Saturday, December 4, 2010

Tsaunuka Masu Aman Wuta da Tasirinsu Ga Muhalli (4)

Shi dai wannan toka da zarar yayi sama, ba ya narkewa. Sabanin irin tokan da muka saba gani da mu’amala da shi. Shawagi yake yi a sama. Don yana dauke ne da sinadarai masu wahalar sha’ani. Da zarar ya hadu da ruwa ko danshi, yakan zubo kasa ne, ya daskare, ya zama gundarin dutse shi ma, amma nau’in Tuff. Yana dauke ne da hayaki mai dauke da sinadarai masu cutarwa. A shekarar 1783, lokacin da tsaunin Leki da ke Tsibirin Iceland yayi amai, wannan tokan kunun dutse ya yi sanadiyyar mutuwar kashi daya bisa biyar na mutanen kasar nan take. Da wannan toka ya garzaya Yammacin Turai, yayi ajalin mutane sama da dubu ashirin da uku a kasar Ingila. Shakar wannan toka dai lalura ce babba, musamman ga masu cutar da ke da alaka da numfashi, irin Asma. Yana sanya kaikayin idanu. Idan kuma ka shake shi lokacin da yake tattare da danshi, to yana tara wasu sinadarai masu dauke da narkakken sinadarin siminti a cikin huhunka. Idan kuwa ya zubo kasa, bayan ya gama shawagi a sama, yana iya rusa rufin gidajen jama’a; iya gwargwadon yawansa a saman rufin gida. Wannan na faruwa ne sanadiyyar sinadaran da ke dauke cikinsa, masu nauyi. Yana lalata amfanin gona, yana kashe dabbobin gida, da na ruwa (irin kifaye da makamantansu), yana lalata hanyoyi, sanadiyyar santsi da hazo da yake haddasawa.

clip_image002Idan kuma yana sama aka fara ruwa mai dauke da walkiya da cida, to yana haddasa daukewar wutar lantarki, da dukkan hanyoyin sadarwar tarho, ya kuma sanya firgici iya kusancinsa da mutane ko garin da ake ruwan. Idan kuma ya riski direban jirgi a sama, lamari ya lalace kenan. Yana iya toshe masa gabansa nan take, yana iya kara wa jirgin nauyi, sanadiyyar zubowar da zai rika yi a saman jirgin. Wannan zai sa wani bangaren jirgin ya fi wani bangaren nauyi, musamman fukafukansa. Idan kuwa haka ta faru, to akwai matsala. Domin jirgi na tafiya lafiya ne idan nauyinsa yayi daidai a dukkan bangarori. Amma idan ya zama wani fiffiken ya fi wani fiffiken nauyi, to yana iya samun matsala nan take. Bayan nan, yana tasiri wajen lalata fitilun da ke taimaka wa jirgin sauka. Yana lalata farfelan jirgin idan ya shige ciki. Dole kuwa haka ta faru, saboda sinadaran da ke dauke cikin wannan toka basu narkewa. Idan jirgi ya ci gaba da tafiya a cikinsa, yana iya toshe masa bututun da yake gejin iska da shi, wanda kuma ke nuna masa iya tazarar tafiyarsa, watau Air Speed Indicator. Kamar yadda bayanai suka gabata a baya, samuwar wannan toka a sama na iya hana direban jirgin sadarwa tsakaninsa da masu lura da shi a tashar da yake son sauka ko ya baro a baya. Illa mafi muni da wannan toka ke yi wa jirigi shi ne ya sanya injin jirgin ya kama zafi, sanadiyyar toshe shi da yake yi. Idan hakan ta faru, jirgin ba zai samu kuzari ba ko kadan, dole ya gangaro kasa-kasa, in kuwa ba haka ba dukkan injinansa na iya daukewa nan take. Wannan shi ne abin da ya faru da wani jirgin British Airways F19, daidai lokacin da tsaunin Galunggung da ke kasar Indonesiya yayi amai, tare da watsa wannan toka a sararin samaniya cikin shekarar 1982. Nan take dukkan injinan jirgin guda hudu suka daina aiki, sai da ya rage tafiya, ta hanyar gangarowa kasa daga tazara nisan kamu dubu talatin da shida (36,000ft) zuwa kamu dubu goma shabiyu (12,000ft). Irin wannan har wa yau ya faru da jirgin KLM Boeing 747 da ya taso daga birnin Amstadam na kasar Nedaland zuwa nahiyar Amurka. Daidai lokacin ne tsaunin Redoubt da ke jihar Alaska ya fara amai. Jirgin bai tsaya ba ya ci gaba da tafiya. Saukarsa ke da wuya sai dukkan injinan jirgin suka yi dameji. Sai da aka kashe dalar Amurka miliyan tamanin ($80M), aka fitar da tokar da mizaninta ya kai kilogiram tamanin (80kg) daga injin, sannan aka kwashe wajen watanni uku ana gyara. Wadannan su ne kadan cikin illolin wannan toka na kunun dutse. Ta bangaren amfani kuwa, yana da tasiri sosai wajen sanya kasar noma ta zama mai amfani da albarka, kamar dai yadda wancan kunun dutse nau’in Passive Lava ke yi.

Kammalawa

Daga bayanan da suka gabata, a bayyane yake cewa tsaunuka masu aman wuta na da matukar tasiri ga al’umma da kuma muhallin da suke ciki. Duk da cewa munanan tasirinsu ya fi bayyana a fili, amma suna da wasu amfanoni da jama’a ke amfanuwa da su bayan lokaci mai tsawo da yin amansu. Wani darasin da ya kamata mu koya daga rayuwa tare da wadannan tsaunuka shi ne, duk wani abin da Allah ya kaddara samuwarsa a doron kasa ko a cikin teku, to don amfanin dan Adam ne. Ko da kuwa wannan abin na masa mummunar illa duk sadda ya bayyana, ko ya faru. Kuma Allah na iya amfani da shi wajen halaka duk wanda ya ga dama cikin bayinsa. Sannan samuwar wannan toka da ta bice sararin samaniya cikin watan Afrilu, wa’azi ne ga duniya baki daya, cewa idan za a yi hasara irin wannan cikin kasa da makonni biyu sanadiyyar aman da wani tsauni guda daya yayi a wata nahiya da ke can kurya, to me zai faru idan aka wayi gari dukkan tsaunuka masu aman wuta suka fara amai a lokaci guda? Don haka mu fadaka, mu kuma shiga taitayinmu.

