Friday, March 5, 2010

Tsaga A Jikin Wata: Mu’ujiza ko Yawan Shekaru?

Mabudin Kunnuwa

Kamar sauraimagen wurare da yanayin zamantakewa na dan Adam, yaduwar jita-jita wata al’ada ce ko dabi’a wacce ke  samuwa a duk inda wannan tsarin zamantakewa take. Tsakanin birni da birni, da kauye da wani kauyen, da kasa da wata kasar, da nahiya da wata nahiyar, duk baka rasa yaduwar jita-jita a tsakani. Haka abin yake a duniyar Intanet. Daga cikin dadaddun jita-jitar da ke yawo da yaduwa a duniyar Intanet akwai hoton Wata, mai dauke da tsaga a samansa, wanda ake ta yadawa da kuma sanar da cewa wannan tsaga ko shata ko shaci da ke saman Wata ya samo asali ne tun lokacin da kafiran Makka suka bukaci Manzon Allah (SAW) yasa Wata ya rabe gida biyu, muddin abinda yake ikirari na cewa shi Annabi ne, gaskiya ne. Wannan hoto mai dauke da Wata da alamar tsagar da ke jikinsa ya shahara sosai a Intanet. A kalla a iya cewa an samu shekaru kusan goma wannan hoto na yawo a Intanet. Sanadiyyar wannan shahara ne ma aka samu yaduwar kasidu da sharhi dabam-daban masu tabbatarwa ko kore ingancin wannan hoto. Har wa yau, wasu na ikirarin cewa an samo wannan hoto ne daga cikin taskar Hukumar Binciken Sararin Samaniya na kasar Amurka, watau NASA, cikin jerin hotunan da masu ziyarar duniyar Wata a kumbon Apollo 11 suka dauko a lokacin ziyararsu, shekaru sama da arba’in da suka gabata.

Kamar yadda mai karatu zai gani a hoton da na dauko mana daga Intanet, akwai tsaga a saman Wata tabbas, to amma meye alakarsa da wannan mu’jiza ta Manzon Allah a Makka? Ina alakar wannan hoto da hukumar NASA? Shin da gaske ne masu binciken Sararin Samaniya a Kumbon Apollo 11 ne suka dauko wannan hoto? In har da gaske sune suka dauko wannan hoto a ziyarar da suka kai, tambaya ta gaba ita ce: ganin cewa tsagewar da Wata yayi mu’jiza ce, ba tsagewa ce irin ta al’ada ba, shin ana iya samun alamar tsagar a jiki har yanzu? Shin meye tasirin mu’jiza a jikin duk wani abinda mu’jizar ta auku? Wa ya musulunta sanadiyyar wannan al’amari, kuma me ya kai shi ga hakan? Kuma meye bambanci tsakanin “Bayanin Tsarin Kimiyya”, da “Mu’jizar Kimiyya”, da kuma “Mu’jizar Annabawa”? Wadannan, da ma wasu tambayoyin da ke tafe ne nayi bincike na musamman don kosar damu kan abinda ya shafi wannan lamari na tsagewar Wata da hoton da ke ta yawo a Intanet - mai kokarin hada alaka a tsakaninsu. Amma kafin mu shiga bayani kan dukkan wadannan, ga takaitaccen bayani nan kan shi kanshi Watan, da tsarin rayuwarsa.

Halittar Wata: Daga Ina Haka?

Bayani kan daga ina Wata ya samimageo asali bai kamata ya dame mu ba, musamman ganin  cewa a jerin kasidun da muka gabatar a shekarar da ta gabata, masu taken: “Kimiyyar Kur’ani da ta Zamani: A Ina Aka Hadu?”, mun yi wannan bayani. Abinda ke da muhimmanci mu sani shine, shi Wata, ko Moon a turance, shine Tauraron Asali (Natural Satellite) da wannan duniya tamu ta mallaka, kuma yake gewaye ta, tare da halittar rana. Malaman Sararin Samaniya sun yi hasashe cewa a kalla halittar Wata tayi shekaru biliyan hudu ko sama da haka, tun samuwarta. Wata kan kare gewaye wannan duniya tamu ne cikin kwanaki ashirin da biyar da rabin rana (25.5days), amma idan aka hada da gibin kwanakin da yake kashewa a halin shawaginsa a falakin rana, sai yayi kwanaki ashirin da tara da rabin kwana (29.5days) yake gama gewaye daya.

