Wednesday, February 13, 2013

Tsokaci da Tambayoyin Masu Karatu



A yau kuma ga mu dauke da sakonnin masu karatu kan wasu daga cikin kasidun da suka gabata; wasu daga ciki tsokaci ne, wasu godiya ne, wasu kuma tambayoyi ne.  Ina mika sakon gaisuwata da godiya ga daukacin masu karatu baki daya.  Allah saka da alherinsa, ya kuma bar zumunci, amin.  Da fatan za mu yi azumin watan Ramalana cikin lafiya da kwanciyar hankali, amin.

Kasidar "Kwakwalwa Da Zuciya"

Assalaamu Alaikum, Allah subhaanahu wa ta'ala ya kara maka hasken makaranta.  Na fa'idantu da makalarka game da zuciya da kwakwalwa. – Idris Salihu Musa

Wa alaikumus salaam, Malam Idris hakika ina matukar farin ciki a duk sadda na fahimci na yi wani tasiri mai girma wajen ci gaban rayuwar wani dan adam.  Allah sa mu dace baki daya, ya kuma amfanar da mu kan duk abin da muke karantawa na ilimi, amin.

Assalaamu alaikum Baban Sadik, ina maka addu'ar alheri duniyarka da lahirarka.  Allah subhaanahu wa ta'ala ya azurta mu da irinka.  Ka huta lafiya.  – Abu Aishah

Wa alaikumus salam Baban Aisha, na gode da wannan addu'a mai girma. Kai ma ina rokon Allah da ya sada ka da alheran wannan duniya da lahira, amin.

Game da rubutunka, a takaice ga abin da na sani daga kwararrun masana; zuciya ce ke tunani, amma kwakwalwa ke tacewa.  Kamar mahaukaci yana tunani, sai dai kwakwalwarsa ba ta tacewa.  Duk abin da ya tuna a zuciya sai ya furzar kawai.  Idan mutum mai hankali yayi ganganci, za ka ji an ce: "ya bi son zuciyarsa."  Ko ka ji an ce: "ya zare."  A kalla kwakwalwar ba ta tacewa kamar yadda ya kamata. 08022462133

Alal hakika abin da ka fada ya bayyana, kamar yadda na san ka karanta dukkan kasidun.  Illa dai fada bayanai da nayi ne kawai bambancin da ke tsakanin mahangar da ka sani da wanda na bayyana.  Shi yasa da ka aiko sakonka a farkon bayyanar kashin farko na kasidar ban baka amsa ba, domin hakan bai dace da dabi'ar bincike ba.  Amma yanzu na tabbata an samu gamsuwa iya gwargwado.  Na ji dadin wannan tsokaci naka. Allah sa mu dace, amin.

Assalaamu Alaikum, Baban Sadik ka yi bayani gamsasshe (kan zuciya da kwakwalwa), kuma muna godiya, Allah saka da mafi alherinsa, amin.  Don Allah ina son ka yi bayani ko kwakwalwa tana cika, kuma yaya take ajiya a cikinta?  Kuma yaya take fitarwa?  -  Aliyu Ibrahim Zawuyya, Gusau.

Wa alaikumus salam, Malam Aliyu wadannan tambayoyi naka na bukatar wani bincike na musamman, saboda samar da gamsuwa filla-filla, kamar yadda muka yi a bangaren tunani a tsakanin zuciya da kwakwalwa.  Amma idan bayar da gajeruwar amsa kan ire-iren wadannan tambayoyi ba ya samar da fa'ida gamsasshe ko kadan.  Allah sa mu dace, amin.

Assalamu alaikum Abdullahi Salihu Abubakar, inda kace: "Wannan a tabbace yake karara a cikin Kur'ani mai girma," da kuma inda kace: "Wannan kuwa a bayyane yake karara a cikin littafinsu," a nan ma ya kamata ka ambaci sunan littafin, watau Baibul.  -  Muhammad Abdul Muhammad.

Wa alaikumus salam, Malam Muhammad na gode da wannan tsokaci da tunatarwa.  A nawa tunanin gani nake kamar kowa ya fahimci inda na dosa.  Amma duk da haka, tunda ka gyara, hakan ya wadatar.  Allah saka da alheri, amin.

Baban Sadik ya kamata wannan kasida (Tsakanin Kwakwalwa da Zuciya…) ka mayar da ita zuwa littafi.  Yin hakan zai taimaka wa iyaye karantar da 'ya'yansu fannin Kimiyya da harshen da za su fahimta, kafin su kai ga karanta shi a makarantu.  -  Mustapha Sakkwato.

