Tuesday, September 8, 2009

“Sinadaran Batir Zasu Kara Samun Tagomashi” – Inji Wani Bincike

Ga dukkan alamu, nan da shekaru uku masu zuwa duk wani mai amfani da batir nau’in Lithium-ion Phospateclip_image002, watau nau’in batiran da muke amfani dasu a wayoyin salularmu da kwamfutocin tafi-da-gidanka (Laptop), da na’urar taskance wutar lantarki (UPS) da sauran makamantansu, zai samu sauki wajen takaitan lokacin caji da kuma karkon rayuwa wajen amfani da shi. Abinda wannan ke nufi shine, nan gaba kana iya caja batirin wayar salularka cikin kasa da minti daya! Ba ma nan aka tsaya ba, batirinka na iya shekaru uku ko sama da haka ba tare da karkonsa ya ragu ba. Wannan shine abinda sakamakon wani bincike da wasu masana kimiyyar lantarki suka gudanar a Cibiyar Fasaha da ke Massachusettes, watau Massachusettes Institute of Technology (MIT) ya tabbatar. Sakamakon binciken, wanda mujallar Nature ta hakaito ranar 12 ga Maris yace masu wannan bincike sun yi tsawon shekaru biyar suna fafatawa kafin gano manyan dalilan da ke jawo saibi wajen cajin batir yayin da aka jona shi da wutar lantarki, duk kuwa da cewa sinadaran lantarkin nau’in Neutrons da ke ciki suna aikinsu yadda ya kamata. Wanda kafin wannan lokaci galibin masanan lantarki na alakanta rashin cajin ire-iren wadannan batira cikin sauri ne da cewa sinadaran da ke ciki ne basu kai-komo cikin gaugawa don tara makamashin lantarkin da batirin ke bukata. Amma a cewar Injiniya Gerbrad Ceder da Byoungwoo Kan, shugabannin tawagar injiniyoyin da suka kaddamar da wannan bincike, wannan ba shine dalilin da ke sa wayar salula ta dauki kusan sa’a guda tana caji ba kafin batirin ya cika, a misali.

Batir nau’in Lithium-ion Phospate dai shine nau’in batiran da wayoyin salula da sauran kayayyakin fasahar zamani masu amfani da batir ke amfani dashi. Har wa yau akwai motocin zamani masu amfani da wannan batiri su ma. Wannan nau’in batir dai ya samu wannan shahara ne sanadiyyar iya taskance makamashin lantarki da yake yi idan an hada shi da wutar lantarki, ya kuma ci gaba da amfani da wanda ya taskance, har sai yayi kasa, sannan a sake caja shi. Wannan ya saba wa batira irin na agogon bango ko na tocila, wadanda da zarar sun yi rauni shikenan, sai dai ka zubar dasu ka sayo wasu. Amma nau’in Lithium-ion Phospate, kana iya shekaru dasu; sai dai kawai ka rika caji idan sun yi kasa, don kara musu kuzari. Matsalar da ke tattare da ire-iren wadannan batira dai a cewan masana fasahar lantarki, shine idan ka jona su da wuta sai sun yi kusan awa guda ko sama da haka, kafin su yi cajin da zai dauke ka kwanaki biyu ko uku kana amfani dasu. Kafin wannan rahoto da aka fitar, galibin masana harkar lantarki na danganta matsalar ne ga yanayin tafiyar sindaran Neutron da ke cikin batirin, wadanda aikinsu ne su rika caja batirin ta hanyar yin tsere a tsakaninsu daga hagu zuwa dama, duk sa’adda ka jona wayar ko batirin kana caji, suna shiga wasu yan ramuka (watau Tunnels) da aka tanada musu. Wannan kai-komo da suke yi shi ke tara makamashin lantarkin da wannan batir ke bukata. Da zarar ya cika, ka jona wa wayar salularka a misali, sai su fara kai-komo daga dama zuwa hagu, duk lokacin da ka kunna wayar. Wannan safa-da-marwa da suke yi, shi zai rika rage yawan makamashin lantarkin da ya taru yayin da suke caja wayar, har sai ya kare. Sannan su canja yanayin tafiya idan ka jona wayar da wutar lantarki don yin caji a karo na gaba. Tsohuwar sakamakon da masana suka fitar a baya ita ce: wadannan sinadarai na Neutron basu tafiya cikin gaugawa don tara makamashin lantarkin da wayar ke bukata ne, shi yasa wayar ke daukar kusan awa guda ko sama da haka kafin cajin ya cika. To amma sakamakon da Injiniya Ceder da abokan bincikensa suka fitar makon jiya ya karyata wannan tsohuwar zato da masana harkar lantarki ke da ita shekaru aru-aru.

