Wednesday, February 13, 2013

Neil Armstrong Ya Kwanta Dama



Gabatarwa

"Ban sani ba, ashe ranar 20 ga watan Yuli na shekarar 1969 an harba kumbo Apollo 11 zuwa duniyar wata. Wannan shi ne karon farko da ƙasar Amurka tayi nasara kan wannan aiki da Neil Armstrong ya shugabanta. Daidai wannan lokaci ne har wa yau, aka yi wa shugaba John F. Kennedy kisan gilla. Tun sannan na riƙe sunan kumbo Apollo 11 a bakina, ba tare da sanin abinda hakan ke nufi ba. Na yi ta kwaikwayon marigayi Mamman Shata cikin waƙar da yayi wa kumbo Apollo 11, duk sa'adda aka sanya waƙar a gidan rediyo. Alhaji Mamman Shata ya yi ta yabon wadanda ke cikin wannan kumbo da ya fara zuwa duniyar wata." 

-          Why Astronomy, Dakta Adnan Abdulhamid, FCE, Kano
Daga cikin waɗanda tarihi ba zai taba mancewa da tasirinsu wajen haɓɓaka fannin kimiyya da fasahar sararin samaniya ba a duniya, akwai mahaya Kumbo Apollo 11, wato: Neil Aldrin Armstrong, da Buzz Aldrin, da kuma Michael Collins, waɗanda suka yi bulaguron farko zuwa duniyar wata a shekarar 1969.  Wanda ya fi shahara daga cikinsu shi ne jagorar tawagar, wato Neil Armstrong.  Wannan bawan Allah bai shahara don kasancewarsa jagorar tafiyar kaɗai ba, sai don kwazonsa, da kuma hangen nesansa wajen iya mu'amala da kumbon sararin samaniya a wancan zamani.  Ranar Asabar, 25 ga watan Agusta da ta gabata ne Allah Yayi wa Neil Aldrin Armstrong cikawa, bayan tiyata da aka masa a zuciyarsa, sanadiyyar toshewar hanyoyin jini da yayi fama da shi na wani lokaci.  Ya rasu yana dan shekara 82 a duniya.  A yau za mu dubi rayuwar Neil ne, da tasirin kokarinsa wajen habbaka fannin bulaguro zuwa sararin samaniya baki ɗaya.  Rayuwar Neil za ta haskaka mana wasu abubuwa masu ɗimbin yawa, musamman ga matasa 'yan makaranta, da kuma tasirin tallafin hukuma, da ƙoƙarin daidaito a tsakanin jama'a, wajen ba duk wanda ya cancanci hakki, hakkinsa.
Rige-rige Zuwa Sararin Samaniya
Shekaru 50 da suka gabata ne ƙasashen Amurka da Rasha suka fara rige-rige da juna wajen ƙoƙarin takawa zuwa sararin samaniya, bayan lafawar yaƙin duniya na biyu.  Kowacce daga cikinsu na ƙera duk abin da zai iya cilla mahayanta zuwa sararin samaniya, ba wai wata duniya ba.  A dai fita daga wannan duniyar, gaba ɗayanta.  Ƙasashen biyu sun killace masanansu a fannin ƙere-ƙere da kimiyyar sararin samaniya don ƙera duk wata na'ura da za ta kai sararin samaniya, don zama na farko a duniya wajen yin hakan.  Ana cikin haka ne sai ƙasar Rasha ta riga ƙasar Amurka, inda ta harba kumbonta na farko mai suna Vostok 1, wanda ke ɗauka  da shahararren mahayin nan mai suna Yuri Gagarin, ranar 12 ga watan Afrailun shekarar 1961.  A tarihin duniya, Yuri Gagarin ne ya fara takawa zuwa sararin samaniyar wannan duniya tamu, a cikin kumbonsa mai suna Vostok 1, inda ya kewaye wannan duniya, kafin ya sauka lafiya.  Allah bai masa tsawon rayuwa ba, domin ya rasu yana ɗan shekaru 34 ne a duniya, sanadiyyar haɗari da yayi sadda yake tuƙa wani jirgi mai suna MiG 5, bayan gama wancan bulaguro nasa.
Wannan ba-zata da ƙasar Rasha tayi wa ƙasar Amurka bai yi wa ƙasar Amurka daɗi ba, domin an kusan samun matsala a tsakanin masananta a wannan fanni.  Ba su so aka ce ƙasar Rasha ta riga ƙasarsu zuwa sararin samaniya ba.  To amma, ƙaddara ta riga fata.  Yuri Gagarin yayi mintuna 108 ne a sararin samaniya.  Daga nan ƙasar Amurka ta biyo baya, inda mahayin kumbonta mai suna Alan Shepard ya haura sararin samaniya shi ma, a cikin shekarar dai har wa yau.  daga nan ƙasashen suka ci gaba da gudanar da bincike a lokuta daban-daban, suna aiwatar da shawagi zuwa ɓangarori daban-daban a sararin wannan duniya, amma babu wanda yayi ƙoƙarin hawa wata duniyar daban.  Sai cikin shekarar 1969, lokacin da ƙasar Amurka ta aika su Neil Aldrin Armstrong zuwa duniyar wata, inda suka kashe sa'a biyu da rabi a kan wata, kafin shigowarsu duniyarmu ranar 21 ga watan Yuli na shekarar 1969.  Wannan tafiya ce ta daɗa fito da Neil Armstrong fili, inda ya zama gwarzo a duniyar sararin samaniya.  To waye Neil Aldrin Armstrong?

