Saturday, December 4, 2010

Tsaunuka Masu Aman Wuta da Tasirinsu Ga Muhalli (4)

Shi dai wannan toka da zarar yayi sama, ba ya narkewa. Sabanin irin tokan da muka saba gani da mu’amala da shi. Shawagi yake yi a sama. Don yana dauke ne da sinadarai masu wahalar sha’ani. Da zarar ya hadu da ruwa ko danshi, yakan zubo kasa ne, ya daskare, ya zama gundarin dutse shi ma, amma nau’in Tuff. Yana dauke ne da hayaki mai dauke da sinadarai masu cutarwa. A shekarar 1783, lokacin da tsaunin Leki da ke Tsibirin Iceland yayi amai, wannan tokan kunun dutse ya yi sanadiyyar mutuwar kashi daya bisa biyar na mutanen kasar nan take. Da wannan toka ya garzaya Yammacin Turai, yayi ajalin mutane sama da dubu ashirin da uku a kasar Ingila. Shakar wannan toka dai lalura ce babba, musamman ga masu cutar da ke da alaka da numfashi, irin Asma. Yana sanya kaikayin idanu. Idan kuma ka shake shi lokacin da yake tattare da danshi, to yana tara wasu sinadarai masu dauke da narkakken sinadarin siminti a cikin huhunka. Idan kuwa ya zubo kasa, bayan ya gama shawagi a sama, yana iya rusa rufin gidajen jama’a; iya gwargwadon yawansa a saman rufin gida. Wannan na faruwa ne sanadiyyar sinadaran da ke dauke cikinsa, masu nauyi. Yana lalata amfanin gona, yana kashe dabbobin gida, da na ruwa (irin kifaye da makamantansu), yana lalata hanyoyi, sanadiyyar santsi da hazo da yake haddasawa.

clip_image002Idan kuma yana sama aka fara ruwa mai dauke da walkiya da cida, to yana haddasa daukewar wutar lantarki, da dukkan hanyoyin sadarwar tarho, ya kuma sanya firgici iya kusancinsa da mutane ko garin da ake ruwan. Idan kuma ya riski direban jirgi a sama, lamari ya lalace kenan. Yana iya toshe masa gabansa nan take, yana iya kara wa jirgin nauyi, sanadiyyar zubowar da zai rika yi a saman jirgin. Wannan zai sa wani bangaren jirgin ya fi wani bangaren nauyi, musamman fukafukansa. Idan kuwa haka ta faru, to akwai matsala. Domin jirgi na tafiya lafiya ne idan nauyinsa yayi daidai a dukkan bangarori. Amma idan ya zama wani fiffiken ya fi wani fiffiken nauyi, to yana iya samun matsala nan take. Bayan nan, yana tasiri wajen lalata fitilun da ke taimaka wa jirgin sauka. Yana lalata farfelan jirgin idan ya shige ciki. Dole kuwa haka ta faru, saboda sinadaran da ke dauke cikin wannan toka basu narkewa. Idan jirgi ya ci gaba da tafiya a cikinsa, yana iya toshe masa bututun da yake gejin iska da shi, wanda kuma ke nuna masa iya tazarar tafiyarsa, watau Air Speed Indicator. Kamar yadda bayanai suka gabata a baya, samuwar wannan toka a sama na iya hana direban jirgin sadarwa tsakaninsa da masu lura da shi a tashar da yake son sauka ko ya baro a baya. Illa mafi muni da wannan toka ke yi wa jirigi shi ne ya sanya injin jirgin ya kama zafi, sanadiyyar toshe shi da yake yi. Idan hakan ta faru, jirgin ba zai samu kuzari ba ko kadan, dole ya gangaro kasa-kasa, in kuwa ba haka ba dukkan injinansa na iya daukewa nan take. Wannan shi ne abin da ya faru da wani jirgin British Airways F19, daidai lokacin da tsaunin Galunggung da ke kasar Indonesiya yayi amai, tare da watsa wannan toka a sararin samaniya cikin shekarar 1982. Nan take dukkan injinan jirgin guda hudu suka daina aiki, sai da ya rage tafiya, ta hanyar gangarowa kasa daga tazara nisan kamu dubu talatin da shida (36,000ft) zuwa kamu dubu goma shabiyu (12,000ft). Irin wannan har wa yau ya faru da jirgin KLM Boeing 747 da ya taso daga birnin Amstadam na kasar Nedaland zuwa nahiyar Amurka. Daidai lokacin ne tsaunin Redoubt da ke jihar Alaska ya fara amai. Jirgin bai tsaya ba ya ci gaba da tafiya. Saukarsa ke da wuya sai dukkan injinan jirgin suka yi dameji. Sai da aka kashe dalar Amurka miliyan tamanin ($80M), aka fitar da tokar da mizaninta ya kai kilogiram tamanin (80kg) daga injin, sannan aka kwashe wajen watanni uku ana gyara. Wadannan su ne kadan cikin illolin wannan toka na kunun dutse. Ta bangaren amfani kuwa, yana da tasiri sosai wajen sanya kasar noma ta zama mai amfani da albarka, kamar dai yadda wancan kunun dutse nau’in Passive Lava ke yi.

