Saturday, December 4, 2010

Tsaunuka Masu Aman Wuta, Da Tasirinsu Ga Muhalli (3)

Abu na farko da ke makare a karkashin tsaunin dai, kamar yadda muka sanar, shi ne damamme, kuma tafasasshen “kunun dutse”. Na kira shi da kalmar “kunu” ne saboda a dame yake, da kaurinsa, kamar kunun gari (ko “jaguda”, ga wadanda suka santa). Na kira shi “tafasasshe” ne saboda yana da matukar zafi. Saboda tsananin zafinsa ma, launinsa ja ne, zur! A karo na karshe, na danganta shi da “dutse” ne (na ce “kunun dutse”) saboda asalinsa kenan. Dutse ne aka rababbaka shi, ya zama damammen kunu, mai kauri, kuma ja zur. Mai karatu ba zai fahimci yadda abin yake ba sai ya ganshi a fili, ko kuma ya kwatanta shi da “damammen kunun karfe”, wanda masana’antar karafa ke narkawa kafin su sandarar da shi zuwa ga abin da suke son kerawa. Hakan ma a babin kwatance ne, ba wai daidai zafinsu daya ba. Wannan kunun dutse da ke makare a karkashin tsaunin dai yana da matukar zafi. Masu bincike sun sanar da cewa mafi karancin zafinsa shine dari bakwai, a ma’aunin zafi na santigireti (700c). A can sama kuma, ya kai dubu daya da dari uku, a wannan ma’auni (1,300c)! Yana cakude ne da sinadaran kimiyya da dama. Daga cikinsu akwai sinadarin gilas, kuma a dauke yake da wata masifaffiyar iska mai kumfa a samansa. Da zarar zafi ya kai zafi, sai wannan masifaffiyar iska ta fetso shi waje, da zafinsa, da kuma kaurinsa. Wannan kunun dutse shi ne ake kira Molten Magma, a Kimiyyance. Kuma shi ne asalin dautse nau’in Igneous da muka sani; watau dunkulalle kuma tsantsar dutse kenan. Wannan shi ne abu na farko da ke fitowa daga karkashin tsauni mai amai, tare da wannan iska, da zafi da kuma sinadaran da ke tattare da shi. Da zarar ya fito, sai ya sake suna, da kuma yanayi.

Wannan ya kawo mu ga nau’in abin da ke samuwa na biyu, a yayin aman tsauni. Fitowar wannan kunun dutse ke da wuya sai ya kasu kashi biyu. Kafin bayanin nau’insa, duk sadda wannan kunun dutse ya fito waje, sunansa ya tashi daga Molten Magma ko Magma, ya koma Lava, ko Lava Flows. Shi wannan Lava ko kace Sandararren Kunun Dutse, shi ne ke yin ambaliya daga saman tsaunin, ya fara gangarowa, kafin ya sandare ya zama dutse curarre. A yayin gangarowarsa ne yake yin iya barnar da yake yi, musamman idan tsaunin a kusa yake da wani kauye, kuma cikin dare aman ya faru. Wanda ke gangarowa ko yin ambaliya, shi ake kira Active Lava, kuma shi ne mai haddasa wuta da ke ci balbal a duk sadda aman ya faru. Wannan ke nuna mana cewa shi tsaunin ba wai wutar yake amanta ba, a a, sinadaran wutar yake amayowa. Wannan nau’i na sandararren kunun dutse mai ambaliya, shi yafi komai barna a lokacin da yake fitowa. A tarihin tsaunuka masu amai, akwai garuruwa ko kauyuka masu yawa da suka kone ko suka tashi karfi da yaji, sanadiyyar wannan ambaliya mai hadari. Misali, akwai wani kauye da ke Jumhuriyar Kwango, ko tsohuwar Zayar ta da, wanda tsaunin Nyiragongo ya kona sanadiyyar aman da yayi cikin dare, lokacin da ‘yan kauyen ke bacci. Haka ma kauyukan Kaimu, da Kalapana, da Kapoho, da Kewaiki, duk kauyuka ne da tsaunin Kilauea da ke Tsibirin Hawaii na kasar Amurka ya kona, sanadiyyar aman da yake yi a-kai-a-kai. Haka ma akwai kauyen San Sebastiano al-Vesuvio da ke kasar Italiya, wanda tsaunin Vesuvius ya kona a shekarar 1944. A kasar Filifins ma akwai wani kauye da Tsaunin Cagsawa ya kona. Wadannan su ne garuruwa ko kauyukan da wannan sandararren kunun dutse mai malala a farfajiyar tsauni ya kora ko kona, tare da salwantar da rayuwan mazauna cikinsu.

