Wednesday, February 13, 2013

Tsakanin Kwakwalwa da Zuciya (3)



Binciken Malaman Kimiyya na Farko

A makon da ya gabata masu karatu sun karanta bayanai kan hakikanin yadda halittar zuciya da kwakwalwa suke a kimiyyance, da kuma irin yadda bincike ya faro kan wadannan gabobin jikin dan adam masu muhimmanci tun daruruwan shekaru da suka gabata.  Kada a mance dai, muna gudanar da bincike ne dalla-dalla kan asalin tunani tsakanin zuciya da kwakwalwar dan adam; wanne ne yake da hakkin samar da tunani?  A yau cikin yardar Allah ga bayanai kan binciken malaman kimiyyar halitta na farko kan wasu daga cikin yanayin da suka shafi zuciya dangane da alakarsa da kwakwalwa, da kuskure ko daidai din da binciken ya kunsa.  Wannan shi ne bincike na uku.  A mako na gaba za mu kawo tsarin tunani a kwakwalwa kamar yadda malaman kimiyyar halittar dan adam ke karantarwa a jami'o'in duniya a yau.  Sannan mu karkare da bincike kan sabon nau'in binciken da ya bullo kan alakar kwakwalwa da zuciyar dan adam, inda a karshe za mu tantance gabar da ke samar da tunani a tsakaninsu; zuciya ne ko kwakwalwa.  Allah sa mu dace.

Bayan sun gudanar da bincike kan hakikanin yadda zuciya da kwakwalwa suke aiki, malaman kimiyyar halittar dan adam a baya sun fitar da sakamakon wasu bincike wadanda a baya aka dogara kansu wajen fahimtar tsarin gudanarwar kwakwalwa da alakarsa da zuciya.  Binciken farko kan alakarsa da bugun zuciya ne.  Bincike na biyu kuma kan alakar kwakwalwa ne da babbar tsarin sadarwar jiki baki daya, watau Automatic Nervous System.  Sai bincike na uku da ya shafi tsarin sadarwa tsakanin zuciya da kwakwalwa.  A halin yanzu ga bayani nan filla-filla.

Bincike na Farko

Nau'in sakamakon bincike na farko da malaman kimiyya suka gudanar a baya ya ta'allaka ne kan kwakwalwa da bugun zuciya.  Suka ce kwakwalwa ne ke haddasa bugun zuciya (watau Heartbeat), ta amfani da jijiyoyin tsarin sadarwar jiki, watau Automatic Nervous System (ANS). Wannan na daga cikin dadaddun bincike da malaman kimiyyar halittar dan adam suka yi kan wannan lamari.  Amma daga baya, bayan habbakan hanyoyin bincike da karuwar ilmi, an gano cewa babu alaka tsakanin bungun zuciya da taimakon kwakwalwa ko kadan, ta wannan bangare.  An kuma gano kuskuren wannan bincike ne lokacin da aka fara aiwatar da tiyata ko dashen zuciya.  A halin yanzu an tabbatar da cewa zuciya ba ta bukatar wayoyin sadarwar da za su samar mata da makamashin maganidisun lantarki don haddasa bugawarta.  Domin ita kanta zuciya tana dauke da irin wadannan wayoyin jijiyoyin sadarwa wajen sama da dubu arba'in (40,000), wadanda ke rike ta, tare da taimaka mata wajen bugawa a kowane lokaci.  Don haka ba ta bukatar taimakon wadannan wayoyin sadarwa daga kwakwalwa.  A karshe, gaskiyar sakamakon wannan bincike yana fitowa fili karara a duk lokacin da ake aikin dashen zuciya. Idan aka zo cire matacciyar zuciyar, ana yanke dukkan jijiyoyin wayoyin sadarwar da suka zo daga kwakwalwa ne, sannan sai a jona sabuwar da ake son dasawa.  An gano cewa da zarar an dasa sabuwar, kafin a jona wayoyin jijiyoyin sadarwar da suka zo daga kwakwalwa, nan take zuciyar ke fara aiki.  Don haka, da bugun zuciya na samuwa ne ta taimakon wayoyin jijiyoyin sadarwar da suka zo daga kwakwalwa, da babu yadda za a yi wannan sabuwar zuciya da aka dasa ta kama aiki ba tare da an jona mata jijiyoyin da suka taso daga kwakwalwa ba.  Nan take aka sake gudanar da bincike cikin zuciya don gano dalilin hakan, sai aka samu akwai ire-iren wadancan wayoyin sadarwa (watau Nerve Cells) a zuciya sama da dubu arba'in.

