Wednesday, November 2, 2011

Yadda Aka Kera Jirgin Ruwan "Titanic"

Shahara

Cikin shekarar 1997 ne kamfanin shirya fina-finai na 20th Century Fox da ke Amurka, ta hadin kai da wasu kamfanoni ‘yan uwansa suka fitar da wani fim mai suna “Titanic”, wanda ya samu shahara fiye da sauran fina-finan da aka fitar cikin shekarar. Wannan fim na “Titanic”, wanda shahararrun ‘yan wasa irinsu Leonardo DiCaprio, da Kate Winslet suka fito a ciki, yayi suna musamman a tsakanin matasa masu sha’awar jigon soyayya a cikin fina-finai. Wannan a bayyane yake. Ba ma a kasashen Turai da Amurka inda aka shirya fim fin kadai ba, hatta a nan gida Nijeriya wannan fim ya samu shahara sanadiyyar wannan jigo na soyayya da aka tsofa cikin fim din; inda jarumi Leonardo DiCaprio, da kuma jaruma Kate Winslet suka narke cikin kogin soyayya. Bayan haka, editan fim din shi ma wani sananne ne wajen sana’ar, watau David Cameron. A takaice dai, an sayar da kwafen fim din na gundarin kudi da kimarsa ta kai dalar Amurka sama da biliyan daya da dubu dari takwas. Kuma har zuwa yau, shi ne fim da aka kashe kudi wajen yinsa fiye da kowane fim a duniya.

Sai dai kuma, sabanin wannan jigo na soyayya da ke cikin wannan fim, wani abin da ya fi kama hankalin wasu cikin masu kallo – musamman masana Kimiyyar Kere-kere - shi ne tarihin da ke tattare da wannan jirgin da dukkan wannan lamari ya faru a cikinsa. Da farko dai, wannan lamari ya faru ne cikin shekarar 1912, a cikin wani tafkeken jirgin ruwa mai suna RMS Titanic da kamfanin White Star Line na kasar Ailand (Ireland) ya kera tsakanin shekarar 1909 zuwa 1912. Sanadiyyar girma da kayan alatun da ke cikin wannan jirgin ruwa, da kuma cewa babu wani jirgin ruwan fasinja mafi girma kamarsa a lokacin, ta sa aka shirya wannan shiri, daidai lokacin da wannan lamari na hadarin jirgin yake cika shekara 85 (1912 – 1997). A halin yanzu akwai buraguzan wannan jirgi na RMS Titanic a karkashin teku, kuma masana kan ilimin karkashin kasa da teku sun yi hasashen cewa nan da shekaru hamsin masu zuwa buraguzan za su dangana da gundarin kasan tekun baki daya, watau Ocean Floor. A yau in Allah Ya so za mu dubi yadda aka kera wannan jirgin ruwa, da wadanda suka zana shi, da kuma yadda aka yi wannan lamari ya faru.

Asali

Kamfanin kera jiragen ruwa mai suna White Star Line da Harland & Wolff da ke kasar Ailand ne suka kera wannan tafkeken jirgin ruwan fasinja mai suna RMS Titanic. Sun yi wannan aiki ne a filin kera jiragen ruwa da suke da shi a birnin Belfast na kasar Ailand din. Kuma hakan ya faro ne cikin shekarar 1909. Kafin wannan shekara, wannan kamfani na White Star Line ya fara kera wasu jirage masu girma wadanda ya sanya wa suna Olympic, sannan ya yi kudurin kera wasu manya na musamman, masu dauke da kayan alatu na kasaita, wadanda kuma babu kamarsu a wancan zamani – wajen girma, da kayan alatu, da fasahar kere-kere da kuma tsarin sadarwa. Asalin sunan da wannan kamfani yayi niyyar baiwa wannan jirgi na Titanic dai shi ne “Gigantic”; ma’anarsu daya ne da “Titanic”. Wannan jirgi na Titanic dai an kera shi ne da mafi kwarewar kwarewa na zamanin, ta amfani da kwararrun injiniyoyin lokacin, da kuma mafi kwarewar fasahar kere-kere na lokacin. Bayan dukkan wannan, shi ne jirgin da ya fi girma a lokacin; domin bayan mutum dubu uku da dari biyar da arba’in da bakwai (3,547) da yake iya dauka, har wa yau yana iya daukan jirgin sama nau’in Airbus 380 guda daya, da manyan motoci nau’in bas, da kuma kanana. A takaice dai, wannan jirgi na iya daukan kaya da mutanen da nauyinsu ya kai tan 46,328. Kamfanin J.P.Morgan da International Mercantile Marine Company ne suka dauki nauyin kera jirgin. Su suka bayar da kudade da kuma kayan aikin da ake bukata wajen kerawa.

Inijiniyoyi

Jirgin ruwan Titanic ya samu albarkar manya da kuma shahararrun injiniyoyin fasaha da kere-kere na wancan zamani. Akwai mutum uku da suka dauki nauyin zana tsari da kira da kuma yanayin rayuwar wannan jirgi. Na farko shi ne Lord Pirrie, wanda Darakta ne a kamfanin Harland Wolff da White Star Line. Sai wani kwararren mai zanen jiragen ruwa mai suna Architect Thomas Andrews, wanda shi ne manajan kere-kere na kamfanin, watau Construction Manager kenan. Sai na ukunsu, watau Alexander Carlisle, watau babban manajan ma’aikatan kera jirgin ne baki daya (Shipyard General Manager).

Tsarin Kira

Kamar yadda bayanai suka gabata a sama, asalin sunan da aka so baiwa wannan jirgin ruwa da farko dai shi ne “Gigantic”, to amma daga baya sai kamfanin White Star Line ya canza wannan suna saboda wasu dalilai. An fara kera jirgin ne a shekarar 1909. Cikin shekarar 1911 ne kuma aka gina mazauninsa, watau kwarangwal din da gaba dayan jikinsa ke zaune a kai. Wannan shi ake kira “Hull” a turancin kere-keren jirgin ruwa. Sauran gangar jikin jirgin, da kayan alatun makale-makalen cikinsa kuma an gama su ne a ranar 31 ga watan Maris na shekarar 1912. Wannan jirgi na Titanic yana da tsawon kamu 882 ne da inci 9, kuma zai iya daukan kayan da nauyinsa ya kai tan 46,328. Akwai injina manya wadanda ruwan zafi ke sarrafa su (watau Steam Engines) tafka-tafka guda hudu. Akwai bututun salansa masu fitar da hayakin injin guda uku, da kuma guda daya mai samar da iska ga jirgin. Dukkan wadannan bututu kowannensu ya kai tsawon kamu 62. A kasan jirgin kuma akwai wasu bututun amayar da ruwa guda takwas da aka tanade su, wadanda kuma aka kiyasta cewa suna iya amayar da ruwa daga cikin jirgin (idan matsala ta kama) sama da galan 420,000 cikin awa guda. Aikinsu shi ne amayar da dukkan wani ruwa da ya shigo cikin jirgin daga kasa.

Kyale-kyale da Kayan Sadarwa

Wannan jirgi na dauke da kayayyakin alatu fiye da tunanin mai karatu. Wadannan kayayyakin alatu kuwa, har a yanzu ana ji da su wajen kyau da tsada. Da farko dai akwai bangori guda uku da jirgin ke dauke da su. Akwai bangaren masu hannu da shuni, watau First Class kenan. Wannan bangare na dauke ne da wurin wanka na kasaita, watau Swimming Pool, da wurin motsa jiki, watau Gymnasium, da bangaren buga kwallon bango, watau Squash, da bangaren wanka na kasaita irin na mutanen kasar Turkiyya da ake ji da su a wancan lokaci, watau Turkish Bath, da bangaren wankan ruwan zafi na wutan lantarki, watau Electric Bath, da bangaren shagunan aski, watau Barber Shops, da bangaren bukkar shan shayi da sauran shaye-shaye kusa da gabar ruwa, watau Veranda Café, sai kuma dakin karatu ga duk mai bukata. Bayan haka, akwai bangaren da ke biye da na farko, watau Second Class kenan. Da kuma matsayin karshe ko na kasa, watau Third Class, kamar dai yadda muke da su a jiragen sama a yau.

Bayan wadannan bangarori, wannan tafkeken jirgin ruwa na RMS Titanic dai yana da babban janareto mai bayar da wutar lantarki guda daya, wanda ke amfani da tsarin bayar da wutar lantarki da ruwan zafi, watau Steam Engine. Mizaninsa ya kai wat dubu daya da dari biyar (1,500 watts). Sannan akwai injinan lifta guda uku masu daukan mutane daga dakunansu ko barandar da suke, zuwa hawa na sama ko can saman jirgin don su shakata. Wadannan injinan lifta duk suna amfani ne da wutar lantarki daga wannan janareto da bayaninsa ya gabata. Sannan akwai babbar masarrafar sadarwar rediyo mai amfani da tsarin sadarwa ta wayar-iska irin na wancan zamani, watau Marconi Radio. Wannan babbar cibiya ce da ke sadar da kira a tsakanin dukkan wadanda ke cikin jirgin, da masu tuka jirgin, da masu kula da jirgin, da kuma fasinjojin jirgin. Har wa yau, sadarwar bata takaitu garesu kadai ba, wannan cibiya ta rediyo na iya daukan murya zuwa sauran kasashen da ke makwabtaka da jirgin, ko wani jirgin da ke gab da su, ko kuma kasar da suka baro a baya. Cibiyar na amfani ne da fasahar sadar da bayanai na rediyo nau’in Spark-Gap Transmitter. An kuma gama kera wannan jirgi ne a ranar 31 ga watan Maris na shekarar 1912, kamar yadda bayanai suka gabata.

Gwaji

Bayan an gama kera wannan jirgi, kamfanin White Star Line ya yi kokarin gwada tafiya da wannan jirgi a cikin teku don ganin yadda abubuwa za su kasance, kafin a sanya ranar wannan bulaguro mai dimbin tarihi da ba a ga karshenta ba. Wannan gwaji kuwa an yi shi ne kwananki goma kafin tafiyar, watau ranar 1 ga watan Afrailun shekarar 1912. Ba a dauki fasinja ko daya a ciki ba, daga masu lura da jirgin sai ma’aikatanta kawai. Akwai ma’aikata guda 78 da aka dauka, tsakanin masu kara wa injin makamashin kol (Stokers), da masu sanya man giris (Greasers), da kuma ‘yan kwana-kwana, watau Firefighters. Bayan wadannan ma’aikata, akwai matuka jirgi guda 41 da suka shigo, sannan da wasu mutane biyu wadanda suke lura da cibiyar sadarwar rediyo, watau Merconi Radio. Wadannan mutane dai su ne Jack Phillips, da kuma Harold Bride. Bayan an yi gwaji babu wata matsala, daga nan aka fara shirye-shiryen tafiya, wacce a karshe aka kasa isa garin da za a je.