AMSOSHIN WASIKUN MASU KARATU TA TES

Assalaamu Alaikum, Baban Sadik na kasance mai bibiyar makarantarka sama da shekara uku, kuma ina maka fatan alheri, Allah shi kara basira, amin. Don Allah ina da waya ne kirar Nokia 6260, ko tana da manhajar Opera? In har akwai, to yaya zan yi in rika shiga Intanet? Na gode. - Aliyu Danlabaran, Zariya: 08036158781

Malam Aliyu mun gode da addu’a, Allah kara basira da juriyar kasancewa tare da mu. Hakika galibin wayoyin salula na zamani suna da nau’in manhajar Opera Mini a tare dasu, ko kuma idan kaje gidan yanar sadarwan Opera, za ka samu nau’in da ya dace da wayarka, tabbas. To amma kafin nan, ina son sanar da kai cewa dukkan wayoyin salula suna da masarrafar lilo da tsallake-tsallake, watau “Browser”, wacce kuma kana iya mu’amala da ita wajen shiga Intanet. Amma idan kana son “Opera Mini” ce, to duk babu damuwa, kana iya saukar da ita zuwa wayarka, sannan ka loda mata. Don haka sai kaje inda ake mu’amala da Intanet a wayarka (watau “Browser”), ka shigar da wannan adireshin http://mini.opera.com/download shafin da ke dauke da manhajar zai budo, sai ka bi umarnin da ke shafin, ka saukar, tare da loda ta a wayarka. Allah sa a dace.

Assalaamu Alaikum, ina fatan kana cikin koshin lafiya tare da iyalanka. Na dade ina karatun shafinka a cikin Jaridar AMINIYA, kuma yana kara min fahimtar ayyuka na. Domin ina da shedar karatu ta NCE a fannin karantar da kimiyyar kere-kere, watau Technical Education, da kuma Difiloma a fannin kwamfuta. Ina jin dadin karatun shafinka. Allah ya kara mana fahimta, amin. - M. A. Faruk, Sokoto: 08036029098

To mun gode mu ma, kuma Allah kara dankon zumunci, da fahimta, da kuma juriya wajen kasancewa tare da mu. Tsarkakakkiya kuma cikakkiyar godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda duk wata ni’ima ta fahimta ko wayewa ko ci gaba, daga gareshi take. Mun gode.

Salamu Alaikum, ina amfani da wayar Nokia 6760 kuma ina da manhajar Opera mini a ciki. Ina son bude Imel ne don karban sako da aikawa, don Allah yaya zan yi? Na gode. - 08036017399

Kamar yadda muka sha bayani kwanakin da suka wuce, bude akwatin Imel ta wayar salula, in dai ba nau’ukan “Smartphones” bane, ba abu bane mai yiwuwa. Na farko dai asalin shafin da za a budo maka don ka yi rajista, ba ya samuwa sai ka aika da sakon “START”, zuwa wata lambar, wacce kuma bamu da kamfanin a nan nahiyar Afirka, ko ince Nijeriya. Wannan sakon da za ka aika ne zai sa a aiko maka da rariyar likau din da zaka bi, don samun shafin. Abu na biyu kuma shi ne, yin rajistan a waya na iya ci maka kudi da yawa. Duk da haka, idan kana amfani da wayar salula nau’in “SmartPhones” ne, (irin su “Blackberry” ko nau’ukan “E-Series” na kamfanin Nokia) to kana iya yin rajista ba matsala. Domin wadannan nau’ukan wayoyin salula suna mu’amala ne da Intanet tamkar kwamfuta cikakkiya. Da fatan an gamsu.

Da fatan Malam yana nan lafiya. Ni matsalata ita ce: a da ina karba ko aika sakon Imel ta hanyar Yahoo a wayata, amma tun shigowar wannan shekarar ko na shiga sai dai in ga tsoffin sakonnin da na aika ko karba. Shin a ina matsalar take ne: daga waya ta ne, ko daga Yahoo? - Sani Abubakar ‘Yankatsare, Jos: 08026023796

Malam Sani barka da war haka kuma ya aka ji da dawainiya da mu? Da fatan ana lafiya. Watau akwai abubuwa guda biyu ko uku. Da farko dai ya danganci tsarinka. Watakila tun da aka shiga wannan shekarar baka aika da sako ko kuma karbi wani sako daga wani ba. In kuwa haka ta kasance, to ai babu yadda za a yi ka samu wani sabon sako a jakar Imel dinka. Na biyu kuma, a iya cewa matsalar daga wayarka ce, amma hakan da kamar wuya, wai gurguwa da auren nesa. Domin in daga wayarka ne, ai baza ka iya ma shiga Imel din ba tun farko. In har kana ganin sakonnin da ka aika a baya, da wadanda aka aiko maka a baya, kuma babu wanda ya sanar da kai cewa ya aiko maka sako amma ka kasa gani, to ba zai zama matsalar daga gareta ba. Abu na uku shi ne a ce laifin kamfanin Yahoo. Hakan kuwa bazai yiwu ba, domin muddin kana iya shiga jakar Imel dinka daga wayarka, to ba yadda za a yi laifin yazo daga kamfanin Yahoo. Da fatan Malam ya gamsu.