Bincike na Biyu

Sakamakon bincike na biyu an fitar da shi ne a shekarar 1970, kamar yadda Cibiyar Binciken Kimiyya da ke Fels ta kasar Amurka ta tabbatar, watau Fels Research Institute, kuma abin da sakamakon ya tabbatar a wancan lokacin dai shi ne: gamammen tsarin sadarwar jikin dan adam (Automatic Nervous System) ne ke hada alaka tsakanin zuciya da kwakwalwar dan adam.  Sakamakon wannan bincike, kamar wanda ya gabace shi, bai dore ba.  Domin bayan tsawon zamani da samuwar karin hanyoyin bincike, an gano cewa ba wannan tsarin sadarwa bane ke hada alaka tsakanin zuciyar dan adam da kwakwalwarsa.  Bayanai na tafe kan bangarorin jikin da ke haddasa wannan tsarin sadarwa, in Allah ya so.

Bincike na Uku

Bincike na uku an gudanar da shi ne a shekarar 1983, kuma abin da sakamakon binciken ke cewa shi ne: akwai wasu sinadaran sadarwar jiki da a Turancin kimiyya ake kira Hormones, masu dauke da maganadisun lantarkin sadarwa, su ne ke haddasa alakar sadarwa a tsakanin kwakwalwa da zuciyar dan adam.  Wannan sabon bincike ne ya inganta, ko ya gyatta kuskurarriyar fahimtar da ake da ita kan binciken shekarar 1970 da ya gabata, cewa gamammen tsarin sadarwar jiki ne ke hada alaka tsakanin zuciya da kwakwalwa.  Wannan sabon bincike dai ya dada samun shahara ne daidai lokacin da cibiyar bincike na HeartMath Institute da ke jihar Kalfoniya ta gudanar da bincike kan hakikanin gabar jikin dan adam da ke samar da tunani. 

Binciken cibiyar HeartMath ya tabbatar da cewa wadannan sinadarai masu gamewa a jikin dan adam, su ne ke daukan maganadisun lantarkin sadarwa – watau Electromagnetic waves – daga zuciya, zuwa dukkan sassan jikin dan adam, ciki har da kwakwalwa.  Shi yasa da zarar zuciyar dan adam ta hankalci canji a yanayin da take, (misali a ce ka shigo inda ake ta hayaniya, ko zage-zage tsakanin mafadata biyu, nan take zuciyarka za ta hankalci yanayin da ta shiga, sai ta aika wa sauran gabobin jiki, sai dabi'arsu ta canza.  Wannan tsarin aika sako na samuwa ne cikin kiftawa da bisimilla, ta hanyar wadannan sinadaran Hormones da ke kaikomo tsakanin zuciya da sauran gabobin jiki, ciki har da kwakwalwa.  Wadannan, a takaice, su ne nau'ukan bincike uku da aka fara gudanarwa a baya wadanda suka danganci alakar da ke tsakanin kwakwalwa da zuciyar dan adam wajen aikawa da sako, wanda hakan, ko shakka babu, yana da alaka ta kai-tsaye wajen kintsa tunani.

Tsakanin Nassin Kur'ani da Binciken Malaman Kimiyya

To, a daya bangaren kuma wasu kan damu cewa, me yasa idan masu bincike suka ce abu kaza kaza ne, daga baya kuma sai su sake cewa ba haka bane, kaza ne. Wannan yasa da yawa cikin mutane, musamman a kasar Hausa, basu cika yarda da binciken Malaman Kimiyyar zamani ba kan wasu abubuwa da suka shafi halittar dan adam, ko sararin samaniya da dai sauran abubuwa makamantansu.  A wasu lokuta za ka samu abin da Malaman Kimiyya suka fada a baya ya saba wa abin da Kur'ani ya tabbatar, daga baya kuma idan suka zurfafa bincike, sai sakamakon bincikensu ya tabbatar da abin da Kur'ani ya fada.  Al'amura irin wannan sun sha faruwa a baya.  Daga cikin shahararrun misalai akwai binciken malaman kimiyya a farkon zamani cewa rana ba ta motsawa, sai dai sauran halittun sararin samaniya.  Amma Kur'ani ya tabbatar da cewa rana tana juyawa ita ma a cikin falakinta, kamar yadda hakan yake tabbace a cikin Suratu Yaasin.  Da bincike ya tsawaita, sai malaman sararin samaniya suka tabbatar cewa  lallai rana ita ma tana juyawa, ba wata da sauran taurari kadai ke juyawa ba.  Me yasa ake samun haka?  Shin, wannan sabani da a farko ake samu tsakanin nassin Kur'ani ko Hadisi da sakamakon binciken malaman kimiyya, dalili ne da zai sa a daina yarda da bincikensu baki daya?

