake tara
bayanai, sannan ya taskance su. Akwai
na'urar sadarwa mai nagarta da aka kera masa, wanda ke dauke da masarrafan
kwamfutar da ke hada alaka tsakaninsa da matukinsa da ke kasa, a can cibiyar
sadarwa da bayaninsa ya gabata. Wannan cibiyar
sadarwa an tsara ko gina masarrafan da ke cikinta ne ta amfani da ka'idojin
tsarin bayanai masu inganci, wanda sai kwararre na hakika a harkar masarrafan
kwamfuta zai iya barkawa cikinsu, sannan hakan na iya daukan shekaru bai gama
ba. Bayan wadannan abubuwa, akwai kuma
ma'adanar makamai ko marikin bamabamai da jirgin ke da shi. Duk da cewa ya danganci yanayin nau'in jirgin
ne. Idan na yaki ne, dole akwai marikin
bamabamai a tsakanin kafafunsa da fuka-fukansa, wanda bayan ya gama nazari da
saitin abin da zai harba, sai kawai ya sake su.
Wadannan, a takaice, su ne muhimman bangarorin da wannan jirgi mai
sarrafa kansa ke dauke dasu. Kamar yadda
bayanai suka nuna a baya, a halin yanzu ire-iren wadannan jirage an fara amfani
da su wajen yaki a tsakanin kasashe. Misali, kasar Amurka ta yi amfani da su a
kasar Iraki, lokacin da ta mamaye kasar a karo na farko. Ta yi amfani da su a mamayarta na biyu, bayan
tumbuke marigayi Saddam Hussein. Sannan
ta yi amfani da su a kasar Afghanistan, ko ince tana ma amfani da su har yanzu,
musamman a bakin iyakar kasar Pakistan da Afghanista. Har wa yau, ta girke ire-iren wadannan jirage
a kasar Djibouti, suna nazarin tsaro, kamar yadda kasar ta riya. Daga cikin wadanda ke kasar Djibouti ne aka
samu daya ya wuce gona da iri har ya shiga kasar Iran, inda ta kado shi. A halin yanzu dai, kamar yadda wani jami'in
sojin kasar Amurka ya sanar a cikin wani shiri na musamman da kamfanin yada
labarun kasar Kanada (Canadian Broadcasting Corporation – CBC) ya shirya
kan ire-iren wadannan jirage mai take: Remote Control Wars, kasar Amurka
ta mallaki jirage masu sarrafa kansu sama da 6,000. Sannan tana da na'urorin yaki masu sarrafa
kansu a sifar dan adam, da tsuntsaye, da kunamu, da kwari, wadanda duk inda aka
watsa su, suna iya tafiya, su nemo bayanai, su sanar da cibiyarsu halin da ake
ciki, ko ma, idan da hali, su kai hari.
Akwai wadanda musamman an yi su ne a sifar mutane, don daukan kaya a
lokutan yaki, ko ka ture su ka ture banza, ba su faduwa. Ire-iren wadannan sun kai guda 14,000. Manufar kasar Amurka na amfani da wadannan
jirage maimakon sojoji, a cewar Janaral Jumper a cikin wancan shiri na
musamman, shi ne rage hasarar rayukan sojojin kasar a filayen daga. To amma da yawa daga cikin masana 'yan kasar
na ganin wannan ba dalili bane, saboda wasu matsaloli da amfani da wannan
jirage lokacin yaki ke haddasawa masu girma.
Matsalolin Jirage Masu Sarrafa Kansu
Kafin mu yi bayani kan matsalolin da masu adawa da wannan sabon
salon yaki ke magana a kai, ya kamata mu san cewa, a irin yadda ake amfani da
su a yanzu, akwai nasaka ainun tattare da wadannan nau'in jirage. Da farko dai, duk da cewa suna iya doguwar
tafiya a sama, amma kuma babu wata dabara da aka tanada musu na fasaha da zai
iya taimaka musu idan man da jirgin ke amfani dashi ya kare. Wannan yana dauke da hadari mai girma. Domin idan bai riga ya kai inda zai aiwatar
da aikinsa ba mai ya kare, yana iya fadowa kan wani gari ko kauye. Bayan haka, wadannan jirage, duk da cewa na
kira su da suna "Jirage Masu Sarrafa" a hakikanin gaskiya ba su da
cikakken iko wajen aiwatar da ayyukansu.