Tafiyar Farko, Kuma ta Karshe

Ranar 10 ga watan Afrailu ne dai jirgin RMS Titanic ya tashi daga babbar tashar jirgin ruwan birnin Southampton na kasar Ingila, zuwa birnin New York da ke kasar Amurka. Da ya dauko hanya sai yayi zango a tashar jirgin ruwa na Cherbourg da ke kasar Faransa, inda ya kara daukan wasu fasinjoji. Bayan wannan tasha, ya sake dakatawa a tashar Queens Town ta kasar Ailand, nan ma ya kara wasu fasinjojin. Duk da cewa ba kai tsaye ya dauki mutane a wannan tasha ba, saboda nauyin jirgin da girmansa sun sha karfin gabar tekun. Don haka da yazo daidai tashar, sai aka saukar da kananan kwale-kwale, aka kwaso fasinjojin da suke son tafiya. Daga wannan tasha ta Queens Town, jirgin bai kara dakatawa a kowace tasha ba. Sai tafiya babu kama hannun yaro. A wannan lokaci jirgin ya dauki mutane 2,227 ne; tsakanin matuka jirgin, da ma’aikata, da injiniyoyi da kuma fasinjoji. Shugaban matuka jirgin gaba daya shi ne Captain Edward J. Smith. Bayan haka, akwai babban daraktan kamfanin White Star Line a cikin tafiyar, watau J. Bruce Ismay, sai kuma wanda ya shugabanci kera jirgin baki daya, watau Thomas Andrews. Daga cikin fasinjojin da ke cikin wannan jirgi, akwai ‘yan kasuwa, da shahararrun ma’aikatan banki, da kuma kasaitattun masu kudin kasar Ingila da Amurka da kasar Ailand. Kudin fasinjan da ke matakin farko, watau First Class, shi ne dala 4,350 ($4,350), wanda aka kiyasta kimarsa da kimar dala a shekarar 2008 ya kai dala 95,860 ($95,860). Idan muka juya kimar wannan kudi a nairan Nijeriya a yau, ya kai naira miliyan goma sha hudu da dubu dari uku da saba’in da tara (=N=14,379,000).

Bayan ya kwashe kwanaki hudu yana tafiya dare da rana safe da yamma, a daren kwana na biyar ne Captain Edwards ya fara samun sakonni daga rediyo cewa akwai curin tsaunin kankara a gabansu, watau Iceberg. Amma sai bai damu ba. Ana cikin tafiya, sai ma’aikatan da aka wakilta su rika lura da tafarkin da jirgin ke bi, watau Lookouts, suka hango wannan tarin kankara a gabansu. Nan take suka sanar da masu lura da cibiyar sadarwa, inda su kuma suka fara watsa sakonni kan wannan lamari. Captain Edwards na jin haka, sai ya bayar da umarnin cewa a rage tafiya, sannan a juya akala zuwa bangaren hagu. To amma wannan bayani bai zo da wuri ba. Kafin su gama juya akala, nan take wannan tsaunin kankara ya gurji mazaunin jirgin daga kasa, wata Hull kenan. Hakan ne ya sabular da karafan da ke rike da mazunin jikin jirgin, inda ruwa ya fara shiga nan take babu kakkautawa. Lokacin da Captain Edwards ya ga haka, sai ya sa aka fara rufe farfajiyar kasan jirgin, watau wurin da aka tanada don zuba kayayyaki kenan. Amma saboda tasiri da karfin wannan ruwa da ya fara shigowa, kafin a rufe sauran, guda hudu daga cikinsu sun fara cikewa da ruwa. Wadancan bututu guda takwas da aka tanada don amayar da ruwa sai suka fara aikinsu, inda suka ta amayar da ruwan zuwa waje, ta baya. Sai dai kuma kash, saboda girman jirgin, da kuma yawan ruwan da ke tudadowa daga gaba inda aka samu huji, wadannan bututun amayar da ruwa sun kasa amayar da ruwan cikin lokaci guda. Nan take kasan jirgi ya fara cikewa, sai cikin dakunan mutane, sai hawa na sama. Ana cikin haka sai jirgi ya fara nutsewa ta baya, saboda tasirin ruwan da ke makare a kasansa. Wannan tasa sai kan jirgin ya daga sama, inda a karshe ya tsage ko ya karye a tsakiya; bangaren bayan yayi kasa cikin teku, kan kuma ya zauna a sama.

Kafin lamarin ya kazamce haka, nan take sun fara aikawa da sakonnin neman agaji. Ana cikin haka sai ga wasu jirage suka kawo dauki. To amma saboda kananan kwale-kwalen ceto (watau Lifeboats) da jirgin ya ke dauke dasu basu kai yawan mutanen da ke cikin jirgin ba, haka wasu suka nutse cikin ruwa, suka mace. Wasu kuma aka ceto su da kyar. Bayan an gama tsamo wadanda suka mutu da masu rai, a karshe dai mutun 1,517 ne suka mutu. Hakan ya faru ne a daren 15 ga watan Afrailu, 1912. Wannan shi ne mafi munin hadarin jirgin ruwa da aka yi a shekarar, kuma yana cikin hadarurrukan da aka yi da suka haddasa sauye-sauye a dokokin tafiyar da jiragen ruwa na duniya, watau International Maritime Laws.

Dalilai

A karshe dai, hukumomi sun sa an gunadar da bincike kan dalilan da suka haddasa wannan hadari. Da farko dai, sabanin yadda wasu ke riyawa cewa wai kamfanin da ya kera wannan jirgi yayi alfahari cewa babu abin da zai iya tarwatsawa ko lahanta wannan jirgi saboda kwarewar da aka yi amfani da ita wajen ginawa, wannan karya ne. Kawai surutai ne na mutane, da kuma hasashe irin na kwakwalwarsu. Daga cikin dalilan da aka ta cewa sun haddasa wannan hadari dai akwai yawan gudu. Wannan shi ne sakamakon da gungun masu bincike da kasar Ingila ta kafa ya tabbatar. Cewa jirgin na gudu ne fiye da kima, don haka ya samu matsala wajen juyawa a lokacin da aka hango wancan tsauni na kankara. Wasu masu binciken kuma suka ce ruhin jirgin ne ke da matsala, watau Rudder kenan a turance. Shi wannan ruhi dai shi ne mai nuna wa jirgin ruwa inda za ta dosa; kamar dai kwakwalwarta kenan. Don haka a lokacin da aka hango wannan tsauni na kankara, jirgin ya kasa juyawa ne yadda ya kamata saboda ba a kera wannan ruhi da irin ka’idojin da suka kamata ba a yau. Wasu kuma a karshe suka ce babban dalili shi ne karafan da aka yi amfani dasu wajen gina mazaunin jirgin, watau Hull kenan, ba su da kauri sosai. In kuwa ba haka ba, ba abin da zai sa wannan tsauni na kanka ya iya bangale karafan da ke jikinsa. Sabanin yadda aka zata da farko cewa wannan tsaunin kankara ya huda jikin jirgin ne, masu wannan ra’ayi sun gudanar da bincike na musamman, inda a karshe suka nuna cewa kwabe karafunan da ke jikin mazaunin jirgin ne yayi, daga nan kuma ruwa ya samu hanyar shiga.

Ko ma dai mene ne, wanann jirgi na RMS Titanic ya kwanta dama, duk da kwarewa, da kayan alatu, da kuma girman da yake da shi. Shi ne jirgin ruwa mafi girma da aka kera shi, mai tsad

Ambaliyan Danyen Mai a Cikin Teku

Mabudin Kunnuwa

Na tabbata masu karatu sun ji ko ma sun karanto daga kafafen yada labaran gida da na waje kan batun ambaliyan danyen mai da ya faru a tekun Meziko na kasar Amurka. Kamar yadda muka sha jin labarai, wannan ambaliya ko hadari ya fara ne tun cikin watan Afrailu, amma ba a samu dama da ikon tsayar da shi ba sai cikin watan Agusta. Wannan ambaliya na danyen mai ya haddasa barna mai yawa, da hasarar rayukar dan Adam da na dabbobi tudu da na teku, da kuma hasarar dukiya da na gurbatar yanayi wanda mummunan tasirinsa na iya daukan tsawon shekaru ana fama da shi.

Wasu cikin masu karatu sun nuna sha’awar jin kwakwaf kan yadda wannan lamari ya faru, da tasirinsa ga muhalli, da kuma cewa ko za a iya sarrafa gurbataccen man da aka yade daga saman tekun ko a a? Kafin wannan bukata ta masu karatu, shafin Kimiyya da Kere-kere ya yanke shawarar kawo bayanai masu nasaba da hakan tun sa’adda da wannan matsala ta fara aukuwa. To amma ganin cewa matsalar ta ci gaba babu kakkautawa, sai na dakata don ganin inda abin zai kai. Domin wannan ne zai bamu damar kawo bayanai ba ma kan wannan ambaliya na tekun Meziko ba kadai, a a, har da tarihin asali da kuma sau nawa aka samun irin ambaliya na danyen mai a cikin teku? Wannan, da ma sauran bayanai ne na debo mana daga rumbun bayanai na duniya, don mu amfana, tare da kara gejin ilminmu kan ire-iren wadannan ambaliyoyi da ke faruwa lokaci-lokaci a tekunan duniya. Sai a biyo mu sannu a hankali.

Tarihin Ambaliyan Danyen Mai a Duniya

Ambaliyan danyen mai a cikin teku, ko “Marine Oil Spill” a harshen Turanci, ya fara aukuwa ne sama da shekaru hamsin a tarihin duniya. Duk da cewa ambaliyan danyen mai a jumlace ya shafi cikin teku da kan tudu, za mu mayar da hankalinmu ne kan tarihin ambaliyansa a cikin teku kadai, don shi ya fi hadari da wuyan sha’ani, kuma shi ne wanda ya fi daukan hankali a duniya.

A tarihin duniya an samu aukuwar ambaliyar danyen mai a saman teku sau goma sha biyar, tare da hasarar dukiya mai dimbin yawa ga kasa ko kamfanin da abin ya shafa; bayan hasarar rayukan dan Adam da na dabbobin da ke karkashin da harabar tekun. Cikin wadannan ambaliya guda goma shabiyar, akwai biyar daga cikinsu wadanda suka shahara sanadiyyar yanayin aukuwarsu. Na farko shi ne ambaliyan daya auku a Tekun Meziko (watau The Gulf of Mexico) da ke Kudancin Amurka, karo na farko. Wannan ambaliya ya auku ne a ranar 3 ga watan Junin shekarar 1979, inda aka ya tuttudar da danyen mai (watau Crude Oil) kimanin Tan 480,000 (480,000 metric tonnes). Cikin jerin ambaliyan danyen mai masu hadari da aka yi a duniya, wannan shi ne na farko da ya dauki hankalin duniya, kamar yadda aukuwansa na biyu cikin watannin Afrailu zuwa Agusta ya yi a wannan shekara. Ambaliya na biyu da ya fi kowannen hadari shi ne wanda ya auku a Tekun Tsibirin Trinidad & Tobago, a ranar 19 ga watan Yulin shekarar 1979; wata guda kenan bayan aukuwar na Tekun Meziko, kamar yadda bayanai suka gabata a sama. Wannan ambaliya kuma ya tuttudar da danyen mai kimanin Tan 287,000 (287,000 metric tonnes) zuwa cikin tekun Atilantika da ke makwabtaka da tsibirin.

