Wednesday, November 2, 2011

Yadda Ruwa ke Samuwa, Da Sinadaran da ke Dauke Cikinsa

Fahimtar Ka'idojin Kimiyya da Nassoshin Kur'ani

Duk wanda ka tambaye shi daga ina ruwa ke samuwa, amsar farko da zai fara baka ita ce: "Daga sama ne." Wannan amsa, duk da cewa haka take, amma ba iyakanta ba kenan. A takaice ma dai, ruwan sama wani yanki ne ko daya ne cikin hanyoyin da ruwa ke samuwa. Kai ba ma wannan ba, abin da mai karatu zai yi mamakin ji shi ne, ruwan sama wata hanya ce ko wani tsari ne na maimaituwar samuwan ruwa a wannan duniya da muke rayuwa a cikinta. Abin da zai tabbatar mana da wannan bayani kuwa shi ne, idan muka yi nazarin ayoyin Kur'ani da kyau, za mu ga cewa idan ana maganar asali ne, to ma iya cewa asalin farko na ruwa shi ne tekuna, da koguna da muke da su a duniya. Bayan Allah ya tsage wannan duniya a halittar farko aka samu sama da kasa, daga baya sai Allah ya kintsa wannan kasa tamu zuwa yanayin da zai dace da zamantakewarmu. Wannan kintsawa kuwa ya samu ne ta hanyar baje kasar, da sanya ta ta zama mai taushi, mai saukin mu'amala, da kuma samar mana da tekuna, da koguna, da rafuka, sannan kuma aka kintsa sama – ta hanyar samar da giragizai da iska – don tabbatar da tsarin samar da ruwa ko maimaituwarsa a duniya. Wadannan bayanai, idan mai karatu zai natsu ko ya tambaya, za a samo masa su a cikin Suratun Naazi'aat da ke Kur'ani mai girma.

Idan muka fahimci haka a karon farko, sai tambaya ta biyu ta biyo baya: shin, ruwa da muke samu daga sama, wani sabon ruwa ne ful, ko kuwa ruwan da muka sani ne yake maimaituwa? Idan muka yi la'akari da sakamakon binciken malaman kimiyya, za mu ga cewa lallai ruwan da muke samu daga sama, ruwa ne da yake maimaituwa, a wani sabon yanayi mai cike da nishadi da sabuntawa. Watakila mai karatu yace: "Shin, da gaske wannan magana haka take cikin Kur'ani?" Amsar ita ce eh. Domin a cikin Kur'ani Allah ya sanar da mu ne cewa shi ne yake saukar da ruwa daga sama, don amfaninmu da dabbobinmu da abin da muke shukawa a kasa. Ba wai yanayin ruwan yake sanar da mu ba, sai dai saukarsa, da cewa shi ne mai saukarwa. Kuma idan ya ga dama sai ya kame ruwan, kamar yadda mun sha ganin hakan. Kafin mu yi nisa, a nan nake ganin dacewan sanar da masu karatu wata ka'idar ilmi tsakanin binciken kimiyyar zamani, da kuma nassoshin da ke cikin Kur'ani. Wannan zai taimaka mana matuka wajen fahimtar binciken malaman kimiyya, da kuma fahimtar nassoshin Kur'ani din.

Duk ayoyin da ke bayanin yiwuwa ko samuwa ko faruwan wasu abubuwa a duniya masu alaka ta kai-tsaye da fannin kimiyya, sakon da ayoyin ke kokarin isar mana a takaice shi ne mu san wanda ke haddasa su, ko yake da ikon sanya su faruwa, ko yake da ikon kame su don hana su tasiri. Wannan tsarin mulki ne na Ubangiji, wanda ya taskance yadda komai ke faruwa karkashin ikonsa, da yadda yake tasarrafin abubuwa cikin mulkinsa. Bayan wannan, har wa yau Allah ya zayyana yadda komai zai faru, da kuma dalilan da za su sa komai din ya faru. Samuwar wadannan dalilai ne ke sa mai ganin abin a fili ya ga faruwarsu, har a karshe, idan ba mai imani bane shi, ya dauka wadannan dalilan zahirin su ne kadai ke sa wannan abin ya faru. Wannan tsari na haddasa faruwan abubuwa sanadiyyar dalilai bayyanannu, shi ake kira "Cause and Effect Theory" a kimiyyance.