A daya bangaren kuma, akwai kauyuka ko garuruwan da yayi musu mummunan ta’asa. Wadannan kauyuka sun hada da: kauyen Catamina da ke kasar Italiya, wanda Tsaunin Etna yayi wa ta’asa a shekarar 1669, sai garin Goma da ke Jumhuriyar Kwango Kinshasa, a shekarar 2002, da garin Haiwaey da ke Tsibirin Iceland, wanda tsaunin Eldfell ya raunata a shekarar 1973. Har wa yau akwai kauyen Royal Gardens da ke Tsibirin Hawaii na kasar Amurka da ya sha lugude a shekarar 1986-87, sai kuma wani kauyen San Juan na kasar Meziko mai suna Paricutin. Wannan shine galibin ta’adin da wannan sandararren kunun dutse mai gangarowa daga saman tsauni ke yi a daidai lokacin da tsaunin ke amai. Nau’i na biyu kuma shine wanda ya riga ya kame, sanadiyyar hucewar da yayi bayan ya gangara, ko ya samu wani kududdufi ya kwanta. Wannan nau’i shi ake kira Passive Lava, watau nau’i mara illa kenan. Idan ya riga ya kame, to nan take yake zama wani nau’in taki mai matukar alfanu wajen harkar noma. Ka ji wata hikimar Ubangiji kuma! Don haka wasu lokuta ake samun wasu kauyuka da ke kusa da tsauni mai aman wuta, wadanda ko an ce su tashi sai su ki. Ko da ya musu ta’adi sanadiyyar aman da yayi, za su sake dawowa inda suke a da. Wannan ma ya sa a Tsibirin Hawaii na kasar Amurka akwai kauyukan da sun kone sanadiyyar wannan ta’adi, amma daga baya sai hukuma ta sake gina su. Mazauna wurin na yin hakan ne sanadiyyar albarkar noma da suke samu. Domin duk kasar da wannan sinadari na Lava yayi ambaliya a kanta, to za ta zamo mai matukar albarka ta fuskar noma.

“Tokar Kunun Dutse” (Ash Plume)

clip_image002To bayan wannan sinadari kuma, sai abu na gaba da ke fitowa daga cikin wannan tsauni, watau “Tokar Kunun Dutse”, ko kuma Ash Plume, ko Volcanic Ash a Kimiyyance. Wannan shi ma yana dauke ne da sidanarai masu cutarwa da amfani. Wannan toka na dauke ne da buraguzan duwatsu da gilasai masu fadin kasa da milimita biyu, da ke samuwa a yayin da wani tsauni yayi amai. Babban abin da ke haifar da wannan toka mai dauke da hayaki kuwa ita ce masifaffiyar iskar da ke cillo wancan damammen kunun dutse mai fitowa daga karkashin tsaunin. Wannan iskar ce ke dauko wannan toka, ta cilla shi sama har cikin sararin samaniya. Wannan tokar kunun dutse na dauke ne da launin ruwan kasa, watau Brownish Ash. Abu na biyu da ke taimakawa wajen samar da wannan tokar kunun dutse shi ne sinadaran haske masu kyastuwa daga wutar da ke kamawa daidai lokacin da wancan kunun dutse ke fitowa daga kasan tsaunin. Sai abu na uku, watau buraguzan laka da ke samuwa yayin da kunun dutsen ke arangama da makogwaron tsaunin wajen fitowa a fusace, watau Volcanic Vent. Idan kuma Tsaunin Kankara ne da ke teku (watau Glacial Ice), da zarar kunun dutsen ya fito, ya hadu da narkakken ruwan kankarar da ke tekun, zai sandarar da shi ne nan take zuwa gari ko tokar gilasai, sannan kuma kurar da ke fitowa daga tsaunin ta tarkata wannan garin gilasai tayi sama da su, don toshe hazo da sararin samaniya. Tirkashi! Kafin mu kai ga amfani, zai dace mu yi bayanin munanan tasirin wannan toka na kunun dutse. Hakan ne zai bamu damar fahimtar cancantarsa wajen haddasa irin hasarar da yayi wa kamfanonin jiragen sama a watan Afrilu.