Sai karo na uku da ya fi kowanne shahara sanadiyyar dimbin hasarar da aka tafka. Wannan ambaliya ya auku ne a Tekun Fasha (Persian Gulf), sanadiyyar ambaliyar danyen mai da aka samu daga rijiyoyin mai na kasar Kuwaiti. Hakan ya faru ne a ranar 23 ga Janairun shekarar 1991, inda rijiyoyin man suka tuttudar da danyen mai da kimarsa ta kai Tan 1,500,000 (1,500,000 metric tonnes) zuwa cikin tekun. Dangane da yawan danyen man da aka rasa, wannan ambaliya ne na daya a duniya. Domin har yanzu ba a samu ambaliyan da ya haifar da hasarar danyen mai mai dimbin yawa irin wannan ba a duniya. Sai kuma ambaliya na gaba, wanda ya auku a tekun da ke makwabtaka da kasar Uzbekistan; can nahiyar Asiya ta Gabas kenan. Shi kuma ya auku ne a ranar 2 ga watan Maris din shekarar 1992, watau shekara guda kenan da aukuwar na kasar Kuwaiti. Kamar wadanda suka gabace shi, shi ma ya haifar da hasarar danyen mai zuwa cikin teku da muhallinsa wanda kimarsa ta kai Tan 285,000 (285,000 metric tonnes). Sai ambaliya na karshe da ya auku baya-bayan nan, watau daga watan Afrailu har zuwa watan Agustan wannan shekara. Kamar yadda masu karatu suka karanta ko ji a kafofin watsa labarai, wannan lamari ya auku ne a cikin Tekun Meziko (The Gulf of Mexico) da ke Kudancin Amurka, kuma a Tarihin kasar baki daya, shi ne ambaliyan da ya fi kowanne wajen hasara.

Wannan ambaliya ya samo asali ne sanadiyyar rubewar da karafunan hako danyen mai na kamfanin British Petroleum (BP) suka yi. Wadannan karafunan hako danyen, watau Oil Drilling Rigs, suna can cikin rijiyoyin hako man ne da ke karkashin teku, wanda aka kiyasta nisan zurfinsa cewa ya kai kilomita 150. Cikin watan Maris ne kamfanin ya fara da lura da wani irin hayaki mai dauke da sinadaran Methane da ke fitowa ta hancin wadannan bututun hako mai. To amma bai dauki wani matakin gaggawa ba sai ji yayi bututun sun fashe, kuma nan take wuta ta kama ci ganga-ganga. Duk da cewa ‘yan kwana-kwana sun kawo dauki nan take, inda aka yi ta kokarin kashe wutan da tuni ya kama babbar injin da ke rike kuma take sarrafa wadannan bututun, ta yi ta ci da wuta ita ma. Da kyar dai aka kashe wannan gagarumar gobara da ta tashi. Kuma duk da cewa an samu kwashe ma’aikatan kamfanin da ke sarrafa wannan inji, amma akwai mutane goma sha bakwai da aka kasa gano inda suke. Ga dukkan alamu dai gobarar ta afka da su, ko kuma a kalla ta tilasta musu fadawa cikin teku ba tare da shiri ba.

Gama kashe wutan ke da wuya sai danyen mai ya fara tudadowa daga rijiyoyin mai da ke can karkashin teku, sanadiyyar fashewar bututun da ke zuko mai daga cikinsu. Wannan ta sa kallo ya koma kasa, bayan kashe gobarar da ta taso. Daga nan danyen mai ya ci gaba da tudadowa a kullum, inda a karshe ya tudado da danyen mai har Tan 574,000 (574,000 metric tonnes) zuwa cikin tekun. Kamfanin British Petroleum ya kashe sama da Dala Biliyan Hudu wajen yade wannan danye ko gurbataccen mai da ya yadu a saman teku, bayan lokaci da kuma danyen man da ya bata ko ya yi hasararsa.

Illolin Ambaliyan Danyen Mai

Wannan ambaliya da ke faruwa a lokuta daban-daban a tekunan duniya na da mummunar tasiri ga rayuwar jama’a da halittun da ke rayuwa cikin tekun, da kuma muhalli gaba daya. Da farko dai yana kyau mai karatu ya san cewa da mai da ruwa ba su haduwa. Duk lokacin da wani ya shiga wani, to dole ne a gane, domin ba su taba hadewa waje daya. Wannan shi ne abin da binciken Kimiyyan sinadarai ya tabbatar. A duk lokacin da aka samu cakuwarsu da juna, to mai ne ke kasancewa a saman ruwa. Bayan haka, tasirin mai a saman teku yana da gamewa sosai, saboda tasirin sinadaran da yake dauke da su.

Idan danyen mai ya game cikin ruwa, yakan haifar da maski – abin da a harshen Kimiyya ake kira “Mousse”. Wannan maski zai yi ta yawo ne a saman ruwa, tare da lakewa a jikin duk abin da ya ci karo da shi. Saboda tasirin gamewa da mai yake dauke das hi, an kiyasta cewa idan aka zuwa mai galan guda a cikin teku, yana iya game fadin eka uku zuwa biyar na saman tekun. Sannan idan ya kama shawagi, zai game jiki ko gashin dukkan dabbobin da yayi karo dasu ne, tare da lakewa a jiki ko fikafikansu. Wannan ke kara musu nauyi, har a karshe su kasa tashi, su yi ta nitsewa cikin tekun, har mutuwa ta cin musu. Bayan haka, idan kifaye suka hangi wannan maski na yawo a saman teku, nan take suna iya cafke shi har su hadiye, suna zaton abin ci ne. Idan kuwa suka hadiye shi, to nan take zai fara musu illa, ta hanyar haifar da wasu nau’ukan guba a cikinsu. Idan kuma ya gangara zuwa can karkashin tekun (watau Ocean Floor), sai ya bata dukkan abincin da suka tara.

Daga cikin illolin wannan danyen mai a saman teku har wa yau, akwai toshe hanyoyin shakar iska da halittun cikin ruwa ke amfani da su wajen numfasawa. Idan kuma maskin ya lake musu a jiki, yakan kashe musu garkuwan jikin (watau Immune System) da ke basu kariya daga cututtukan muhallin da suke rayuwa cikinsa. Sannan yana hargitsa musu tsarin hayayyafa, tare da gurbata dukkan kwayayen da suke jiran kyankyasa. A wasu lokuta a kan samu iska mai karfi ko kuma taguwar ruwa da ke hankada wannan maski na mai zuwa gabar teku, inda yake lakewa a jikin dukkan ciyayin da ke gabar, tare da gurbata abincin dabbobin wannan bigire. Idan kuma a gefen tsibiri ne ambaliyan ya auku, wannan maskin mai na iya daskarewa a karkashin tsibirin na lokaci mai tsawo, kuma dukkan kifayen da ke neman abinci a wannan bigire suna iya kamuwa da cuta sanadiyya cakuduwarsa da dukkan nau’ukan abincinsu da ke wajen. Idan kuwa haka ta faru, to, akwai jin tsoron wadannan kifaye suna iya harban dukkan sauran halittun da ke rayuwa tare da su cikin tekun, musamman ma manyan kifaye da zasu ci wadanda suka harbu, ko kuma manyan halittu irin su kada ko tsuntsayen da rayuwa a gaban tsibirin, masu cin kifaye. Wannan tsari na yaduwar cuta daga wata halitta zuwa wata halittar, shi ake kira “Cycle of Poisoning” a harshen Kimiyya.

A karshe, mummunan tasirin wannan maski da ke kwanciya a saman ruwa bai tsaya kan halaka dukkan dabbobin da ke rayuwa cikin tekun kadai ba, hatta dan Adam yana iya kamuwa da wasu cututtuka. Misali, bincike ya nuna cewa mata masu ciki na iya kamuwa da cuta idan suka shaki doyin wannan maski. Haka kuma masu ciwon da ke da alaka da numfashi su ma suna kamuwa da karuwar cututtuka. A karshe, bincike ya sake tabbatar da cewa sinadaran da ke cikin wannan maski da suka hadu da ruwa, suna iya hadda cutar kansa (Cancer) ga dan Adam muddin ya shake su.

Ina Amfanin Gurbataccen Man?

Da ma zasu so sanin shin, wannan gurbataccen mai da ake yadewa daga saman teku – ganin cewa asalinsa danyen mai ne mai dauke abubuwa da dama – ko za a iya sarrafa shi don yin abu ko tace shi don amfani da sinadaran da ke cikinsa kuwa? Wannan tambaya ce Malam Kimiyyar sinadara suka tabbatar da rashin yiwuwan hakan. Sun nuna cewa tunda har man ya riga ya cakudu da ruwa, to ya riga ya lalace kenan. Kuma ma bayan nan, sau tari ba a rasa tarkacen cikin teku da aka yado su tare da wannan gurbataccen mai, wanda kuma asalinsu ko dai ciyayi ne, ko ruwa, ko kuma tabo da kasar lakar da aka debo su tare. Bayan haka kuma, akwai sinadaran gishin ruwan teku da ke cakuduwa da man, wanda kumake rage masa karfi da karsashinsa. Wannan cakudadden danyen mai dauke da wasu ababe daban, shi ake kira “Chocolate Mousse”. In kuwa haka ne, ashe babu yadda za a yi a tace su. Domin dai mai ba zai taba yin aikinsa ba idan akwai ruwa a cikinsa, ko tabo, ko kuma duk wani abin da ba daga asali daya suka fito ba.

Wannan tasa a kasashen Turai misali, bayan an gama redo wannan maski na danyen mai daga saman teku, sai a tara shi waje daya, sannan a rika cike hanyoyi da su, ko kuma wasu bangarorin kasa da suka rifta. Hakan na da tasiri sosai wajen tabbatar da cikon da aka yi, domin wannan cakudadden danyen mai da ke dauke da ruwa da sauran karikitai, ba ya afkawa a duk inda aka yi ciko da shi. Domin haduwa yake yi da wadannan karikitai, ya sandare a karkashin kasa. Ya koma inda ya fito kenan.

Kammalawa

Kamar yadda bayanai suka gabata, ambaliyan danyen mai wani abu ne da wannan duniya ta fara jarabtuwa da shi tun ba yau ba, kuma aukuwansa na yin mummunan tasiri kan muhalli baki daya, da masu rayuwa a cikinsa. Duk da cewa ci gaban kere-kere a duniya ya samar da wasu sinadai da kuma hanyoyin narkar da wannan gurbataccen mai a saman teku, har yanzu ba a raja’a wajen amfani da wannan sinadari na musamman ba, domin bincike ya nuna cewa yana iya cutar da ma’aikatan da ke amfani da shi. Kuma cikin ambaliya goma shabiyar da aka taba yi a tekunan duniya, babu wanda ya haifar da hasara mai dimbin yawa irin na tekun Meziko da ya auku a watannin baya. Saboda an rasa rayukan mutane, da dabbobi, da hasarar danyen mai, da kudi, da kuma lokacin aiki mai dimbin yawa, irin wanda ba a taba yi a baya ba.

Kasar Sin ta Kera Makamin Kariya daga Teku

Ranar 5 ga watan Maris da ya gabata ne kasar Sin ta cilla gungun tauraron dan Adam mai suna “Yaogan-IX Naval Ocean Surveillance System (NOSS)” zuwa sararin samaniya, wanda kuma shi ne ayarin taurarin dan Adam na musamman kashi na uku da kasar ta tanada don taimaka wa sabon makami mai linzami na kariyar hari daga teku da ma sararin samaniya (Anti Ship Ballistic Missile – ASBM) da ta kera don kare kasarta. Wannan sabon makami mai linzami da ta sanya wa suna “DengFeng 21D”, ko kuma “DF-21” a gajarce, makami ne mai linzami (missile) mai cin matsaikacin zango, kuma mai karfin darkake duk abin da yake hari a ko ina ne yake cikin kadadar tazararsa. Makamin DengFeng 21D, wanda a Hausance yake nufin “Iskar Gabas”, shi ne irinsa na farko a duniya baki daya. Makamin, wanda aka yi masa gwajin farko a shekarar 1985-6, an gama kera shi ne a shekarar 1991. Gwajin baya-bayan nan da aka yi na wannan makami ya faru ne cikin shekarar 2005. Kuma idan aka gama tsara makamin, an kiyasta cewa zai iya daukan kawunan nukiliya guda 60 zuwa 80 a cikin kowane makami mai linzami guda daya. A halin yanzu ana gab da gama kintsa shi don fara aiki.