Kamar yadda bayanai suka gabata a sama, wannan duniya tamu bata da wani Tauraro na Asali (Natural Satellite) da ya wuce Wata, kuma idan aka kwatanta shi da girman duniyar, kusan shine Tauraron Asali da yafi girma a dukkan Taurarin Asali da ke gewaye da sauran duniyoyin da ke makwabtaka damu. Shi Wata bashi da hasken da yake kyallarowa na kansa, sai dai ya lakato haske daga rana a yayin da take nata shawagin, idan ta juya mana baya kuma muka shiga dare ko duhu, sai ya hasko mana wannan haske, kamar dai yadda bayanai suka gabata a kasidun baya. Kamar wannan duniya tamu da sauran duniyoyi ko halittun da ke sama, Wata a cure yake, ko ince a mulmule. Bangaren da ke fuskanto mu a lokacin da yake shawagi, shi ake kira The Near Side, a turancin Kimiyyar Sararin Samaniya. Wannan bangare ne ke darsano hasken rana don haskaka duniyarmu, kuma an kiyasta cewa darajar zafin da ke wannan bangare ya wuce digiri dari da talatin da bakwai a ma’aunin zafi na santigireti (watau 1370C). Dayan bangaren da ke shiga duhu kuma daga baya, shi ake kira The Far Side. Amma kuma sabanin bangaren farko, wannan bangare bai da zafi sai sanyi mai tsanani. An kiyasta sanyin wannan bangare na Wata cewa ya kai dari da hamsin da shida a kasa da mizanin zafi (watau -1560C).

Binciken baya-bayan nan da aka yi ya tabbatar da cewa halittar Wata na dauke ne da duwatsu nau’uka dabam-daban, da sinadaran kimiyya masu inganci irin wadanda bamu dasu a wannan duniya tamu. Kari a kan haka, jikin Wata, inji masu wannan bincike, kamar gilashi yake wajen mu’amala da haske; duk ta inda ka cillo haske, zai dauka, ya kuma cilla hasken zuwa inda yake fuskanta. Kamar dai yadda gilashi ke yi idan ka cilla masa haske. Wannan tasa idan rana ta cillo haskenta, sai Wata ya dauka, ya kuma cillo hasken zuwa wannan duniya tamu, kasancewar shine tauraron mu. Allah Buwayi gagara misali! Ba nan aka tsaya ba, babu iska balle guguwa a duniyar Wata. Wannan tasa duk inda ka taka a saman Wata, gurabun sawunka zasu ci gaba da kasancewa a wurin, tsawon zamani. Har zuwa yau akwai gurabun takun wadanda suka ziyarci duniyar Wata tun shekarar 1969 a Kumbon Apollo 11. A karshe, akwai buraguzan taurarin da rayuwarsu ta kare (watau Meteorite) masu shawagi a saman Sararin Samaniya, wadanda kuma ke shigowa wannan duniya tamu lokaci-lokaci. Ire-iren wadannan buraguzai ne ke afkawa cikin Wata a lokuta dabam-daban, iya gwargwadon girmansu. Don haka Malaman Kimiyyar Sararin Samaniya suka ce galibin ramuka da tsagan da ke jikin Wata sun samo asali ne sanadiyyar illolin da wadannan buraguzai masu shawagi a can sama ke yi a saman Wata. Wannan shine dan abinda zai samu na bayanai kan yanayin da Wata ke rayuwa a ciki.

Daga Ina Wannan Hoto Ya Fito?