Haihuwa da Asali

An haifi Neil ne a a ranar 5 ga watan Agusta, 1930, a birnin Wapakoneta na jihar Ohio ta ƙasar Amurka.  Mahaifinsa shi ne Stephen Koeing Armstrong, ma'aikacin gwamnati ne.  Ya yi ta yawace-yawace tsakanin jihohin ƙasar, sanadiyyar aiki.  A yayin wannan zirga-zirgar aiki ne aka haifi Neil.  Ya kuma fara sha'awar tuƙa jirgin sama ne tun yana dan ƙarami.  Daga nan mahaifinsa ya sa shi a makarantar koyon tuƙin jirgin sama, inda ya samu shedar kammalawa tun yana ɗan shekara 15 a duniya.  Ya samu lasisin tuƙin jirgin sama tun kafin samun lasisin tuƙin mota, wanda sai an kai shekaru 18 ake bayarwa. 

Karatu da Aikin Soji

Daga nan ya samu aiki da hukumar sojin ruwa, inda ya mayar da hankalinsa wajen tuki jirgin sama dai har wa yau.  Cikin shekarar 1947 sai ka koma jami'a, inda ya samu shiga jami'ar Purdue don karanta fannin Kanikancin Jiragen sama, wato Aerospace Engineering.  Ya kasance mai hazaka matuka, inda a shekarar 1955 ya fita da digiri a fannin.  Ya ci gaba da aikinsa, inda ya kasance daya daga cikin masu sarrafa jiragen sama a bangaren hukumar sojin ruwa na kasar Amurka.  Ya halarci yakin Koriya da aka yi a shekarar 1951. 

Cikin shekarar 1956 ya auri matarsa na farko mai suna Elizabeth Shearon, ranar 28 ga watan Janairu.  Ya yanke shawarar barin aikin sojin ruwa a shekarar 1960.  Kafin barin wannan hukuma, an kididdige cewa Neil ya hau jirage nau'uka 78, ya kuma kwashe sa'o'i 121 a sama yana shawagi da jirgi a matsayinsa na direba.  Bayan barin aikin sojin ruwa, sai ya sake ci gaba da karatu a wannan fanni a jami'ar Kudancin Kalfoniya (University of Southern California), inda a karshe ya fito da digiri na biyu a fannin a shekarar 1970.  

Magwajin Jiragen Sama

Zummar Neil na ganin ya kware a fannin hawa jiragen sama bai gushe ba duk da ajiye aiki da yayi da hukumar sojin ruwan kasar Amurka.  Bayan gama digirinsa na biyu kan Kanikancin Jiragen Sama (Aerospace Engineering), sai ya koma cibiyar gwajin jiragen sama na hukumar Sojin Sama na kasar.  A wannan cibiya mai suna Edwards Airforce Base, yayi aiki ne a bangaren gwajin jiragen sama masu gudun tsiya, wato High Speed Flight Station.  Ya yi gwajin jirage na musamman da aka kera masu hikimar bin abokan gaba a fagen fama, wato Chase Planes.  A karshe dai, Neil bai bar wannan Cibiyar Gwajin Jiragen Sama ba sai da yayi gwajin jirage daban-daban har sama da 200.