Mu sani, Kur'ani ba littafin kimiyya bane, duk da cewa akwai bayanai masu alaka da kimiyya sosai a ciki. Allah ya saukar da shi ne don shiriya, don a bauta masa, ba wai sinadaran rayuwa ba. Wannan ne ma yasa littafin ya zo a tsarin sura-sura, ba babi-babi ba kamar yadda littattafan kimiyya suke. Kuma kasancewar fannin kimiyya ba wani fanni bane da kowa zai iya gudanar da bincike har ya gano abin da aka fada a Kur'ani, kuma bincike a fannin kan dauki lokaci mai tsawo, sai wasu ke ganin kamar akwai cin karo tsakanin wannan fanni da abin da Kur'ani ke tabbatarwa. Ko kadan babu. Matsalar da ke tsakanin masu gudanar da wannan bincike da Kur'ani, shi ne na rashin imani ko samuwarsa. Galibinsu ba su yi imani da Allah ba, don haka duk binciken da suke yi, ba su danganta sakamakon abin da suka gano ga Allah madaukakin sarki, sai dai ga dalilai na zahiri da suka haddasa abin. Wannan kuwa ba karamin hadari bane.

To amma kowane musulmi ya san cewa Allah ne mahallicin komai, kuma shi ne yake sarrafa duniya baki daya. A matsayinka na makarancin fannin kimiyya ko mai karanta rubuce-rubucen malaman kimiyya, dole ne ka kiyaye wannan ka'ida a kwakwalwarka, don kada ka rudu da dalilan da suke bayarwa kan cewa su ne kadai ke haddasa abin da ke faruwa, ko ke haddasa samuwar wata halitta ko wani yanayi da ke maimaituwa. Bayan dukkan wannan, yanzu za mu shiga bayani kan yadda samuwar ruwa ke maimaituwa a duniya, abin da malaman kimiyya ke kira Water Cycle, ko Hydrologic Cycle. Wannan bayani ne zai tabbatar mana cewa lallai ruwan sama da muke samu a duk shekaru ko damina, ruwa ne da ke maimaituwa a wani yanayi.

Tsarin Maimaituwar Ruwa a Duniya (Hydrological Cycle)

Kamar yadda bayanai suka gabata a baya, ruwan da ake samu a duniya, daga na cikin teku, da wanda ke cikin kogi, da na rafi, da na karkashin kasa, da ruwan sama da muke samu, da tsaunukan kankara na cikin teku, watau Glacier, da Kankaran da ke saukowa daga sama lokacin ruwan sama, da dusar kankara (Ice Pellets, ko Snow) da ake samu a kasashe masu sanyi irin su Rasha da sauran kasashen Turai, duk abu ne guda daya da ke maimaituwa lokaci-lokaci, cikin wani tsari da Allah ya tanada, mai cike da ban mamaki ko al'ajabi. Wannan tsari da ke samar da wadannan nau'ukan ruwa a yanayi uku – narkakken ruwa, da kankara, da tururin iska mai dauke da ruwa – shi ake kira Water Cycle ko Hydrological Cycle a kimiyyance. Wannan tsari yana kunshe da matakai hudu ne muhimmai, masu maimaita shi a duk lokacin da dalilan da ke samar da su suka samu. Bayan wadannan bayanai ne mai karatu zai fahimci yadda ruwan sama ke samuwa, da dalilin da ke sa tekuna da kogi suke yin ambaliya, da yadda ruwa ke taskance kansa a cikin iska cikin yanayin tururi, sannan ya haura zuwa sararin wannan duniya tamu.

Matakin Farko

Wannan shi ne matakin ma'adana, watau lokacin da ruwa ke taskance ko dai a cikin kogi, ko a cikin teku, ko a cikin rafi; a yanayin narkakken ruwa yake ko a yanayin kankara narkakke, watau Melting Ice, da ke cikin teku, ko daskararre. Sai kuma ruwan da ke cikin karkashin kasa mai bubbuga cikin teku. Dukkan wannan ruwa yana cikin ma'adana ne, wanda Allah ya samar da shi don amfanin bayi, kuma shi ne matakin farko na samuwan ruwa a duniya, kamar yadda bayanai suka gabata.