Tsaunuka Masu Aman Wuta, Da Tasirinsu Ga Muhalli (3)

Abu na farko da ke makare a karkashin tsaunin dai, kamar yadda muka sanar, shi ne damamme, kuma tafasasshen “kunun dutse”. Na kira shi da kalmar “kunu” ne saboda a dame yake, da kaurinsa, kamar kunun gari (ko “jaguda”, ga wadanda suka santa). Na kira shi “tafasasshe” ne saboda yana da matukar zafi. Saboda tsananin zafinsa ma, launinsa ja ne, zur! A karo na karshe, na danganta shi da “dutse” ne (na ce “kunun dutse”) saboda asalinsa kenan. Dutse ne aka rababbaka shi, ya zama damammen kunu, mai kauri, kuma ja zur. Mai karatu ba zai fahimci yadda abin yake ba sai ya ganshi a fili, ko kuma ya kwatanta shi da “damammen kunun karfe”, wanda masana’antar karafa ke narkawa kafin su sandarar da shi zuwa ga abin da suke son kerawa. Hakan ma a babin kwatance ne, ba wai daidai zafinsu daya ba. Wannan kunun dutse da ke makare a karkashin tsaunin dai yana da matukar zafi. Masu bincike sun sanar da cewa mafi karancin zafinsa shine dari bakwai, a ma’aunin zafi na santigireti (700c). A can sama kuma, ya kai dubu daya da dari uku, a wannan ma’auni (1,300c)! Yana cakude ne da sinadaran kimiyya da dama. Daga cikinsu akwai sinadarin gilas, kuma a dauke yake da wata masifaffiyar iska mai kumfa a samansa. Da zarar zafi ya kai zafi, sai wannan masifaffiyar iska ta fetso shi waje, da zafinsa, da kuma kaurinsa. Wannan kunun dutse shi ne ake kira Molten Magma, a Kimiyyance. Kuma shi ne asalin dautse nau’in Igneous da muka sani; watau dunkulalle kuma tsantsar dutse kenan. Wannan shi ne abu na farko da ke fitowa daga karkashin tsauni mai amai, tare da wannan iska, da zafi da kuma sinadaran da ke tattare da shi. Da zarar ya fito, sai ya sake suna, da kuma yanayi.

Wannan ya kawo mu ga nau’in abin da ke samuwa na biyu, a yayin aman tsauni. Fitowar wannan kunun dutse ke da wuya sai ya kasu kashi biyu. Kafin bayanin nau’insa, duk sadda wannan kunun dutse ya fito waje, sunansa ya tashi daga Molten Magma ko Magma, ya koma Lava, ko Lava Flows. Shi wannan Lava ko kace Sandararren Kunun Dutse, shi ne ke yin ambaliya daga saman tsaunin, ya fara gangarowa, kafin ya sandare ya zama dutse curarre. A yayin gangarowarsa ne yake yin iya barnar da yake yi, musamman idan tsaunin a kusa yake da wani kauye, kuma cikin dare aman ya faru. Wanda ke gangarowa ko yin ambaliya, shi ake kira Active Lava, kuma shi ne mai haddasa wuta da ke ci balbal a duk sadda aman ya faru. Wannan ke nuna mana cewa shi tsaunin ba wai wutar yake amanta ba, a a, sinadaran wutar yake amayowa. Wannan nau’i na sandararren kunun dutse mai ambaliya, shi yafi komai barna a lokacin da yake fitowa. A tarihin tsaunuka masu amai, akwai garuruwa ko kauyuka masu yawa da suka kone ko suka tashi karfi da yaji, sanadiyyar wannan ambaliya mai hadari. Misali, akwai wani kauye da ke Jumhuriyar Kwango, ko tsohuwar Zayar ta da, wanda tsaunin Nyiragongo ya kona sanadiyyar aman da yayi cikin dare, lokacin da ‘yan kauyen ke bacci. Haka ma kauyukan Kaimu, da Kalapana, da Kapoho, da Kewaiki, duk kauyuka ne da tsaunin Kilauea da ke Tsibirin Hawaii na kasar Amurka ya kona, sanadiyyar aman da yake yi a-kai-a-kai. Haka ma akwai kauyen San Sebastiano al-Vesuvio da ke kasar Italiya, wanda tsaunin Vesuvius ya kona a shekarar 1944. A kasar Filifins ma akwai wani kauye da Tsaunin Cagsawa ya kona. Wadannan su ne garuruwa ko kauyukan da wannan sandararren kunun dutse mai malala a farfajiyar tsauni ya kora ko kona, tare da salwantar da rayuwan mazauna cikinsu.

A daya bangaren kuma, akwai kauyuka ko garuruwan da yayi musu mummunan ta’asa. Wadannan kauyuka sun hada da: kauyen Catamina da ke kasar Italiya, wanda Tsaunin Etna yayi wa ta’asa a shekarar 1669, sai garin Goma da ke Jumhuriyar Kwango Kinshasa, a shekarar 2002, da garin Haiwaey da ke Tsibirin Iceland, wanda tsaunin Eldfell ya raunata a shekarar 1973. Har wa yau akwai kauyen Royal Gardens da ke Tsibirin Hawaii na kasar Amurka da ya sha lugude a shekarar 1986-87, sai kuma wani kauyen San Juan na kasar Meziko mai suna Paricutin. Wannan shine galibin ta’adin da wannan sandararren kunun dutse mai gangarowa daga saman tsauni ke yi a daidai lokacin da tsaunin ke amai. Nau’i na biyu kuma shine wanda ya riga ya kame, sanadiyyar hucewar da yayi bayan ya gangara, ko ya samu wani kududdufi ya kwanta. Wannan nau’i shi ake kira Passive Lava, watau nau’i mara illa kenan. Idan ya riga ya kame, to nan take yake zama wani nau’in taki mai matukar alfanu wajen harkar noma. Ka ji wata hikimar Ubangiji kuma! Don haka wasu lokuta ake samun wasu kauyuka da ke kusa da tsauni mai aman wuta, wadanda ko an ce su tashi sai su ki. Ko da ya musu ta’adi sanadiyyar aman da yayi, za su sake dawowa inda suke a da. Wannan ma ya sa a Tsibirin Hawaii na kasar Amurka akwai kauyukan da sun kone sanadiyyar wannan ta’adi, amma daga baya sai hukuma ta sake gina su. Mazauna wurin na yin hakan ne sanadiyyar albarkar noma da suke samu. Domin duk kasar da wannan sinadari na Lava yayi ambaliya a kanta, to za ta zamo mai matukar albarka ta fuskar noma.

