Matakan Bacci
Baya bayani ya gabata cewa akwai nau'ukan
bacci guda biyu; da bacci mai nauyi, da mara nauyi. Mai nauyin, wanda Malaman Kimiyya ke kira Non-Rapid
Eye Movement (NREM) Sleep, yana dauke ne da matakai guda hudu. Da gajeren
bacci ko gyangyadi, kamar yadda na kira shi, da mataki na biyu wanda ke dauke
da bacci na hakika. Wannan shi ne
matakin da malaman kimiyya ke kira True Sleep. Har dai zuwa mataki na hudun. Nau'i na biyu kuma shi ne madaidaicin bacci,
wanda suka kira Rapid Eye Movement (REM) Sleep. A wannan mataki ne
kwayan idanun mai bacci ke jujjuya a sadda yake bacci. Sai dai kuma, sabanin yadda bayanai suka zo,
idan dan adam ya shiga bacci, matakan da yake bi cikin baccin sun sha
bamban. Ba wai daga gyangyadi yake
farawa, daga nan ya wuce matakan nau'i na farko, ya shiga na biyu, daga nan ya
farka ba. Abin ya wuce haka.
Da zarar mutum ya kwanta bacci zai bi
matakin farko na bacci mai nauyi, zuwa matakin bacci na biyu, da mataki na uku,
da mataki na hudu. Wannan kan faru har
na tsawon mintuna 90, kafin mai bacci ya shiga nau'in bacci na biyu, wato
madaidaicin bacci kenan. Idan ya shiga
madaidaicin bacci, zai ci gaba da yin bacci, kafin wani lokaci sai kuma ya sake
dawowa matakin bacci mai nauyi na uku,
wato Delta Sleep kenan, kamar yadda bayani ya gabata a baya. Daga nan ya
sake gangarowa matakin bacci na biyu, wato True Sleep. Da zarar ya kwashi mintuna 20 a wannan
mataki na bacci, sai kuma ya sake komawa nau'in bacci na biyu, wato nau'in
baccin da kwayar idanunsa za su rika jujjuyawa a ciki. Bincike ya nuna cewa masu bacci kan maimaita
wannan yanayi sau uku zuwa hudu a kowane lokacin baccinsu, daga nan kuma sai su
farka. Wannan ke nuna mana cewa, bayan
mai bacci ya wuce mataki na farko har zuwa na hudu, zai shiga yanayin bacci
madaidaici, daga nan sai baccinsa ya sake nauyaya, sanadiyyar komawa mataki ba
uku, daga nan kuma ya saukaka, sanadiyyar shiga mataki ba biyu, sai ya sake
komawa yanayi madaidaici. Wannan zai
maimaitu kamar sau uku ko hudu kafin farkawa.
To me ke haddasa bacci ne?
Me Ke Haddasa Bacci?
Wannan tambaya ce da galibin masana suka
ta kokarin amsa ta tsawon shekaru, amma har zuwa wannan lokaci samun amsa
gamsasshiya ya gagara. Wani mai tambaya
a yanar sadarwa ta duniya ya jera wasu tambayoyi kan asali da samuwar bacci ga
dukkan masu binciken kimiyya a duniya, wanda a cawarsa har yanzu sun kasa
amsawa. Yace me yasa, duk kwarewarsu a
fannin kimiyya, da samuwar hanyoyi da na'urorin sadarwa da binciken kimiyya a
duniya, amma sun kasa gano abin da ke haddasa bacci? Yace idan har da gaske suke yi a fanninsu na
bincike wanda a kanshi suka kware kuma aka sansu, me yasa har yanzu suka kasa
gano dalilin da yasa dan adam da sauran halittu ke bacci? Ta yaya aka yi suka kera kumbo har suka je
duniyar wata, suka jefa wasu kumbon nazari da bincike zuwa wasu duniyoyin, suka
gano cututtuka da yadda ake tiyata har ma a cire zuciya a dasa wata, a cire
koda a dasa wata, amma ga bacci, wanda dabi'a ce da dan adam ya sifatu da ita,
kuma shi ne abin da dan adam yafi yi cikin kashi biyu na ukun rayuwarsa, amma sun
kasa gano dalili da abin da ke haddasa shi?
A hakikanin gaskiya akwai alamar cewa
lallai malaman kimiyya sun gaza a wannan janibi. Farfesa Allan Rechtschaffin, babban malami a
fannin bincike kan bacci da yadda yake samuwa, wanda farfesa ne a Jami'ar Chicago
da ke kasar Amurka, ya kwashe shekaru 50 yana gudanar da bincike kan bacci
yadda yake samuwa da dukkan alamunsa.
Amma da kansa ya sanar da mujallar New York Times cewa, sadda aka
masa tambaya kan dalilin da ke sa dan adam ya shiga yanayin bacci, yace:
"Wannan wani kalubale ne mai girma ga malaman ilmin halitta
(Biologists)." A wani wuri kuma da
tambaya makamanciyar wannan ta sake maimaituwa, sai ya sake cewa: "A
takaice dai, har yanzu babu wani bayani kan me yasa muke bacci; kawai muna yi
ne a duk sadda baccin ya dauke mu."
Wannan kamar alamar gazawa ce, to amma akwai da yawa cikin malaman
kimiyya da ke ganin har yanzu bincike ake yi, kuma ba a fid da rai ba.A
hakikanin gaskiya dai gano hakikanin abin da ke haddasa bacci abu ne mai
wahala, domin alakar da ke tsakanin bacci da ruhin dan adam.