A tunani na hakan ba dalili bane, ko kadan.  Illa dai, a matsayinmu na musulmi, duk abin da Kur'ani ya tabbatar da shi wajibi ne mu gasgata shi, ko da kuwa ba mu iya hankaltar faruwa ko yiwuwarsa a lokacin da aka gaya mana.  Domin nassin Kur'ani ko Hadisi ba su canzawa, amma binciken duk wani mai bincike, yana iya dacewa, sannan yana iya kuskure.  Abin da ke nuna dacewarsa shi ne yayi daidai da abin da nassin shari'a ya tabbatar.  Abin da zai nuna kuskurensa kuma shi ne ya saba wa abin da nassin shari'a ya tabbatar.  Domin masu gudanar da binciken nan 'yan adam ne kamarmu.  Bambancin da ke tsakaninmu (wadanda ba masana ko kwararru a fannin) da su, shi ne, suna da kwarewa da kuma mizanin ilmi da suke amfani da su; ba wai da ka kawai suke kiyastawa su ce abu kaza kaza bane.  Don haka wajibi ne a kan kowane Musulmi muddin Kur'ani ya tabbatar da samuwa ko yiwuwa ko yanayin wani abu, to, dole ne ya gasgata shi, ko da kuwa ba ya iya fahimta ko hankaltar abin a zahiri ko a hankalce; kuma ko da binciken mai bincike ya tabbatar da akasin abin da Kur'ani ya tabbatar. 

Amma muddin Kur'ani bai fada ba, ko kuma bai tantance wani abu ba, idan masu bincike suka ce ga yanayinsa, ko ga yadda yake faruwa, ko kuma abu kaza kaza ne, to a nan ba wajibi bane sai ya gasgata bincikensu.  Idan kuma malaman kimiyya suka tabbatar da wani abin da Kur'ani bai tabbatar ba, musamman kan tarihin baya, to a nan shi ma sai dai ka yi zugum; kada ka gasgata, kuma kada ka karyata.  Misali, dukkan malaman musulunci sun yarda cewa babu wanda ya san adadin shekarun wannan duniyar da muke rayuwa a cikinta sai Allah.  Dukkan hadisan da suka zo masu nuna adadin shekarun duniya ko na rana ko na wata, duk masu rauni ne, ba a kafa hujja da su.  Don haka idan malaman kimiyya suka ce duniya ta yi shekaru kaza ne, to a nan sai dai kayi shiru kai Musulmi; kada ka karyata, kuma kada ka gasgata.  Domin zai iya yiwuwa abin da suka fada haka ne, zai iya yiwuwa kuma ba haka bane; tunda ba da ka suka fada ba, kuma ba sihiri suka yi wajen gano hakan ba, sun bi dalilai ne na alamun da suka bayyana musu.  Idan kayi shiru a nan ka fitar da kanka daga tuhuma, tunda daman Allah bai wajabta maka yin imani ko rashin imani da hakan ba.

Abin da yasa na kawo wannan bayani shi ne, nan gaba za mu karo da abubuwa makamantan wanann, ba sai na maimaita mana dalilin faruwansu ba.  Allah sa mu dace, ya kuma amfanar da mu abin da ya sawwake mana nemansa na ilmi, amin.

Tsakanin Kwakwalwa da Zuciya (2)



Tsarin Halittar Zuciya da Kwakwalwar Dan Adam

Jikin dan Adam na dauke ne da bangarori nau'uka daban-daban, masu kamanni daban- daban, a wurare daban-daban, don aiwatar da ayyuka daban-daban, a yanayi daban-daban, cikin umarni mai dauke da girman kudurar Ubangiji mahaliccin bayinsa masu kamanni da kintsi daban-daban.  Halittar dan adam abu ne mai matukar ban al'ajabi, cike da hikima da kwarewar da babu wanda zai iya samar da ita har abada.  Daga cikin muhimman bangarorin jikin dan adam da yake ji da su saboda kebantacciyar matsayinsu wajen tafiyar da rayuwarsa, akwai zuciya da kuma kwakwalwa.  Wadannan bangarorin jiki na dan adam sun shahara sosai, saboda kebantattun aikin da suke gudanarwa a jikinsa.  Ba ma shi kadai ba, malaman kimiyya sun tabbatar, ta hanyar bincike na kwakwaf, cewa dukkan dabbar da ke da kashin baya (watau Backbone, ko Vertebral Column, ko Spinal Column), to, tana dauke da kwakwalwa da kuma zuciya. Kamar yadda bayanai suka gabata a makon jiya, yau ga mu dauke da bayani kan halittar zuciya da kwakwalwar dan adam.  Wadannan bayanai sun ta'allaka ne kai tsaye ga sifofinsu, da ayyukansu, da kuma yanayinsu a jikin dan adam; a mahangar malaman kimiyyar halitta na zamani.

Zuciyar Dan Adam

Zuciyar dan adam wani curin nau'in nama ne mai gautsi, mai asali daga yadin jijiyoyin jikinsa masu taushi da a harshen Turanci ake kira Cardiac Muscle.  Wannan curin nama na dauke ne cikin kogon kirjin dan adam, daga bangaren hagunsa.  Girman zuciya duk bai shige dunkulen yatsun dan adam matashi ba.  Kuma tana dauke ne da wasu kwaroron jijiyoyi guda hudu masu taimakawa wajen shigi-da-ficin jini a bangaren dama da hagu, da bangaren sama da kasanta. Akwai bambanci tsakanin girma da nauyin zuciyar namiji da zuciyar mace.  A yayin da nauyin zuciyar namiji ke tsakanin giram 300 – 350, nauyin zuciyar mace bai wuce tsakanin giram 250 -  300 ba.  Allah kadai ya san hakikanin hikimar da ke tsakanin bambanta girmansu.