Injiniya Ceder yace sun yi nazarin wannan safa-da-marwa da sinadaran Neutron ke yi yayin caji basu samu wata matsala da abinda ya shafi yanayin tafiyarsu ba, sam ko kadan. Suka ce sun lura da wannan tafiya ta hanyar na’urar kwamfuta, inda suka jona batir nau’in Lithium-ion Phospate, suna kallon yadda wadannan sinadaran na Neutron ke tafiya a guje, suna gudanar da aikinsu yadda ya kamata. Wannan, a cewarsu, ba shine matsalar da ke haddasa rashin cajin batir din da wuri ba. Suka ce matsalar da ke haddasa wannan saibi wajen caji ita ce: ba dukkan wadannan sinadaran na Neutron ne ke shigewa cikin wadannan ramuka da aka tanada musu ba a lokaci guda. Galibinsu, musamman wadanda ke sama-sama, suna sulmuya ne a wofi, basu samun damar shiga ramin balle caji yayi sama cikin lokaci. Abinda zai warware wannan matsala kuwa, a cewar wadannan injiniyoyi, shine a sake tsara wasu ramukan (Tunnels) daga sama (watau cikin kogin sinadaran da ke cikin batirin kenan), don baiwa wadannan sinadaran da ke sulmuya a sama damar samun shiga su ma, don kauce wa sulmuyar wofi da suka yi ta fama da shi a baya. Wannan shine kadai abinda zai sa batir ya dauki karancin lokaci wajen caji, kuma bayan haka ma, zai samo rayuwa mai karko da inganci.

Wannan ikirari ba da ka suka yi shi ba. Rahoton da Injiniya Kan da tawagarsu ya fitar a mujallar Nature, yace sun aiwatar da bincike kan batira guda biyu; batir na farko sabo ne, wanda suka kera ta hanyar amfani da sabon tsarin da suka tabbatar a bincikensu, dayan kuma irin wanda kowa ke amfani ne dashi, ma’ana mai dauke da tsohuwar fasaha kenan. Dukkan batiran mizaninsu daya ne, sinadaran da ke cikinsu iri daya ne, kuma dukkansu nau’in Lithium-ion Phospate ne. Da suka jona su da caji, batirin farko mai dauke da sabuwar fasaha ya samu cikakkiyar caji tsakanin dakiku goma zuwa ashirin (10 – 20 Seconds), yayin da dayan batirin mai dauke da tsohuwar fasaha ya dauki tsawon mintuna shida (6 minutes) kafin ya cika. Sun kuma sake tabbatar da cewa lallai wannan batir mai dauke da sabuwar fasaha zai yi karko fiye da wanda ake amfani da shi a yanzu. A karshe suka tabbatar da cewa: “samun damar caji da kuma amfani da batira cikin sauki da gaugawa zai dada samar da damar kera wasu sabbin kayayyakin fasaha ne, wanda hakan ke iya zama sanadiyyar tafiyar da rayuwa cikin sauki da inganci”. Tuni dai hukumar NASA da kuma Hukumar Makamashi na kasar Amurka suka karbi sakamakon wannan bincike da hannu bibbiyu. Kuma har an samu wasu kamfanonin fasaha guda biyu ma da suka karbi lasisin amfani da wannan sabuwar fasaha ta inganta batir nau’in Lithium-ion. Nan da shekaru uku masu zuwa ake sa ran fitar wadannan batira masu dauke da wannan sabuwar fasaha.