Mahayin Kumbo
 
Tun sadda ya fara rayuwa da nuna sha'awarsa kan tukawa da sarrafa jiragen sama, Neil bai taba tunanin hawa kumbo zuwa sararin samaniya ba.  Wannan ba shi daga cikin abin da yake tunani, ko ma sha'awar yi dai a takaice.  To amma bayan ya bar Cibiyar Gwajin Jirage da Edwards Air Force Base, sai hukumar kasar Amurka ta fara neman wadanda za su fara hawa kumbo don yin zirya a sararin samaniya, a shekarar 1960.  Wannan shiri nata mai take: Man In Space Soonest, ta faro shi ne tun shekarar 1958.  Kuma don aiwatar da wannan shiri ne aka kera kumbo mai take Boeing X-20 Dyna-Soar.  Jin wannan sanarwa ke da wuya ya mika kansa.  Daga nan aka zabe shi cikin mutane 6 da za su yi wannan bulagura da wannan kumbo.  Wannan ya faru ne cikin shekarar 1962.  Wannan shi ne lokacin farko da ya fara bulaguro zuwa sararin samaniya.

Cikin watan Yuni hukumar NASA ta fara neman ma'aikata masu sha'awar zuwa sararin samaniya.  A ranar da za a rufe karbar takardun neman shiga Neil ya tura nashi. Da kyar ya sha, domin har an rufe, amma daya daga cikin manyan ma'aikatan ya karbi takardarsa, ya saci idon abokan aikinsa ya tsofa ta a karkashi, saboda cancantarsa.  Cikin watan Satumba aka kira shi, bai taba tunanin zai sha ba.  Daga nan aka sanar da shi cewa, idan yana sha'awa, za a sa shi cikin sahun matuka kumbon Gemini 8, wanda zai yi bulaguro na gaba zuwa sararin samaniya.  Da shiri ya zo gaban goshi cikin shekarar 1965, sai aka sanar da cewa Neil ne Kwamandan matukin kumbon zuwa sararin samaniya, wato Pilot Commander kenan.  A watan Maris din shekarar 1966 suka yi wannan tafiya zuwa sararin samaniya, inda suka je lafiya, amma wajen dawowa an samu tangarda karama, inda jirgin da ke dauke da su ya kasa tashi sai da Neil yayi amfani da dabarunsa, da kyar suka sauka lafiya.

Watanni biyu bayan dawowa daga wannan bulaguro sai aka sake neman Neil don yin wata tafiyar da kumbon Gemini 11, inda aka bashi mataimakin matukin kumbo.  Sun yi tafiyar ne a ranar 12 ga watan Satumba ta shekarar 1966, tare da Matukin Kumbo Pete Conrad da Dick Gordon.  Bayan dawowarsu ne shugaban kasar Amurka na wancan lokaci, wato Lyndon B. Johnson, ya karrama su da ziyarar kasashen Kudancin Amurka, tare da iyalansu.

Bulaguro Zuwa Duniyar Wata

Musabaka dai bai kare ba tsakanin kasar Amurka da Rasha wajen rige-rigen haurawa zuwa sararin samaniya.  Wannan ya sa kasar Amurka ta sake tunani; maimakon yawo ko shawagi da kumbo a sararin samaniyar wannan duniya kadai, me zai hana a gwada zuwa duniyar wata ma baki daya?  Wannan ya zaburar da kasar Amurka, inda nan take a boye ta fara shirye-shirye don aika mahaya kumbo zuwa duniyar wata, su dubo don ganin ko dan adam zai iya rayuwa a can.  Daga nan aka fara shiri mai suna Apollo 11, cikin watan Janairu na shekarar 1967.  An gayyaci Neil tare da wasu abokan aikinsa da suka yi bulaguro a baya, cewa suna cikin masu zuwa duniyar wata.  Neil bai yi mamaki ba ko kadan da wannan sanarwa.  Sun yi gwajin farko a watan Disamba na shekarar 1968.

Da aka shiga shekarar 1969 aka sanar da cewa Neil ne zai jajgoranci tafiyar ma gaba dayanta.  Shugabannin NASA suka ce sunyi wannan zabi ne don ganin cewa shi mutum ne mai natsuwa, kuma abin duniya bai dame shi ba. Ba shi da azarbabi. Kuma ya san abin da yake yi.  Wannan sheda ce mai kyau, kuma hakan na cikin abin da ya taimaka masa kaiwa wannan matsayi.  A watan Yuli aka damka masa sakakken hoton wata, abin da aka sanar da shi cewa: "Makullin shiga duniyar wata" ne. Abin dariya, wai yaro ya tsinci hakori.  Raha ce kawai aka yi, don kayatar da tafiyar.