“Tokar Kunun Dutse” (Ash Plume)

clip_image002To bayan wannan sinadari kuma, sai abu na gaba da ke fitowa daga cikin wannan tsauni, watau “Tokar Kunun Dutse”, ko kuma Ash Plume, ko Volcanic Ash a Kimiyyance. Wannan shi ma yana dauke ne da sidanarai masu cutarwa da amfani. Wannan toka na dauke ne da buraguzan duwatsu da gilasai masu fadin kasa da milimita biyu, da ke samuwa a yayin da wani tsauni yayi amai. Babban abin da ke haifar da wannan toka mai dauke da hayaki kuwa ita ce masifaffiyar iskar da ke cillo wancan damammen kunun dutse mai fitowa daga karkashin tsaunin. Wannan iskar ce ke dauko wannan toka, ta cilla shi sama har cikin sararin samaniya. Wannan tokar kunun dutse na dauke ne da launin ruwan kasa, watau Brownish Ash. Abu na biyu da ke taimakawa wajen samar da wannan tokar kunun dutse shi ne sinadaran haske masu kyastuwa daga wutar da ke kamawa daidai lokacin da wancan kunun dutse ke fitowa daga kasan tsaunin. Sai abu na uku, watau buraguzan laka da ke samuwa yayin da kunun dutsen ke arangama da makogwaron tsaunin wajen fitowa a fusace, watau Volcanic Vent. Idan kuma Tsaunin Kankara ne da ke teku (watau Glacial Ice), da zarar kunun dutsen ya fito, ya hadu da narkakken ruwan kankarar da ke tekun, zai sandarar da shi ne nan take zuwa gari ko tokar gilasai, sannan kuma kurar da ke fitowa daga tsaunin ta tarkata wannan garin gilasai tayi sama da su, don toshe hazo da sararin samaniya. Tirkashi! Kafin mu kai ga amfani, zai dace mu yi bayanin munanan tasirin wannan toka na kunun dutse. Hakan ne zai bamu damar fahimtar cancantarsa wajen haddasa irin hasarar da yayi wa kamfanonin jiragen sama a watan Afrilu.

AMSOSHIN WASIKUN MASU KARATU TA TES

Salamun Alaikum Baban Sadik, tambayata ita ce: yaya tsarin amfani da Intanet na tafi-da-gidanka (watau Datacard Internet ko “F@stlink”) da kamfanonin wayar salula na kasar nan ke bayarwa? Kuma kasashen ketare ma suna da irin wannan tsarin? - Aliyu Mukhtar Sa’idu (IT), Kano: 08034332200

Malam Aliyu, wannan tsari na “F@stlink” kamar yadda kamfanin MTN ke kiransa, ba wani tsari bane sabo. Hasali ma dai an dade ana amfani da shi a wasu kasashe kafin zuwansa nan kasar. Tsari ne da ya kunshi amfani da fasahar Intanet a kwamfutar tafi-da-gidanka, watau Laptop, ta hanyar amfani da Makalutun Sadarwa, watau “Internet Modem”. Idan ba a mance ba, bayanai sun gabata cewa kwamfuta na iya mu’amala da fasahar Intanet ko Giza-gizan sadarwa ne ta hanyar wannan makalutun sadarwa, wacce ke zakulo bayanan da ke Intanet a matsayin siginar lantarki, ta kuma juya su zuwa haruffa ko hotuna ko sauti, kamar dai yadda suke a uwar garken da ta zakulo su.

Wannan tsari na zakulo bayanai a siffarsu, a mayar da su zuwa siginar lantarki, sannan idan sun zo muhallin da ake son amfani da su su bayyana kamar yadda aka dauko su, shi ake kira “Modulation and Demodulation”, wanda kuma daga wadannan sunaye biyu ne aka samo sunan wannan makalutu da ake kira “Modem” a turancin Kimiyyar sadarwa ta zamani. To wannan makalutu kuwa asalinsa babba ne, kamar dai irin wayoyin tarho da muke amfani dasu a da. Idan ka saya za ka jona shi ne da kwamfutarka, ta wayar da yazo da ita. To amma da zamani ya ci gaba, sai aka mayar da su kanana, sirara, wasu ma girmansu bai wuce dan yatsan hannu, wasu kuma kamar tafin hannu suke. Ya dai danganci kamfanin da ya kera su. Da zarar ka saya, sai ka tsofa shi a jikin kwamfutar tafi-da-gidanka, ka kuma loda mata masarrafar da take zuwa da shi a faifan CD ko makamancin wannan, don ta haddace dukkan tsare-tsaren da ke ciki. Har wa yau, wannan tsari na amfani ne da lambar wayar tarho da ke dauke cikin katin SIM da kamfanin wayar ke bayarwa. Idan ka tashi shiga Intanet, sai ka sayi katin kira (watau “Recharge Card”) ka loda mata, sannan ka fara tsallake-tsallakenka. Kamar yadda bayanai suka gabata a sama, sauran kasashe ma na amfani da wannan tsari, kusan shahararsa a wasu kasashen ma yafi na nan Nijeriya. Da fatan ka gamsu.

Assalaamu Alaikum, don Allah Baban Sadik wai shin mai yiwuwa ne mutum ya iya gina Mudawwanarsa (blog) ta wayar salula ko kuwa dole sai a kwamfuta? - Jamilu Ahmad, Kaduna: 08032424168

Malam Jamilu ya danganci irin wayar da kake da ita. Idan babbar waya ce, mai shafi mai fadi, da kuma saurin sadarwa da Intanet, kana iyawa. Amma idan ba haka ba, zai dace ka yi amfani da kwamfuta. Domin zai dauke ka tsawon lokaci, sannan galibin gidajen yanar sadarwa na Mudawwanai suna da shafuka zubi biyu ne; da wanda ake iya shiga da kwamfuta, da kuma shafin da ake shiga ta amfani da wayar salula. Idan ka shiga shafin da ake shiga ta kwamfuta a wayarka, ba za kaji dadin mu’amala da shafin ba, domin zai kasance mai fadi ne, kuma yana dauke da hotunan da za su ci maka kudi sosai kafin ka gama gabatar da dukkan abin da kake son gabatarwa. A takaice dai ka yi amfani da kwamfuta wajen ginawa, in yaso sai ka rika shiga ta wayarka kana aikawa da sakonni. Da fatan ka gamsu.

