Matashiya
Wannan shi ne kashi na 6 a jerin kasidun da muka fara kawowa a
watannin baya. Muna dada tunatar da masu
karatu cewa duk mai rubuto tambaya, to, ya sa suna da adireshinsa. Idan babu cikakkiyar suna da adireshi ba za a
buga sako ba. Sai a kiyaye. Bayan haka, ina sanar da masu karatu musamman
wadanda ke garin Katsina, cewa ranar Asabar, 5 ga watan Janairu, zan zo garin
Katsina don gabatar da lacca mai taken: "Rayuwar Matasa a Shafukan Sada
Zumunta na Intanet," wanda kungiyar Tsangayar Alheri ta gayyace ni. Za a yi taron ne a Makera Hotel da ke hanyar
Daura, a Katsina.
Tallafi Daga Fannin Kwamfuta da Sadarwa
Kamar yadda mai karatu ya karanta a baya, wannan fanni na Tsarin
Gadon Dabi'u da Siffofin Halitta, wato Genetics, fanni ne da ke saurin
habaka, duk da tsauri da tsananin tsadar bincike da fannin ya siffantu da
su. Daga cikin dalilan da suka haddasa
wannan ci gaba a cikin shekarun da basu wuce ashirin da biyar ba, akwai ci gaba
a fannin sadarwa da kwamfuta, ko kuma fannin sarrafa bayanai dai a takaice,
wato Information Technology kenan.Wannan a fili yake. Domin duk wanda ya dubi tsarin gudanar da
bincike a wannan fanni, ya san kwarin idanu, da kaifin gani kadai ba su isa su
taimaka wa fannin ci gaba ba, sai da tallafin ci gaban kimiyyar sadarwa da
kere-kere. Domin dukkan sinadaran da ake
gudanar da bincike a kansu ba abubuwa bane da ake iya gani da kwayar idanu, nan
take. Galibinsu sai ta hanyar na'urar
kambama abubuwa (Microscope) ake iya hangarsu, a fahimci yanayinsu, a yi
nazarin tsarinsu da abin da suka kunsa, kafin a gano duk abin da ake son ganowa
don taskance su a rubuce ko a zane.
Wannan sashe zai yi dubi ne zuwa ga wasu daga cikin shahararrun
masarrafai ko manhajojin kwamfuta da kwararru kan wannan fanni suke amfani da
su wajen tantance tsarin bincike a wannan fanni na Tsarin Gadon Dabi'u da
Siffofin Halitta (Genetics). Akwai bangarori
shahararru da wadannan masarrafai suka shafa, kuma za mu dubi nau'ukan
manhajojin kwamfuta da aka gina a cikinsu, masu amfani a babbar manhajar Windows
na kamfanin Microsoft Inc. Na
farko, kwai manhajoji na musamman a bangaren nazari da tantance yanayin Madarar
Dabi'un Halitta, wato: "Deoxyribonucleic Acid" ko "DNA" a
takaice. A bangare na biyu kuma, akwai
manhajoji ko masarrafan kwamfuta da aka gina don nazarin mahallin DNA, da
sauran sinadaran da suka dangance shi, wajen fahimtar tsarinsu da gudanar da
bincike kansu. Na uku akwai manhajoji na
musamman kan nazarin sinadaran kara kuzari da ke cikin kwayar halitta, wato: Cell
Protein Analysis. Na hudu kuma sai manhajoji da aka gina kan nazarin fannin
alakar da ke tsakanin kwayoyin halitta wajen bunkasa da habaka, ba bangaren
kamaiceceniya wajen dabi'u ba kadai.
Wannan fanni kuwa shi ake kira Phylogenetics. Duk da cewa a farko ba mu tabo wannan
fanni ba, amma ganin cewa muna nazarin manhajojin ne a jumlace, shi yasa na
kawo mana. Bayan wadannan fanno akwai
wasu fannonin dai daban.
Kafin mu ci gaba, zai dace mai karatu ya fahimci cewa, su wadannan
manhajoji na kwamfuta aikin su shi ne tantance bayanan da aka shigar musu a
rubuce, ko a tsarin hotuna, ko kuma a tsari ko yanayin zane. Sannan bayanan na iya kasancewa ta hanyar
tsarin shigar da bayanai ne, wato a rubuta da hannu ta hanyar allon shigar da
bayanai na kwamfuta, wato: Keyboard, ko kuma ta tsarin wasu manhajoji ko
na'urorin sadarwa, irin su na'urar daukan hotuna, wato Scanning Machine, ko
na'urarorin tantance zafi ko adadin sinadarai da ake amfani da su irin su: PCR
Machine (wato Polymerase Chain Reaction Analysis) da aka saba amfani
dasu a dakunan binciken kimiyyar sinadarai tun sama da shekaru ashirin da suka
gabata. Ta wadanan hanyoyi ne ake samun
bayanan da wadannan manhajojin kwamfuta da za mu yi magana a kansu yanzu ke
sarrafawa, don taimaka wa likitoci ko masu bincike a wannan fanni fahimtar
alaka, da kamaiceceniya, ko bambance-bambancen da ke tsakanin nau'ukan kwayoyin
halitta da siiffofi da kuma dabi'unsu.