Malam Mustapha wannan shawara ce mai kyau, duk da cewa na zurfafa bincike, idan aka tace ta, aka rairaye, sannan aka dada kyautata lafuzzan da ke cikinta, yara ma za su amfana da ita sosai.  Ina duba yiwuwar buga kasidun ma gaba daya cikin littafi guda, ba wai wata kasida kebantacciya ba.  Na gode da wannan shawara.

Salam Baban Sadik, yaya aiki?  Gaskiya ina jinjina maka da irin wannan kokari da kake yi, wajen taimaka wa al'ummar Musulmi.  Da fatan Allah ya kara maka koshin lafiya da kai da iyalanka.  -  Idris Isa Lamido, Potiskum.

Wa alaikumus salam Malam Idris, na gode da wannan jinjina da kuma addu'a. Allah saka da alherinsa, amin summa amin.

Assalaamu alaikum, Baban Sadik ina fatan kana cikin koshin lafiya. Ina tambaya ne game da Rai; yadda addinai da masana suka bayyana shi, yadda yake, inda yake a jikin dan adam?  Kuma yaya yake rabuwa da gangar jiki?  -  R. Usman Gabari

Wa alaikumus salaam, wannan bincike ne na musamman, wanda idan aka samu daman gudanar da shi zai amfani al'umma sosai.  A baya na sanar da cewa shi ne layin bincike na gaba da nake son bi, bayan bincike kan Dabi'u da Siffofin Haitta.  Na gode da wannan shawara. Allah saka da alheri, amin.

Salam, Baban Sadik yaya ayyuka?  Allah Ya taimaka, amin.  Don Allah ka daure a karasa mana maganar da ka faro a kan kwakwalwa da zuciya. Don wallahi mun kagara mu ga yadda za a kaya.  Makonni biyun nan (da ba a buga ba) baka ga yadda muka damu ba.  Allah ya saka maka da mafificin alherinsa, amin. – 08030735272

Wa alaikumus salam, Alhamdulillah.  Na san yanzu an samu gamsasshen bayani kan al'amuran.  Na dan samu shagulgula ne da suka dabaibayeni a baya sadda na faro kasidar.  Cikin taimakon Allah kuma an samu gamawa.  Na gode da zumunci.

Aminci a gare ka Baban Sadik.  Kamar yadda bayani ya gabata game da samuwar tunani tsakanin kwakwalwa da zuciya, Musulunci ya tabbatar da samuwar tunanin dan adam daga zuciya ne.  To, kaman mutanen da ke samun matsala a zuciyarsu har ya kai ga an cire zuciyar an musu dashen sabuwa, to, tunanin dake tsohuwar zuciyar ya salwanta kenan, tunda an cire ta, ko yaya abin yake ne?  Allah ya kara maka imani da basira, amin.  -  Yusha'u Adamu, Suleja.

Malam Yusha'u wannan tambaya ce mai matukar mahimmanci. Amma saboda ta game fannoni da dama, hakan na bukatar fadada bincike don samun amsa guda daya.  Domin ta kunshi fannin ilimin dabi'a (Psychology), da fannin ilimin kwakwalwa a kimiyyance (Neuroscience), sannan da fannin shari'ar musulunci; shin, meye matsayin sanya wa musulmi zuciyar wanda ba musulmi ba, misali?  Ko sanya wa mutumin kirki zuciyar mutumin banza?  Kafin malaman addini su ba da fatawa, dole suna bukatar sanin tasirin dashen zuciya ga wanda aka dasa masa.  Shi, ana samun "gadon dabi'u" a tsakaninsu ko ba a samu?  Wannan duk yana bukatar bincike don tantance hakikanin al'amura.  Allah sa mu dace, amin.

Baban Sadik, wannan doguwar mukarana (tsakanin kwakwalwa da zuciya) tana nuni ga jajircewarka domin amfanar da mu abin da bamu sani ba.  Ina fatan ya kasance tsani.  -  Hamzah Osama, Zaria.

Malam Hamza ina godiya da wannan jinjina.  Allah saka da alheri.  A duk sadda aka ga kuskure ina neman agaji da a nusar da ni.  A shirye nake a kullum don karbar gyara.  Na gode.

Salam Baban Sadik, yaya aiki?  Allah ya taya maka amin.  Jinjina gare ka marar iyaka, Allah ya kara basira amin.  Don Allah ina neman wata alfarma a gare ka.  Ina son in ka gama kasidar maganar zuciya da kwakwalwa, ka taimaka mini a matsayina na daliba, ka hada min gaba dayan kasidar a hade daga farko har karshe.  Na gode.  