Ranar 20 ga watan Yuli suka shiga cikin wannan kumbo na Apollo 11, daga nan motar da ke cilla kumbo zuwa sararin samaniya ta cilla su.  Tsarin ginin wannan kumbo ya sha bamban da na sauran baya.  Domin an tsara dakin shugaban tafiyar ne da kyau, da manufar za su samu aiwatar da tafiyar har su dawo babu wanda ya kamu da wata cuta, sabanin yadda tsarin yake a baya.  Bayan sun fara tafiya an lura cewa zuciyar Neil ta rika bugawa ne a 110 cikin kowane minti daya.  Abin da ke nuna sauyin yanayin da suka shiga cikinsa ne.  Haka suka ci gaba da tafiya lafiya lau. 

Lokacin da suka zo gab da sauka, sai suka fara samun wasu sakonni daga shafin kumbon, masu nuna cewa akwai matsala.  Wasu lambobi masu nuna matsala ko tangardar manhaja suka fara bayyana.  Da suka sanar da cibiyar da ke lura dasu a kasa, sai aka ce musu kada su damu, kwamfutar da ke kasa ce ke da matsala, bai shafe su ba.  Da kumbon ya zo sauka, daidai lokacin da aka haddade musu na sauka  a ka'idar tafiya, sai Neil ya lura cewa idan suka sauka a inda kumbon ke kokarin saukar da su, za a samu matsala ko tangarda.  Sai ya ja giyar kumbon ta hannu (wato Manual Switch), sai kumbon ya sake dagawa suka koma wani bangare da yafi dacewa da sauka. Sai ya bar kumbon ya sauka da kansa.  Wannan tasa suka samu jinkirin sauka, sabanin lokacin da aka haddade musu.  Nan take suka fara tsoron za a samu matsala, tunda sun samu dan jinkiri. Sun sauka a saman wata ne daidai karfe 9 da minti 17, da sakwan 13 na dare, bayan sun shafe tafiyar tazarar mil 250,000.

Da kumbon Apollo 11 ya sauka lafiya, kafin su fito, sai Neil ya sanar da cibiyar da ke lura da su a jihar Houston, cewa: "Ya ku jama'ar Houston, (ga mu cikin wani) muhalli mai cike da natsuwa a nan.  Kumbon Eagle ya sauka lafiya."  Daga nan sauran abokan aikinsa, wato Buzz Aldrin da Michael Collins, suka fara duba tsare-tsaren sarrafa kumbon, don neman mafita, ko da wata matsala tana iya tasowa a wannan bakon wuri da suka samu kansu.  Shi kuma Neil, a matsayinsa na jagora, sai miko kafarsa ta hagu, ya taka saman wata, sannan yace: "Wannan wani matakin farko ne ga wani mutum, kuma wani babban ci gaba ga bil'adama baki daya."  Nan take kafafen watsa labaru na VOA da BBC suka watsa wannan zance nashi, tare da sauran kafafen watsa labarai na duniya a lokacin.  An kiyasta cewa mutum miliyan 450 ne suka saurari wannan zance na Neil.  Daga nan ya fara tafiya a kan wata, ya nemi wani wuri ya dasa tutar kasar Amurka, sannan yayi tattaki har na tazarar yadi 60. Wannan, a cewar masana fannin sararin samaniya, ita ce tazara mafi tsawo da nisa da aka taba yi a saman wata.

Bayan mintuna 20 kuma sai mataimakinsa mai suna Buzz Aldrin ya sauko ya same shi, suka ci gaba da nazarin muhallin wata.  Sun kwashe tsawon sa'o'i biyu da rabi suna nazari, sannan a karshe suka  ajiye wasu abubuwa masu nuna alamar wani ya zo.  Suka shige cikin kumbon, suka zauna.  Da aka zo tayar da injin kumbo, sai aka lura ashe maballin ya karye, saboda kaurin tufafin da suke sanye dasu.  Wajen jujjuyawa ne suka karya.  Daga nan sai Aldrin ya ciro biro daga aljihunsa, ya kunna injin daga cibiyar lantarkin da ke jikin kumbon.  An ce har yanzu akwai wannan biro a ajiye, don tarihi.  Daga nan kumbo ya daga, suka ci gaba da tafiya.  Sun sauka wannan duniya ta mu ranar 21 ga watan Yuli, inda suka sauko cikin tekun Pacific, aka zo da babban jirgin ruwan kasar Amurka mai suna USS Hornet (CV-12), aka dauke su.