Asali

Cikin shekarar 1960 ne dai kasar Sin ta fara tunanin kirkiro wani makami da zai bata kariya daga irin barazanar da makamai masu linzami da kasar Amurka ta tanada a farfajiyarta cikin teku, suke mata. Hukumar da gwamnatin kasar ta dora wa nauyin kera wannan makami mai linzami dai ita ce “China Changfeng Mechanics Electronics Technology Academy”, watau Cibiyar Kimiyyar Kere-kere ta kasar kenan. Cibiyar ta fara ne da kera makami mai linzami nau’in DF-21 mai cin gajeren zango, mai dauke da kawunan nukiliya (Nuclear War Head) guda 500 (watau 500Kt), kuma zai iya tafiyar tazarar kilomita 1,700 (1,700km) daga inda aka harba shi. Sai dai kuma, a lokacin ba a yi amfani da shi ba.

A shekarar 1996 sai wannan Cibiya ta Kimiyya ta kara masa tagomashi, inda ta samar da nau’in DF-21A, mai cin tazarar kilomita 2,700 (2,700km), amma kawunan nukiliya guda 90 kadai yake iya daukawa a cikin kwansonsa. Ana shiga shekarar 2006 sai wannan hukuma, a bisa umarni da tsarin hukumar kasar, ta kara ingantawa tare da kayatar da wannan nau’in makami mai linzami zuwa nau’in DF-21C, amma mai cin gajeren zango, kuma duk tazararsa bata wuce kilomita 1,700 ba. Sai dai kuma, Cibiyar ta shirya shi ne ta yadda zai rika amfani da fasahar GPS (Global Positioning System) wajen ganowa tare da kai hari kan abokan gaba a daidai tazarar da aka haddade masa. Bayan haka, wannan nau’in makami na DF-21C na iya riskar duk abin da ya hango kuma yake hari, kai tsaye ba tare da ya kuskure shi ba.

Bayan ‘yan shekaru sai Cibiyar kuma ta kara wa wannan makami tagomashi har wa yau, don samun inganci. Bayan dacewa wajen riskar duk abin da ya hango kuma yake hari, ana iya harba shi ne a kan na’urar harba makami mai linzami na musamman da aka tanada masa, mai tafiya – watau “Mobile Antiship Ballistic Missile Launcher” – maimakon amfani da kananan jiragen sama kamar yadda sauran makamai masu linzami ke yi kafin riskar abin da suke hari. Kari kan haka, wannan ingantaccen nau’i da Cibiyar ta canza wa suna daga DF-21C zuwa DF-21D na iya tarwatsa jiragen saman yaki da suka taso daga teku, ko sararin samaniya, ko kuma darkake jiragen ruwan yaki na musamman masu buya a karkashin teku – watau “Submarine War Ships”. Bayan haka, wannan makami mai linzami da kasar ta kera, duk da cewa mai cin matsakaicin zango ne, yana iya kai hari daga nahiyar Asiya har zuwa nahiyoyin da ke makwabtaka da ita.

Bayan dukkan wannan kudura da karfi, wannan makami mai linzami na DF-21D zai rika karban umarnin kai hari ne daga tashar da aka cilla shi, ba wai daga wani tauraron dan Adam da ke shawagi a sararin samaniya ba, sabanin sauran makamai masu linzami irin na da. Wannan zai ba shi damar tashi cikin tsari, da tafiya cikin natsuwa, da kai hari a daidai inda ake son ya kai, sannan ya kamo hanyar dawowarsa tiryan-tiryan zuwa tasharsa ba tare da wata na’ura ta kawo masa cikas ba wajen karban umarnin da ake bashi daga tashar da ya baro. Kari a kan wannan, akwai gungun taurarin dan Adam masu taimaka masa wajen hango abokan gaba a ko ina suke, amma ba su suke sarrafa tafiya ko dawowarsa tasharsa ba. Wannan irin kudura da makamin DF-21D ya samu shi ya kebance shi daga sauran makamai masu linzami masu amfani da kawunan nukiliya wajen kai hari a duniya. Duk abin da ya dosa, sai ya darkake shi, kuma duk abin da aka harbo zuwa bigirensa, to yana iya mukabalantarsa, ya kuma tarwatsa shi nan take. Wannan ne ma yasa galibin masana ke masa lakabi da “makamin kariya daga teku”, watau “Anti Ship Ballistic Missile” ko “ASBM” a gajarce.

Kafin wannan makami ya fara aikinsa, akwai ayarin na’urorin tauraron dan Adam da yake bukata masu taimaka masa wajen aiwatar da aikinsa ba tare da wata matsala ba. Kuma tuni kasar Sin ta gama cilla su zuwa sararin samaniya don su kama wajen zamansu. Ayarin farko an cilla su ne ranar 9 ga watan Disamba, cikin shekarar 2009. Kwanaki biyar bayan wannan, sai aka aika ayari na biyu: ranar 14 ga watan Disamba din shekarar dai har wa yau. Ayari na karshe kuma an aika su ne ranar 5 ga watan Maris na wannan shekara. Ayarin farko dai su ne: “Yaogan-VII Electro-optical Satellite”, ayari na biyu kuma kasar ta kira su “Yaogan-VIII Synthetic Aperture Radar”, sai kuma ayari na karshe, wanda ta kira “Yaogan-IX Naval Ocean Surveillance System (NOSS) Constellation.” Ana sa ran gabatar da gwajin wannan makami a karo na karshe a karshen wannan shekara. Dukkan sauran gwaje-gwajen da aka gudanar a baya an samu cin nasara kansu; babu matsala.

Tasiri a Siyasar Duniya

A bayyane yake cewa mallakar wannan makami ga kasar Sin zai canza tsarin siyasar duniya da na zaman lafiya da kuma kawancen da ke tsakanin kasashen Asiya da kasar Amurka; musamman ma kasashen Jafan, da Koriya ta Kudu, da Filifins, da kuma kasar Taiwan. Kusan kashi sittin cikin dari na labarun da ke fitowa kan kera wannan makami da kasar Sin ke yi, na samuwa ne daga Hukumar Sojin Ruwa na Kasar Amurka (US Naval Force); abin da ke nuna cewa lallai hakan yana tasiri wajen haddasa fargaba ga sojin kasar.

Masu lura da harkokin tsaro a duniya sun tabbatar da cewa muddin kasar Sin ta gama kera wannan makami mai linzami na DF-21D, to babu abin da ya rage wa kasar Amurka illa ta kwashe komatsenta daga nahiyar Asiya ta koma wata nahiyar daban, ko kuma, a kalla, dole ne ta jirga baya sosai da tafkeken jirgin ruwan yakinta mai suna USS George Washington da ke dauke da jiragen yaki nau’in F18 sama da dubu daya da casa’in da biyu a gab da gabar tekun kasar Jafan. Zaman kasar Amurka a tekun Pacific dai tana yinsa ne da biyu; na farko shi ne, akwai yarjejeniyar tsaro (Defense Pact) tsakaninta da wasu kananan kasashe, irinsu Jafan da Koriya ta Kudu misali. Dalili na biyu kuma shi ne lura da shirye-shiryen tsaro da kasar Sin da Koriya ta Arewa ke yi. To amma samuwar wannan sabon makami mai linzami na iya yi wa shirye-shiryenta targade, domin a halin yanzu dai kasar Amurka ba ta da wani kudurar da za ta iya kare jiragenta daga hadarin da ke dauke cikin wannan makami, balle kare kasashen da ke biyanta sanadiyyar kariyar da take basu a nahiyar.

Masana harkokin tsaro a nahiyar Asiya sun tabbatar da cewa kasar Sin ta fara wannan yunkuri ne don ganin ta kawar da zama da kuma barazanar da kasar Amurka ke mata a farfajiyarta. Sannan kuma akwai tunanin cewa tana son jawo ra’ayin wasu daga cikin kasashen da ke makwabtaka da ita, don wasu manufofi na siyasa. A karshe kuma, akwai tunanin cewa kasar Sin na kokarin hakimtar da kanta ne a nahiyar gaba daya, kamar yadda kasar Amurka ke tutiyar yi a duniya. A karshe suka ce, hasashen da kasar Sin ke yi na ganin hakan ta hanyoyi biyu, a fili suke. Da farko dai kasar Sin ta janye kasuwar duniya gaba daya, ta inda ta zama gagarabadau wajen habakar tattalin arzikin kasa. Abu na biyu kuma shi ne wannan kokari da take yi wajen samun kebantacciyar kudura ta hanyar tsaro a duniya gaba daya. Wannan, a cewar kwararru, shi zai bata ‘yancin tattalin arzikin kasa da na siyasa, a siyasar duniya.

A karshe, wani hasashe da wasu kwararru suka kara yi shi ne, da wannan makami mai linzami na DF-21D, kasar Sin na iya darkake wannan tafkeken jirgin ruwan yaki na kasar Amurka da ke tekun Pacific cikin kiftawa da bisimilla, saboda tsananin sauri da tasirinsa, wanda kuma kafin kasar Amurka ta iya kawo harin daukan fansa, dole tana bukatar kusanci da kasar Sin matuka; hakan kuma ba zai iya kara bata damar hakan ba; domin iya kusancinta da kasar, iya hadarin da za ta kara shiga. Domin kuwa, a cewar wannan hasashe, wannan makami mai linzami na DF-21D na iya jirkice abokan gaba ta hanyoyi uku; a karon farko zai haddasa wuta da hayaki mai tarin yawa, mai iya hana dukkan wani jirgin saman yaki tashi, balle yayi wani tasiri. Na biyu kuma, zai salwantar musu da injinansu gaba daya, tare da darkake su ta sama. A karo na uku kuma, idan jiragen yakin suna kan babban jirgin ruwan yaki mai daukan kananan jirage ne (watau Supercarrier), wannan makami na DF-21D na iya dulmuyar da jirgin ruwan zuwa karkashin teku gaba daya ma a huta.