Kammalawa

Daga bayanan da suka gabata, a bayyane yake cewa tsaunuka masu aman wuta na da matukar tasiri ga al’umma da kuma muhallin da suke ciki. Duk da cewa munanan tasirinsu ya fi bayyana a fili, amma suna da wasu amfanoni da jama’a ke amfanuwa da su bayan lokaci mai tsawo da yin amansu. Wani darasin da ya kamata mu koya daga rayuwa tare da wadannan tsaunuka shi ne, duk wani abin da Allah ya kaddara samuwarsa a doron kasa ko a cikin teku, to don amfanin dan Adam ne. Ko da kuwa wannan abin na masa mummunar illa duk sadda ya bayyana, ko ya faru. Kuma Allah na iya amfani da shi wajen halaka duk wanda ya ga dama cikin bayinsa. Sannan samuwar wannan toka da ta bice sararin samaniya cikin watan Afrilu, wa’azi ne ga duniya baki daya, cewa idan za a yi hasara irin wannan cikin kasa da makonni biyu sanadiyyar aman da wani tsauni guda daya yayi a wata nahiya da ke can kurya, to me zai faru idan aka wayi gari dukkan tsaunuka masu aman wuta suka fara amai a lokaci guda? Don haka mu fadaka, mu kuma shiga taitayinmu.

AMSOSHIN WASIKUN MASU KARATU TA TES

Assalaamu Alaikum, Baban Sadik na kasance mai bibiyar makarantarka sama da shekara uku, kuma ina maka fatan alheri, Allah shi kara basira, amin. Don Allah ina da waya ne kirar Nokia 6260, ko tana da manhajar Opera? In har akwai, to yaya zan yi in rika shiga Intanet? Na gode. - Aliyu Danlabaran, Zariya: 08036158781

Malam Aliyu mun gode da addu’a, Allah kara basira da juriyar kasancewa tare da mu. Hakika galibin wayoyin salula na zamani suna da nau’in manhajar Opera Mini a tare dasu, ko kuma idan kaje gidan yanar sadarwan Opera, za ka samu nau’in da ya dace da wayarka, tabbas. To amma kafin nan, ina son sanar da kai cewa dukkan wayoyin salula suna da masarrafar lilo da tsallake-tsallake, watau “Browser”, wacce kuma kana iya mu’amala da ita wajen shiga Intanet. Amma idan kana son “Opera Mini” ce, to duk babu damuwa, kana iya saukar da ita zuwa wayarka, sannan ka loda mata. Don haka sai kaje inda ake mu’amala da Intanet a wayarka (watau “Browser”), ka shigar da wannan adireshin http://mini.opera.com/download shafin da ke dauke da manhajar zai budo, sai ka bi umarnin da ke shafin, ka saukar, tare da loda ta a wayarka. Allah sa a dace.