Wa alaikumus salaam, ina godiya da addu'o'in da aka yi.  Allah saka da alherinsa amin.  Kamar yadda na tabbata kin samu, na hada kasidun, na yi "binding", sannan na aika.  Allah taimaka.  Sai a dage da karatu, kada a yi wasa.  A rike dabi'un hakuri da juriya wajen lazimtar karatu, sannan a yawaita addu'ar neman cin nasara.  Da haka ake samun nasarar karatu.  Alah sa a dace, amin.

Salam, Alhamdulillah, gaskiya muna amfana sosai da wannan makala ta "Tsakanin kwakwalwa da zuciya, wa ke samar da tunani?"  Allah saka da alheri, ya kara ilmi mai amfani, amin.  -  07039819621

Wa alaikumus salam, to ina murna da jin haka.  Allah sa ya amfani al'umma baki daya, ya kuma bamu dacewa cikin al'amuranmu duniya da lahira, amin.  Na gode da addu'a.

A baya akwai inda kayi maganar lissafin yawan bugun da zuciyar mutum za ta yi a rayuwarsa idan aka auna da yawan shekarun da zai yi a duniya, to, ta yaya ake dashen zuciyar matacce kuma ta kama aiki bayan ta riga ta gama aikinta?  Don Allah in da hali, muna so a binciko mana, a mana rubutu a kan haka. -  07039819621

Na'am, tabbas haka ne.  Amma ina ganin sunyi wannan hasashe ne kan mutumin da zai yi rayuwa har ya mutu ba tare da an bukaci amfani da zuciyar ba bayan mutuwarsa.  Amma duk da haka, tunda ilimi ne, bincike zai iya zakulo shi da yardar Allah.  A dai ci gaba da hakuri da ni, na dauki bashi da yawa.

Salam Baban Sadik, barka da kokarin bincike.  Shawarata ita ce, ka mayar da wannan kasida taka mai take: "Tsakanin Kwakwalwa da Zuciya, wa ke Samar da Tunani?" zuwa littafi, saboda muhimmancinsa.  -  Salisu Lawal Dan-Indo, Katsina.

Wa alaikumus salaam, Malam Salisu na gode da wannan shawara.  Allah sa mu dace, ya kuma ba da ikon taimakon al'umma ta hanyoyin da suka dace, kuma ake fahimta. 

Assalamu alaikum, Baban Sadik na barka da warhaka.  Ina karatun Masters ne a fannin "Physiology", a nan Jami'ar ABU Zariya. To wallahi cikin ikon Allah akwai kasidar da zan gabatar a wani taron kara wa juna sani mai taken: "The Intelligent Heart", to jiya kawai sai na ga littafinka mai taken: "Tsakanin Kwakwalwa da Zuciya, Wa Ke Samar da Tunani?" a wurin abokina, sai na ga kusan abu daya ne da nawa.  Ina godiya.  -  Abubakar Shehu

Wa alaikumus salam, lallai dole a samu dacewa tsakanin kasidar da wannan maudu'i naka.  Ina kuma fatan ka samu wasu fa'idoji komai kankantarsu daga kasidar tawa.  Ina rokon Allah ya albarkaci al'umma da abin da ka gabatar.

Malam Abdullahi,  gaisuwa mai yawa da fatan alheri ina maka godiya da hidiman da kayi tsawon sati 9 wajen amsa tambayar da aka yi akan cewa wa ke samar da tunani tsakanin kwakwalwa da zuciya. Allah Ta'ala Ya saka maka da alheri.  Ina da wani dan tsokaci a kan amsar da ka bayar wanda a dunkule ya karkata ne ga tabbatar da cewa ainihin zuciya ita ce kashin bayan tunani wajen 'yan adam.

Tsokacina a nan ita ce, bayanin da kayi wajen kammala makalar cewa ba a ambaci kwakwalwa a zahiri a Kur'ani ba, sabanin zuciya wadda kace ambatonta ya shahara a Kur'ani a karshen bayaninka na 9 na ranar Juma'ah 20 ga Afrilu 2012 a Jaridar Aminiya.