Saturday, December 4, 2010

Tsaunuka Masu Aman Wuta da Tasirinsu Ga Muhalli (4)

Shi dai wannan toka da zarar yayi sama, ba ya narkewa. Sabanin irin tokan da muka saba gani da mu’amala da shi. Shawagi yake yi a sama. Don yana dauke ne da sinadarai masu wahalar sha’ani. Da zarar ya hadu da ruwa ko danshi, yakan zubo kasa ne, ya daskare, ya zama gundarin dutse shi ma, amma nau’in Tuff. Yana dauke ne da hayaki mai dauke da sinadarai masu cutarwa. A shekarar 1783, lokacin da tsaunin Leki da ke Tsibirin Iceland yayi amai, wannan tokan kunun dutse ya yi sanadiyyar mutuwar kashi daya bisa biyar na mutanen kasar nan take. Da wannan toka ya garzaya Yammacin Turai, yayi ajalin mutane sama da dubu ashirin da uku a kasar Ingila. Shakar wannan toka dai lalura ce babba, musamman ga masu cutar da ke da alaka da numfashi, irin Asma. Yana sanya kaikayin idanu. Idan kuma ka shake shi lokacin da yake tattare da danshi, to yana tara wasu sinadarai masu dauke da narkakken sinadarin siminti a cikin huhunka. Idan kuwa ya zubo kasa, bayan ya gama shawagi a sama, yana iya rusa rufin gidajen jama’a; iya gwargwadon yawansa a saman rufin gida. Wannan na faruwa ne sanadiyyar sinadaran da ke dauke cikinsa, masu nauyi. Yana lalata amfanin gona, yana kashe dabbobin gida, da na ruwa (irin kifaye da makamantansu), yana lalata hanyoyi, sanadiyyar santsi da hazo da yake haddasawa.

clip_image002Idan kuma yana sama aka fara ruwa mai dauke da walkiya da cida, to yana haddasa daukewar wutar lantarki, da dukkan hanyoyin sadarwar tarho, ya kuma sanya firgici iya kusancinsa da mutane ko garin da ake ruwan. Idan kuma ya riski direban jirgi a sama, lamari ya lalace kenan. Yana iya toshe masa gabansa nan take, yana iya kara wa jirgin nauyi, sanadiyyar zubowar da zai rika yi a saman jirgin. Wannan zai sa wani bangaren jirgin ya fi wani bangaren nauyi, musamman fukafukansa. Idan kuwa haka ta faru, to akwai matsala. Domin jirgi na tafiya lafiya ne idan nauyinsa yayi daidai a dukkan bangarori. Amma idan ya zama wani fiffiken ya fi wani fiffiken nauyi, to yana iya samun matsala nan take. Bayan nan, yana tasiri wajen lalata fitilun da ke taimaka wa jirgin sauka. Yana lalata farfelan jirgin idan ya shige ciki. Dole kuwa haka ta faru, saboda sinadaran da ke dauke cikin wannan toka basu narkewa. Idan jirgi ya ci gaba da tafiya a cikinsa, yana iya toshe masa bututun da yake gejin iska da shi, wanda kuma ke nuna masa iya tazarar tafiyarsa, watau Air Speed Indicator. Kamar yadda bayanai suka gabata a baya, samuwar wannan toka a sama na iya hana direban jirgin sadarwa tsakaninsa da masu lura da shi a tashar da yake son sauka ko ya baro a baya. Illa mafi muni da wannan toka ke yi wa jirigi shi ne ya sanya injin jirgin ya kama zafi, sanadiyyar toshe shi da yake yi. Idan hakan ta faru, jirgin ba zai samu kuzari ba ko kadan, dole ya gangaro kasa-kasa, in kuwa ba haka ba dukkan injinansa na iya daukewa nan take. Wannan shi ne abin da ya faru da wani jirgin British Airways F19, daidai lokacin da tsaunin Galunggung da ke kasar Indonesiya yayi amai, tare da watsa wannan toka a sararin samaniya cikin shekarar 1982. Nan take dukkan injinan jirgin guda hudu suka daina aiki, sai da ya rage tafiya, ta hanyar gangarowa kasa daga tazara nisan kamu dubu talatin da shida (36,000ft) zuwa kamu dubu goma shabiyu (12,000ft). Irin wannan har wa yau ya faru da jirgin KLM Boeing 747 da ya taso daga birnin Amstadam na kasar Nedaland zuwa nahiyar Amurka. Daidai lokacin ne tsaunin Redoubt da ke jihar Alaska ya fara amai. Jirgin bai tsaya ba ya ci gaba da tafiya. Saukarsa ke da wuya sai dukkan injinan jirgin suka yi dameji. Sai da aka kashe dalar Amurka miliyan tamanin ($80M), aka fitar da tokar da mizaninta ya kai kilogiram tamanin (80kg) daga injin, sannan aka kwashe wajen watanni uku ana gyara. Wadannan su ne kadan cikin illolin wannan toka na kunun dutse. Ta bangaren amfani kuwa, yana da tasiri sosai wajen sanya kasar noma ta zama mai amfani da albarka, kamar dai yadda wancan kunun dutse nau’in Passive Lava ke yi.

Kammalawa

Daga bayanan da suka gabata, a bayyane yake cewa tsaunuka masu aman wuta na da matukar tasiri ga al’umma da kuma muhallin da suke ciki. Duk da cewa munanan tasirinsu ya fi bayyana a fili, amma suna da wasu amfanoni da jama’a ke amfanuwa da su bayan lokaci mai tsawo da yin amansu. Wani darasin da ya kamata mu koya daga rayuwa tare da wadannan tsaunuka shi ne, duk wani abin da Allah ya kaddara samuwarsa a doron kasa ko a cikin teku, to don amfanin dan Adam ne. Ko da kuwa wannan abin na masa mummunar illa duk sadda ya bayyana, ko ya faru. Kuma Allah na iya amfani da shi wajen halaka duk wanda ya ga dama cikin bayinsa. Sannan samuwar wannan toka da ta bice sararin samaniya cikin watan Afrilu, wa’azi ne ga duniya baki daya, cewa idan za a yi hasara irin wannan cikin kasa da makonni biyu sanadiyyar aman da wani tsauni guda daya yayi a wata nahiya da ke can kurya, to me zai faru idan aka wayi gari dukkan tsaunuka masu aman wuta suka fara amai a lokaci guda? Don haka mu fadaka, mu kuma shiga taitayinmu.

AMSOSHIN WASIKUN MASU KARATU TA TES

Assalaamu Alaikum, Baban Sadik na kasance mai bibiyar makarantarka sama da shekara uku, kuma ina maka fatan alheri, Allah shi kara basira, amin. Don Allah ina da waya ne kirar Nokia 6260, ko tana da manhajar Opera? In har akwai, to yaya zan yi in rika shiga Intanet? Na gode. - Aliyu Danlabaran, Zariya: 08036158781

Malam Aliyu mun gode da addu’a, Allah kara basira da juriyar kasancewa tare da mu. Hakika galibin wayoyin salula na zamani suna da nau’in manhajar Opera Mini a tare dasu, ko kuma idan kaje gidan yanar sadarwan Opera, za ka samu nau’in da ya dace da wayarka, tabbas. To amma kafin nan, ina son sanar da kai cewa dukkan wayoyin salula suna da masarrafar lilo da tsallake-tsallake, watau “Browser”, wacce kuma kana iya mu’amala da ita wajen shiga Intanet. Amma idan kana son “Opera Mini” ce, to duk babu damuwa, kana iya saukar da ita zuwa wayarka, sannan ka loda mata. Don haka sai kaje inda ake mu’amala da Intanet a wayarka (watau “Browser”), ka shigar da wannan adireshin http://mini.opera.com/download shafin da ke dauke da manhajar zai budo, sai ka bi umarnin da ke shafin, ka saukar, tare da loda ta a wayarka. Allah sa a dace.

Assalaamu Alaikum, ina fatan kana cikin koshin lafiya tare da iyalanka. Na dade ina karatun shafinka a cikin Jaridar AMINIYA, kuma yana kara min fahimtar ayyuka na. Domin ina da shedar karatu ta NCE a fannin karantar da kimiyyar kere-kere, watau Technical Education, da kuma Difiloma a fannin kwamfuta. Ina jin dadin karatun shafinka. Allah ya kara mana fahimta, amin. - M. A. Faruk, Sokoto: 08036029098

To mun gode mu ma, kuma Allah kara dankon zumunci, da fahimta, da kuma juriya wajen kasancewa tare da mu. Tsarkakakkiya kuma cikakkiyar godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda duk wata ni’ima ta fahimta ko wayewa ko ci gaba, daga gareshi take. Mun gode.

Salamu Alaikum, ina amfani da wayar Nokia 6760 kuma ina da manhajar Opera mini a ciki. Ina son bude Imel ne don karban sako da aikawa, don Allah yaya zan yi? Na gode. - 08036017399

Kamar yadda muka sha bayani kwanakin da suka wuce, bude akwatin Imel ta wayar salula, in dai ba nau’ukan “Smartphones” bane, ba abu bane mai yiwuwa. Na farko dai asalin shafin da za a budo maka don ka yi rajista, ba ya samuwa sai ka aika da sakon “START”, zuwa wata lambar, wacce kuma bamu da kamfanin a nan nahiyar Afirka, ko ince Nijeriya. Wannan sakon da za ka aika ne zai sa a aiko maka da rariyar likau din da zaka bi, don samun shafin. Abu na biyu kuma shi ne, yin rajistan a waya na iya ci maka kudi da yawa. Duk da haka, idan kana amfani da wayar salula nau’in “SmartPhones” ne, (irin su “Blackberry” ko nau’ukan “E-Series” na kamfanin Nokia) to kana iya yin rajista ba matsala. Domin wadannan nau’ukan wayoyin salula suna mu’amala ne da Intanet tamkar kwamfuta cikakkiya. Da fatan an gamsu.

Da fatan Malam yana nan lafiya. Ni matsalata ita ce: a da ina karba ko aika sakon Imel ta hanyar Yahoo a wayata, amma tun shigowar wannan shekarar ko na shiga sai dai in ga tsoffin sakonnin da na aika ko karba. Shin a ina matsalar take ne: daga waya ta ne, ko daga Yahoo? - Sani Abubakar ‘Yankatsare, Jos: 08026023796

Malam Sani barka da war haka kuma ya aka ji da dawainiya da mu? Da fatan ana lafiya. Watau akwai abubuwa guda biyu ko uku. Da farko dai ya danganci tsarinka. Watakila tun da aka shiga wannan shekarar baka aika da sako ko kuma karbi wani sako daga wani ba. In kuwa haka ta kasance, to ai babu yadda za a yi ka samu wani sabon sako a jakar Imel dinka. Na biyu kuma, a iya cewa matsalar daga wayarka ce, amma hakan da kamar wuya, wai gurguwa da auren nesa. Domin in daga wayarka ne, ai baza ka iya ma shiga Imel din ba tun farko. In har kana ganin sakonnin da ka aika a baya, da wadanda aka aiko maka a baya, kuma babu wanda ya sanar da kai cewa ya aiko maka sako amma ka kasa gani, to ba zai zama matsalar daga gareta ba. Abu na uku shi ne a ce laifin kamfanin Yahoo. Hakan kuwa bazai yiwu ba, domin muddin kana iya shiga jakar Imel dinka daga wayarka, to ba yadda za a yi laifin yazo daga kamfanin Yahoo. Da fatan Malam ya gamsu.

Tsaunuka Masu Aman Wuta, Da Tasirinsu Ga Muhalli (3)

Abu na farko da ke makare a karkashin tsaunin dai, kamar yadda muka sanar, shi ne damamme, kuma tafasasshen “kunun dutse”. Na kira shi da kalmar “kunu” ne saboda a dame yake, da kaurinsa, kamar kunun gari (ko “jaguda”, ga wadanda suka santa). Na kira shi “tafasasshe” ne saboda yana da matukar zafi. Saboda tsananin zafinsa ma, launinsa ja ne, zur! A karo na karshe, na danganta shi da “dutse” ne (na ce “kunun dutse”) saboda asalinsa kenan. Dutse ne aka rababbaka shi, ya zama damammen kunu, mai kauri, kuma ja zur. Mai karatu ba zai fahimci yadda abin yake ba sai ya ganshi a fili, ko kuma ya kwatanta shi da “damammen kunun karfe”, wanda masana’antar karafa ke narkawa kafin su sandarar da shi zuwa ga abin da suke son kerawa. Hakan ma a babin kwatance ne, ba wai daidai zafinsu daya ba. Wannan kunun dutse da ke makare a karkashin tsaunin dai yana da matukar zafi. Masu bincike sun sanar da cewa mafi karancin zafinsa shine dari bakwai, a ma’aunin zafi na santigireti (700c). A can sama kuma, ya kai dubu daya da dari uku, a wannan ma’auni (1,300c)! Yana cakude ne da sinadaran kimiyya da dama. Daga cikinsu akwai sinadarin gilas, kuma a dauke yake da wata masifaffiyar iska mai kumfa a samansa. Da zarar zafi ya kai zafi, sai wannan masifaffiyar iska ta fetso shi waje, da zafinsa, da kuma kaurinsa. Wannan kunun dutse shi ne ake kira Molten Magma, a Kimiyyance. Kuma shi ne asalin dautse nau’in Igneous da muka sani; watau dunkulalle kuma tsantsar dutse kenan. Wannan shi ne abu na farko da ke fitowa daga karkashin tsauni mai amai, tare da wannan iska, da zafi da kuma sinadaran da ke tattare da shi. Da zarar ya fito, sai ya sake suna, da kuma yanayi.