Manhajojin
A fannin nazarin Madarar Bayanan Dabi'ar Halitta, wato DNA, akwai
manhajar MyRAST wacce ke taimakawa wajen tantance nau'ukan kwayoyin halittar
dabbobin da kwayar halittarsu bata kai ta dan adam ba wajen bunkasa. A baya abu
ne mai wahala a iya tantace wadannan kwayoyin halitta a bangare daya, tare da
sanya musu rubutacciyar alama, cikin tsibin bayanan da ake dasu kan nau'ukan
kwayoyin halitta. Amma samuwar wannan
manhaja ya taimaka matuka, inda a rana daya, bayan tara dukkan bayanan da ake
dasu kan kwayoyin halitta, da wannan manhaja sai a tantance kowane irin kwayar
halitta daban, tare da alamar kowanne, don sawwake ayyuka da tsarin
bincke. Sai manhaja mai suna Gene
Designer, wadda ke taimakawa wajen tattaro bayanan sinadaran Amino Acid da
ke kwayar halitta, da kuma sinadaran Madarar Dabi'ar Halitta a daya bangaren,
don fahimtar yadda wadannan sinadarai ke haduwa wajen samar da kamaiceceniya
tsakanin halittu ko zuri'o'i.
Sai manhajar CLC Free Workbench, wadda ke taimakawa wajen
hado bayanan da suka shafi Madarar Dabi'ar Halitta (DNA) da sinadaran kara
kuzari na kwayar halitta (Cell Protein), tare da tsara su a reshe daya, don
taimaka wa masu bincike yin fashin-baki kan alakokin da ke tsakaninsu. Mai nazari na iya samun wadannan bayanai
cikin shafi guda, ta hanyar wannan masarrafa.
Sai masarrafa mai suna Geneious, wadda kamfanin Alexei
Drummond Biomatters Ltd da ke birnin Auckland na kasar New Zealand ya
gina. Amfanin wannan masarrafa dai shi
ne taskance bayanan da suka shafi dukkan Taswirar Dabi'ar Halittar dan adam
baki daya, wato Human Genome, a cikin kwamfuta, tare da sawwake hanyoyin
mu'amala da bayanan cikin sauki. A
takaice dai wannan masarrafa ko manhaja kamar "Rumbun Bayanan Kwayoyin
Halitta" ne, mai dauke da kafofin karawa, ko ragewa, ko nemowa, ko
adanawa, ko kuma tasarrafi da su baki daya.
Akwai kuma manhajar ganin taswira da hotuna da bayanan da suka
shafi kwayoyin halitta da dukkan abin da ya dangance su, cikin sauki. Wannan manhaja kuwa ita ce: Genome2D, wacce
aikinta shi ne budo bayanan kawai, a kowane irin siffa ko yanayi suke. Sannan kana iya aikawa da bayanan da kake
bukata cikin sauki, zuwa wani mahallin don sarrafa su. Sai manhajar PHIRE, wanda aka gina da
tsarin gina manhajar kwamfuta mai suna Visual Bacic na kamfanin Microsoft. Wannan manhaja dai aikinta shi ne
taimakawa wajen binciko (ta hanyar tambaya – search) nau'ukan kwayoyin halitta
masu dauke da cututtuka (Bacteriophage) da ke jerin bayanan Taswirar Dabi'ar
Halitta, tare da tare da tantance su ta yanayi da tsari mai kayatarwa ga masu
bincike ko nazari. Su wadannan kwayoyin
dabi'un halitta da suka harbu da cututtuka, ana amfani ne dasu wajen yin
kwaskwariman wasu kwayoyin halittar, don haka ake taskance bayanansu don amfanin
gaba.
Akwai kuma manhajar MB DNA Analysis, wadda Mista Oleg
Simakov ya gina. Wannan manhaja dai
kyauta ce, kuma amfaninta shi ne iya tantace bayanan siffofin sinadaran kwayar
halitta da ake bukata don yanke hukunci kansu.