An kiyasta cewa akwai ruwa a yanayin gundarin kankara wanda kauri da fadinsa ya kai nisan murabba'in kilomita 17 (17km2) a nahiyar Antaktika (Antarctica), da nahiyar Greeland. Wadannan su ne wurare masu matukar sanyi a duniya. Malaman kimiyya sun ce ba a samun idaniyar ruwa ko ruwan karkashin kasa a wadannan nahiyoyi, saboda daskarewan ruwan a karkashin kasa. Shekaru dubu 22 da suka wuce ne aka yi mummunar sanyi a wadannan wurare, inda har kankara ta mamaye ilahirin kasar Kanada, da Arewarin Amurka, da Arewacin Turai, da kuma Saiberiya. Wannan kankara ta mamaye wuraren da aka kiyaska sun yi fadi da nisan murabba'in kilomita miliyan 20 (20m km2).

Daga cikin ruwan da ke karkashin kasa akwai wadanda suke cikin duwatsu. Wadanda suke cikin duwatsu masu taushi, watau Sedimentary Rocks, wadanda kuma aka kiyasta cewa sun mamaye kusan kashi 20 zuwa 40 na duwatsun da suke cikinsu. Samuwar ruwa a wadannan ma'adanai – na kogi, da teku, da rafi, da kankara, da karkashin kasa – shi ne matakin farko da ke sawwake samuwar mataki na biyu, don haddasa tsarin maimaituwar ruwa a duniya.

Mataki Na Biyu

A yayin da ruwa ke taskance cikin wadancan ma'adanai na teku ko kogi ko rafi da dai sauransu, a kullun ruwan na raguwa, yana bin iska a yanayin tururi, har ya haura zuwa cikin wata ma'adana da ke cikin sararin wannan duniyar ta mu. Wannan ma'adana ita ake kira Water Vapour, kamar yadda bayani ya zo a makon baya. Haka ma kankaran da ke narkewa a cikin teku, duk wannan tsari yake bi. Wannan tsari na bacewar ruwa ta hanyar bin iska a yanayin tururi, shi ake kira Evaporation a turancin kimiyya. Haka ruwan zai ta taruwa zuwa cikin wancan ma'adana ta sararin duniya. Bayan wannan tururin iska da ke samuwa daga teku ko kogi, akwai wani tururin da ke fitowa daga ramukan jikin ganyayyaki da ciyayi da kuma kasa mai danshi (ko duk inda aka zubar da ruwa a kasa), yana haurawa zuwa sama shi ma. Wannan tsari na bacewar ruwa daga jikin ganyayyaki da ciyayi don bin iska a yanayin tururi, shi ake kira Transpiration a turancin kimiyya. Dukkan wannan tururi na ruwa da ke bin iska zuwa sama, asalin ruwa ne da ke ma'adanar da muke da su a wannan duniya – ko dai teku ko kogi ko kankara ko wanda ke jikin sauran halittu.

Malaman kimiyya suka ce a kullum ana samun adadin ruwa da yawansa ya kai 1,200 a ma'aunin kimar ruwa, watau 1,200 cubit km. A kullum sai wannan adadi na yawan ruwa a yanayin tururi ya bi iska zuwa ma'adanar ruwa da ke sararin duniyarmu. Don haka malaman kimiyya suka ce, da a ce za a samu tangarda har wannan adadi ya daina haurawa sama, nan da kwanaki 10 ma'adanar da ke sararin duniyarmu za ta kafe, a rasa ruwa a cikinta. Wannan ke nuna mana a fili karara cewa, Allah ya tanada wa bayinsa dukkan abin da za su dogara da shi na arziki, tare da tsarin samuwarsa. Wannan zance yana nan cikin Suratul Hijri – inda Allah ya ce dukkan wata arziki taskarta na wajensa ne, kuma ba ya saukar ta da ita ga bayinsa sai iya gwargwadon yadda zai zama maslaha a gare su.