Bayan takaitaccen bayanin da muka samu kan Wata, ya kamata mu dawo kan wannan hoto da ke ta yawo a Intanet, da kuma alakarsa da mu’jizar tsagewar Wata a lokacin Manzon Allah a Makka. Daga ina wannan hoto ya fito? A iya bincike na, ban samu wata alama da ke nuna cewa wannan hoto ya samo asali ne daga Hukumar NASA ba. Na shiga gidan yanar sadarwar hukumar na tsawon lokaci, amma ban samu wani bayani makamancin hakan ba. Labarin da na samo a wasu gidajen yanar sadarwa, mai kokarin hada alaka a tsakanin hukumar NASA ko masu binciken da suka yi wannan tafiya, da wannan hoto, shine wanda wani bawan Allah dan kasar Ingila mai suna Dawood Mousa Biskok, shugaban Jam’iyyar Musulunci ta Burtaniya, (watau British Islamic Party), ya bayar lokacin da wani babban malami masanin Kimiyyar Sararin Samaniya dan kasar Masar ya kai ziyara Ingila.

Wannnan bawan Allah yace ya dade yana ta bincike kan addinan duniya, da neman wanda zai bi. Yana cikin hakan ne wata rana wani musulmi ya bashi kyautar Kur’ani mai tarjamar turanci, don ya karanta. Budewarsa ke da wuya, sai yayi arba da shafin da ke dauke da ayoyin da ke tabbatar da tsagewar Wata (a farkon suratul Kamar). Yace bayan ya karanta wannan shafi, sai yace: “kai, duk wannan tatsuniyoyi ne”. Yace “sai na jefar da littafin kawai, na kama sabga na.” “Wata rana ina zaune ina kallon wani shiri mai nasaba da fannin kimiyyar Sararin Samaniya a talabijin BBC, cikin shekarar 1978, inda mai gabatar da shirin ya gabatar da wasu masana kan wannan fanni daga kasar Amurka, sai lamarin ya sake dawowa. A cikin hirar da yake yi dasu ne har bayani ya fado kan ziyarar da hukumar NASA na kasar Amurka ta shirya don kai ziyara a shekarar 1969.” Wannan bawan Allah yaci gaba da cewa: “sai mai gabatar da shirin ke tambayarsu cewa, ‘shin ba almubazzaranci bane a ce hukumar Amurka ta kashe dala biliyan dari don wannan bincike, a yayin da akwai miliyoyin mutane masu kwana da yunwa da cututtuka a duniya?’” Yace sai daya daga cikin wadannan masana yace masa ba al’mubazzaranci bane. Idan an ga yawan kudin, a cewarsa, to ya kamata a san cewa a daya bangaren kuma, hukumar taci nasarar gabatar da binciken da ya gasgata hasashen da aka dade ana yi. Wannan sakamakon bincike kuwa, inji su, shine, sanadiyyar wannan tafiya ko ziyara da aka kai zuwa duniyar Wata, an gano cewa lallai a wasu lokuta ko shekaru masu yawa da suka wuce, Wata ya taba rabewa gida biyu, sannan ya sake hadewa. Suka ce an gano hakan ne kuwa ta hanyar alamar tsaga da ke jikin Watan.

“Ina jin haka”, a cewar Dawood Mousa Biskok, “sai kawai nayi maza na dauko Kur’anin da aka taba bani kyauta, na budo shafin da na taba karantawa. Nan take, sai naga tabbacin abinda wadannan mutane suka binciko. Ga shi Allah ya tilasta Amurka ta kashe biliyoyin daloli don gabatar da binciken da ke tabbatar da gaskiyar littafin Musulmai. Wannan yasa na musulunta.” Har zuwa lokacin da nake wannan rubutu, Dawood Mousa Biskok na raye, kuma har yanzu shine jagorar Jam’iyyar Musulunci da ke kasar Burtaniya. Wannan labari, kamar yadda mai karatu ya gani, bai rasa alaka da samuwar wannan hoto a Intanet tsawon shekarun da suka gabata. Amma kamar yadda na sanar, ban samu bayanai na hakika masu nuna alakar da ke tsakanin hoton da hukumar NASA ba. Amma na dada fadada bincike kan halittar Wata baki dayanta, ban samu bayanin da ke nuna cewa wannan alamar tsaga (da ma wasu masu yawa da suka fi wanda ke jikin hoton nan), alama ce da ke nuna cewa Wata ya taba tsagewa sannan ya koma yadda yake ba. To amma tunda hukumar NASA bata taba fitowa fili ta karyata wannan labari ko hoto da ake ta yadawa ba, sannan kuma ga wannan labari na shugaban Jam’iyyar Musulunci da ke Burtaniya ya shahara sosai, shi ma ban samu bayanai da ke nuna ta karyata ba, shi yasa wasu ke ganin akwai alaka mai karfi a tsakanin hoton da abinda ake riyawa. Amma kafin mu yanke hukunci, zai dace mu duba wasu ka’idoji ko al’amura guda uku masu nasaba da fannin kimiyya da mu’jiza.