Dumamar Yanayi: Ma’ana, Dalilai da Musabbabai (1)

Gabatarwa

Kamar kowanclip_image002e irin halitta da Allah Madaukakin Sarki ya halitta, wannan tsari da yanayin da wannan duniya tamu ke gadanuwa na canzawa ne iya canjin zamanin da muke ciki; iya gwargwadon jujjuyawar dan Adam wajen nemo hanyar sarrafa wannan muhalli da Allah Ya zaunar dashi a ciki; iya gwargwadon ilimi da wayewarsa; iya girma ko fadin tasirin da zai yi wajen sarrafa wannan muhalli. Har wa yau, wannan tasiri na dan Adam na caccanzawa ne shi ma zamani-zamani. Don haka idan muka dubi bangaren lafiya, za mu ga cewa mutanen da suka yi rayuwa shekaru dari biyu ko sama da haka da suka gabata, basu san wata cuta mai suna kanjamau ba, ko ciwon siga, ko ciwon asma da dai sauransu. Haka kuma ire-iren cututtukar da aka yi fama da su cikin wadancan zamunna ko karnoni da suka gabata, a halin yanzu bamu dasu. Idan muka dubi bangaren sadarwa har wa yau, zamu sake ganin irin wannan bambanci; shekaru dari biyu da suka gabata babu wani fasaha da dan Adam ya kirkira a matsayin abin hawa daga gari zuwa gari, sai dai dabbobi irin dawaki da rakuma da jakuna da sauran makamantansu. Haka hanyoyin da yayi amfani dasu wajen sadar da sakonni a wancan lokaci, a yanzu duk ba a amfani dasu. Idan muka koma kan yanayin isar sakon kuma, shekaru dari ko tamanin da suka gabata, ba ma can nesa ba, ba kowa zai yarda ba idan aka ce masa nan gaba cikin ‘yan dakiku kana iya aika sako daga bangon duniya ta gabas zuwa bangonta da ke yamma, cikin kasa da minti daya! Amma yanzu ba yarda da yiwuwar hakan bane abin mamaki, a a, rashin yarda shine abin mamaki.

Duk dai wannan, a takaice, na nuna mana ne cewa iya nisan zamani, iya girma da nau’in tasirin da dan Adam ke yi a doron wannan kasa. In kuwa haka ne, to dole akwai amfani da yake samu, wanda a bayyane yake; ga motoci, ga jiragen sama, ga gidaje nau’uka dabam-daban, ga nau’ukan abinci nan kala-kala, ga kuma kayayyakin sadarwa da fasaha masu tasiri fiye da tunanin dan Adam wajen samar masa da amfani ta hanyar wayar da shi, da kara masa ilimi da hore masa hanyoyin sarrafa muhallinsa. Haka kuma a daya bangaren, akwai wasu illoli da suka haddasu sanadiyyar wannan juyin zamani da dan Adam ke samu a rayuwarsa. To wasu illoli ne? Akwai illoli da dama; ga karuwar cututtuka, ga matsalolin tattalin arzikin kasa – irin su yawaitan marasa aikin yi, talauci da ire-irensu - ga rashin zaman lafiya ga al’umma, ga rashin sukuni ga daidaikun mutane, ga kuma uwa uba, dumamar yanayi da muhallin da ake rayuwa ciki. Wannan matsala ta dumamar yanayi da a harshen Turanci ake kira Global Warming, na cikin manyan matsalolin da duniyar yau ke fama da su, musamman a kasashen da suke ikirarin ci gaba a fannonin tafiyar da rayuwa. Shin, me ake nufi da “dumamar yanayi”? Yaushe duniya ta fara samun irin wannan matsala da har Turawa ke ganin babu matsala irin ta a yanzu? Me ke haddasa haka? Wasu illoli wannan matsala ta dumamar yanayi ke haddasawa? A karshe, me duniya (ina nufin kasashen Turai da Amerika) ke yi wajen ragewa ko takaita shi? Cikin wannan silsila da muka faro yau, zamu gabatar da amsoshin wadannan tambayoyi iya gwargwadon hali da sani. Hakan na da muhimmanci don samun karuwar ilimi, musamman ganin cewa wannan kalma ta “Dumamar Yanayi” ko Global Warming a harshen Turanci, na cikin kalmomin da kusan a kullum sai an ambace su a kafafen watsa labaru, har kafafen watsa labaru cikin harshen Hausa da ke sauran kasashen duniya. Na kuma tabbata da dama cikinmu bamu taba damuwa da neman bayani kan ma’ana ko abinda wannan kalma ta kunsa ba. To ga budi Allah Ya kawo cikin sauki. Sai a gyara zama don bibiyar wannan shafi sau da kafa. Sai dai kafin mu shiga fagen bayani kan dumamar yanayi, ga wata ‘yar tunatarwa nan.

