Tsarin
Halittar Zuciya da Kwakwalwar Dan Adam
Jikin dan Adam na dauke ne da bangarori nau'uka daban-daban, masu
kamanni daban- daban, a wurare daban-daban, don aiwatar da
ayyuka daban-daban, a yanayi daban-daban, cikin umarni mai dauke da girman
kudurar Ubangiji mahaliccin bayinsa masu kamanni da kintsi daban-daban. Halittar dan adam abu ne mai matukar ban
al'ajabi, cike da hikima da kwarewar da babu wanda zai iya samar da ita har
abada. Daga cikin muhimman bangarorin
jikin dan adam da yake ji da su saboda kebantacciyar matsayinsu wajen tafiyar
da rayuwarsa, akwai zuciya da kuma kwakwalwa.
Wadannan bangarorin jiki na dan adam sun shahara sosai, saboda
kebantattun aikin da suke gudanarwa a jikinsa.
Ba ma shi kadai ba, malaman kimiyya sun tabbatar, ta hanyar bincike na
kwakwaf, cewa dukkan dabbar da ke da kashin baya (watau Backbone, ko Vertebral
Column, ko Spinal Column), to, tana dauke da kwakwalwa da kuma
zuciya. Kamar yadda bayanai suka gabata a makon jiya, yau ga mu dauke da
bayani kan halittar zuciya da kwakwalwar dan adam. Wadannan bayanai sun ta'allaka ne kai tsaye
ga sifofinsu, da ayyukansu, da kuma yanayinsu a jikin dan adam; a mahangar
malaman kimiyyar halitta na zamani.
Zuciyar Dan Adam
Zuciyar dan adam wani curin nau'in nama ne mai gautsi, mai asali
daga yadin jijiyoyin jikinsa masu taushi da a harshen Turanci ake kira Cardiac
Muscle. Wannan curin nama na dauke
ne cikin kogon kirjin dan adam, daga bangaren hagunsa. Girman zuciya duk bai shige dunkulen yatsun
dan adam matashi ba. Kuma tana dauke ne
da wasu kwaroron jijiyoyi guda hudu masu taimakawa wajen shigi-da-ficin jini a
bangaren dama da hagu, da bangaren sama da kasanta. Akwai bambanci tsakanin
girma da nauyin zuciyar namiji da zuciyar mace.
A yayin da nauyin zuciyar namiji ke tsakanin giram 300 – 350, nauyin
zuciyar mace bai wuce tsakanin giram 250 -
300 ba. Allah kadai ya san
hakikanin hikimar da ke tsakanin bambanta girmansu.
Zuciyar dan adam na gudanar da ayyuka masu dimbin yawa wadanda har
yanzu malaman kimiyyar halittar jikin dan adam sun kasa tantance adadinsu. Abin da ake ta yi dai shi ne bincike, har
zuwa wannan lokaci da nake wannan rubutu.
Amma muhimmi daga cikin ayyukan zuciya da ake iya gani da jinsa, shi ne
lura da babban tsarin sadar da jini ga dukkan bangarorin jikin adan adam; daga
yatsun kafafunsa zuwa jijiyoyin kwakwalwarsa, dare da rana da safe da
yamma. Zuciya ce ke taimaka wa tsarin
gewayen jini a jikin dan adam (watau Circulatory System), wajen fanfon
jini daga kasa zuwa sama, da akasin hakan.
Zuciya ce injin da ke fanfon jini a wannan tsari. Wannan aiki na samuwa ne ta hanyar bugun
zuciya (Heartbeat) da ke samuwa a duk sadda zuciyar ta takura (don harba
jini) sannan ta sake (don jawo jini) daga wani bangare zuwa wani bangare. An kiyasta cewa zuciyar kowane matashi kan
buga sau 72 a cikin minti daya.
Malaman kimiyyar halittan jikin dan adam sun tabbatar da cewa
zuciyar dan adam na fara aikinta ne (ta hanyar bugawa don aikawa da karban jini
a jiki), makonni uku da gama tsara halittar dan tayi a mahaifa. Ma'ana, da zarar Allah ya busa rai a jikin
dan tayin da ke mahaifa, nan take zuciyarsa ke fara aikinta. Kuma haka za ta ci gaba da bugawa har tsawon
rayuwarsa. Wadannan jijiyoyi da ke aikin
takurawa da sakewa a zuciya ba su samun hutu sai na 'yar tazarar lokacin da ke
tsakanin takura da sakewar. Ma'ana, tsawon lokacin da bai kai dakika daya ba kenan. Bincike ya kuma tabbatar da cewa, mutumin da
zai yi shekaru 76 a duniya, zuciyarsa za ta buga sau biliyan biyu da miliyan
dari takwas (2.8 billion beats), kuma za ta harba jinin da adadinsa ya
kai lita miliyan 169 a yayin wannan bugawa nata. Dankari!
Wannan ke nuna cewa a dukkan jikin dan adam, babu bangaren da yafi
zuciyarsa tsawon lokacin aiki, da yawan aiki, da kuma inganci wajen
halitta. Duk da cewa sauran suna da
inganci su ma.