Alakar Kimiyya da Mu’jizar Annabawa

Wannan shi ya kawo mu ga duba alakar da ke tsakanin fannin kimiyya, watau Science a bangare daya, da kuma Mu’jizar Annabawa watau Prophetic Miracle, a daya bangaren. Wannan sharhi ne zai iya taimaka mana wajen sanin tasirin abubuwan da ke faruwa a duniya ko a duniyar Wata, wadanda suka danganci tsarin kimiyya tsantsa, da kuma abubuwan da ke faruwa na mu’jiza da Annabawan Allah ke yi, wanda ya sha karfin fahimta da binciken duk wani mai bincike. Hakan har wa yau zai iya taimaka mana wajen fahimtar tsaga da ke jikin Wata a halin yanzu: shin, tsaga ne na yawan shekaru, saboda tasirin muhallin da yake ciki, ko kuwa alamar tsagewar da ya taba yi ne sanadiyyar Mu’jizar Manzon Allah (SAW), lokacin da ya bashi umarni har ya rabe gida biyu a gaban kafiran Makka, suna gani? Mu je kasar Siriya.

Dakta Muhammad Ratib Nablusi, daya cikin malaman kasar Siriya, ya kawo bambancin da ke tsakanin Kalmar “Sharhi ko Bayanin Tsarin Kimiyya” (Scientific Explanation), da “Mu’jizar Kimiyya” (Scientific Miracle), da kuma Kalmar “Mu’jizar Annabawa” (Prophetic Miracle). Daktan yayi wannan sharhi ne cikin laccar da ya gabatar kan wannan lamari a shekarun baya. A cewar Malamin, “Sharhin Tsarin Kimiyya” shine yin bayanin wani abu da ya auku a kimiyyance, a tsari ko al’adar rayuwa. Ire-iren wadannan sun hada da ruwan sama, da yadda yake samuwa, da tsarin rayuwar taurari, da zazzabin Wata ko Rana (Moon/Solar Exclipse) da dai sauran makamantansu. A samu masanin kimiyya yayi sharhi kan yadda wadannan abubuwa ke yiwuwa ko faruwa, shi ake kira “Sharhin tsarin Kimiyya.” Dakta Ratib ya kawo wasu misalai da kowa zai iya fahimta cikin sauki. Da farko yace lokacin da Ibrahim, dan Manzon Allah (SAW) ya rasu a Madina, daidai lokacin ne aka samu yanayin kisfewar rana ko husufin rana a takaice. Sai mutane suka kama surutu suna cewa rana tayi husufi ne sanadiyyar rasuwar wannan jariri. Nan take sai Manzon Allah (SAW) ya mike ya fahimtar dasu abinda ya faru. Cewa da Rana da Wata duk ayoyin Allah ne; basu yin husufi don rayuwa ko mutuwar wani. Abinda Manzon Allah (SAW) yayi a nan shine “bayani ko sharhin tsarin kimiyya”. Ma’ana, wani abu ne da ke faruwa lokaci-lokaci, sanadiyyar tsari da yanayin da Allah ya dora duniya a kai. Ba wai karama bace ko mu’jiza ta musamman.