Manyan dalilai na fili da ke sawwake wannan tsari na bacewar ruwa cikin iska a yanayin tururi da ke haurawa zuwa ma'adanar sararin duniyarmu kuwa, su ne tsananin zafin rana da haskenta, da iskar da ke bugawa – a tudu ko a saman teku – da inuwar da ke saman shuke-shuke ko ciyayi, da kuma danshin kasa ko duk inda aka zubar da wani ruwa a nan duniya inda muke rayuwa. Wadannan dalilai ne ke haddasa samuwar wadannan yanayi guda biyu na Evaporation da kuma Transpiration. Kuma wannan mataki ne ke haifar da matakin samuwar ruwa na uku, watau abin da ake kira Precipitation.

Mataki Na Uku

Wannan mataki kuwa shi ne matakin saukar ruwa daga sama, ko Precipitation kamar yadda malaman kimiyya ke ambatonsa. Kafin mu ci gaba, na san da yawa daga cikinmu mun sha jin cewa, a kimiyyance abin da ke haddasa ruwan sama shi ne tururin teku ko kogi da ke haurawa sama, sannan ya zubo. Sai dai da yawa daga cikinmu muna karyata wannan ka'ida ta kimiyya, amma kuma hakan shi ne abin da yake kusa da daidai. Babban kuskuren da muke yi kuwa shi ne, muna dauka cewa ruwan da ke zubowa daga sama, yana zuba ne daga asali ko jikin bangon saman da muke gani. Wannan kuskuren fahimta ne babba. Domin hatta a cikin Kur'ani mai girma Allah ya ambaci jihohi guda biyu ne wajen zuban ruwan sama. Amma kuma dukkan malaman tafsiri sun yarda cewa jihohin nan guda biyu da Allah ya ambata, abu ne guda daya, ko jiha daya ne yake nufi. Allah ya ambaci cewa shi ne yake saukar da ruwa "daga sama". A wasu wuraren kuma ya ambaci cewa, shi ne ya ke saukar da ruwa "daga giragizai." Malaman tafsiri suka ce ya ambaci sama ne don nufin alaka da nasaba, dangane da inda dan adam ke zaune. Amma asali ruwa na zuba ne daga jikin giragizai ba daga can asalin sama ba. Amma an ambaci sama ne saboda a can giragizai suke; ma'ana a saman dan adam. Bayan nan, da yake zamani ya kawo samuwar jirgin sama, duk wanda ya taba hawa jirgin sama yayi doguwar tafiya, zai ga cewa sai jirgin ya "keta hazo" ko "giragizai" kafin ya daidaita a sama ya ci gaba da tafiya. Abin da yin hakan ke nufi kuwa shi ne, da za a yi ruwa a duniya – a kowane bangaren duniya ne kuwa – wadanda ke cikin jirgin nan ba za su sani ba sai sun sauka. Domin ruwan daga jikin girgije yake zuba, shi kuma jirgin ya wuce inda girgijen yake. Idan mun fahimci wannan tsari, sai mu koma kan bayaninmu.

Yadda Ruwan Sama ke Samuwa

Da zarar wannan ma'adana mai dauke da danshin ruwa a yanayin tururi (watau Water Vapour) ta tumbatsa, sai ruwan ya sake saukowa kasa a yanayi uku. Yanayin farko shi ne yanayin ruwan sama, kamar yadda muka sani. Yanayi na biyu kuma shi ne yanayin kankara; ko dai wanda ke zubowa a tare da ruwan sama (watau Ice Pellets), ko kuma dusar kankara da ke zuba a wasu kasashe inda sanyi ya kai matuka (watau Snow). Sai yanayi na uku kuma shi ne yanayin raba; watau danshin ruwa mai sanyi da ke zuba cikin dare (ko Dew kimiyyance). Wannan ruwa da ke zuba, yana zuba ne a kullum, kamar yadda wancan tururin danshin ruwa da ke haurawa ma'adanar ruwa a sama a kullum. Bayan nan, malaman kimiyya suka ce a kowace rana a kan samu a kalla adadin yawa da fadin ruwa a ma'aunin yawa, wajen 300 (watau 300 Cubic Km). Kuma cikin wannan adadi na ruwa da ke zuba a matsayin ruwan sama, ko kankara, ko raba, kashi daya cikin uku (⅓) ne kadai ke zuba a gundarin kasa, sauran kashi biyu bisa ukun (⅔) na zuba cikin teku ne, ko kogi, ko kuma rafukan da muke da su a duniya – su sake komawa cikin sama a yanayin da bayaninsa ya gabata. Sai dai kuma, na san mai karatu zai so sanin yadda ruwan sama ke sauka, a kimiyyance.