Wannan ya kawo mu ga nau’in abin da ke samuwa na biyu, a yayin aman tsauni. Fitowar wannan kunun dutse ke da wuya sai ya kasu kashi biyu. Kafin bayanin nau’insa, duk sadda wannan kunun dutse ya fito waje, sunansa ya tashi daga Molten Magma ko Magma, ya koma Lava, ko Lava Flows. Shi wannan Lava ko kace Sandararren Kunun Dutse, shi ne ke yin ambaliya daga saman tsaunin, ya fara gangarowa, kafin ya sandare ya zama dutse curarre. A yayin gangarowarsa ne yake yin iya barnar da yake yi, musamman idan tsaunin a kusa yake da wani kauye, kuma cikin dare aman ya faru. Wanda ke gangarowa ko yin ambaliya, shi ake kira Active Lava, kuma shi ne mai haddasa wuta da ke ci balbal a duk sadda aman ya faru. Wannan ke nuna mana cewa shi tsaunin ba wai wutar yake amanta ba, a a, sinadaran wutar yake amayowa. Wannan nau’i na sandararren kunun dutse mai ambaliya, shi yafi komai barna a lokacin da yake fitowa. A tarihin tsaunuka masu amai, akwai garuruwa ko kauyuka masu yawa da suka kone ko suka tashi karfi da yaji, sanadiyyar wannan ambaliya mai hadari. Misali, akwai wani kauye da ke Jumhuriyar Kwango, ko tsohuwar Zayar ta da, wanda tsaunin Nyiragongo ya kona sanadiyyar aman da yayi cikin dare, lokacin da ‘yan kauyen ke bacci. Haka ma kauyukan Kaimu, da Kalapana, da Kapoho, da Kewaiki, duk kauyuka ne da tsaunin Kilauea da ke Tsibirin Hawaii na kasar Amurka ya kona, sanadiyyar aman da yake yi a-kai-a-kai. Haka ma akwai kauyen San Sebastiano al-Vesuvio da ke kasar Italiya, wanda tsaunin Vesuvius ya kona a shekarar 1944. A kasar Filifins ma akwai wani kauye da Tsaunin Cagsawa ya kona. Wadannan su ne garuruwa ko kauyukan da wannan sandararren kunun dutse mai malala a farfajiyar tsauni ya kora ko kona, tare da salwantar da rayuwan mazauna cikinsu.

A daya bangaren kuma, akwai kauyuka ko garuruwan da yayi musu mummunan ta’asa. Wadannan kauyuka sun hada da: kauyen Catamina da ke kasar Italiya, wanda Tsaunin Etna yayi wa ta’asa a shekarar 1669, sai garin Goma da ke Jumhuriyar Kwango Kinshasa, a shekarar 2002, da garin Haiwaey da ke Tsibirin Iceland, wanda tsaunin Eldfell ya raunata a shekarar 1973. Har wa yau akwai kauyen Royal Gardens da ke Tsibirin Hawaii na kasar Amurka da ya sha lugude a shekarar 1986-87, sai kuma wani kauyen San Juan na kasar Meziko mai suna Paricutin. Wannan shine galibin ta’adin da wannan sandararren kunun dutse mai gangarowa daga saman tsauni ke yi a daidai lokacin da tsaunin ke amai. Nau’i na biyu kuma shine wanda ya riga ya kame, sanadiyyar hucewar da yayi bayan ya gangara, ko ya samu wani kududdufi ya kwanta. Wannan nau’i shi ake kira Passive Lava, watau nau’i mara illa kenan. Idan ya riga ya kame, to nan take yake zama wani nau’in taki mai matukar alfanu wajen harkar noma. Ka ji wata hikimar Ubangiji kuma! Don haka wasu lokuta ake samun wasu kauyuka da ke kusa da tsauni mai aman wuta, wadanda ko an ce su tashi sai su ki. Ko da ya musu ta’adi sanadiyyar aman da yayi, za su sake dawowa inda suke a da. Wannan ma ya sa a Tsibirin Hawaii na kasar Amurka akwai kauyukan da sun kone sanadiyyar wannan ta’adi, amma daga baya sai hukuma ta sake gina su. Mazauna wurin na yin hakan ne sanadiyyar albarkar noma da suke samu. Domin duk kasar da wannan sinadari na Lava yayi ambaliya a kanta, to za ta zamo mai matukar albarka ta fuskar noma.

“Tokar Kunun Dutse” (Ash Plume)

clip_image002To bayan wannan sinadari kuma, sai abu na gaba da ke fitowa daga cikin wannan tsauni, watau “Tokar Kunun Dutse”, ko kuma Ash Plume, ko Volcanic Ash a Kimiyyance. Wannan shi ma yana dauke ne da sidanarai masu cutarwa da amfani. Wannan toka na dauke ne da buraguzan duwatsu da gilasai masu fadin kasa da milimita biyu, da ke samuwa a yayin da wani tsauni yayi amai. Babban abin da ke haifar da wannan toka mai dauke da hayaki kuwa ita ce masifaffiyar iskar da ke cillo wancan damammen kunun dutse mai fitowa daga karkashin tsaunin. Wannan iskar ce ke dauko wannan toka, ta cilla shi sama har cikin sararin samaniya. Wannan tokar kunun dutse na dauke ne da launin ruwan kasa, watau Brownish Ash. Abu na biyu da ke taimakawa wajen samar da wannan tokar kunun dutse shi ne sinadaran haske masu kyastuwa daga wutar da ke kamawa daidai lokacin da wancan kunun dutse ke fitowa daga kasan tsaunin. Sai abu na uku, watau buraguzan laka da ke samuwa yayin da kunun dutsen ke arangama da makogwaron tsaunin wajen fitowa a fusace, watau Volcanic Vent. Idan kuma Tsaunin Kankara ne da ke teku (watau Glacial Ice), da zarar kunun dutsen ya fito, ya hadu da narkakken ruwan kankarar da ke tekun, zai sandarar da shi ne nan take zuwa gari ko tokar gilasai, sannan kuma kurar da ke fitowa daga tsaunin ta tarkata wannan garin gilasai tayi sama da su, don toshe hazo da sararin samaniya. Tirkashi! Kafin mu kai ga amfani, zai dace mu yi bayanin munanan tasirin wannan toka na kunun dutse. Hakan ne zai bamu damar fahimtar cancantarsa wajen haddasa irin hasarar da yayi wa kamfanonin jiragen sama a watan Afrilu.

AMSOSHIN WASIKUN MASU KARATU TA TES

Salamun Alaikum Baban Sadik, tambayata ita ce: yaya tsarin amfani da Intanet na tafi-da-gidanka (watau Datacard Internet ko “F@stlink”) da kamfanonin wayar salula na kasar nan ke bayarwa? Kuma kasashen ketare ma suna da irin wannan tsarin? - Aliyu Mukhtar Sa’idu (IT), Kano: 08034332200

Malam Aliyu, wannan tsari na “F@stlink” kamar yadda kamfanin MTN ke kiransa, ba wani tsari bane sabo. Hasali ma dai an dade ana amfani da shi a wasu kasashe kafin zuwansa nan kasar. Tsari ne da ya kunshi amfani da fasahar Intanet a kwamfutar tafi-da-gidanka, watau Laptop, ta hanyar amfani da Makalutun Sadarwa, watau “Internet Modem”. Idan ba a mance ba, bayanai sun gabata cewa kwamfuta na iya mu’amala da fasahar Intanet ko Giza-gizan sadarwa ne ta hanyar wannan makalutun sadarwa, wacce ke zakulo bayanan da ke Intanet a matsayin siginar lantarki, ta kuma juya su zuwa haruffa ko hotuna ko sauti, kamar dai yadda suke a uwar garken da ta zakulo su.

Wannan tsari na zakulo bayanai a siffarsu, a mayar da su zuwa siginar lantarki, sannan idan sun zo muhallin da ake son amfani da su su bayyana kamar yadda aka dauko su, shi ake kira “Modulation and Demodulation”, wanda kuma daga wadannan sunaye biyu ne aka samo sunan wannan makalutu da ake kira “Modem” a turancin Kimiyyar sadarwa ta zamani. To wannan makalutu kuwa asalinsa babba ne, kamar dai irin wayoyin tarho da muke amfani dasu a da. Idan ka saya za ka jona shi ne da kwamfutarka, ta wayar da yazo da ita. To amma da zamani ya ci gaba, sai aka mayar da su kanana, sirara, wasu ma girmansu bai wuce dan yatsan hannu, wasu kuma kamar tafin hannu suke. Ya dai danganci kamfanin da ya kera su. Da zarar ka saya, sai ka tsofa shi a jikin kwamfutar tafi-da-gidanka, ka kuma loda mata masarrafar da take zuwa da shi a faifan CD ko makamancin wannan, don ta haddace dukkan tsare-tsaren da ke ciki. Har wa yau, wannan tsari na amfani ne da lambar wayar tarho da ke dauke cikin katin SIM da kamfanin wayar ke bayarwa. Idan ka tashi shiga Intanet, sai ka sayi katin kira (watau “Recharge Card”) ka loda mata, sannan ka fara tsallake-tsallakenka. Kamar yadda bayanai suka gabata a sama, sauran kasashe ma na amfani da wannan tsari, kusan shahararsa a wasu kasashen ma yafi na nan Nijeriya. Da fatan ka gamsu.

Assalaamu Alaikum, don Allah Baban Sadik wai shin mai yiwuwa ne mutum ya iya gina Mudawwanarsa (blog) ta wayar salula ko kuwa dole sai a kwamfuta? - Jamilu Ahmad, Kaduna: 08032424168

Malam Jamilu ya danganci irin wayar da kake da ita. Idan babbar waya ce, mai shafi mai fadi, da kuma saurin sadarwa da Intanet, kana iyawa. Amma idan ba haka ba, zai dace ka yi amfani da kwamfuta. Domin zai dauke ka tsawon lokaci, sannan galibin gidajen yanar sadarwa na Mudawwanai suna da shafuka zubi biyu ne; da wanda ake iya shiga da kwamfuta, da kuma shafin da ake shiga ta amfani da wayar salula. Idan ka shiga shafin da ake shiga ta kwamfuta a wayarka, ba za kaji dadin mu’amala da shafin ba, domin zai kasance mai fadi ne, kuma yana dauke da hotunan da za su ci maka kudi sosai kafin ka gama gabatar da dukkan abin da kake son gabatarwa. A takaice dai ka yi amfani da kwamfuta wajen ginawa, in yaso sai ka rika shiga ta wayarka kana aikawa da sakonni. Da fatan ka gamsu.