Misali na biyu shine wani abinda ya faru dashi Daktan, lokacin da yaje yin umara a Makka. Yana isa Makka, sai yaji wasu mutane suna cewa idan yamma tayi, magriba ta gabato, wani haske na hudowa daga saman kabarin Manzon Allah (SAW) a Madina, zuwa sama. Wannan haske, a cewar masu bayar da wannan labari, mu’jizar manzon Allah ce mai tabbatar da darajarsa har yanzu. Bayan ya gama umara, sai ya wuce Madina don yin ziyara. Yana shiga masallacin, daidai lokacin sallar magriba, sai ya tarar wani malami na gabatar da karatun fikihu a masallacin, kamar yadda aka saba. Yace bayan malamin ya gama karatu, sai yayi sanarwa cewa, sun yi hira da Sarkin Madina, inda Sarkin ya sanar dashi cewa hukumar Saudiyya ta sanya wata fitila mai haske, mai kuma dauke da sinadaran haske nau’in Laser, wadda ke cillawa cikin Sararin Samaniya, don ya zama alama ga direbobin jirgin sama a lokacin da suke halin tafiyarsu a sama. Da zarar sun zo wajen wannan haske, zasu kauce, don kada su wuce ta saman kabarin Manzon Allah (SAW). Wannan, a cewar Dakta Ratib, sharhin kimiyya ne yaji a bakin wannan malami. Ma’ana ba mu’jiza bace, sabanin labarin da yaji a Makka.

Kalma ta biyu, watau “Mu’jizar Kimiyya” (Scientific Miracle), shine faruwar wani abu a kimiyyance, wanda ba a iya gane tasirin abin ko hikimar da ke tattare cikinsa sai bayan bincike ko lokaci mai tsawo. Ma’ana, ba wani abu bane da kowa zai iya ganewa ba nan take, sai wadanda suka shahara a fannin kimiyya, kuma sai bayan lokaci da bincike mai tsawo. Misali, a cikin hadisan Manzon Allah (SAW) an nuna cewa idan kuda ya fada cikin abinci ko abin sha, to a dulmuya shi cikin abin da ya fada ciki baki daya, sannan a ciro shi a yar. Domin a dayan fiffikensa akwai cuta, wacce da ita yake fadawa cikin duk abinda zai fada. A daya fiffiken kuma, wacce yake dage ta sama, akwai maganin wannan cutar. Kenan idan aka dulmuya shi baki daya, anyi maganin cutar kenan. Hadisi irin wannan, da sauran makamantansa, ba kowa ke iya hararo gaskiyar abinda aka fada ba, sai wanda ya gabatar da bincike na musamman kan hakan, bayan lokaci mai tsawo. Amma a lokacin da aka fade su, sai dai ayi imani dasu kawai. Wannan mu’jiza ce ta kimiyya wacce ta sha karfin tunanin dan Adam sai bayan lokaci mai tsawo yake gano tabbacin hakan.