Zuciyar dan adam na gudanar da ayyuka masu dimbin yawa wadanda har yanzu malaman kimiyyar halittar jikin dan adam sun kasa tantance adadinsu.  Abin da ake ta yi dai shi ne bincike, har zuwa wannan lokaci da nake wannan rubutu.  Amma muhimmi daga cikin ayyukan zuciya da ake iya gani da jinsa, shi ne lura da babban tsarin sadar da jini ga dukkan bangarorin jikin adan adam; daga yatsun kafafunsa zuwa jijiyoyin kwakwalwarsa, dare da rana da safe da yamma.  Zuciya ce ke taimaka wa tsarin gewayen jini a jikin dan adam (watau Circulatory System), wajen fanfon jini daga kasa zuwa sama, da akasin hakan.  Zuciya ce injin da ke fanfon jini a wannan tsari.  Wannan aiki na samuwa ne ta hanyar bugun zuciya (Heartbeat) da ke samuwa a duk sadda zuciyar ta takura (don harba jini) sannan ta sake (don jawo jini) daga wani bangare zuwa wani bangare.  An kiyasta cewa zuciyar kowane matashi kan buga sau 72 a cikin minti daya.

Malaman kimiyyar halittan jikin dan adam sun tabbatar da cewa zuciyar dan adam na fara aikinta ne (ta hanyar bugawa don aikawa da karban jini a jiki), makonni uku da gama tsara halittar dan tayi a mahaifa.  Ma'ana, da zarar Allah ya busa rai a jikin dan tayin da ke mahaifa, nan take zuciyarsa ke fara aikinta.  Kuma haka za ta ci gaba da bugawa har tsawon rayuwarsa.  Wadannan jijiyoyi da ke aikin takurawa da sakewa a zuciya ba su samun hutu sai na 'yar tazarar lokacin da ke tsakanin takura da sakewar. Ma'ana, tsawon lokacin da bai kai dakika daya ba kenan.  Bincike ya kuma tabbatar da cewa, mutumin da zai yi shekaru 76 a duniya, zuciyarsa za ta buga sau biliyan biyu da miliyan dari takwas (2.8 billion beats), kuma za ta harba jinin da adadinsa ya kai lita miliyan 169 a yayin wannan bugawa nata.  Dankari!  Wannan ke nuna cewa a dukkan jikin dan adam, babu bangaren da yafi zuciyarsa tsawon lokacin aiki, da yawan aiki, da kuma inganci wajen halitta.  Duk da cewa sauran suna da inganci su ma.

Masana basu gushe ba tun farkon zamani wajen binciken halin da zuciyar dan adam ke aiki a yanayi daban-daban. Daga lokacin da aka fara rubutun tarihi zuwa yanzu, an gano abubuwa da dama dangane da abin da ya shafi zuciyar dan adam.  Wadanda tarihi ya tabbatar da kokarinsu dai su ne likitocin Kibdawan kasar Masar, sai kuma likitocin Girkawa (Greek Physicians), sai likitocin Daular Rumowa. Daga nan sai likitocin karni na 16 da 17 da suka tagaza nasu kokarin, wajen binciko bangaren jikin dan adam da ke da alhakin harba jini zuwa sauran bangarorin jikinsa. Kokarin masana irin su Michael Servetus da William Harvey ne ya taimaka wajen gano hakikanin bangaren da ke wannan aiki; watau zuciya. Muna shiga karni na 20 kuma sai wannan tsarin bincike ya dauki wani sabon salo, inda aka samu likitan farko da yayi kurum wajen gunadar da tiyar zuciya (Heart Surgery) na farko a duniya a kasar Amurka. Wannan likita kuwa shi ne L.L. Hill, a shekarar 1902.  A wannan karni ne har wa yau aka gudanar da bincike don samar da na'urar binciken zuciya, watau ECG.  Wanda yayi wannan hobbasa kuwa shi ne wani likita dan kasar Jamus mai suna Willem Einthoven, a shekarar 1924. Daga nan dai tsarin bincike ya ci gaba da habaka, har muka samu kanmu cikin wannan zamani mai dauke da nau'urori kala-kala da ake amfani da su wajen gwajin bugun zuciya, da na daukan hoton zuciya, da wukaken da ake amfani da su wajen yin tiyatar zuciya da dai sauran makamantansu.  A farkon lamari likitoci basu yarda cewa za a iya yi wa zuciya tiyata ba, saboda tsananin taushi da gautsin da ke tattare da ita.  Har sai  da likita L.L. Hill ya gwada yi wa wani yaro dan shekaru 8 a shekarar 1902, kamar yadda bayani ya gabata.  Don haka, a mahangar malaman kimiyyar halittar dan adam (Physiologists), muhimmin aikin zuciya shi ne samar da bugawar jini zuwa sassan jiki, da kuma daidai harbawar zuciya, da taimaka wa sauran bangarorin jiki wajen samar da jini mai dauke da sinadaran iska, don tafiyar da rayuwa.