Assalaamu Alaikum, ina fatan kana cikin koshin lafiya tare da iyalanka. Na dade ina karatun shafinka a cikin Jaridar AMINIYA, kuma yana kara min fahimtar ayyuka na. Domin ina da shedar karatu ta NCE a fannin karantar da kimiyyar kere-kere, watau Technical Education, da kuma Difiloma a fannin kwamfuta. Ina jin dadin karatun shafinka. Allah ya kara mana fahimta, amin. - M. A. Faruk, Sokoto: 08036029098

To mun gode mu ma, kuma Allah kara dankon zumunci, da fahimta, da kuma juriya wajen kasancewa tare da mu. Tsarkakakkiya kuma cikakkiyar godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda duk wata ni’ima ta fahimta ko wayewa ko ci gaba, daga gareshi take. Mun gode.

Salamu Alaikum, ina amfani da wayar Nokia 6760 kuma ina da manhajar Opera mini a ciki. Ina son bude Imel ne don karban sako da aikawa, don Allah yaya zan yi? Na gode. - 08036017399

Kamar yadda muka sha bayani kwanakin da suka wuce, bude akwatin Imel ta wayar salula, in dai ba nau’ukan “Smartphones” bane, ba abu bane mai yiwuwa. Na farko dai asalin shafin da za a budo maka don ka yi rajista, ba ya samuwa sai ka aika da sakon “START”, zuwa wata lambar, wacce kuma bamu da kamfanin a nan nahiyar Afirka, ko ince Nijeriya. Wannan sakon da za ka aika ne zai sa a aiko maka da rariyar likau din da zaka bi, don samun shafin. Abu na biyu kuma shi ne, yin rajistan a waya na iya ci maka kudi da yawa. Duk da haka, idan kana amfani da wayar salula nau’in “SmartPhones” ne, (irin su “Blackberry” ko nau’ukan “E-Series” na kamfanin Nokia) to kana iya yin rajista ba matsala. Domin wadannan nau’ukan wayoyin salula suna mu’amala ne da Intanet tamkar kwamfuta cikakkiya. Da fatan an gamsu.

Da fatan Malam yana nan lafiya. Ni matsalata ita ce: a da ina karba ko aika sakon Imel ta hanyar Yahoo a wayata, amma tun shigowar wannan shekarar ko na shiga sai dai in ga tsoffin sakonnin da na aika ko karba. Shin a ina matsalar take ne: daga waya ta ne, ko daga Yahoo? - Sani Abubakar ‘Yankatsare, Jos: 08026023796

Malam Sani barka da war haka kuma ya aka ji da dawainiya da mu? Da fatan ana lafiya. Watau akwai abubuwa guda biyu ko uku. Da farko dai ya danganci tsarinka. Watakila tun da aka shiga wannan shekarar baka aika da sako ko kuma karbi wani sako daga wani ba. In kuwa haka ta kasance, to ai babu yadda za a yi ka samu wani sabon sako a jakar Imel dinka. Na biyu kuma, a iya cewa matsalar daga wayarka ce, amma hakan da kamar wuya, wai gurguwa da auren nesa. Domin in daga wayarka ne, ai baza ka iya ma shiga Imel din ba tun farko. In har kana ganin sakonnin da ka aika a baya, da wadanda aka aiko maka a baya, kuma babu wanda ya sanar da kai cewa ya aiko maka sako amma ka kasa gani, to ba zai zama matsalar daga gareta ba. Abu na uku shi ne a ce laifin kamfanin Yahoo. Hakan kuwa bazai yiwu ba, domin muddin kana iya shiga jakar Imel dinka daga wayarka, to ba yadda za a yi laifin yazo daga kamfanin Yahoo. Da fatan Malam ya gamsu.

No comments:

Post a Comment