Binciken Malaman Kimiyya na Farko
A makon da ya gabata masu karatu sun
karanta bayanai kan hakikanin yadda halittar zuciya da kwakwalwa suke a
kimiyyance, da kuma irin yadda bincike ya faro kan wadannan gabobin jikin dan
adam masu muhimmanci tun daruruwan shekaru da suka gabata. Kada a mance dai, muna gudanar da bincike ne
dalla-dalla kan asalin tunani tsakanin zuciya da kwakwalwar dan adam; wanne ne
yake da hakkin samar da tunani? A yau
cikin yardar Allah ga bayanai kan binciken malaman kimiyyar halitta na farko
kan wasu daga cikin yanayin da suka shafi zuciya dangane da alakarsa da
kwakwalwa, da kuskure ko daidai din da binciken ya kunsa. Wannan shi ne bincike na uku. A mako na gaba za mu kawo tsarin tunani a
kwakwalwa kamar yadda malaman kimiyyar halittar dan adam ke karantarwa a
jami'o'in duniya a yau. Sannan mu
karkare da bincike kan sabon nau'in binciken da ya bullo kan alakar kwakwalwa
da zuciyar dan adam, inda a karshe za mu tantance gabar da ke samar da tunani a
tsakaninsu; zuciya ne ko kwakwalwa.
Allah sa mu dace.
Bayan sun gudanar da bincike kan hakikanin yadda zuciya da
kwakwalwa suke aiki, malaman kimiyyar halittar dan adam a baya sun fitar da
sakamakon wasu bincike wadanda a baya aka dogara kansu wajen fahimtar tsarin
gudanarwar kwakwalwa da alakarsa da zuciya.
Binciken farko kan alakarsa da bugun zuciya ne. Bincike na biyu kuma kan alakar kwakwalwa ne
da babbar tsarin sadarwar jiki baki daya, watau Automatic Nervous
System. Sai bincike na uku da ya
shafi tsarin sadarwa tsakanin zuciya da kwakwalwa. A halin yanzu ga bayani nan filla-filla.
Bincike na Farko
Nau'in sakamakon bincike na farko da malaman kimiyya suka gudanar a
baya ya ta'allaka ne kan kwakwalwa da bugun zuciya. Suka ce kwakwalwa ne ke haddasa bugun zuciya
(watau Heartbeat), ta amfani da jijiyoyin tsarin sadarwar jiki, watau Automatic
Nervous System (ANS). Wannan na daga cikin dadaddun bincike da malaman
kimiyyar halittar dan adam suka yi kan wannan lamari. Amma daga baya, bayan habbakan hanyoyin
bincike da karuwar ilmi, an gano cewa babu alaka tsakanin bungun zuciya da
taimakon kwakwalwa ko kadan, ta wannan bangare.
An kuma gano kuskuren wannan bincike ne lokacin da aka fara aiwatar da
tiyata ko dashen zuciya. A halin yanzu
an tabbatar da cewa zuciya ba ta bukatar wayoyin sadarwar da za su samar mata
da makamashin maganidisun lantarki don haddasa bugawarta. Domin ita kanta zuciya tana dauke da irin
wadannan wayoyin jijiyoyin sadarwa wajen sama da dubu arba'in (40,000), wadanda
ke rike ta, tare da taimaka mata wajen bugawa a kowane lokaci. Don haka ba ta bukatar taimakon wadannan
wayoyin sadarwa daga kwakwalwa. A
karshe, gaskiyar sakamakon wannan bincike yana fitowa fili karara a duk lokacin
da ake aikin dashen zuciya. Idan aka zo cire matacciyar zuciyar, ana yanke
dukkan jijiyoyin wayoyin sadarwar da suka zo daga kwakwalwa ne, sannan sai a
jona sabuwar da ake son dasawa. An gano
cewa da zarar an dasa sabuwar, kafin a jona wayoyin jijiyoyin sadarwar da suka
zo daga kwakwalwa, nan take zuciyar ke fara aiki. Don haka, da bugun zuciya na samuwa ne ta
taimakon wayoyin jijiyoyin sadarwar da suka zo daga kwakwalwa, da babu yadda za
a yi wannan sabuwar zuciya da aka dasa ta kama aiki ba tare da an jona mata
jijiyoyin da suka taso daga kwakwalwa ba.