Kwakwalwar Dan Adam

Kwakwalwar dan adam wani curin gungun jijiyoyin yadi ne masu dauke da sinadaran kara kuzari (Protein), da hanyoyin jini, wadanda kuma ke kunshe cikin kokon kan dan adam (Human Skull).  Wannan curin gungun jijiyoyi na da sila ne na kai tsaye da kashin bayan jikin dan adam, kuma wani bangare ne mai muhimmanci wajen hada alaka tsakanin dukkan bangarorin jiki, ta hanyar babbar tafarkin sadarwar bayanai na jikin dan adam, watau Central Nervous System kenan.  Ita kwakwalwa kamar yadda malaman kimiyyar halitta suka tabbatar a binciken baya, wata cibiya ce da ke da tasiri wajen aiwatar da sadarwa ga dukkan bangarorin jikin dan adam.  Ita ce bangaren da ke lura da dabi'ar kauna, da tsana, da tsoro, da fushi, da farin ciki, da bakin ciki.  Har wa yau malaman kimiyyar halitta sun danganta kwakwalwa da samar da tunani, da hazaka, da koyon harshe, da tantance abubuwa, da haddace bayanai, da kuma tuno su bayan haddace su.  Ita ce ke lura da bacci, da kishirwa, da dabi'un da ke lura da rayuwar dan adam baki daya.

Yadda kwakwalwa ke aiki abu ne mai matukar ban al'ajabi.  Wannan ne ma yasa galibin masana ke ganin cewa, ita ce jagora a dukkan bangarorin jikin dan adam.  (Nan gaba za mu gane, shin wannan tabbaci haka yake a yanzu?).  Kwakwalwa na gudanar da ayyukanta ne ta hanyar wasu sinadaran maganadisun lantarki (watau Neurons) da ke makare cikin jijiyoyin da ke kwakwalwar (watau Nerves), wadanda ke aika sakon sadarwar bayanai daga kwakwalwa zuwa sauran bangarorin jiki, ta hanyar wani tsarin sadarwa mai ban al'ajabi.  Wadannan bayanan sadarwa na dauke ne cikin abubuwa guda biyu; da sinadaran jiki (Chemical) da ke dauke cikin yadin jijiya (Nerve Cells).  Sai kuma ballin maganadisun lantarki (watau Electrical Pulse).  Wadannan su ne madaukan bayanai da ke aiwatar da sadarwa daga kwakwalwa zuwa sauran bangarorin jiki, ta hanyar kwayoyin halittar sadarwa da ake kira Neurons, wadanda ke amfani da sinadaran maganadisun lantarkin sadarwar da ke cikinsu da ake kira Neurotransmitters.  Kowane Neuron na dauke ne da rassa da ke karba ko mika bayanan da ya sarrafa zuwa wani Neuron din.  Wadannan rassa dai sun hada da Dendrites, da kuma Axons, wadanda su ne kamar ressan sadarwa tsakanin kwayoyin halittar kwakwalwa, don aiwatar da sadarwa na bayanai ko sinadarai a tsakaninsu.

An gunadar da bincike masu dimbin yawa kan kwakwalwar dan adam, da irin kudurar da Allah ya nuna a cikinta, wajen iya sarrafa bayanai da sadar da su ga sauran bangarorin jikin dan adam.  Binciken baya-bayan nan da aka gudanar mai alaka da kwakwalwa kai tsaye shi ne wanda Roger Sperry ya gudanar kan tsarin gudanarwar kwakwalwa, tsakanin bangaren hagu da bangaren dama.  Ya fitar da sakamakon bincike ne da ke nuna cewa, mutane sun sha bamban wajen tunani ne saboda irin bangaren da suke tunani da shi daga kwakwalwarsu.  A karshen bincikensa ya tabbatar da cewa, bangaren kwakwalwar dan adam na hagu shi ne wanda ke taimaka wa dan adam tunani ta hanyar dabi'a.  Ma'ana, dukkan abin da dan adam ya ci karo da shi na bayanai ko gwagwarmayar rayuwa, yakan sarrafa bayanan ne a tsarin da Allah ya halicce shi da ita na tunani, don fitar da sakamako.  Misali, idan mutum ya fito daga gidansa, ya baro iyalinsa a ciki, yana fitowa sai ya ci karo da babban amininsa da ya saba zuwa gidansa, suna gaisawa sai abokinsa yace ya zo ne su gaisa da iyalinsa, abin da wannan mutum zai ayyana kawai shi ne, gaisuwa ce ta yau da kullum.  Ba wata damuwa. 