Tsaunuka Masu Aaman Wuta, da Tasirinsu ga Muhalli (2)

Sai nau’i na biyu, wanda ke samuwa sanadiyyar afkawar wani faranti a saman wani, mai haifar da ninkewar wasu farantan a sanan wasu, har su yi toroko a doron wannan kasar tamu, su zama tsauni. Nau’in tsaunin da ke samuwa ta wannan hanya shi ake kira Fold Mountain a Kimiyyance. A Hausar zamani kana iya kiransa da suna ‘Ninkakken Tsauni’. Domin haka sifarsu take; a tattare a waje daya, wani a saman wani. Irin wannan nau’in tsauni shi ma yana nan birjik a duniya. Babban misali da zan iya kawowa yanzu shi ne na wadanda ke warwatse a garuruwan Jura da Zagros na kasar Iran. Su ne shahararrun nau’in Ninkakken Tsauni da ake misali da su a duniya. Nau’i na karshe kuma shi ne wanda ke samuwa sanadiyyar riftawar wani bangaren farantin karkashin kasa, tare da barin dayan bangaren a tsaye. Wannan ke haifar da samuwar tsauni nau’in Block Mountain a Kimiyyance, ko kuma ka ce ‘Dunkulallen Tsauni’ a Hausance. Ire-iren wadannan tsaunuka a tsaye su ke caras, tare da samuwar kwari a gefensu; abin da ke nuna alamar riftawar wani bangaren faranti ne daga dan uwansa. Wadannan, a takaice, su ne nau’ukan tsaunuka guda uku da ake da su a duniya a yanzu; ba su da na hudu.
Tsaunuka Masu Aman Wuta (Volcanic Mountains)
Kamar yadda bayanai suka gabata, nau’ukan tsaunuka masu aman wuta su ne wadanda suka samu sanadiyyar gibi a tsakanin farantan kasa guda biyu. Wanda kuma ke aman wuta lokaci-lokaci. Su kansu sun kashi zuwa kashi uku ne, dangane da yanayin aman da suke yi. Nau’i na farko su ne wadanda suke yin amai a-kai-a-kai, babu kakkautawa. Ko dai a dukkan shekara, ko bayan shekaru bibbiyu, ko kuma bayan shekaru biyar-biyar ko duk wata tazarar da ba mai tsawo bane a zamaninsu. Idan tsauni yayi suna wajen yawan amai a-kai-a-kai, akan kira shi da suna Active Volcano. Watau “Rayayyen Tsauni mai Aman Wuta” kenan, a Hausar zamani. Idan daga baya ya daina amai, bayan ya shahara da amai na tsawon lokaci, to akan kira shi Extinct Volcano a Kimiyyance. Watau “Mataccen Tsauni mai Amai”. A karo na uku, idan bayan ya daina na tsawon zamani ko shekaru masu dimbin yawa, har an yanke kauna an kuma daina tsammanin zai sake amai, sai ya ci gaba da amai kamar yadda yake yi a baya, shi kuma akan kira shi Dormant Volcano; ko kace “Farfadadden Tsauni mai Amai”.
A iya binciken Malaman Kimiyyar Kasa, an kasa bambacewa tsakanin nau’in Extinct Volcano da kuma Dormant Volcano. Domin sau tari an sha samun wasu tsaunukan da suka daina amai, aka yanke kauna da za su kara yi, sai kawai ga shi sun ci gaba da amai. Babban misali shine wani tsauni mai suna Fourpeaker Volcano da ke Lardin Alaska ta kasar Amurka. Wannan tsauni, a iya tarihi, ya shekara sama da shekaru dubu goma bai sake amai ba. Wannan ta sa aka cire shi daga sahun nau’ukan tsaunuka masu rai, zuwa matattu, watau Extinct. Cikin shekarar 2007, watan Satumba, sai ya farfado, ya ci gaba da amai. Wannan tasa masana suka ce tsaunuka masu amai nau’i biyu ne kawai; ko dai masu cikakken rai ne, watau Active, ko kuma masu sumewa ne su sake farfadowa, watau Dormant.
Bayan haka, akwai wasu tsaunuka masu aman wuta da suka shahara a duniya sanadiyyar barnar da suke yi a duk sadda suka yi amai. Wadannan tsaunuka dai guda goma sha shida ne, kuma galibinsu suna Yammaci ne ko Gabashin duniya. Masana sun sanya musu lakabi da “The 16 Decade Mountains”. Abin da wannan lakabi ke nufi a ma’anance dai shi ne: “Tsaunuka Sha Shida Masu Aman Wuta da Suka fi Hadari”. Wadannan tsaunuka a halin yanzu suna warwatse ne a kasashe guda goma sha uku. Kasashen dai su ne: kasar Rasha, da Meziko, da Jafan, da Italiya, da Kolombiya, da Amurka, da Indonesiya, da Jamhuriyar Kwango (watau tsohuwar Zayar kenan), da Gwatemala, da Girka, da Filifin, da Andalus (watau Spain), sai kuma kasar Papua New Guinea. Wadannan su ne kasashen da ke dauke da tsaunuka masu aman wuta da suka fi kowanne zama hadari idan suka fara amai, sanadiyyar mummunar ambaliyar tafasasshen kunun dutse da suke yi, mai haddasa mummunar illa ga garuruwan da ke makwabtaka da su, ko kuma muhallin da suke.
Tsaunukan Kasar Iceland
Kasancewar wannan lamari na toka mai guba da ya haddasa mummunar hasara ga kasashe da kamfanonin jiragen sama ya samo asali ne daga kasar Iceland, na ga dacewar gabatar da dan takaitaccen bayani kan wannan kasa, da adadin tsaunuka masu aman wuta da take dauke dasu, da kuma tsarin aman da suke yi, lokaci-lokaci. Hakan zai taimaka wa mai karatu wajen fahimtar yanayi da kuma dalilan da suka sa hasarar ta yawaita, da kuma dalilan da suke haddasa yawaitan aman da tsaunukan da suke yawan yi a-kai-a-kai.
Kasar Iceland dai tsibiri ce; ma’ana, a gewaye take da teku, daga dukkan bangarorinta. Kuma an kafa kasar ne tun shekarar 874AD, watau shekaru sama da dari biyar kenan ya zuwa yanzu. Wannan kasa na sarkafe ne a tsakiyan daya daga cikin manyan tekunan duniya da ake ji da su, watau tekun Atlantika. Kuma kamar yadda muke da farantai a karkashin kasar da muke takawa ko rayuwa a kanta, haka ma a karkashin tekunan duniya akwai ire-iren wadannan farantai, ko Plates. Bayan haka, Tsibirin Iceland na dore ne a daidai inda farantan kasan tekun suke makwabtaka da juna; tsakanin farantan da suka taso daga Arewacin Amurka, suka yi kudu (watau North American Plates), da kuma wadanda suka taso daga Nahiyar Turai, suka yi Arewa (watau Eurasian Plates).
Zaman Tsibirin Iceland a wannan muhalli ya sa ta samu kanta a “mabubbugan kunun dutse mai haddasa aman tsauni”, watau Volcanic Hotspots. Wannan tasa har wa yau Tsibirin ya wayi gari a matsayin kasar da tafi kowace kasa yawan tsaunuka masu aman wuta a duniya. Kididdiga sun nuna cewa akwai tsaunuka masu aman wuta guda dari da talatin (130) a kasar Iceland. Cikin wannan adadi, bincike ya nuna cewa guda goma shatakwas ne kadai suka yi amai ya zuwa yanzu. Wannnan a iya sanin masu bincike kenan. Allah kadai ya san yaushe sauran suka daina, bayan tsawon lokacin da suka dauka suna yi, kafin wannan zamani. Manyan tsaunuka guda biyu da suka yi amai kwanan nan su ne tsaunin Fimmvorouhab, wanda ya dauki tsawon kwanaki ashirin da biyu yana amai (daga ranar 20 ga watan Maris, zuwa 12 ga watan Afrilu), sai kuma tsaunin Eyjafjallajokull (ana furutu shi da: Aya-fyatla-jo-kult), wanda shi kuma ya dauka daga ranar 14 ga watan Afrilu, har zuwa karshen watan. Wannan tsaunin karshen ne ya haddasa samuwar wannan toka mai guba da bayanansa ke tafe. To me da me suke fitowa daga cikin tsauni, a yayin da ya fara amai?
Abubuwan da Tsauni ke Amayarwa
Idan aka ce tsauni na amai, to dole ne a samu abin da yake amayarwa. Tabbas kalmar da ta shahara a fassarar Hausa ita ce: “aman wuta”, to amma wuta ne kadai tsaunin ke amayarwa, ko kuwa wasu abubuwa ne masu haddasa samuwar wutar a inda aman ya samu? Wannan tasa muka kebance wannan sashe don bayyana wasu cikin shahararrun abubuwan da tsauni ke yin amansu. Kada a mance, mun riga mun yi bayanai kan dalilan da ke haddasa aman a baya, ba sai mun sake maimaitawa ba. A yanzu ga wadannan bayanai nan a fayyace.
AMSOSHIN WASIKUN MASU KARATU TA TES