Kamar yadda bayani ya gabata, ruwan da ke zuba daga sama shi ne ruwan da ke makare cikin ma'adanar danshin ruwa da ke yanayin tururi a sararin wannan duniyar tamu, watau Water Vapour kenan. Daga nan sai su zubo, amma ba kai tsaye suke zubowa ba. Domin ruwa, kamar yadda yake, yana zubowa ne daga jikin giragizai, watau Clouds a turance. Su wadannan giragizai a sama suke, haka ma wannan ma'adana ta sararin duniyarmu. Sai dai kuma, sabanin giragizai da dan adam ke iya ganinsu da ido, ita wannan ma'adana a yanayin iska take, a makare da ruwa cikin yanayin tururi mai danshi.

Tsakanin sararin samaniyar wannan duniyar ta mu da saman tekuna, akwai iska nau'uka daban-daban. Akwai iskar da ke kada ruwan teku har a samu taguwar ruwa, sanadiyyar juyawar bigiren rana da wata. Wannan iskar kan yi sanadiyyar ambaliyar ruwa. Akwai iskar da ke kintsa kasar da muke takawa kafin zuwan ruwan sama. Akwai iskar da Allah ke kado ta zuwa duniya a matsayin bushara gare mu don samuwar ruwan sama. Akwai iskar da ke taskance ruwa a yanayin danshi kamar yadda bayanai suka gabata. Akwai iskar da ke hado kan giragizai waje daya. Akwai iskar da ke yin barbaran giragizai, har su cika da ruwa, sannan ruwan ya zubo kasa. Akwai iskar da ke rarraba giragizan da ke shake da ruwa zuwa jihohin duniya daban-daban, iya yadda Allah ke so. Sannan kuma akwai nau'in iskar da ke kora giragizai masu dauke da ruwa. Dukkan wadannan nau'ukan iskoki suna nan, kuma ba iyakansu ba kenan, sai dai wadanda suka danganci ruwan sama ne wadannan. Kuma wani abin sha'awa shi ne, dukkansu Allah ya yi bayaninsu, da yanayin aikinsu a cikin Kur'ani.

Da zarar Allah ya nufi saukar ruwa, sai ya aiko iskar da za ta kintsa kasa don karban ruwan da ke tafe. Sannan sai iskar da ke bushara ta biyo baya. Ita ce iskar da ke zuwa da karfi, cike da kura ko tarkacen da take dibowa. Sakon da take aiko mana shi ne, "kowa ya kintsa kayansa, ga ni'ima nan tafe." Wannan iska ce ta bushara, musamman ga al'ummar da aka de ba a musu ruwa ba, ko suke fama da fari. Daga nan kuma sai wannan iska mai makare da ruwa a yanayin danshi ta kada, sannan ta yi barbarar giragizai, ta cika su da ruwa. Nan take sai ka ga giragizai sun yi baki kirin, sai kaji rugugi, sai cida; ga kuma iskar bushara na bugawa. Daga nan sai iskar da ke kada giragizan su fara nasu aikin, sai ruwan sama ya fara zuba. Daga nan sai iskar da ke rarraba wannan ruwa ta biyo baya, ta rika warwatsa giragizan zuwa jiha ko bigiren da aka nufe su da samun wannan ni'ana. Nan take sai ka ga hadari ya fara zama fari daga launin bakin da yake a farko. Saboda ruwa ya fara zuba. Dangane da bayanan da suka shafi nau'ukan iska, da yadda suke barbarar giragizai, da rarraba su, da kora su, mai karatu na iya duba wadannan ayoyin Kur'ani: Suratul Hijri, aya ta 22; A'raaf, aya ta 57; Noor, aya ta 43 da 45; Furqaan, aya ta 48 da 49; Room, aya ta 48.