Tsarin Turawa Wajen Binciken Kimiyya

Yana da kyau a kullum mai karatu ya fahimci tsarin da turawa ke amfani da shi wajen binciken da suke yi musamman na ilimi kan abinda ya shafi kimiyya da fasaha. Wannan zai sa ka fahimci abubuwa da dama; mai yasa suke danganta kaza ga kaza? Me ya sa suke ganin kaza ne ya haddasa kaza ba Allah ba a misali? A takaice, shin duk abinda suka binciko ne daidai ko kuwa? In haka ne, mai yasa wasu lokuta suke fadan wasu abubuwa sabanin yadda Allah Ya fade su ko yadda yake a zahiri ko a Kur’ani? To ga amsa. A karo na farko dai, ‘yan Adam ne irinmu; suna da tawaya da nakasa irin wacce muke da ita, iya gwrgwadon sani ko jahiltar abinda suke tutiyar saninsa. Sannan, kashi casa’in da takwas cikin dari (98%) na masu binciken kimiyya ba musulmi bane. A wasu lokuta ma ba Kiristoci bane su. Galibinsu basu da addini. A inda aka samu Kiristoci ko Musulmi a wasu fannonin, zaka samu addini baya tasiri a rayuwarsu. To me yasa?

An samu wani zamani a kasashen Turai, daidai lokacin da suke kokarin fitowa daga kaidin jahilci a dukkan bangaren rayuwa (watau Dark Ages), inda aka yi ta samun masana a fannonin rayuwa musamman na kimiyya suna ta kirkirar abubuwan mamaki da dama, irin su Galileo, wanda ya kirkiro na’urar hangen nesa da a Turance ake kira Telescope. Ba shi kadai ba, akwai da dama da suka yi zamani daya. Daidai wannan lokaci kuma shugabannin majami’a ne ke da karfi, watau addinin Kirista kenan. Sai aka shiga kama su, ana karkashe su; don me zasu rika binciko abubuwa irin haka? Wannan, a cewar wadannan shugabanni, ya saba wa karantarwar addininsu, kuma fito-na-fito ne da Ubangiji, inji su. Don haka duk wanda aka samu ya kirkiro wani abu mai ban mamaki, sai kawai a kashe shi. Haka dai abubuwa suka ci gaba da faruwa har zuwa lokacin da ruwa ya kare wa kada, lokacin da mulki ya koma hannun ‘yan boko, wanda kuma sun san abubuwan da suka faru a baya. Suna samun shugabanci, sai suka yi juyin juya hali, inda aka tumbuke shugabannin addini daga mulki zuwa majami’ansu. Kuma sakamakon wannan ta’addanci da Malaman majami’a suka yi a baya, wadannan sabbin shugabanni suka sanya dokar raba shugabanci da addini, ko kuma dukkan wata ka’ida ta rayuwa aka raba ta da addini; in za ka yi addininka, a cewar wannan ka’ida, ka yi a gidanka, ko a wajen ibadanka, amma ba a bainar jama’a ko hukumomin gwamnati ba. Wannan tsari, kamar yadda na tabbata duk mun santa, ita ake kira Secularism, kuma daga cikinta ne aka fitar da wata ka’ida da galibin malamai masu binciken kimiyya a Turai suke amfani da ita.