Tsaunuka Masu Aaman Wuta, da Tasirinsu ga Muhalli (2)

Sai nau’i na biyu, wanda ke samuwa sanadiyyar afkawar wani faranti a saman wani, mai haifar da ninkewar wasu farantan a sanan wasu, har su yi toroko a doron wannan kasar tamu, su zama tsauni. Nau’in tsaunin da ke samuwa ta wannan hanya shi ake kira Fold Mountain a Kimiyyance. A Hausar zamani kana iya kiransa da suna ‘Ninkakken Tsauni’. Domin haka sifarsu take; a tattare a waje daya, wani a saman wani. Irin wannan nau’in tsauni shi ma yana nan birjik a duniya. Babban misali da zan iya kawowa yanzu shi ne na wadanda ke warwatse a garuruwan Jura da Zagros na kasar Iran. Su ne shahararrun nau’in Ninkakken Tsauni da ake misali da su a duniya. Nau’i na karshe kuma shi ne wanda ke samuwa sanadiyyar riftawar wani bangaren farantin karkashin kasa, tare da barin dayan bangaren a tsaye. Wannan ke haifar da samuwar tsauni nau’in Block Mountain a Kimiyyance, ko kuma ka ce ‘Dunkulallen Tsauni’ a Hausance. Ire-iren wadannan tsaunuka a tsaye su ke caras, tare da samuwar kwari a gefensu; abin da ke nuna alamar riftawar wani bangaren faranti ne daga dan uwansa. Wadannan, a takaice, su ne nau’ukan tsaunuka guda uku da ake da su a duniya a yanzu; ba su da na hudu.
Tsaunuka Masu Aman Wuta (Volcanic Mountains)
Kamar yadda bayanai suka gabata, nau’ukan tsaunuka masu aman wuta su ne wadanda suka samu sanadiyyar gibi a tsakanin farantan kasa guda biyu. Wanda kuma ke aman wuta lokaci-lokaci. Su kansu sun kashi zuwa kashi uku ne, dangane da yanayin aman da suke yi. Nau’i na farko su ne wadanda suke yin amai a-kai-a-kai, babu kakkautawa. Ko dai a dukkan shekara, ko bayan shekaru bibbiyu, ko kuma bayan shekaru biyar-biyar ko duk wata tazarar da ba mai tsawo bane a zamaninsu. Idan tsauni yayi suna wajen yawan amai a-kai-a-kai, akan kira shi da suna Active Volcano. Watau “Rayayyen Tsauni mai Aman Wuta” kenan, a Hausar zamani. Idan daga baya ya daina amai, bayan ya shahara da amai na tsawon lokaci, to akan kira shi Extinct Volcano a Kimiyyance. Watau “Mataccen Tsauni mai Amai”. A karo na uku, idan bayan ya daina na tsawon zamani ko shekaru masu dimbin yawa, har an yanke kauna an kuma daina tsammanin zai sake amai, sai ya ci gaba da amai kamar yadda yake yi a baya, shi kuma akan kira shi Dormant Volcano; ko kace “Farfadadden Tsauni mai Amai”.
A iya binciken Malaman Kimiyyar Kasa, an kasa bambacewa tsakanin nau’in Extinct Volcano da kuma Dormant Volcano. Domin sau tari an sha samun wasu tsaunukan da suka daina amai, aka yanke kauna da za su kara yi, sai kawai ga shi sun ci gaba da amai. Babban misali shine wani tsauni mai suna Fourpeaker Volcano da ke Lardin Alaska ta kasar Amurka. Wannan tsauni, a iya tarihi, ya shekara sama da shekaru dubu goma bai sake amai ba. Wannan ta sa aka cire shi daga sahun nau’ukan tsaunuka masu rai, zuwa matattu, watau Extinct. Cikin shekarar 2007, watan Satumba, sai ya farfado, ya ci gaba da amai. Wannan tasa masana suka ce tsaunuka masu amai nau’i biyu ne kawai; ko dai masu cikakken rai ne, watau Active, ko kuma masu sumewa ne su sake farfadowa, watau Dormant.
Bayan haka, akwai wasu tsaunuka masu aman wuta da suka shahara a duniya sanadiyyar barnar da suke yi a duk sadda suka yi amai. Wadannan tsaunuka dai guda goma sha shida ne, kuma galibinsu suna Yammaci ne ko Gabashin duniya. Masana sun sanya musu lakabi da “The 16 Decade Mountains”. Abin da wannan lakabi ke nufi a ma’anance dai shi ne: “Tsaunuka Sha Shida Masu Aman Wuta da Suka fi Hadari”. Wadannan tsaunuka a halin yanzu suna warwatse ne a kasashe guda goma sha uku. Kasashen dai su ne: kasar Rasha, da Meziko, da Jafan, da Italiya, da Kolombiya, da Amurka, da Indonesiya, da Jamhuriyar Kwango (watau tsohuwar Zayar kenan), da Gwatemala, da Girka, da Filifin, da Andalus (watau Spain), sai kuma kasar Papua New Guinea. Wadannan su ne kasashen da ke dauke da tsaunuka masu aman wuta da suka fi kowanne zama hadari idan suka fara amai, sanadiyyar mummunar ambaliyar tafasasshen kunun dutse da suke yi, mai haddasa mummunar illa ga garuruwan da ke makwabtaka da su, ko kuma muhallin da suke.
Tsaunukan Kasar Iceland
Kasancewar wannan lamari na toka mai guba da ya haddasa mummunar hasara ga kasashe da kamfanonin jiragen sama ya samo asali ne daga kasar Iceland, na ga dacewar gabatar da dan takaitaccen bayani kan wannan kasa, da adadin tsaunuka masu aman wuta da take dauke dasu, da kuma tsarin aman da suke yi, lokaci-lokaci. Hakan zai taimaka wa mai karatu wajen fahimtar yanayi da kuma dalilan da suka sa hasarar ta yawaita, da kuma dalilan da suke haddasa yawaitan aman da tsaunukan da suke yawan yi a-kai-a-kai.
Kasar Iceland dai tsibiri ce; ma’ana, a gewaye take da teku, daga dukkan bangarorinta. Kuma an kafa kasar ne tun shekarar 874AD, watau shekaru sama da dari biyar kenan ya zuwa yanzu. Wannan kasa na sarkafe ne a tsakiyan daya daga cikin manyan tekunan duniya da ake ji da su, watau tekun Atlantika. Kuma kamar yadda muke da farantai a karkashin kasar da muke takawa ko rayuwa a kanta, haka ma a karkashin tekunan duniya akwai ire-iren wadannan farantai, ko Plates. Bayan haka, Tsibirin Iceland na dore ne a daidai inda farantan kasan tekun suke makwabtaka da juna; tsakanin farantan da suka taso daga Arewacin Amurka, suka yi kudu (watau North American Plates), da kuma wadanda suka taso daga Nahiyar Turai, suka yi Arewa (watau Eurasian Plates).
Zaman Tsibirin Iceland a wannan muhalli ya sa ta samu kanta a “mabubbugan kunun dutse mai haddasa aman tsauni”, watau Volcanic Hotspots. Wannan tasa har wa yau Tsibirin ya wayi gari a matsayin kasar da tafi kowace kasa yawan tsaunuka masu aman wuta a duniya. Kididdiga sun nuna cewa akwai tsaunuka masu aman wuta guda dari da talatin (130) a kasar Iceland. Cikin wannan adadi, bincike ya nuna cewa guda goma shatakwas ne kadai suka yi amai ya zuwa yanzu. Wannnan a iya sanin masu bincike kenan. Allah kadai ya san yaushe sauran suka daina, bayan tsawon lokacin da suka dauka suna yi, kafin wannan zamani. Manyan tsaunuka guda biyu da suka yi amai kwanan nan su ne tsaunin Fimmvorouhab, wanda ya dauki tsawon kwanaki ashirin da biyu yana amai (daga ranar 20 ga watan Maris, zuwa 12 ga watan Afrilu), sai kuma tsaunin Eyjafjallajokull (ana furutu shi da: Aya-fyatla-jo-kult), wanda shi kuma ya dauka daga ranar 14 ga watan Afrilu, har zuwa karshen watan. Wannan tsaunin karshen ne ya haddasa samuwar wannan toka mai guba da bayanansa ke tafe. To me da me suke fitowa daga cikin tsauni, a yayin da ya fara amai?
Abubuwan da Tsauni ke Amayarwa
Idan aka ce tsauni na amai, to dole ne a samu abin da yake amayarwa. Tabbas kalmar da ta shahara a fassarar Hausa ita ce: “aman wuta”, to amma wuta ne kadai tsaunin ke amayarwa, ko kuwa wasu abubuwa ne masu haddasa samuwar wutar a inda aman ya samu? Wannan tasa muka kebance wannan sashe don bayyana wasu cikin shahararrun abubuwan da tsauni ke yin amansu. Kada a mance, mun riga mun yi bayanai kan dalilan da ke haddasa aman a baya, ba sai mun sake maimaitawa ba. A yanzu ga wadannan bayanai nan a fayyace.
AMSOSHIN WASIKUN MASU KARATU TA TES

Assalaamu Alaikum, na karanta shafinka na “Kimiyya da Kere-kere” a cikin jaridar AMINIYA. Allah Ya kara hazaka. Don Allah a taimaka mani da wasu bayanai masu alaka. Ga adireshin Imel dina: yunusayunusa43@yahoo.com. Daga Yunusa Hussaini, Samaru, Zaria.
Malam Yunusa mun gode da addu’a. Kai ma Allah kara maka hazaka da juriyar kasancewa tare damu. Dangane da bukatarka, na rasa me zan aika maka, musamman ganin cewa dukkan abin da nake rubutawa a wannan fanni ne ake bugawa a shafin. Sai dai idan kana da bukatar kasidun da suka gabata a baya ko shekarun baya, kana iya zuwa shafin Makarantar Kimiyya da Fasahar Sadarwa da ke http://fasahar-intanet.blogspot.com, ko wanda muka kebe don zuba kasidun Kimiyya da Fasahar Kere-kere, da ke http://kimiyyah.blogspot.com. Duk kasidun da da ke bayyana a wannan shafi suna can a taskance. Da fatan ka gamsu.
Assalaamu Alaikum, Malam Abdullahi yaya kokari? Tambayata ita ce: in har Malaman Kimiyya da Fasaha a wajensu komai ya faru, akwai abin da ya haddasa shi, ba Allah ba, to wai me za su ce, ko me suka ce dangane da masu tsafi, wanda ke hada wani abu sai wani abu ya tashi; ba kuma a kimiyyance suke yi ba? Daga Khaleel Nasir Kuriwa, Kiru, Kano: 07069191677
Malam Khaleel barka da kokari. Hakika har yanzu dai basu yarda da ire-iren wadannan abubuwa ba, kuma ba su kididdige su a matsayin wata ci gaba ta ilimi a fannin Kimiyya. Kamar yadda kai ma ka kira su da “matsafa”, haka su ma suke kiransu. A turance sukan kira su “magicians”. Su malaman kimiyya suna da wasu ka’idoji ne da suke bi wajen bincike, masu basu irin sakamakon da suke bukata dangane da kowane irin yanayi. A tsarinsu, duk wani bincike da bai da asali daga wadannan ka’idojin, to ba su bashi wata kima. Da fatan ka gamsu.