Agogon Dabi'a (Biological Clock)
Duk da cewa ba a gano hakikanin abin da
ke haddasa dan adam bacci ba, cikin bincike da ake yi an gano lallai akwai wani
yanayi na dabi'a da ke cikin jikin dan adam, wanda ke la'akari da yanayin
mahalli, don tilasta wa jiki shiga yanayin bacci. Wannan yanayin dabi'a kuwa shi ne abin da a
turancin kimiyya suke kira Biological Clock, ko Circadian
Rhythm. Wannan yanayi tun cikin
shekarar 1960 malaman kimiyya suka tabbatar da samuwarsa a jikin dan adam. Wasu malamai kan kira shi Cibiyar Bacci, wato
Sleep Center, amma babu wanda ya san a ina yake a jikin dan adam. Wasu na ganin a kwakwalwa yake. Sai dai wannan hasashe ne. yanayi ne kawai gamamme, wanda ke amfani da
mahallin da dan adam ke rayuwa a ciki.
Malaman kimiyya suka ce idan dan adam
yana rayuwa a wuri, sai dare ko yamma ya shiga, nan take dabi'ar halittar jikinsa
zai fahimci canjin yanayi a muhalli. Daga nan
sai wannan agogon dabi'a ya tilasta wa jikin dan adam samar da wani
sinadari mai suna Melatonin wanda ke haddasa bacci nan take. Da zarar gari ya fara wayewa kuma, jikin adam
zai sinsini irin canjin da ke faruwa a lokacin da gari ya fara wayewa, sai
wannan sinadari na Melatonin ya fara narkewa ko zagwanyewa, sai bacci ya
kaura daga idanun mai bacci, ya farka. Da zarar rana ta fito, ko an shiga
lokacin yini kuma, sai hasken rana ya hana wannan sinadari na Melatonin zuba.
Wannan abu ne mai kamar saukin fahimta, amma yiwuwarsa ya sha bamban da yadda
mai karatu ke karantawa ko hankaltarsa a zuciyarsa daga abin da yake karantawa
a yanzu. Domin na san yanzu haka wani
zai ce ya aka yi wasu ke yin bacci da rana?
Wannan tambayar ma dai har yanzu tana jiran amsa.
Sabubban Samuwar Bacci
Duk da cewa malamai basu gano hakikanin
abin da ke haddasa bacci ba, amma sun gano sabubba da dama, wadanda ke da alaka
na kut-da-kut wajen jefa dan adam cikin yanayin bacci. Daga cikinsu akwai yawan gajiya. Kamar yadda
masu karatu suka sani, yawan gajiya kan sabbaba bacci. Abu na biyu shi ne cin bashin bacci. Ma'ana, a rashin kwanciya a lokacin da ya kamata
mutum ya kwanta, wato lokacin da bacci ya bijiro masa kenan. Galibi mukan sha shayin kahwa ko mu tauna
goro don hana bacci zuwa, ko mu sha wasu kwayoyi ko a mana allura. Duk wadannan kan hana bacci ne na wani dan
gajeren lokaci, amma ba har abada ba.
Binciken malamai ya nuna cewa cin wani abu ko shan wani abu da manufar
hana bacci zuwa a lokacin da ya kamata a yi shi, yana da cutarwa mai girma,
sannan hakan kan canza dabi'ar jikinsa (ma'ana agogon dabi'arsa) wanda ke
bayuwa zuwa ga canza masa lokacin bacci.
Cin bashin bacci, abin da malamai ke kira
Sleep Debt, yana da illa sosai, kuma kwashe tsawon yini ana bacci ba ya
sa mutum ya biya bashin baccin da ake binsa.
Domin kuwa lokacin baccinsa ya riga ya canza, dole sai ya sake tarbiyyar
dabi'ar jikinsa wajen tilasta mata yin bacci a lokacin da ya kamata yayi. Galibin masu gadi a lokutan dare kan samu
matsalar bashin bacci, musamman idan aka sake canza musu lokacin aiki zuwa
rana.
Daga cikin dalilan da ke haddasa bacci
akwai yanayin mahalli, kamar yadda bayani ya gabata. Da zarar yamma ya gabato, akan samu sauyin
yanayin dabi'ar jiki (Biological Clock), wanda hakan ke haddasa samuwar
sinadarin Melatonin, nan take sai jiki ya fara canza yanayinsa, daga
farkawa zuwa kasalar da ke kai mutum ga bacci.
Daga cikin abin da ke canza yanayin zuban wannan sinadari dai akwai
yawan zama cikin duhu a kullum, da yawan zama cikin haske a lokacin dare; duk
suna canza yanayin zubansa.
Rashin Bacci
Rashin bacci matsala ne mai girman gaske
ga dan adam. Domin yana rage kaifin
fahimta. Sannan dan adam kan shiga wani
yanayi na rashin daidaituwar kwakwalwa da fahimtar abubuwa. Rashin bacci kan taimaka wajen yawan zuban
sinadaran insulin a jikin dan adam, wanda hakan ke taimakawa wajen haddasa
yawan kiba a jiki Rashin bacci na
haddasa yawan mantuwa, domin kwakwalwa kan samu kanta ne cikin halin rudu. Bincike ya nuna cewa rashin bacci na tsawon
awanni 17 na iya haddasa nakasar darajar fahimta a kwakwalwar dan adam da kashi
0.05%, iya gwargwadon abin da zai iya sa mutum ya shiga halin maye idan ya sha
barasa cikin moda biyu. Rashin bacci na
haddasa hauhawan jini ga dan adam, da kuma yawan kiba, kamar yadda bayani ya
gabata.