Amma bangaren kwakwalwa na dama kuma shi ne ke taimakawa wajen tara bayanai, da irin yanayin da abubuwa ke faruwa, da dalilan da suka sa su faruwa, kafin fitar da hukunci kan wani abin da ya faru a lokacin Magana.  A misalin da muka kawo a sama, mai tunani da bangaren damansa ba zai amince cewa gaisuwa ce kadai ta kawo wannan abokin nasa ba.  Har sai ya yi la'akari da irin lokacin da abokinsa ya zo (da safe ko da rana ko da yamma ko da dare?), da irin yanayin da yazo a ciki (farin ciki ko bakin ciki?), da irin yanayin da alakarsu ta abota take ciki (suna cikin shiri ne ko bayan sun bata?), sannan zai yanke hukunci ko gaisuwar ta Allah-da-Annabi ce ko kuma da wata a kasa.

A takaice dai, an gudanar da bincike da dama kan kwakwalwar dan adam, kuma ana kai.  Ba don komai ba sai don irin muhimmancin da ke tattare da wannan gaba na jikinsa.  A gaba mai karatu zai ga bayanai kan abin da ya shafi zuciya da kwakwalwar dan adam. A ci gaba da kasancewa tare da mu.

Tsakanin Kwakwalwa da Zuciya, Wa Ke Samar da Tunani? (1)




Musabbabi

Assalaamu alaikum Baban Sadik, Allah maka sakayya a kan dimbin abin da kake koya mana mu masu karatun wannan jarida mai albarka.  Ina rokonka arziki ka yi mana karin bayani game da aikin kwakwalwa da na zuciya.  A musulunci malamai sun yi bayanin cewa zuciya ke tunani, su kuma masana kimiyyar zamani sun ce kwakwalwa ce.  Ina rokonka cikakken bayani a kan haka, gwargwadon abin da Allah ya fahimtar da kai.  Na gode.  Mrs. M. Likoro, Zariya.

A yau cikin yardar Allah ga mu dauke da bayani iya gwargwado kan asalin tunani a jikin dan adam.  Kamar yadda mai tambaya tayi a sama, shin, daga ina ne tunani ke samuwa?  Daga kwakwalwa ne ko daga zuciyar dan adam?  Kamar yadda muka sani, akwai ra'ayoyi da dama kan abin da ya shafi asali da samuwar tunanin dan adam.  Amma shahararru daga cikinsu su ne wadanda galibi muka sani a yau.  Watau mahangar addini (musamman Musulunci da Kiristanci), da mahangar malaman kimiyyar zamanin da muke ciki, kamar yadda mai tambaya ta ambata a sama.  Mahanga ta uku da zan kara ita ce mahangar al'ada dangane da asali da samuwar tunanin dan adam.  Ban sani ba, watakila saboda da karancin karatu, ko mahangar al'ada ta samo asali ne daga mahangar addinin musulunci, saboda tasirin addini a rayuwar malam Bahaushe.  A takaice dai, wadannan su ne wadanda galibi muka sani. 

To amma bincike ya nuna akwai ra'ayoyi wajen bakwai da suka sha bamban da juna wajen neman sanin da wani bangare ne dan adam ke tunani a jikinsa?   Wannan shi ne sakamakon bincike na farko da za mu fara kawowa.  Sannan mu dubi hakikanin halittar zuciya a bangare daya, da hakikanin halittar kwakwalwar dan adam, a daya bangaren.  Bayanai kan hakikanin halittar zuciya da kwakwalwar dan adam za su zo ne ta mahangar binciken kimiyyar halitta, watau Biology.  A gaba kuma mu dubi tsarin tunani ta mahangar malaman kimiyyar halitta a zamanin farko, da irin kurakuran da ke cikin bincikensu na farko sanadiyyar bayyanar sabon tsarin bincike da wannan zamani ya zo da shi.  Sannan mu yi bayani kan tsarin tunani a kwakwalwa, kamar yadda malaman kimiyyar halitta na yanzu suke karantarwa, sannan mu ga ko akwai wani sabon bincike da ke nuna cewa tunani daga wani bangare yake zuwa ba daga kwakwalwar dan adam ba, ko kuma bayan kwakwalwar dan adam, shin akwai wani bangaren jikinsa da ke taimakawa wajen aiwatarwa ko samar da tunani gare shi? A karshe za mu rufe wannan bincike da bayanai masu nuna alakar sabon binciken malaman kimiyyar halittar dan adam, da mahangar addinin Musulunci kan abin da ya shafi asali da samuwar tunanin dan adam, kamar yadda mai tambaya ta bukata.