A ka'ida, duk wadanda suka je bulaguro zuwa sararin samaniya suka dawo, a kan ajiye su ne a wani muhalli daban, a musu magani, don tabbatar da cewa basu kamu da wata sabuwar cuta a muhallin da suka je ba.  Wannan tsari shi ake kira Quarantine.  Sun yi kwanaki 18 a wannan wuri, sannan aka fito da su. Saboda sha'awar abin da suka yi, kowa na son ganinsu. Don haka gwamnatin Amurka ta shirya musu bulaguro don zagaye kasar baki daya, cikin kwanaki 45.

Rashin Lafiya da Rasuwa

Bayan wannan bulaguro Neil bai sake sha'awar yin wata bulaguro zuwa sararin samaniya ba.  Sai ya ci gaba da ba da shawarwari, da tallafi ga masu sha'awar wannan fanni a ilimance. A karshe ya kamu da cutar toshewar hanyoyin jini a zuciyarsa, bayan an masa tiyata a garin Ciccinati ta jihar Ohio, Allah ya masa cikawa.  Ya rasu yana dan shekara 82 a duniya.   A rayuwarsa baki daya, Neil ya kwashe kwanaki 8, da sa'o'i 14, da mintuna 12, da kuma sakwanni 30 a sararin samaniya.

Darussa

Rayuwar Neil tana dauke ne da kalubale, da nasara, da kuma cin ma buri, bayan jajircewa da juriya mara misaltuwa.  Akwai jami'o'i, da tituna, da makarantu, da hukumomi da aka sa musu sunan Neil tun da dadewa.  Ya samu kyaututtukan karramawa da yawa, mara kidanyuwa.

Rayuwarsa na nuna cewa duk abin da ka sa a gaba kana son yi, to, ka ci gaba dashi. Watarana za ka kai ga gaci.  Bayan haka, muddin ka lazimci abin da ka iya, kuma kake da sha'awar yi, to za ka taka matsayin da kake son takawa, har ma ka wuce, in Allah yaso.  Wannan shi ne abin da rayuwar wannan bawan Allah ke nunawa karara.

Abu na gaba, duk ilimi da kwarewarka, kada ka zama mai yawan cika baki, mai son duniya, mai azarbabi.  Wannan ba zai kaika ko ina ba.  Neil, duk da cewa ba Musulmi bane  shi, amma ya kasance mai tawali'u, mai kawar da kai daga abin duniya.  Daga cikin dalilan da suka kai shi ga daukaka bayan kwarewa ta ilimi da hazaka, akwai tawali'u da kawar da kai kan abin duniya. haka yayi rayuwarsa babu wanda ke jinsa har bayan barin wannan fanni.  Har wa yau mutum ne mai son ci gaban al'umma, ba na kasar Amurka kadai ba, da sauran kasashe.  Misali, ya kasance mai adawa matuka ga dabi'ar kasar Amurka wajen danniya da mamaya, da zama dan sandan duniya a ko ina.  A cewarsa, wannan bai dace ba. 

Rayuwar Neil har wa yau na nuna yadda gwamnatin kasar Amurka take bin tsare-tsaren ci gaban kasa ba tare da yankewa ba, duk da bambancin shugabanci da jam'iyyar  siyasa.  Babban abin da kasarmu dai musamman ta rasa kenan.  Duk shugaban da yazo, sai tarwatsa tsarin tsohon shugaban da ya maye masa, ba tare da duba manufar da tasa aka assasa wadancan tsare-tsare ba.  An kiyasta cewa a halin yanzu akwai tsare-tsaren ci gaba sama da dubu 3 a warwatse a jihohin kasar nan wadanda ba a kammala su ba. Bincike ya nuna cewa ba abin da ya hana a kammala su sai don bambancin gwamnatoci, sanadiyyar bambancin ra'ayin siyasa.  Amma a sauran kasashe, duk tsarin da tsohon shugaba ya fara, duk wanda ya zo zai ci gaba ne da shi.  Da ace irin tsarinmu ake bi a kasar Amurka, da watakila ba a samu mutane irin su Neil ba, ko irin su Yuri Gagarin ba a kasar Rasha.  Domin dukkan tsare-tsaren da suka basu fice a fannonin da suke kai, ba a lokaci daya aka yi su ba.   Gwamnatoci ne daban-daban.