Assalaamu Alaikum, na karanta shafinka na “Kimiyya da Kere-kere” a cikin jaridar AMINIYA. Allah Ya kara hazaka. Don Allah a taimaka mani da wasu bayanai masu alaka. Ga adireshin Imel dina: yunusayunusa43@yahoo.com. Daga Yunusa Hussaini, Samaru, Zaria.
Malam Yunusa mun gode da addu’a. Kai ma Allah kara maka hazaka da juriyar kasancewa tare damu. Dangane da bukatarka, na rasa me zan aika maka, musamman ganin cewa dukkan abin da nake rubutawa a wannan fanni ne ake bugawa a shafin. Sai dai idan kana da bukatar kasidun da suka gabata a baya ko shekarun baya, kana iya zuwa shafin Makarantar Kimiyya da Fasahar Sadarwa da ke http://fasahar-intanet.blogspot.com, ko wanda muka kebe don zuba kasidun Kimiyya da Fasahar Kere-kere, da ke http://kimiyyah.blogspot.com. Duk kasidun da da ke bayyana a wannan shafi suna can a taskance. Da fatan ka gamsu.
Assalaamu Alaikum, Malam Abdullahi yaya kokari? Tambayata ita ce: in har Malaman Kimiyya da Fasaha a wajensu komai ya faru, akwai abin da ya haddasa shi, ba Allah ba, to wai me za su ce, ko me suka ce dangane da masu tsafi, wanda ke hada wani abu sai wani abu ya tashi; ba kuma a kimiyyance suke yi ba? Daga Khaleel Nasir Kuriwa, Kiru, Kano: 07069191677
Malam Khaleel barka da kokari. Hakika har yanzu dai basu yarda da ire-iren wadannan abubuwa ba, kuma ba su kididdige su a matsayin wata ci gaba ta ilimi a fannin Kimiyya. Kamar yadda kai ma ka kira su da “matsafa”, haka su ma suke kiransu. A turance sukan kira su “magicians”. Su malaman kimiyya suna da wasu ka’idoji ne da suke bi wajen bincike, masu basu irin sakamakon da suke bukata dangane da kowane irin yanayi. A tsarinsu, duk wani bincike da bai da asali daga wadannan ka’idojin, to ba su bashi wata kima. Da fatan ka gamsu.