Wannan kasida ce da za ta dan yi tsawo, don haka zan gutsuttsira ta zuwa kashi-kashi, kamar yadda aka saba.  Ina kuma rokon masu karatu da su yi hakuri da irin usulubin da bayanan ke zuwa; ma'ana za a ta cin karo da kalmomin Hausa masu tsauri, da wasu kalmomin turanci da zan rika tsofa su cikin bayanan, don kokarin tabbatar da abin da na fahimta, a matsayina na mai bincike kan wannan mau'du'i. A halin yanzu dai ga nau'ukan ra'ayoyin da ake dasu a duniya kan abin da ya shafi asali da samuwar tunani a jikin dan adam; shin, daga kwakwalwarsa yake tunani, ko daga zuciyarsa?

Ra'ayoyi Kan Asali da Samuwar Tunanin Dan Adam

Malaman ilmin hikimar zance, watau Mandiki, kamar yadda muka sansu a harshen Larabci, sun ce dan Adam dabba ne mai yin Magana.  Sabanin sauran dabbobin da Allah ya halitta wadanda ba su iya Magana, sai dai kuka, ko tsowa ko wata alama makamanciyar haka, don nuna halin da suke ciki, ko wani bakon yanayin da rayuwarsu ta samu kanta a ciki.  A matsayinsa na wanda Allah ya hore wa tsarin Magana da hankali, dan Adam yana yin tunani. Kuma a galibin lokuta tunaninsa na yin kama ne da irin halin da ya samu kansa, ko yanayin da ya tsinci kansa, ko kuma irin muhallin da yake rayuwa a ciki.  Dangane da haka mahangar masu bincike ya sha bamban kan daga ina dan yake tunani.

Mazhabar farko ita ce mahangar addinin Musulunci, wacce kai tsaye ta nuna cewa ba komai bane dan Adam face irin nau'in tunaninsa, wanda ke bubbugowa daga zuciyarsa.  Wannan a 
tabbace yake karara a cikin Kur'ani mai girma.  A wasu lokuta Allah kan yi ishara ga zuciya kai tsaye a matsayin wata ala da dan Adam ke tunani da ita. Hatta ayyukan dan Adam, inganci ko rashin ingancinsu na ta'allaka ne ga zuciyarsa.  Wannan abin da Allah ya tabbatar kenan a cikin Kur'ani.  Haka a cikin Hadisan Manzon Allah ma ishara ya zo kan muhimmancin zuciyar dan adam wajen tunani.  Akwai shahararren Hadisi inda Manzon Allah ke tabbatar da cewa: idan zuciya ta gyaru, to sauran bangaren jiki ya gyaru, haka idan zuciya ta baci, gaba daya sauran gangar jikinsa ta baci.  Bayan haka, a wasu lokuta Kur'ani kan yi ishara ga kirji don nufin matsayin zuciya wajen tunani.  Wannan ya zo a cikin Suratun Naas, inda Allah ke nuna tasirin wasiwasin shedan ga zuciya.  Malaman tafsiri sun nuna cewa Allah ya ambaci kiraza ne (watau jam'in kirji) a surar, don nufin gamewar wasiwasin shedan, ba wai don cewa kirjin dan Adam ne ke tasirantuwa da wasiwasin ba.  Don haka, muhimmancin da Kur'ani ya baiwa zuciya ga rayuwar dan adam da ingancin ayyukansa, bai baiwa kwakwalwarsa ba, a zahiri dai.  Wannan ke nuna mana cewa a mahangar Musulunci dai, tunanin dan adam ko galibinsa, na samuwa ne daga zuciyarsa.

Mazhaba ta biyu kuma ita ce mahangar addinin Kiristanci, watau Christianity.  A wannan mahanga, kamar mahangar da ta gabace ta, tunani na samuwa ne daga zuciya. Wannan kuwa a bayyane yake karara a cikin littafinsu, musamman dai littafin Tsohon Alkawari, watau Old Testament.  Hakan ba zai rasa alaka ba da asalin addinin, kasancewar asalinsa da na Kur'ani daya ne, in muka dauke tsawon zamani da ya bambanta su, da kuma tasirinsa a kan kowanne daga cikin littattafan biyu.  A takaice dai mahangar Kiristanci kan asalin tunanin adan adam shi ne daga zuciya yake samuwa, duk da cewa Musulunci ya fi karfafa wannan ra'ayi karara, a cikin Kur'ani.

Mazhaba ta uku ita ce mahangar malaman falsafa, watau Philosophers kenan.  Wadanda suke kiyasta abubuwa da hankali, ba da wahayi ba, a galibin lokuta.  A wannan mazhaba sun nuna cewa tunanin dan adam na samuwa ne ta hanyar kwakwalwar dan adam, sabanin ra'ayin addinai biyu da ya gabata.  Masu wannan mazhaba suka ce sun fahimci hakan ne ta hanyar tasirin kwakwalwa wajen tunani, da tasirin tunani shi kanshi a kwakwalwar dan adam, da kuma tasirin yanayi wajen tunani.  Har wa yau masu wannan mazhaba suna kokarin hada alaka ne tsakanin kwakwalwa da ruhin dan adam, watau Human Soul kenan, a Turance.  Wannan mazhaba dai ya samo asali ne daga masu hikima cikin Girkawa, watau Greek Philosophers.  Shahararru daga cikinsu su ne Martin Heidegger, wanda ya samar da ka'idar Phenomenological Analysis, da kuma Renes Descartes, wanda ya samar da shahararriyar ka'idar Mind-body Problem, wacce ke kokarin neman alakar da ke tsakanin ruhi da jikin dan adam ko kwakwalwarsa, a kaikaice.  A tunaninsu, kamar yadda mai karatu zai gani, tunanin dan adam na samuwa ne daga kwakwalwarsa, ta alaka da ruhinsa, wacce ba a iya gani.