Tsaunuka Masu Aaman Wuta, da Tasirinsu ga Muhalli (1)

Laraba, 14 ga Watan Afrilu, 2010

Cikin makonni biyun karshe na watan Afrilun da ya gabata ne wani sashen sararin samaniyan duniya ya shiga wani yanayi mai ban mamaki da rudani, inda jirage suka lazimci tashoshinsu, matafiya suka shafe sama da kwanaki goma a filayen jirgin sama suna kwana a tsakanin jakunkunansu, sanadiyyar gurbatan yanayi da ya samo asali daga wasu sinadarai masu guba da cutarwa da suka killace tafarkin hanyan jirage a sararin samaniyan nahiyar Arewaci da Yammacin Turai, da ma wani bangare na nahiyar Gabashin Amurka. Wannan sinadari mai kama da toka yayi ta tuttudowa ne daga aman wutar da wani babban tsaunin kasar Iceland ya fara yi tun daga ranar Laraba, 14 ga watan Afrilu, har zuwa kusan karshen watan. Daga baya an samu yaduwar wannan toka har zuwa kasar Turkiyya, inda ya toshe sararin samaniyar kasar, da wasu cikin kasashen Arewacin Afirka, kamar Maroko da sauransu. Wannan toka mai hadari a farko ya toshe sararin samaniyan wannan kasa ta Iceland, daga nan iska ta kada shi zuwa Arewa maso Yammacin Turai, inda ya toshe wa kasashe har wajen ashirin sararin samaniya su ma, ya hana jirage tashi tsawon wannan lokaci. A tarihin safaran jiragen sama a duniya, ba a taba samun yanayin da ya tayar da hankali, ya haifar da hasara mafi girma, ya kuma shafi kasashe da dama irin wannan ba.

Kasancewar kasar Iceland na tsakanin manyan nahiyoyi ne guda uku musamman, kuma masu karfin tattalin arzikin kasa a duniya, tasa wannan lamari ya haifar da hasarar dukiya mai dimbin yawa cikin wadannan kwanakin da basu kai wata guda ba. Nan take kallo ya koma sama. Kamfanonin jiragen sama suka yi zugum. Fasinjoji suka kama zaman dirshan; ga tikiti amma babu damar tafiya. Harkoki suka tsaya cak. An kiyasta cewa kamfanonin jiragen sama sunyi hasarar sama da dala miliyan dari biyu a duk rana guda. Kafin sararin samaniya ya gama kwaranyewa har jirage su fara tashi kuwa, kamfanonin safarar jiragen sun yi hasarar kudi sama da dalar Amurka miliyan dubu dari da dubu saba’in. Watau Biliyan daya da digo bakwai kenan ($1.7 billion). Bayan tarin tikitin da aka soke saboda lokacinsu ya wuce, wadanda kuma a ka’idar safaran jiragen sama na kasuwanci, ba su da Inshora balle a fanshe haushi da hasaransu, da dama cikin kasashe da kamfanoni daban-daban sun tafka hasara mai dimbin yawa sanadiyyar wannan toka da Allah Ya aiko. Jiragen kaya da dama sun yi kwantai, dauke da kayayyakin abinci, ko magunguna; ko dauke da wasiku, ko man jirgin sama, ko man gas na injina da za a kai wasu kasashen ko biranen, ko kayan alatu, da dai sauran abubuwa masu amfani da suka kasa kaiwa masaukinsu cikin lokaci. Wadansu sun lalace a cikin jiragen, wasu kuma sun yi kwantai. Abu na karshe kuma shi ne, nan take farashin hannayen jarin wadannan kamfanonin jirage ya fadi warwas a kasuwannin hannayen jari da ke kasashen Turai da Amurka da Asiya.

Duk wannan hasara ta samo asali ne sanadiyyar aman wuta (Volcanic Eruption) da wani tsauni yayi a kasar Iceland, kamar yadda na tabbata masu karatu sun sha labarun tuni. Wannan amai ne ya haifar da samuwar wannan sinadari a yanayin toka, wanda kuma sanadiyyar hadarinsa ga jirage da masu tuka su ne aka samu tsaikon da ya haifar da wancan hasara. Da dama cikin masu karatu sun dauka cewa babban dalilin da ya hana jirage tashi shi ne don watakila direbobin ba za su ga hanya da kyau ba, sanadiyyar kura ko tokar da ta hada duhu mai tsanani a nahiyar da abin ya shafa. Wannan ko kadan ba haka bane. Wannan tasa ma muka ga dacewar gabatar da bayanai gamsassu a kimiyyance, don nuna muni da kuma tasirin wannan lamari da na sauran bayanai masu nasaba da tsaunuka masu aman wuta, watau Volcanic Mountains, da kuma abin da ire-iren wadannan tsaunuka ke fitarwa idan hakan ta kasance. Amma kafin nan, ga mukaddima nan kan ma’ana da nau’ukan tsaunukan da muke dasu, da kuma yadda suke samuwa a duniya baki daya – duk a mahangar kimiyyar kasa. Don sai mun san wadannan sannan za mu iya fahimtar tasirin wannan toka ta aman wuta da tsaunin yayi, watau Ash Plume, ko Volcanic Ash, a Kimiyyance.

Tsaunuka da Nau’ukansu a Kimiyyance

A fannin Kimiyyar Kasa (watau Geology ko Earth Science ko Geography), Tsauni – ko Mountain a harshen Turanci - wani tarin kasa ne a doron kasar da muke takawa, mai cakude da dutse ko duwatsu, wanda ke samuwa sanadiyyar hargitsin da ke faruwa tsakanin farantai ko fallayen kasa masu tsauri da ke can karkashin kasar da muke rayuwa a kai. Wadannan farantai – ko Plates a Kimiyyance – wasu nau’ukan shimfidun kasa ne da ke karkashin wannan kasar da muke takawa. Hargitsin da ake samu a tsakaninsu lokaci-lokaci ne ke haifar da samuwar nau’ukan tsaunukan da muke gani a doron wannan kasa tamu. Wannan “hargitsi” kuma da ke faruwa a tsakaninsu, shi ake kira Plates Tectonics, a turancin Kimiyyar Kasa. Bigiren da wannan hargitsi ke faruwa kuma shi ake kira Fault Lines, a Kimiyyance.

Duk sadda aka samu wani hargitsi – na gocewa, ko karyewa ko riftawa – a tsakanin wadannan shimfidun kasa da ke karkashinmu, dayan abubuwa uku ne ke samuwa ko faruwa. Akan samu ninkewar wani farantin kasa a saman wani. Ko kuma a samu burmawar wata shimfidar da ke gefen wani farantin. Ko kuma, a karo na karshe, a samu kaucewa ko gocewar wani farantin daga wani. Hakan shi zai samar da kogo a tsakanin farantan biyu; abin da ke nuna akwai rauni a wannan muhalli kenan. Wannan ya kawo mu ga na’ukan tsaunuka guda uku a duniya, kamar yadda ake da dalilai guda uku masu haddasa hargitsi a tsakanin farantan da ke karkashin wannan kasar tamu.

Nau’in tsauni na farko shi ne wanda ke samuwa sanadiyyar gocewar wani faranti daga wani farantin, wanda kuma ke haifar da samuwar kogo a tsakanin farantan biyu masu makwabtaka da juna. Idan haka ta faru, dole za a samu rauni a tsakanin farantan, kamar yadda bayani ya gabata a sama. Wannan raunin ne ke samar da wani “tafasasshe kuma damammen kunun dutse”, watau Molten Magma a Kimiyyance. Idan tafiya tayi nisa, sai wannan tafasasshe kuma damammen kunun dutse ya feso waje, tare da iska mai tsanani, mai kuma dauke da guba. Fetsowarsa waje ke da wuya, sai ya daskare, yayi tudu. A haka zai yi ta yi har sai ya samar da tsauni mai zaman kansa. Nau’in tsaunin da ke samuwa sanadiyyar wannan rauni da ke samar da wannan fitinannen kunun dutse, shi ake kira Volcanic Mountain, a turance. Ko kuma kace ‘Tsauni Mai Aman Wuta’, a Hausar zamani. Irin wannan tsaunin ne ke bulbulo da wannan toka da ta mamaye sasannin nahiyar turai kamar yadda bayanai suka gabata. Basu takaita ga doron kasa kadai ba, har a cikin teku ana samun ire-iren wadannan tsaunuka; da na tudun kasa, da kuma na kankara. Babban misali kan na teku shine irin bala’in da ya samu a shekarar 2004 a nahiyar Asiya, sanadiyyar mahaukaciyar guguwar da ta taso daga cikin teku ta tafka barna mai dimbin yawa. Wannan mahaukaciyar guguwa da ake kira Tsunami, ta samo asali ne sanadiyyar irin wannann aman wuta da ya faru a karkashin tekunan da ke wadannan kasashen Asiya. Akwai nau’in tsaunuka masu aman wuta a warwatse a dukkan nahiyoyin duniya.

TAKAITACCEN TARIHIN “BABAN SADIK”

Wasu cikin masu karatu sun bugo waya suna neman in rubuta takaitaccen tarihi na don su karanta. Na basu uzuri kan cewa babu wani abin ji a cikin tarihi na, amma sun dage sai sun ji. Don haka na dan tsakuro muku wani abu cikin tarihin rayuwata.

Suna na Abdullahi Salihu Abubakar, an kuma haife ni ne a Unguwar Hausawa ta Garki Village da ke Karamar Hukumar Municipal, a babban birnin tarayya ta Abuja, cikin shekarar 1976. Shekaru na 34 kenan. Mahaifi na shi ne Malam Abubakar Salihu, shi kuma Salihu kakana ne. Asalin kakanni na (da ma sauran mazauna Unguwar Hausawa a Garki Village) daga Kano suke. Zama ne ya kawo su wannan wuri, wacce a wancan lokaci ta zama kamar zango, kusan shekaru dari biyu da suka gabata. Kuma ma saboda tsawon zamani da halin zamantakewa, a halin yanzu duk mun rikide mun zama Hausawan Abuja. Na yi makarantar Firamare, da Sakandare da kuma Jami’a duk a Abuja. A halin yanzu ina da digiri kan fannin Tattalin Azkirin Kasa (Economics), wanda na samu daga Jami’ar Abuja. Ina kuma kan neman ilmin Kur’ani da sauran fannonin Ilmin musulunci har yanzu.

Ni mutum ne mai sha’awar rubuce-rubuce da karance-karance. Ina kuma sha’awar binciken ilmi kan fannoni irinsu Tattalin Arzikin Kasa (Economics), da Fasahar Sadarwar Zamani (Information Technology), da Fasahar Intanet, da Tsarin Harsuna (Linguistics), da Fassara (Translation), da Aikin Jarida (Journalism) da Kimiyya (Science) da dai sauran fannoni masu nasaba da wadannan. Allah Ya hore min juriyar karatu da rubutu iya gwargwado. A halin yanzu na rubuta littafi kan fasahar Intanet, mai suna “Fasahar Intanet a Sawwake”, wanda ake gab da bugawa. Akwai kuma wadanda nake kan rubutawa a halin yanzu, kamar “Tsarin Mu’amala da Fasahar Intanet”, da kuma “Wayar Salula da Tsarin Amfani da Ita”. Sai kuma kasidun da nake rubutawa a wannan shafi a duk mako. A yanzu ina zaune ne a Sabon Garin Garki (watau New Garki Town) da ke nan Abuja. Ina da mata daya, da ‘ya’ya uku: Abubakar Sadiq, da Nabeelah, sai kanwarsu Hanan.

GODIYA DA BAN-GAJIYA

Shafin Kimiyya da Kere-kere na mika godiyarsa ga daya cikin manyan dalibansa, watau Malam Aliyu Mukhtar Sa’idu (IT) da ke Kano, sanadiyyar dawainiya da jigilar da yayi ta yi da ni lokacin da naje ziyarar aiki a Kano, daga ranar talata, 11 zuwa laraba, 12 ga watan Mayu. Allah saka da alheri, ya kuma jikan mahaifa, am