Wannan ka’ida dai ‘yar zahiriyya ce. Kuma ka’ida ce da a Turance ake kira The Cause and Effects Theory. Wannan ka’ida abinda ta kumsa shine, “duk abinda ka ga ya faru ko yake faruwa, to dole wani abu ne yayi sanadiyyarsa, kuma wannan abin da yayi sanadi, dole ya zama ana ganin shi ko jin shi ko iya taba shi”. In kuwa babu daya cikin wannan, to, zamani ko tsawon lokaci ne ke tafiyar da shi, amma ba wai wani Allah ba. Basu yarda akwai wani mai tafiyar da duniya, mai haddasa faruwar abubuwan da ke faruwa a zahiri ba, in dai ba ganin shi ake yi, ko jin shi ko kuma hankaltarsa ba. Ma’ana, su basu yarda wani abu na iya faruwa ba tare da samun wata alama bayyananniya da ke sanadin faruwarsa ba. Inda suka kasa gane dalili kuwa, sai su yi kirdadon wani dalili na wucin-gadi, sannan su ci gaba da bincike. Abinda ya sha karfinsu kuma tun fil azal, sai su jingina shi ga dabi’a kawai, watau Nature, kamar yadda suke fada. Kai kuma Musulmi ka saba da yin imani da abinda baka gani ba, watau gaibu, don shine asalin addini da imani. Dole kaji abin yai maka bambarakwai, wai namiji da sunan Rakiya!

Bayan wannan tunani ko ka’ida da suka kudurce, Allah Ya hore musu kayan bincike. Don haka duk abinda hankalinsu bai kwanta da shi ba, sai su bincika. Wasu lokuta sakamakon bincikensu ya zama daidai da abinda Allah ya fada ko tsara. Wasu lokuta kuma sakamakon ya karyata abinda Allah Ya fada, ko kuma rabi ya dace, rabi ya kauce. Wasu lokuta abinda suka tabbatar a matsayin sakamakon wani bincike, ya canza sanadiyyar tsawon zamani da yawaitan ilimi da canjin tsarin bincike. Wannan ke sa ka samu ka’idojin fahimtar wani nau’in ilimi sama da guda biyar. Hakan na faruwa ne saboda karancin kayan aikin mai bincike, da karancin fahimtar mai bincike, da kuma kasawarsa wajen sanin komai da komai game da abinda yake bincike. Dole kuwa haka ta kasance, domin shi mai bincike ba Allah bane, halittarsa aka yi. To amma tunda su ba damuwa suka yi da hakkin Allah ba, idan ma suna da addinin kenan, sai kawai su toge a kan sakamakon bincikensu. Kuma tunda su ne da kafafen watsa labarai, su ne ke tsara wa duniya tsarin karantar ilimi da bincike, su ne ke tsara ka’idojin bincike da karatu da karantarwa, sai su rubuta abinda yayi musu daidai, su watso wa duniya don kowa ya ci gaba da tafiya a kan turbarsu. Hakan shine daidai a garesu, domin duniya ce manufarsu, kuma ita suka sa a gaba. Duk abinda ya wuce wannan duniyar, to sai dai ka basu labari, amma ba su baka ba.

A musulunci ba yin amfani da wannan ka’ida bane kuskure, a a, illa dai dole ne ka hada da cewa Allah ya kaddara wa kowane abu lokaci da yanayi da kimtsi da kuma tsarin da yake gudanuwa. Ko ka yarda ko kada ka yarda, wannan abin a haka zai ci gaba da kasancewa zuwa lokacin da Allah Ya haddade masa. Wasu kan ce tunda wannan ita ce dabi’a da tsarin turawa wajen bincike, to kenan galibin abinda suke fada a matsayin sakamako duk karya ne, kuma baza mu yi amfani da shi ba. Wannan kuskure ne babba. Abinda ya kamata shine a yi amfani da abinda suka fada wanda zai kaimu ga samun rayuwa mai sauki da warware dukkan matsalolinmu a matsayinmu na al’umma, wanda ya saba masa kuma, ko zai kai mu ga halaka, dole ne a guje masa. Hanya mafi sauki a karshe dai ita ce samun ‘yancin kai a ilimance; mu yi karatun, mu yi binciken da kanmu, a nan kadai zamu iya gane zurfin karyarsu ko rashinsa. Don haka, a cikin wannan dan karamin bincike da zamu gabatar kan dumamar yanayi zamu rika cakuda dalilai ne tsakanin wadanda bincike ya tabbatar dasu a wannan zamani, da kuma wadanda daman can akwai su a zamunnan baya. Abubuwa ne da suke tabbatattu kana iya jinsu, wasu kuma kana iya fahimtarsu idan ka kwatanta lokacin da kake rayuwa ciki yanzu da lokutan baya. Don haka duk abinda ba a fahimta ba a yi tambaya. Allah sa mu dace, amin. (Zamu ci gaba)