Ina ganin Ubangiji me Girma da Daukaka Ya nuna cewa tunani daga kwakwalwa ne tun a Surah ta farko da aka saukar wato Suratul Alaq, Aya ta 14 zuwa ta 15 inda Allah Ta'ala ke cewa: "Kalla la in lam yantahi lanas fa'an bin naasiya, nasiyatin kazibatin khadi'ah…"  Ma'anar kalmar "Naasiya" shi ne "Muqaddamul ra'asi" wato "goshi" kamar yanda fassarar take a Kamus na Larabci. A aya na 15 bayanin "Naasiya" ya zo a matsayin makaryaciya, mai kuskure. Karya da kuskure daga tunani ne, tunani na gaskiya da tunani na kuskure.

Don haka, ta wadannan ayoyi guda 2 muna iya fahimtar Kur'ani tun a surar farko ya nuna tunani na iya zuwa daga kwakwalwa. Kari a kan haka, akwai Hadisi wanda zai iya karkafa cewa "Naasiya" din nan ba yana nuna gashi ne ba a'a, har da inda gashin yake. Hadisin shi ne wanda aka nuna cewa: "Manzon Allah (SAW) Ya saki naasiyatahu, maa sha'Allahu thumma farraka ba'ada zaalika," sannan Ya mayar da shi baya.

Na kawo Hadisin don karfafa cewa "Naasiya" ita ce "Muqaddamil ra'asi" wato goshi, ba don karfafa tunani ba. A karshe ina kara jinjina maka kan wannan jihadi da kayi wajen bada taka gudummuwar ga ci gaban addinin muslunchi. Allah Taala Ya Saka maka da AljannarSa.   Na gode. -  Sani Ibrahim: msani12@yahoo.com

Assalaamu Alaikum,  Malam Sani  da fatan an tashi kuma ana lafiya.  Na gode matuka da wannan fadakarwa.  Hakika ka yi hangen nesa kuma ka zurfafa tunani wajen fahimtar madloolaat na wannan aya da ke cikin Suratul Alaq.  Allah saka da alheri.

Watau abin da nake nufi da cewa ba a ambaci kwakwalwa ba karara a cikin Kur'ani shi ne, yadda kalmar "Qalbu" tazo cikin Kur'ani, da yadda ta yi ta maimaituwa, hakan ke nuna karfin tasirinta kan kwakwalwa, wanda kamar yadda kai ma za ka sheda, kalmar "Ad-dimaagh" wanda ke nufin kwakwalwa karara, bata zo ba.  Tabbas na yarda kalmar "naasiyah" na nufin "muqaddimatur ra'asi" ne, kuma za mu iya daukan ma'anarta a matsayin majaaz kan cewa tana wakilatar kwakwalwa ne, tunda akwai qareena, watau sifofi guda biyu da Allah ya baiwa kalmar, watau "kaazibah", da "khaati'ah."  Wannan zai tabbatar mana cewa kwakwalwa ake nufi.  Amma na kwatanta yawan maimaituwa ne, da kuma tabbatar da suna a fili, tsakanin zuciya da kwakwalwa.  Wanda kuma idan ka duba za ka samu zuciya ta fi maimaituwa kuma an fi bayyana ta a fili karara.  Wallaahu a'alam.

Bayan wannan, akwai tsokaci da su Sheikhul Islam ibn Taimiyya suka yi da sauran malamai da ke nuna lallai tunani na samuwa a kwakwalwa, sai dai abin da suka nuna shi ne, asalinsa daga zuciya ne, ita kwakwalwa saita tunanin take yi.  Kamar yadda asalin "hankali" (watau "al-aqlu") daga zuciya yake, sai yayi rassa a kwakwalwa.  Wasu malamai kuma suka ce tunani nau'i biyu ne, akwai wanda ke zuwa daga zuci, wanda ya shafi al'amuran imani da taqawa da karbar gaskiya da jujjuya shi.  Nau'i na biyu kuma suka ce shi ne nau'in tunanin da yake darsuwa a kwakwalwa kan abin da ya shafi kere-kere da hazaka. To amma dukkan wadannan ba abubuwa bane da za ka iya kawo musu hujjoji cikin sauki da ruwan sanyi ba, sai an ta tsawaita bincike, ta yadda har mai karatu na iya bacewa ya kasa bin sakamakon bincikenka.  Shi yasa na dakata kan abin da ka gani.  Don ko a hakan na san akwai da yawa cikin masu karatu da suka bace saboda tsawaitar kasidar.

Alaa ayyi haalin, na gamsu da wannan tsokaci naka wallahi, kuma naji dadi matuka, domin na karu da abin da ka rubuta.  Don haka na gode matuka. Allah saka maka da alheri. 


No comments:

Post a Comment