Misali na biyu kuma shine, akwai lokacin da wasu mahaya kumbo suka haura can saman Sararin Samaniya, ma’ana suka ketare dukkan iskar da ke saman wannan duniya mai tazarar kilomita sittin da hudu (64km). Suna gama wuce wannan tazara, sai suka shiga yanayin da basu ganin komai sai duhu. Nan take daya daga cikinsu yace: “mun makance; bamu gani”. A daidai wannan lokaci da yake sanar da masu lura da tafiyarsu a tashar da suka baro a duniya, sai aka yi dace akwai wani Balaraben kasar Masar masanin Kur’ani kuma masanin Kimiyyar Sararin Samaniya a wajen. Yana jin haka, sai yace musu “wannan Mu’jizar Kimiyya ce”. Da aka tambaye shi me yake nufi da hakan, sai yace ai Allah Ya fadi hakan cikin Kur’ani, inda yake cewa: “…kuma da mun bude wata kofa daga sama a kansu har suka wuni a ciki suna takawa (zuwa sama). Lallai ne da sun ce, “ai ba abinda aka yi sai rufe mana idanu kawai. A a, mu mutane ne da aka sihirce.” (Suratul Hijri: 14-15). Me ya faru? Wannan bawan Allah dan kasar Masar ya tuna cewa, da zarar ka wuce sararin wannan samaniya tamu bayan tafiyar tazarar kilomita sittin da hudu, to ba abinda zaka samu sai duhu mai tsanani. Wannan tasa wancan bawan Allah da ke cikin kumbo yace “mun makance”, saboda sun daina ganin haske. Daman iskar da ke sararin wannan duniya ce ke rarraba hasken da ke zuwa daga jikin rana. Wannan tsari, wanda ake kira Scattering of Light a Kimiyyar Sararin Samaniya, yana samuwa ne a tazarar tafiyar da bata wuce kilomita sittin da hudu ba daga doron kasa. Da zarar ka wuce wannan tazara, ba abinda ya saura sai duhu. Wannan misali na biyu na nuna mana ne karara, cewa Allah ya tabbatar a Kur’ani cewa da za a bude wa kafirai wata kofa zuwa sama suna ta tafiya a cikinta, zasu kai wani tazara da zasu daina ganin haske. Wannan zai sa su ce, “lallai sihiri aka mana”. To amma a lokacin tunda ba a yi haka ba, babu wanda zai iya tabbatar da gaskiyar hakan. Sai bayan shekaru sama da dubu daya aka samu bincike da ya tabbatar da hakan. Wannan, a cewar Dakta Ratib, “Mu’jiza ce ta Kimiyya”.

Sai kalma ta uku, watau “Mu’jizar Annabawa”. Kalmar mu’jiza asali kalmar larabci ce, wacce Hausawa suka aro don nufin abin da take nufi a larabce, ma’ana: “wani abin da ya sha karfin tunani da hankalin dan Adam; ya gagare shi wajen karfi ko tunani”. Mu’jiza sifa ce ta Annabawa, su kadai Allah ke ba wannan baiwa don gamsar da mutanensu cewa daga Allah suke, ba su suka aiko kansu ba. Misalin mu’jiza na nan barkatai. Akwai sandar Annabi Musa (AS), wacce ke zama macijiya, akwai taguwar Annabi Salihu (AS), da dai sauransu. Mu’jizar Manzon Allah (SAW) mafi girma ita ce littafin da Allah Ya aiko shi da shi, watau Al-Kur’ani mai girma. Sannan akwai Isra’i da Mi’raji da Allah yayi dashi zuwa saman sama na bakwai. Dukkan wadannan mu’jizozi ne wadanda suka sha karfin wani dan Adam ya iya bayanin yadda suka auku. Misali, babu wani Malamin Kimiyyar Sararin Samaniya da ya isa yayi bayanin tsarin tafiyar da Manzon Allah yayi daga Masallacin Baitul Makdisi zuwa sama, a kimiyyance. Wannan, a turance, shi ake kira Prophetic Miracle. A wannan tsari, duk abinda ya faru na mu’jiza a kimiyyance (kamar tafiyar da Manzon Allah yayi zuwa sama), abu ne da ba wanda zai iya fahimtar yadda abin ya faru, kuma ba lale bane a ga wani gurbi bayan faruwar mu’jizar. Misali, akwai lokacin da Manzon Allah (SAW) ya sunkuyar da yatsan hannunsa kasa, ruwa yayi ta zuba sahabbai suna sha, wusa na alwala da ruwan. Hakan ya faru ne lokacin da aka je daya daga cikin yake-yaken da aka yi, inda aka yi karancin ruwa. Bayan kowa ya gama amfana da ruwan, sai Manzon Allah (SAW) ya yarfar da yatsansa, ruwan ya dauke. Wannan abu da ya faru bai sa an ga wata alama ko huji a yatsansa ba, saboda “mu’jiza ce ta annabta”, ba wani abu bane da ya saba faruwa ga mutane a al’adance.