AMSOSHIN WASIKUN MASU KARATU TA TES

Salamun Alaikum Baban Sadik, tambayata ita ce: yaya tsarin amfani da Intanet na tafi-da-gidanka (watau Datacard Internet ko “F@stlink”) da kamfanonin wayar salula na kasar nan ke bayarwa? Kuma kasashen ketare ma suna da irin wannan tsarin? - Aliyu Mukhtar Sa’idu (IT), Kano: 08034332200

Malam Aliyu, wannan tsari na “F@stlink” kamar yadda kamfanin MTN ke kiransa, ba wani tsari bane sabo. Hasali ma dai an dade ana amfani da shi a wasu kasashe kafin zuwansa nan kasar. Tsari ne da ya kunshi amfani da fasahar Intanet a kwamfutar tafi-da-gidanka, watau Laptop, ta hanyar amfani da Makalutun Sadarwa, watau “Internet Modem”. Idan ba a mance ba, bayanai sun gabata cewa kwamfuta na iya mu’amala da fasahar Intanet ko Giza-gizan sadarwa ne ta hanyar wannan makalutun sadarwa, wacce ke zakulo bayanan da ke Intanet a matsayin siginar lantarki, ta kuma juya su zuwa haruffa ko hotuna ko sauti, kamar dai yadda suke a uwar garken da ta zakulo su.

Wannan tsari na zakulo bayanai a siffarsu, a mayar da su zuwa siginar lantarki, sannan idan sun zo muhallin da ake son amfani da su su bayyana kamar yadda aka dauko su, shi ake kira “Modulation and Demodulation”, wanda kuma daga wadannan sunaye biyu ne aka samo sunan wannan makalutu da ake kira “Modem” a turancin Kimiyyar sadarwa ta zamani. To wannan makalutu kuwa asalinsa babba ne, kamar dai irin wayoyin tarho da muke amfani dasu a da. Idan ka saya za ka jona shi ne da kwamfutarka, ta wayar da yazo da ita. To amma da zamani ya ci gaba, sai aka mayar da su kanana, sirara, wasu ma girmansu bai wuce dan yatsan hannu, wasu kuma kamar tafin hannu suke. Ya dai danganci kamfanin da ya kera su. Da zarar ka saya, sai ka tsofa shi a jikin kwamfutar tafi-da-gidanka, ka kuma loda mata masarrafar da take zuwa da shi a faifan CD ko makamancin wannan, don ta haddace dukkan tsare-tsaren da ke ciki. Har wa yau, wannan tsari na amfani ne da lambar wayar tarho da ke dauke cikin katin SIM da kamfanin wayar ke bayarwa. Idan ka tashi shiga Intanet, sai ka sayi katin kira (watau “Recharge Card”) ka loda mata, sannan ka fara tsallake-tsallakenka. Kamar yadda bayanai suka gabata a sama, sauran kasashe ma na amfani da wannan tsari, kusan shahararsa a wasu kasashen ma yafi na nan Nijeriya. Da fatan ka gamsu.

Assalaamu Alaikum, don Allah Baban Sadik wai shin mai yiwuwa ne mutum ya iya gina Mudawwanarsa (blog) ta wayar salula ko kuwa dole sai a kwamfuta? - Jamilu Ahmad, Kaduna: 08032424168

Malam Jamilu ya danganci irin wayar da kake da ita. Idan babbar waya ce, mai shafi mai fadi, da kuma saurin sadarwa da Intanet, kana iyawa. Amma idan ba haka ba, zai dace ka yi amfani da kwamfuta. Domin zai dauke ka tsawon lokaci, sannan galibin gidajen yanar sadarwa na Mudawwanai suna da shafuka zubi biyu ne; da wanda ake iya shiga da kwamfuta, da kuma shafin da ake shiga ta amfani da wayar salula. Idan ka shiga shafin da ake shiga ta kwamfuta a wayarka, ba za kaji dadin mu’amala da shafin ba, domin zai kasance mai fadi ne, kuma yana dauke da hotunan da za su ci maka kudi sosai kafin ka gama gabatar da dukkan abin da kake son gabatarwa. A takaice dai ka yi amfani da kwamfuta wajen ginawa, in yaso sai ka rika shiga ta wayarka kana aikawa da sakonni. Da fatan ka gamsu.

No comments:

Post a Comment