Hakan kuwa ya hada da yanayin alakokin da ke tsakaninsu, da girman
yanayinsu, da kuma lissafin madaukan da ke cikinsu, don tantance hakikaninsu,
da dai sauran abubuwa masu gamsarwa wajen nazari da bincike. Sai manhajar GenePalette, wacce ake
amfani da ita wajen iya tsakuro bayanan taswirar dabi'ar halitta daga rumbun
adana wadannan bayanai na kasar Amurka (GenBank Database), kan nau'ukan
kwayoyin halittar dabbobi daban-daban, tare da jero su ta yadda mai nazari zai
iya ganinsu tsaf, har ya gudanar da nau'in nazarin da yake son gudanarwa a
kansu. Akwai kuma manhajar UniPro
DPview wadda kamfanin UniPro Bioinformatics Groups da ke kasar Rasha
ya gina. Wannan manhaja na da muhimmanci
ne wajen iya nemo bayanan taswirar dabi'ar halitta, tare da tantance
kamaiceceniyar da ke tsakaninsu, sannan ta taimaka wa mai bincike wajen tsara
alaka a tsakanin bayanan, ta hanyar wasu ka'idoji da zai iya ginawa.
Bayan wadannan har wa yau, akwai manhaja mai suna SEQtools, ita
ma manhaja ce ta musamman da ake amfani da ita wajen gudanar da nazari kan madarar
bayanan dabi'ar halitta, tare da sinadaran kara kuzarin kwayar halitta (Cell
Protein), tare da jera su, da tantance bayanan da suka shafi sinadaran Enzymes
da dai sauransu. Akwai kuma manhajar
GENtle mai taimakawa wajen gyara bayanan da suka shafi Madarar Dabi'ar
Halitta (DNA), da sinadaran Amino Acid, da lura da rumbun bayanan
kwayoyin halitta, da dai sauransu makamantansu.
Sai manhaja ta karshe da za mu dakata a kanta a bangaren nazarin madarar
bayanan dabi'ar halitta (DNA) mai suna DNA Club. Wannan manhaja aikinta shi ne yin amfani
da tsarin zanen hotuna mai inganci (Vector Graphics) wajen nazarin
bayanan da suka shafi dukkan sinadaran kwayar halitta (Cell Properties).
A bangaren nazarin zane ko hotunan da suka shafi sinadaran mahallin
Ma'adanar Dabi'ar Halitta (Plasmid Graphics), akwai manhajoji masu
mahimmanci sosai. Da farko akwai
manhajar Ape Plasmid Editor, wadda Mista Wayne Davis da ke Jami'ar Utah
ta kasar Amurka ya gina. Wannan masarrafa
aikinta shi ne zanen hotunan bayanan kwayoyin halitta da take daukowa daga
Babbar Rumbun Bayanan Dabi'ar Halitta (GenBank) don nazarinsu, da kuma tsara
taswira na musamman da ake iya amfani da masarrafar BLAST don tantance
su. Wannan masarrafa na amfani da
launuka wajen tsara wadannan zane don kayatarwa. Manhaja ta gaba a wannan fanni
ita ce: pDRAW32 wadda ake amfani da ita wajen shigar da sunayen
sinadaran madarar dabi'ar halitta (DNA), tare da tantance kusurwarsu a zanen
taswirar mahallinsu. Kamfanin da gina wannan manhaja shi ne AcaClone
Software Inc.
Sai manhaja ta musamman mai suna Plasmid Processor, wadda
ake amfani da ita wajen bayyana hoton sinadaran da ke mahallin madarar dabi'ar
halitta (DNA) don yin nazarinsa a makarantun jami'o'i da sauran cibiyoyin
binciken kimiyyar sinadaran jikin dan adam.
Akwai kuma manhajar BVTch Plasmid wadda ake amfani dai ita wajen
zanen hoton taswirar sinadaran mahallin dabi'ar halitta (Plasmid Map), a
siffar tagwaye ko tilo (Double or Single Strand). Da wannan masarrafar za ka iya yin zanen,
tare da lika wa kowane bangaren sinadarin suna ko alamar rubutu da ke nuna
yanayi ko hakikaninsa. Sai masarrafa ta
karshe a wannan fanni mai suna PlasmaDNA, wadda ta masu koyon nazari ne
a wannan fanni. Tana taimakawa ne wajen gwama
nau'ukan dabi'un halitta daban-daban don samun kamaiceceniya, wato Gene
Cloning kenan. Sai kuma bayar da dama wajen taskance bayanan da suka shafi
ayyukan da mai nazari yayi kan wadannan nau'ukan dabi'un halitta. Wannan
manhaja ce mai sauki wajen ta'ammali ga dukkan mai nazari.
Kammalawa
Wadannan su ne shahararrun manhajoji da aka gina masu taimaka wa
masu nazarin sinadaran kwayoyin halitta a kimiyyance, tare da tsara su, don
kokarin samar da waraka ga galibin matsalolin da ake dasu na cututtuka masu alaka
da Tsarin Gadon Dabi'u da Siffofin Halitta a tsakanin jinsin mutane, da wuraren
da suka fito, da kuma yanayin jikinsu.
No comments:
Post a Comment