Tantancewa Tsakanin Hujjoji

Daga bayanan da suka gabata, a bayyane yake cewa tsagewar Wata mu’jiza ce ta Annabta, ba wai mu’jiza ta Kimiyya ba. Domin babu wanda zai iya gano yadda tsagewar ta kasance, balle ya san kimar abin. To amma kuma meye alakar hakan, da wannan hoto da ake ta yadawa? A iya karatu da bincike na, idan ka dauke wancan labari na Dawood Mousa Biskok, inda wadancan masana Kimiyya suka tabbatar da cewa an gano alamar tsagewar Wata a wasu lokuta ko shekaru masu yawa da suka wuce a rayuwarsa, babu wani bayani na kimiyya tabbatacce da ke nuna gaskiyar abinda wannan hoto ke dauke dashi, duk kuwa da shahararsa. Sabanin haka ma, abinda galibin bayanai ke tabbatarwa a kimiyyance shine, galibin tsage-tsagen da ke jikin Wata a halin yanzu, sun samo asali ne daga yawan buraguzan taurari masu tarwatsewa suna afkawa cikin wasu duniyoyin da ke makwabtaka dasu. Ire-iren wadannan buraguzai su ake kira Meteriote a turance. Don haka tsagar da ke jikin Wata, ko kadan, bata da alaka da wannan lamari na mu’jiza.

Bayan haka, malaman kimiyya sun kimanta zurfin tsagar da ke jikin Wata a halin yanzu da cewa ta kai tafiyar nisar kilomita dubu goma sha uku. Amma idan muka dubi hoton da ke like a nan, zamu ga cewa alamar da ke jikin Watan, ko kadan bai shiga ciki ba. Kamar ma zane ne kawai, ba tsaga ba. Har wa yau, wannan hoto, idan muka dube dashi da kyau, karshenta ma wani ne ya zauna ya zana shi da manhajar zane na kwamfuta, watau Graphics Software, bayan wancan labari da masana suka bayar. Ba lale bane ya zama hoto ne na gaskiya da aka dauko daga can ba.

A karshe kuma idan aka ce abu kaza mu’jiza ce, to akwai siffofi guda uku da suka kamata a gane hakan. Na farko shine ya zama ya sha karfi da tunanin mutane, babu wanda zai iya yin shi duk cikin mutane sai Annabi ko wani Manzo da Allah ya aiko. Idan muka dubi tsagewar Wata, zamu ga haka ne. Na biyu kuma ya zama babu wani zamani da za a kaiwa, ko mataki na ilimi, da wani zai ce ya gano wani abu daban cikin abinda ya faru, sabanin abinda ya faru din. Abu na karshe kuma, wanda ke da nasaba da wannan hoto shine, ba ka’ida bace cewa idan mu’jiza ta auku kan wani abu, dole sai an samu alama bayan aukuwarta. Kamar yadda ba a samu Wata alama ba a yatsar Manzon Allah (SAW) bayan bubbugar ruwan da ya faru, kamar yadda bayani ya gabata a kai. Don haka ba dalili bane cewa don an ce an samu alama a jikin Wata, wani yace “dole ne ya zama alamar tsagewar da yayi ne lokacin Manzon Allah (SAW)”. Ba hujja bace wannan.

Kammalawa

A karshe dai, ma iya cewa wannan hoto bai da alaka da rahoton binciken da wannan hukuma ta NASA tayi, shekaru sama da arba’in da suka gabata. Ta yiwu wani ne ya zauna ya zana hoton, don suranta abinda wadancan masana suka tabbatar a hirar da talabijin BBC yayi dasu a shekarar 1978. Sannan ba hujja bace cewa lallai alamar da ke jikin Wata ta samu ne sanadiyyar tsagewar da yayi lokacin Manzon Allah (SAW). Domin ba ka’ida bace cewa idan mu’jiza ta auku dole sai an samu alama a gurbinta. Tabbas Allah na iya tabbatar da wannan alama a jikin Wata, amma ba dole bane sai an samu alamar sannan abinda ya faru zai zama gaskiya. Wannan mu’jiza da ta auku: ko da alama ko babu wata alama a jikin Watan, mu munyi imani da aukuwarta.

No comments:

Post a Comment