Tsaunuka Masu Aaman Wuta, da Tasirinsu ga Muhalli (1)

Laraba, 14 ga Watan Afrilu, 2010

Cikin makonni biyun karshe na watan Afrilun da ya gabata ne wani sashen sararin samaniyan duniya ya shiga wani yanayi mai ban mamaki da rudani, inda jirage suka lazimci tashoshinsu, matafiya suka shafe sama da kwanaki goma a filayen jirgin sama suna kwana a tsakanin jakunkunansu, sanadiyyar gurbatan yanayi da ya samo asali daga wasu sinadarai masu guba da cutarwa da suka killace tafarkin hanyan jirage a sararin samaniyan nahiyar Arewaci da Yammacin Turai, da ma wani bangare na nahiyar Gabashin Amurka. Wannan sinadari mai kama da toka yayi ta tuttudowa ne daga aman wutar da wani babban tsaunin kasar Iceland ya fara yi tun daga ranar Laraba, 14 ga watan Afrilu, har zuwa kusan karshen watan. Daga baya an samu yaduwar wannan toka har zuwa kasar Turkiyya, inda ya toshe sararin samaniyar kasar, da wasu cikin kasashen Arewacin Afirka, kamar Maroko da sauransu. Wannan toka mai hadari a farko ya toshe sararin samaniyan wannan kasa ta Iceland, daga nan iska ta kada shi zuwa Arewa maso Yammacin Turai, inda ya toshe wa kasashe har wajen ashirin sararin samaniya su ma, ya hana jirage tashi tsawon wannan lokaci. A tarihin safaran jiragen sama a duniya, ba a taba samun yanayin da ya tayar da hankali, ya haifar da hasara mafi girma, ya kuma shafi kasashe da dama irin wannan ba.

Kasancewar kasar Iceland na tsakanin manyan nahiyoyi ne guda uku musamman, kuma masu karfin tattalin arzikin kasa a duniya, tasa wannan lamari ya haifar da hasarar dukiya mai dimbin yawa cikin wadannan kwanakin da basu kai wata guda ba. Nan take kallo ya koma sama. Kamfanonin jiragen sama suka yi zugum. Fasinjoji suka kama zaman dirshan; ga tikiti amma babu damar tafiya. Harkoki suka tsaya cak. An kiyasta cewa kamfanonin jiragen sama sunyi hasarar sama da dala miliyan dari biyu a duk rana guda. Kafin sararin samaniya ya gama kwaranyewa har jirage su fara tashi kuwa, kamfanonin safarar jiragen sun yi hasarar kudi sama da dalar Amurka miliyan dubu dari da dubu saba’in. Watau Biliyan daya da digo bakwai kenan ($1.7 billion). Bayan tarin tikitin da aka soke saboda lokacinsu ya wuce, wadanda kuma a ka’idar safaran jiragen sama na kasuwanci, ba su da Inshora balle a fanshe haushi da hasaransu, da dama cikin kasashe da kamfanoni daban-daban sun tafka hasara mai dimbin yawa sanadiyyar wannan toka da Allah Ya aiko. Jiragen kaya da dama sun yi kwantai, dauke da kayayyakin abinci, ko magunguna; ko dauke da wasiku, ko man jirgin sama, ko man gas na injina da za a kai wasu kasashen ko biranen, ko kayan alatu, da dai sauran abubuwa masu amfani da suka kasa kaiwa masaukinsu cikin lokaci. Wadansu sun lalace a cikin jiragen, wasu kuma sun yi kwantai. Abu na karshe kuma shi ne, nan take farashin hannayen jarin wadannan kamfanonin jirage ya fadi warwas a kasuwannin hannayen jari da ke kasashen Turai da Amurka da Asiya.

Duk wannan hasara ta samo asali ne sanadiyyar aman wuta (Volcanic Eruption) da wani tsauni yayi a kasar Iceland, kamar yadda na tabbata masu karatu sun sha labarun tuni. Wannan amai ne ya haifar da samuwar wannan sinadari a yanayin toka, wanda kuma sanadiyyar hadarinsa ga jirage da masu tuka su ne aka samu tsaikon da ya haifar da wancan hasara. Da dama cikin masu karatu sun dauka cewa babban dalilin da ya hana jirage tashi shi ne don watakila direbobin ba za su ga hanya da kyau ba, sanadiyyar kura ko tokar da ta hada duhu mai tsanani a nahiyar da abin ya shafa. Wannan ko kadan ba haka bane. Wannan tasa ma muka ga dacewar gabatar da bayanai gamsassu a kimiyyance, don nuna muni da kuma tasirin wannan lamari da na sauran bayanai masu nasaba da tsaunuka masu aman wuta, watau Volcanic Mountains, da kuma abin da ire-iren wadannan tsaunuka ke fitarwa idan hakan ta kasance. Amma kafin nan, ga mukaddima nan kan ma’ana da nau’ukan tsaunukan da muke dasu, da kuma yadda suke samuwa a duniya baki daya – duk a mahangar kimiyyar kasa. Don sai mun san wadannan sannan za mu iya fahimtar tasirin wannan toka ta aman wuta da tsaunin yayi, watau Ash Plume, ko Volcanic Ash, a Kimiyyance.

Tsaunuka da Nau’ukansu a Kimiyyance

A fannin Kimiyyar Kasa (watau Geology ko Earth Science ko Geography), Tsauni – ko Mountain a harshen Turanci - wani tarin kasa ne a doron kasar da muke takawa, mai cakude da dutse ko duwatsu, wanda ke samuwa sanadiyyar hargitsin da ke faruwa tsakanin farantai ko fallayen kasa masu tsauri da ke can karkashin kasar da muke rayuwa a kai. Wadannan farantai – ko Plates a Kimiyyance – wasu nau’ukan shimfidun kasa ne da ke karkashin wannan kasar da muke takawa. Hargitsin da ake samu a tsakaninsu lokaci-lokaci ne ke haifar da samuwar nau’ukan tsaunukan da muke gani a doron wannan kasa tamu. Wannan “hargitsi” kuma da ke faruwa a tsakaninsu, shi ake kira Plates Tectonics, a turancin Kimiyyar Kasa. Bigiren da wannan hargitsi ke faruwa kuma shi ake kira Fault Lines, a Kimiyyance.