Nan take aka sake gudanar da bincike cikin zuciya don gano dalilin
hakan, sai aka samu akwai ire-iren wadancan wayoyin sadarwa (watau Nerve
Cells) a zuciya sama da dubu arba'in.
Bincike na Biyu
Sakamakon bincike na biyu an fitar da shi ne a shekarar 1970, kamar
yadda Cibiyar Binciken Kimiyya da ke Fels ta kasar Amurka ta tabbatar,
watau Fels Research Institute, kuma abin da sakamakon ya tabbatar a
wancan lokacin dai shi ne: gamammen tsarin sadarwar jikin dan adam (Automatic
Nervous System) ne ke hada alaka tsakanin zuciya da kwakwalwar dan
adam. Sakamakon wannan bincike, kamar
wanda ya gabace shi, bai dore ba. Domin
bayan tsawon zamani da samuwar karin hanyoyin bincike, an gano cewa ba wannan
tsarin sadarwa bane ke hada alaka tsakanin zuciyar dan adam da
kwakwalwarsa. Bayanai na tafe kan
bangarorin jikin da ke haddasa wannan tsarin sadarwa, in Allah ya so.
Bincike na Uku
Bincike na uku an gudanar da shi ne a shekarar 1983, kuma abin da
sakamakon binciken ke cewa shi ne: akwai wasu sinadaran sadarwar jiki da a
Turancin kimiyya ake kira Hormones, masu dauke da maganadisun lantarkin
sadarwa, su ne ke haddasa alakar sadarwa a tsakanin kwakwalwa da zuciyar dan
adam. Wannan sabon bincike ne ya
inganta, ko ya gyatta kuskurarriyar fahimtar da ake da ita kan binciken
shekarar 1970 da ya gabata, cewa gamammen tsarin sadarwar jiki ne ke hada alaka
tsakanin zuciya da kwakwalwa. Wannan
sabon bincike dai ya dada samun shahara ne daidai lokacin da cibiyar bincike na
HeartMath Institute da ke jihar Kalfoniya ta gudanar da bincike kan
hakikanin gabar jikin dan adam da ke samar da tunani.
Binciken cibiyar HeartMath ya tabbatar da cewa wadannan
sinadarai masu gamewa a jikin dan adam, su ne ke daukan maganadisun lantarkin
sadarwa – watau Electromagnetic waves – daga zuciya, zuwa dukkan sassan
jikin dan adam, ciki har da kwakwalwa.
Shi yasa da zarar zuciyar dan adam ta hankalci canji a yanayin da take,
(misali a ce ka shigo inda ake ta hayaniya, ko zage-zage tsakanin mafadata
biyu, nan take zuciyarka za ta hankalci yanayin da ta shiga, sai ta aika wa
sauran gabobin jiki, sai dabi'arsu ta canza.
Wannan tsarin aika sako na samuwa ne cikin kiftawa da bisimilla, ta
hanyar wadannan sinadaran Hormones da ke kaikomo tsakanin zuciya da
sauran gabobin jiki, ciki har da kwakwalwa.
Wadannan, a takaice, su ne nau'ukan bincike uku da aka fara gudanarwa a
baya wadanda suka danganci alakar da ke tsakanin kwakwalwa da zuciyar dan adam
wajen aikawa da sako, wanda hakan, ko shakka babu, yana da alaka ta kai-tsaye
wajen kintsa tunani.