Daga lokacin tashi har zuwa lokacin sauka, akwai wanda ke sarrafa tafiya
da tsarin gudanarwarsu. A hakan ma akwai
matsala, domin wadannan jirage ba su iya gano waye hakikanin abokin gaba da ake
son su darkake? Kuma idan abokan gaba
suka kama wasu sojojin kasar Amurka misali, ta yaya wadannan jirage za su iya
bambance su da wadanda suka kamo su, balle har su kashe abokan gabansu, ba tare
da sojojin Amurka sun raunatu ba? Har wa
yau, wadannan jirage ba za su iya gane yara da mata da tsofaffi ba a fagen
fama, balle su iya bambance su kafin su saki makamansu. Amma na kira su da wannan suna ne don
bambance su da makamai masu linzami.
Sannan ta tunani da cewa nan kadan za a samu masu cikakkiyar ikon
sarrafa kansu, kamar yadda za a karanta nan gaba.
Sanadiyyar ire-iren wadannan matsaloli ne ake ta samun kashe-kashen
fararen hula a dukkan kasashen da Amurka tayi amfani da irin wadannan jirage,
musamman kasar Iraki da Afghanista da Pakistan.
Cikin watan Nuwamba ne ma irin wannan jirgi ya kashe sojojin kasar
Pakistan guda 24, saboda bai iya tantance su da 'yan Taliban da yake son
kashewa. Wadannan jirage dai ba mutane
bane, balle su iya kyautata tunani ko su san ya-kamata. Shi yasa wani dan jaridar New York Times da
'yan Taliban suka yi garkuwa da shi a kasar Afghanistan yake ta addu'a. Domin sun kasa ajiye shi wuri daya; yau su
kai shi can, gobe su canza masa wurin
zama. Kuma a mota ake tafiya dashi,
inda, a cewarsa, suna jin karar jiragen nan a samansu. Ana cikin haka ne wani jirgi mai sarrafa
kansa ya darkake gidan da ke makwabtaka da inda aka ajiye shi. A cikin wannan shiri na CBC mai take Remote
Control Wars, wannan dan jarida yace Allah ya masa gyadan dogo da an aika
da shi barzahu. Babbar matsala ta karshe
ita ce, idan wannan sabon salon yaki na taimakawa wajen rage yawan mace-macen
sojoji a fagen fama, to, a daya bangaren
kuma, kamar yadda wani masanin harkar tsaro ya tabbatar, amfani da su na
taimakawa wajen kara tsana da kyamatar kasar Amurka a zukatan talakawan
kasashen da take da'awan ta ci su da yaki.
Wadannan su ne manyan matsalolin da ke tattare da amfani da wannan sabon
salon yaki.
Samar da Inganci
Daga cikin matsalolin da ke tattare da tsarin gudanarwar wannan
jirgi, akwai kokari da kasar Amurka ke yi wajen ganin ta samar da inganci,
musamman a bangarori guda biyu. Bangare
na farko shi ne kan abin da ya shafi matsalar karin mai a halin shawagi, kamar
yadda bayanai suka gabata. Cikin shekarar
2010 ne kasar Amurka ta dora wa masu bincike nauyin gudanar da bincike na
musamman don samo hanyar da jiragen za su rika shan mai a halin shawagi, ba
tare da wata matsala ba. Wannan tsari da
kasar ke bukatar a samar shi ake kira Inflight Refuelling. Sannan a daya
bangaren ta bayar da kwangilar kera wani jirgi mai cikakkiyar 'yanci da ta sa
wa suna Vulture, wanda ake tsammanin zai iya yin shekaru biyar yana
shawagi a sararin samaniya ba tare da ya sauka ba. Dankari! Wani aikin sai ilmi.