Duk sadda aka samu wani hargitsi – na gocewa, ko karyewa ko riftawa – a tsakanin wadannan shimfidun kasa da ke karkashinmu, dayan abubuwa uku ne ke samuwa ko faruwa. Akan samu ninkewar wani farantin kasa a saman wani. Ko kuma a samu burmawar wata shimfidar da ke gefen wani farantin. Ko kuma, a karo na karshe, a samu kaucewa ko gocewar wani farantin daga wani. Hakan shi zai samar da kogo a tsakanin farantan biyu; abin da ke nuna akwai rauni a wannan muhalli kenan. Wannan ya kawo mu ga na’ukan tsaunuka guda uku a duniya, kamar yadda ake da dalilai guda uku masu haddasa hargitsi a tsakanin farantan da ke karkashin wannan kasar tamu.

Nau’in tsauni na farko shi ne wanda ke samuwa sanadiyyar gocewar wani faranti daga wani farantin, wanda kuma ke haifar da samuwar kogo a tsakanin farantan biyu masu makwabtaka da juna. Idan haka ta faru, dole za a samu rauni a tsakanin farantan, kamar yadda bayani ya gabata a sama. Wannan raunin ne ke samar da wani “tafasasshe kuma damammen kunun dutse”, watau Molten Magma a Kimiyyance. Idan tafiya tayi nisa, sai wannan tafasasshe kuma damammen kunun dutse ya feso waje, tare da iska mai tsanani, mai kuma dauke da guba. Fetsowarsa waje ke da wuya, sai ya daskare, yayi tudu. A haka zai yi ta yi har sai ya samar da tsauni mai zaman kansa. Nau’in tsaunin da ke samuwa sanadiyyar wannan rauni da ke samar da wannan fitinannen kunun dutse, shi ake kira Volcanic Mountain, a turance. Ko kuma kace ‘Tsauni Mai Aman Wuta’, a Hausar zamani. Irin wannan tsaunin ne ke bulbulo da wannan toka da ta mamaye sasannin nahiyar turai kamar yadda bayanai suka gabata. Basu takaita ga doron kasa kadai ba, har a cikin teku ana samun ire-iren wadannan tsaunuka; da na tudun kasa, da kuma na kankara. Babban misali kan na teku shine irin bala’in da ya samu a shekarar 2004 a nahiyar Asiya, sanadiyyar mahaukaciyar guguwar da ta taso daga cikin teku ta tafka barna mai dimbin yawa. Wannan mahaukaciyar guguwa da ake kira Tsunami, ta samo asali ne sanadiyyar irin wannann aman wuta da ya faru a karkashin tekunan da ke wadannan kasashen Asiya. Akwai nau’in tsaunuka masu aman wuta a warwatse a dukkan nahiyoyin duniya.

TAKAITACCEN TARIHIN “BABAN SADIK”

Wasu cikin masu karatu sun bugo waya suna neman in rubuta takaitaccen tarihi na don su karanta. Na basu uzuri kan cewa babu wani abin ji a cikin tarihi na, amma sun dage sai sun ji. Don haka na dan tsakuro muku wani abu cikin tarihin rayuwata.

Suna na Abdullahi Salihu Abubakar, an kuma haife ni ne a Unguwar Hausawa ta Garki Village da ke Karamar Hukumar Municipal, a babban birnin tarayya ta Abuja, cikin shekarar 1976. Shekaru na 34 kenan. Mahaifi na shi ne Malam Abubakar Salihu, shi kuma Salihu kakana ne. Asalin kakanni na (da ma sauran mazauna Unguwar Hausawa a Garki Village) daga Kano suke. Zama ne ya kawo su wannan wuri, wacce a wancan lokaci ta zama kamar zango, kusan shekaru dari biyu da suka gabata. Kuma ma saboda tsawon zamani da halin zamantakewa, a halin yanzu duk mun rikide mun zama Hausawan Abuja. Na yi makarantar Firamare, da Sakandare da kuma Jami’a duk a Abuja. A halin yanzu ina da digiri kan fannin Tattalin Azkirin Kasa (Economics), wanda na samu daga Jami’ar Abuja. Ina kuma kan neman ilmin Kur’ani da sauran fannonin Ilmin musulunci har yanzu.

Ni mutum ne mai sha’awar rubuce-rubuce da karance-karance. Ina kuma sha’awar binciken ilmi kan fannoni irinsu Tattalin Arzikin Kasa (Economics), da Fasahar Sadarwar Zamani (Information Technology), da Fasahar Intanet, da Tsarin Harsuna (Linguistics), da Fassara (Translation), da Aikin Jarida (Journalism) da Kimiyya (Science) da dai sauran fannoni masu nasaba da wadannan. Allah Ya hore min juriyar karatu da rubutu iya gwargwado. A halin yanzu na rubuta littafi kan fasahar Intanet, mai suna “Fasahar Intanet a Sawwake”, wanda ake gab da bugawa. Akwai kuma wadanda nake kan rubutawa a halin yanzu, kamar “Tsarin Mu’amala da Fasahar Intanet”, da kuma “Wayar Salula da Tsarin Amfani da Ita”. Sai kuma kasidun da nake rubutawa a wannan shafi a duk mako. A yanzu ina zaune ne a Sabon Garin Garki (watau New Garki Town) da ke nan Abuja. Ina da mata daya, da ‘ya’ya uku: Abubakar Sadiq, da Nabeelah, sai kanwarsu Hanan.

GODIYA DA BAN-GAJIYA

Shafin Kimiyya da Kere-kere na mika godiyarsa ga daya cikin manyan dalibansa, watau Malam Aliyu Mukhtar Sa’idu (IT) da ke Kano, sanadiyyar dawainiya da jigilar da yayi ta yi da ni lokacin da naje ziyarar aiki a Kano, daga ranar talata, 11 zuwa laraba, 12 ga watan Mayu. Allah saka da alheri, ya kuma jikan mahaifa, am