Tsakanin Nassin Kur'ani da Binciken Malaman Kimiyya
To, a daya bangaren kuma wasu kan damu cewa, me yasa idan masu
bincike suka ce abu kaza kaza ne, daga baya kuma sai su sake cewa ba haka bane,
kaza ne. Wannan yasa da yawa cikin mutane, musamman a kasar Hausa, basu cika
yarda da binciken Malaman Kimiyyar zamani ba kan wasu abubuwa da suka shafi halittar
dan adam, ko sararin samaniya da dai sauran abubuwa makamantansu. A wasu lokuta za ka samu abin da Malaman
Kimiyya suka fada a baya ya saba wa abin da Kur'ani ya tabbatar, daga baya kuma
idan suka zurfafa bincike, sai sakamakon bincikensu ya tabbatar da abin da
Kur'ani ya fada. Al'amura irin wannan
sun sha faruwa a baya. Daga cikin
shahararrun misalai akwai binciken malaman kimiyya a farkon zamani cewa rana ba
ta motsawa, sai dai sauran halittun sararin samaniya. Amma Kur'ani ya tabbatar da cewa rana tana
juyawa ita ma a cikin falakinta, kamar yadda hakan yake tabbace a cikin Suratu
Yaasin. Da bincike ya tsawaita, sai
malaman sararin samaniya suka tabbatar cewa
lallai rana ita ma tana juyawa, ba wata da sauran taurari kadai ke
juyawa ba. Me yasa ake samun haka? Shin, wannan sabani da a farko ake samu
tsakanin nassin Kur'ani ko Hadisi da sakamakon binciken malaman kimiyya, dalili
ne da zai sa a daina yarda da bincikensu baki daya?
A tunani na hakan ba dalili bane, ko kadan. Illa dai, a matsayinmu na musulmi, duk abin
da Kur'ani ya tabbatar da shi wajibi ne mu gasgata shi, ko da kuwa ba mu iya
hankaltar faruwa ko yiwuwarsa a lokacin da aka gaya mana. Domin nassin Kur'ani ko Hadisi ba su canzawa,
amma binciken duk wani mai bincike, yana iya dacewa, sannan yana iya
kuskure. Abin da ke nuna dacewarsa shi
ne yayi daidai da abin da nassin shari'a ya tabbatar. Abin da zai nuna kuskurensa kuma shi ne ya
saba wa abin da nassin shari'a ya tabbatar.
Domin masu gudanar da binciken nan 'yan adam ne kamarmu. Bambancin da ke tsakaninmu (wadanda ba masana
ko kwararru a fannin) da su, shi ne, suna da kwarewa da kuma mizanin ilmi da
suke amfani da su; ba wai da ka kawai suke kiyastawa su ce abu kaza kaza bane. Don haka wajibi ne a kan kowane Musulmi
muddin Kur'ani ya tabbatar da samuwa ko yiwuwa ko yanayin wani abu, to, dole ne
ya gasgata shi, ko da kuwa ba ya iya fahimta ko hankaltar abin a zahiri ko a
hankalce; kuma ko da binciken mai bincike ya tabbatar da akasin abin da Kur'ani
ya tabbatar.
Amma muddin Kur'ani bai fada ba, ko kuma bai tantance wani abu ba,
idan masu bincike suka ce ga yanayinsa, ko ga yadda yake faruwa, ko kuma abu
kaza kaza ne, to a nan ba wajibi bane sai ya gasgata bincikensu. Idan kuma malaman kimiyya suka tabbatar da
wani abin da Kur'ani bai tabbatar ba, musamman kan tarihin baya, to a nan shi
ma sai dai ka yi zugum; kada ka gasgata, kuma kada ka karyata. Misali, dukkan malaman musulunci sun yarda
cewa babu wanda ya san adadin shekarun wannan duniyar da muke rayuwa a cikinta
sai Allah. Dukkan hadisan da suka zo
masu nuna adadin shekarun duniya ko na rana ko na wata, duk masu rauni ne, ba a
kafa hujja da su. Don haka idan malaman
kimiyya suka ce duniya ta yi shekaru kaza ne, to a nan sai dai kayi shiru kai
Musulmi; kada ka karyata, kuma kada ka gasgata.
Domin zai iya yiwuwa abin da suka fada haka ne, zai iya yiwuwa kuma ba
haka bane; tunda ba da ka suka fada ba, kuma ba sihiri suka yi wajen gano hakan
ba, sun bi dalilai ne na alamun da suka bayyana musu. Idan kayi shiru a nan ka fitar da kanka daga
tuhuma, tunda daman Allah bai wajabta maka yin imani ko rashin imani da hakan
ba.
Abin da yasa na kawo wannan bayani shi ne, nan gaba za mu karo da
abubuwa makamantan wanann, ba sai na maimaita mana dalilin faruwansu ba. Allah sa mu dace, ya kuma amfanar da mu abin
da ya sawwake mana nemansa na ilmi, amin.
No comments:
Post a Comment