Ta yiwu mai karatu ya ce me yasa ruwan sama ke zuwa da kankara, kuma ruwan da sanyi yake zuwa, haka ma kankaran? Kuma hatta raba da ke sauka cikin dare, da sanyi yake zuwa. Me yasa? Fahimtar haka abu ne mai sauki. Domin idan ba a mance ba, a kasidar farko na sanar da mu cewa wannan duniya ta mu Allah ya ajiye ta ne a wani bigire matsakaici, wanda ke dauke da yanayin zafi ko sanyin da suka yi daidai da yanayin dabi'a da rayuwar halittu. Wannan yanayin zafi da sanyi su ne suke sa duk wani ruwa da ya bi iska ya haura sama a yanayin tururi, ya zama mai sanyi, a wasu lokuta ma har ya daskare. A wasu duniyoyin, musamman duniyar Satun, babu ruwa narkakke, saboda yanayin wurin ya wuce kimar da za a samu ruwa narkakke kamar yadda muke da shi a duniyarmu. Don haka duk ruwan da ke makare a sararin duniyar Satun, gundarin kankara ne, wanda ba a tunanin ranar fashewa balle narkewarsa. Dangane da duniyarmu kuwa, tunda akwai sabanin yanayi madaidaici, don haka muke samun ruwa narkakke da wanda ke yanayin kanka, da kuma raba, da ma ruwan da ke yanayin danshin tururi da ke bin iska.

Har wa yau, mai karatu na iya tambayar dalilan da suka sa ake samun canjin yanayin damina tsakanin kasashe, ko nahiyoyin duniya. Shi ma amsar wannan ba nesa take ba. Babban dalilin da ke haddasa hakan shi ne jujjuyawan lokutan dare da yini, da samun canji a yanayin bigiren rana da wata. Da kuma tsarin juyawan duniya a kwanakin shekara. Wadannan, na tabbata, suna cikin bayanan da muka karanta cikin littafin Dakta Adnan, na Gwagwarmaya kan Ilmin Sararin Samaniya. To, bayan saukar ruwan sama, sai me?

Mataki na Hudu

Kashi biyu cikin uku (⅔) na ruwan da ke saukowa daga sama – a yanayin narkakken ruwa, ko kankara, ko raba - yan zarcewa ne cikin tekuna, da koguna, da kuma rafuka. Kashi daya cikin ukun (⅓) ne kawai ke zuba a saman kasa. Wannan kaso kan gangara cikin tekuna shi ma daga inda ya zuba, kasa tasa iya shanta. Wadannan rafuka sukan cika su batse, daga nan su antayar da raran ruwan zuwa cikin teku. Kamar yadda muka sani, dukkan tekunan duniya a jone suke da juna ta wasu hanyoyi. Sannan dukkan kogunan da ke cikin kasashenmu, da rafukan da ke ciki, duk karshensu yana hadewa ne da wadannan manyan tekuna da ke tsakani ko bayan kasashen duniya. Dukkan kankaran dake fadowa a kasa, sukan narke, kuma ruwan kan gangara zuwa cikin rafuka ko kogunan da muke da su. Da zarar sun antayo cikin tekuna, sai a sake samun maimaituwan wannan tsari kamar yadda bayanai suka gabata a baya. Wannan shi ne mataki na karshe.

Daga bayanan da suka gabata, mai karatu zai ga cewa lallai ruwan sama da ake samu, da sauran hanyoyin samun ruwa a duniya, duk abu ne guda daya, wanda ke maimaituwa, cikin kudura da iradar Ubangiji. A mako mai zuwa za mu ci gaba, inda bayanai za su zo kan nau'ukan sinadaran da ke dauke cikin ruwa; narkakke ne, ko daskararre a yanayin kankara, ko kuma wanda ke yanayin tururi a cikin iska.

No comments:

Post a Comment