A karshe, rayuwar Neil na fahimtar damu cewa, muddin za a ba mutum abin da ya cancance shi, wajen ilimi ne, ko wajen mulki, ko duk wani abin da ya shafi hakki, to al'amura za su tafi daidai.  Duk da cewa iyayensa ba kowa bane, sannan ba masu hali bane, amma sanadiyyar kwarewarsa, ya samu abin da ya cancance shi na matsayi.  A wasu lokuta ma yayi latti, amma saboda ya cika ka'idar hazaka da kwarewa, sai aka bashi.  Samun daidaito a tsakanin jama'ar kasa, da tabbatar da adalci a tsakanin al'umma, duk ba su yiwuwa sai ta wannan hanya; a ba duk mai hakki hakkinsa, duk wanda ya cancanci abu, a bashi. Da haka ake samun ci gaba.  Da haka ake samun kwararru a wuraren da suka kamata a same su, don samar da ci gaba ga al'umma baki daya.

Kammalawa

A karshe, duniyar kimiyyar sararin samaniya musamman ta girgiza sanadiyyar rashin wannan babban gwarzo. Domin sanadiyyar hazaka da kwazonsa ne aka ci gaba da habbaka bincike kan zuwa bulaguro a duniyar wata, da ma sauran taurari masu girma da aka gano daga baya.  Neil ya sadaukar da rayuwarsa ga kasarsa, da al'ummarsa, da kuma abokan aikinsa.  Daga cikin ra'ayinsa na baya-bayan nan, ya nuna cewa, ana iya zuwa bulaguro a duniyar Mas (duniyar da tafi kowanne zafi kenan), ya kuma ce idan an tashi aiwatar da wannan aiki, aka bukace shi, zai bayar da hadin gwiwi.  Tirkashi!  Neil Armstrong ya ba da wannan tabbaci ne a babban taro da aka gudanar kan fannin Kimiyya da Kere-kere, a ranar 18 ga watan Nuwamba ta shekarar 2010, a birnin Hague na kasar Nedaland.  Rayuwar Neil Aldrin Armstrong dai a takaice, fitila ce ga dukkan dalibai masu neman ci gaba a kowane fannin ilimi ne, ga dukkan gwamnatoci masu neman kwararru, a kowane fanni ne, ga dukkan al'umma mai neman hanyoyin ci gaba, a kowane fanni ne.

1 comment:

  1. KAMI SEKELUARGA MENGUCAPKAN BANYAK TERIMA KASIH ATAS BANTUANNYA MBAH , NOMOR YANG MBAH BERIKAN/ 4D SGP& HK SAYA DAPAT (350) JUTA ALHAMDULILLAH TEMBUS, SELURUH HUTANG2 SAYA SUDAH SAYA LUNAS DAN KAMI BISAH USAHA LAGI. JIKA ANDA INGIN SEPERTI SAYA HUB MBAH_PURO _085_342_734_904_ terima kasih.

    KAMI SEKELUARGA MENGUCAPKAN BANYAK TERIMA KASIH ATAS BANTUANNYA MBAH , NOMOR YANG MBAH BERIKAN/ 4D SGP& HK SAYA DAPAT (350) JUTA ALHAMDULILLAH TEMBUS, SELURUH HUTANG2 SAYA SUDAH SAYA LUNAS DAN KAMI BISAH USAHA LAGI. JIKA ANDA INGIN SEPERTI SAYA HUB MBAH_PURO _085_342_734_904_ terima kasih.


    KAMI SEKELUARGA MENGUCAPKAN BANYAK TERIMA KASIH ATAS BANTUANNYA MBAH , NOMOR YANG MBAH BERIKAN/ 4D SGP& HK SAYA DAPAT (350) JUTA ALHAMDULILLAH TEMBUS, SELURUH HUTANG2 SAYA SUDAH SAYA LUNAS DAN KAMI BISAH USAHA LAGI. JIKA ANDA INGIN SEPERTI SAYA HUB MBAH_PURO _085_342_734_904_ terima kasih.

    ReplyDelete