Bangaren matsala ta biyu, wanda ya kunshi rashin 'yancin da
wadannan jirage ke fama da shi – musamman rashin hankaltar abubuwa, da rashin
iya tantancewa tsakanin mutane biyu, da rashin iya tantancewa tsakanin abokin
gaba da sojin kasar Amurka misali – za a shawo kansu ne kadai idan aka iya
inganta tsarin gudanarwar jirgin. Hakan
zai samu ne ta hanyar amfani da "Fasahar Cikakkiyar 'Yanci" ko Autonomous
Technology a harshen Turanci. Wannan
sabuwar fasaha ce za ta iya mayar da jirgin ya zama kamar wani dan adam, mai
tunani, mai hangen nesa, mai mizanin tantance abubuwa, mai fahimtar muhallin da
yake, da dai sauransu. Wannan fasaha na
dogaro ne da tsarin gudanarwa kamar haka: samar da ingantacciyar tsarin tara
bayanai daga irin muhallin da yake ciki, watau Sensor Fusion kenan. Sai tsarin sarrafa bayanai da sadar da shi a
tsakanin jiragen, idan bukatar su yi aiki a muhalli guda ta kama, watau Communication
kenan. Sai tsarin tsara bigiren
tafiya, ta la'akari da yanayin matsaloli, da karancin mai da sauransu, watau Path
Planning kenan. Sai tsarin samar da
dabarun gociya ko kauciya ga jirgin a tafarkin tafiyarsa, idan wani abu ya
gabato, watau Trajectory Generation and Regulation kenan. Sai samar da tsarin tsara ayyukan gudanarwa a
tsakanin wani jirgi da abokan ayyukansu, watau Task Allocation &
Scheduling kenan. Sai kuma dabi'ar
gudanarwa da hadin kai a tsakanin wani jirgi da abokan ayyukansa, watau Cooperative
Tactics kenan.
Dukkan wadannan sababbin tsare-tsare da ake kokarin samarwa,
manufarsu ita ce, samar da tsarin tunani, da yanke shawara, da hangen nesa ga
wadannan jirage masu sarrafa kansu, ba tare da taimakon wani mutum da zai
sarrafa su daga wata uwa duniya ba.
Hakan kuma ba ya samuwa ta dadi, zunzurutun bincike ne ake ta gudanarwa
a halin yanzu, kan fannonin kimiyyar sadarwa da kere-kere irinsu: Control
Science, da Artificial Intelligence, da Expert Systems, da
Neural Networks, da Machine Learning, da Natural Language Processing,
da kuma fannin Vision. Dukkan
wadannan fannonin ilmi ne masu zurfi masu taimakawa wajen koya wa na'ura yadda
za ta yi tunani, da yadda za ta iya yanke shawara nan take, da yadda za ta iya
hangen nesa, da yadda zata iya yanke shawara sanadiyyar abin da ta hango, da
yadda za ta iya fahimtar muryar mutane, da bambancewa tsakanin mutane masu
murya biyu, da yadda za ta iya mallakar kanka, ta sanya wa kanta takunkumi, da
dai sauransu.
Shahararrun Nau'ukan Jirage Masu Sarrafa Kansu
A zangon karatu na baya masu karatu sun samu bayanai kan ma'ana da
tarihin jirage masu sarrafa kansu, watau Drine Aircraft, ko Pilotless
Aircraft, sannan muka ga yadda tsarin gudanarwarsu take, da yadda suke
tashi da yadda suke sauka, da kuma irin hadarin da ke tattare da su, wanda
wannan na cikin jerin matsalolin da a halin yanzu masana ke kokarin ganin sun
gyara, don samar da inganci mai gamewa. Mun kuma yi bayani cewa ire-iren
wadannan jirage, duk da cewa kasar Amurka ce ta fi zakewa wajen amfani da su a
duniyar yau, akwai wasu kasashe da dama da su ma suke da su a jibge. Daga cikinsu akwai kasar Ingila, da kasar
Isra'ila (wacce ta riga kasar Amurka mallakansu a farkon lamari), da kasar
Rasha, da kasar Jamus, da kasar Holand, da dai sauran kasashen nahiyar Turai. A yau za mu kawo bayani ne kan wasu daga
cikin shahararrun nau'ukan jirage masu sarrafa kansu. Sai dai galibi duk na kasar Amurka ne, domin
ita ce ta bayyana nata a fili fiye da sauran kasashe.