Mazhaba ta hudu ita ce mahangar malaman kimiyyar halittar dan adam, watau Biologists ko Physiologists ko Neurologists.  Wannan su ne gungun masu bincike kan halittar kwakwalwar dan adam a zahirance.  Likitoci ne masu lura da tsarin jikin dan adam da yadda yake aiki, musamman kwakwalwarsa.  Sun yi nazarin kwakwalwarsa, da abin da ke dauke a ciki, da muhimman bangarorin da ke cikinsa, da kuma yadda tunani, da ji, da gani, da hankaltar abubuwa ke samuwa ta hanyar wasu sinadaran halitta masu aiwatar da sadarwa tsakanin kwakwalwa da sauran bangarorin jikin dan adam.  Wadannan kananan sinadaran halitta su ake kira Neurons, kuma su ne ke isar da sakon da kwakwalwa ke harbawa zuwa ga sauran bangarorin jiki, ciki har da zuciya.  Bayan su akwai sinadaran halitta masu aikawa da sakon sinadaran maganadisun lantarkin sadarwa (watau Electromagnetic radiation), masu suna Neurotransmitters.  Sai wadanda ke karban sako daga gare su masu suna Axons da dai sauran bangarori makamantansu.  A wajen malaman kimiyyar halittar dan adam, kamar yadda muka gani, tunanin dan adam na samuwa ne ta hanyar kwakwalwarsa.  A takaice ma dai suna ganin kwakwalwar dan adam ne ke sarrafa sauran bangarorin jikinsa baki daya.  Wannan shi ne ra'ayin farko da suka dogara a kai.  Nan gaba kadan za mu gani ko wannan ra'ayi na ci har zuwa yau.

Mazhaba ta biyar ita ce mahangar malaman fannin ilmin dabi'a da ke lura da tsarin tunani, watau Cognitive Psychology.  A nasu ra'ayi suka ce tunanin dan adam na samun asali ne ta la'akari da wasu bangarorin jikinsa ko tasirinsu wajen gina tunaninsa, kafin ya aiwatar.  A takaice dai, suna binciken tsarin tunanin dan adam ne ta la'akari da matsayin kwakwalwa, da kudurar haddace faruwar abubuwa ko bayanai, da koyon ilmi, da kuma tasirin harshe ko yare wajen gina tunanin dan adam.  Wannan mazhaba yana da zurfi, don ya kunshi bincike kan abubuwa da yawa da suka shafi bangarorin jikin dan adam, kafin a fahimci yadda tsarin tunaninsa yake.  A takaice dai, su ma ra'ayinsu shi ne, tunanin dan adam na da alaka mai karfi da kwakwalwa, ta hanyar sauran hanyoyi ko bangarorin da bayanansu suka gabata.
Mazhaba ta shida tana da alaka mai karfi wajen asali da mazhabar da ta gabata.  Wannan mahanga tana binciken asalin tunanin dan adam ne ta la'akari da sha'awa da soye-soyen zuciyarsa (watau Egocentrism kenan).  Wannan fanni na ilmi kuwa shi ake kira Psychoanalysis.  A nasu tunani suka ce abin da ya kamata a lura da shi wajen tantance asali da nau'in tunanin dan adam shi ne bukatunsa na zuci, da abubuwan da yake sha'awa; na ci ne, ko na sha, ko bukatun rayuwa.

Sai mazhaba ta karshe, watau fannin ilmin zamantakewa da dabi'ar zuci, ko Social Psychology a harshen Turanci.  A nasu bangare, suna binciken tsari da asalin tunanin dan adam ne ta hanyar tasirin da al'adunsa suke yi a rayuwarsa, da tasirin yanayin zamantakewarsa.  Suka ce duk wani tunani da ke samuwa daga gare shi, sanadiyyar tasirin wadannan abubuwa ne guda biyu; tasirin al'ada, da kuma tsarin zamantakewa.  A wajensu, kamar mazhabar da ta gabata, tunanin dan adam na ginuwa ne ta la'akari da tsarin al'ada da zamantakewa.  Basu damu da tasirin kwakwalwa ko zuciya ba wajen tunani.

Wadannan, a iya bincike na, su ne nau'ukan mahangar asalin tunanin dan adam.  Idan Allah ya kai mu mako mai zuwa za mu dora a inda muka kwana.  Allah sa mu dace.