Nau'in jirgi na farko shi ne mai suna QinetiQ Zephyr Solar
Electric, wanda a halin yanzu an kiyasce cewa yayi shawagi na tsawon sa'o'i
336 da mintuna 22, watau kwatankwacin kwanaki 14 kenan tun bayan kera shi da
aka yi a watan Yuli na shekarar 2010. Akwai wani makamancinshi da aka kera a watan
Yuli na shekarar 2008, shi kuma ya kwashe sa'o'i 82 ne da mintuna 37 a sararin
samaniya. Wannan sunansa daya ne da
wanda ya gabace shi.
Sai kuma nau'i na gaba mai suna Boeing Condor, wanda aka
kera a shekarar 1989. Shi kuma a iya
tsawon rayuwarsa yayi shawagi na tsawon sa'o'i 58 da mintuna 11 ne kacal. A halin yanzu an masa ritaya, yana can a
girke a Gidan Tarihin kayayyakin sojin sama na kasar Amurka da ke Jihar
Kalfoniya. Sai wani nau'in QinetiQ
Zephyr da aka sake kerawa a shekarar 2007, wanda shi kuma aikin sa'o'i 54
kacal yayi. Sai nau'in IAI Heron, wanda
ba a tantance shekarar da aka kera shi ba, shi kuma shawagin sa'o'i 52 kacal ya
kwashe a sararin samaniya.
Akwai kuma wani nau'i mai suna AC Propulsion Solar Electric da
aka kera a watan Yuni na shekarar 2005.
Shi kuma sa'o'i 48 da mintuna 11 ya kwashe a iya shawaginsa. Sai kuma MQ-1 Predator da ba a
tantance shekarar da aka kera shi ba.
Sa'o'insa 40 ne da mintuna 5 a sararin samaniya. Sai GNAT-750 da aka kera a shekarar
1992, yana daga cikin tsofaffin jirage.
Ya kwashe sa'o'i 40 ne kacal yana shawagi. Akwai TAM-5 da ya bayyana a watan
Agusta na shekarar 2003. Shi kuma ya
kwashe sa'o'i 38 ne da mintuna 52 a sararin samaniya. Wannan shi ne mafi kankanta daga cikin jirage
masu sarrafa kansu da kasar Amurka ta kera, wadanda za a iya cilla su sararin
samaniya su yi dogon zango; TAM-5 ne mafi kankanta daga cikinsu.
Sai kuma nau'in Aerosonde da aka kera a watan Mayu na
shekarar 2006. Ya kwashe sa'o'i 38 ne
kacal da mintuna 48 a shawaginsa. Sai
wani nau'i da aka kera don daukan kayan soji mai suna Vanguard Defense. An kera shi ne a watan Fabrairu na
shekarar 2011, watau shekarar da ta gabata kenan. Shi kuma ya zuwa yanzu ya kwashe sa'o'i 2 ne
da mintuna 55. Tunda ba a jima da kera
shi ba. Sai nau'i na karshe da za mu
dakata a kansu mai suna TAI Anka da aka kera a watan Disamba na shekarar
2010. Shi kuma tafiyar kwana daya kacal
yayi, watau sa'o'i 24 kenan.
Wadannan, a takaice, su ne shahararrun jirage masu sarrafa kansu da
suka yi dogon zango a rayuwarsu. Akwai
wadanda ake kerawa a halin yanzu da aka sa ran su kwashe watanni ko ma shekara
suna shawagi a sararin samaniya wajen tattaro bayanai ko kai hari ko kuma yin
dako don gano shirye-shiryen abokan gaba.
Yanzu aka fara, wai mahaukaciya ta shiga gada sau tara. Wannan wani zamani da muka shigo da kowace
kasa ke kokarin kwatan kanta a bangaren tsaro ta hanyar kwarewarta a fannin
kimiyya da fasahar sadarwar zamani.
Wacce bata fadaka ba kuma, ita ta jiwo, sautun mahaukaciya. Allah mana gamo
da katar, amin.
No comments:
Post a Comment