Masana basu gushe ba tun farkon zamani wajen binciken halin da
zuciyar dan adam ke aiki a yanayi daban-daban. Daga lokacin da aka fara rubutun
tarihi zuwa yanzu, an gano abubuwa da dama dangane da abin da ya shafi zuciyar
dan adam. Wadanda tarihi ya tabbatar da
kokarinsu dai su ne likitocin Kibdawan kasar Masar, sai kuma likitocin Girkawa (Greek
Physicians), sai likitocin Daular Rumowa. Daga nan sai likitocin karni na
16 da 17 da suka tagaza nasu kokarin, wajen binciko bangaren jikin dan adam da
ke da alhakin harba jini zuwa sauran bangarorin jikinsa. Kokarin masana irin su
Michael Servetus da William Harvey ne ya taimaka wajen gano hakikanin bangaren
da ke wannan aiki; watau zuciya. Muna shiga karni na 20 kuma sai wannan tsarin
bincike ya dauki wani sabon salo, inda aka samu likitan farko da yayi kurum
wajen gunadar da tiyar zuciya (Heart Surgery) na farko a duniya a kasar
Amurka. Wannan likita kuwa shi ne L.L. Hill, a shekarar 1902. A wannan karni ne har wa yau aka gudanar da
bincike don samar da na'urar binciken zuciya, watau ECG. Wanda yayi wannan hobbasa kuwa shi ne
wani likita dan kasar Jamus mai suna Willem Einthoven, a shekarar 1924. Daga
nan dai tsarin bincike ya ci gaba da habaka, har muka samu kanmu cikin wannan
zamani mai dauke da nau'urori kala-kala da ake amfani da su wajen gwajin bugun
zuciya, da na daukan hoton zuciya, da wukaken da ake amfani da su wajen yin
tiyatar zuciya da dai sauran makamantansu.
A farkon lamari likitoci basu yarda cewa za a iya yi wa zuciya tiyata
ba, saboda tsananin taushi da gautsin da ke tattare da ita. Har sai
da likita L.L. Hill ya gwada yi wa wani yaro dan shekaru 8 a shekarar
1902, kamar yadda bayani ya gabata. Don
haka, a mahangar malaman kimiyyar halittar dan adam (Physiologists),
muhimmin aikin zuciya shi ne samar da bugawar jini zuwa sassan jiki, da kuma
daidai harbawar zuciya, da taimaka wa sauran bangarorin jiki wajen samar da
jini mai dauke da sinadaran iska, don tafiyar da rayuwa.
Kwakwalwar Dan Adam
Kwakwalwar dan adam wani curin gungun jijiyoyin yadi ne masu dauke
da sinadaran kara kuzari (Protein), da hanyoyin jini, wadanda kuma ke
kunshe cikin kokon kan dan adam (Human Skull). Wannan curin gungun jijiyoyi na da sila ne na
kai tsaye da kashin bayan jikin dan adam, kuma wani bangare ne mai muhimmanci
wajen hada alaka tsakanin dukkan bangarorin jiki, ta hanyar babbar tafarkin
sadarwar bayanai na jikin dan adam, watau Central Nervous System kenan. Ita kwakwalwa kamar yadda malaman kimiyyar
halitta suka tabbatar a binciken baya, wata cibiya ce da ke da tasiri wajen
aiwatar da sadarwa ga dukkan bangarorin jikin dan adam. Ita ce bangaren da ke lura da dabi'ar kauna,
da tsana, da tsoro, da fushi, da farin ciki, da bakin ciki. Har wa yau malaman kimiyyar halitta sun
danganta kwakwalwa da samar da tunani, da hazaka, da koyon harshe, da tantance
abubuwa, da haddace bayanai, da kuma tuno su bayan haddace su. Ita ce ke lura da bacci, da kishirwa, da
dabi'un da ke lura da rayuwar dan adam baki daya.
Yadda kwakwalwa ke aiki abu ne mai matukar ban al'ajabi. Wannan ne ma yasa galibin masana ke ganin
cewa, ita ce jagora a dukkan bangarorin jikin dan adam. (Nan gaba za mu gane, shin wannan tabbaci
haka yake a yanzu?). Kwakwalwa na
gudanar da ayyukanta ne ta hanyar wasu sinadaran maganadisun lantarki (watau Neurons)
da ke makare cikin jijiyoyin da ke kwakwalwar (watau Nerves), wadanda ke
aika sakon sadarwar bayanai daga kwakwalwa zuwa sauran bangarorin jiki, ta
hanyar wani tsarin sadarwa mai ban al'ajabi.
Wadannan bayanan sadarwa na dauke ne cikin abubuwa guda biyu; da
sinadaran jiki (Chemical) da ke dauke cikin yadin jijiya (Nerve
Cells). Sai kuma ballin maganadisun
lantarki (watau Electrical Pulse). Wadannan
su ne madaukan bayanai da ke aiwatar da sadarwa daga kwakwalwa zuwa sauran
bangarorin jiki, ta hanyar kwayoyin halittar sadarwa da ake kira Neurons, wadanda
ke amfani da sinadaran maganadisun lantarkin sadarwar da ke cikinsu da ake kira
Neurotransmitters. Kowane Neuron
na dauke ne da rassa da ke karba ko mika bayanan da ya sarrafa zuwa wani Neuron
din. Wadannan rassa dai sun hada da Dendrites,
da kuma Axons, wadanda su ne kamar ressan sadarwa tsakanin kwayoyin
halittar kwakwalwa, don aiwatar da sadarwa na bayanai ko sinadarai a
tsakaninsu.
An gunadar da bincike masu dimbin yawa kan kwakwalwar dan adam, da
irin kudurar da Allah ya nuna a cikinta, wajen iya sarrafa bayanai da sadar da
su ga sauran bangarorin jikin dan adam.
Binciken baya-bayan nan da aka gudanar mai alaka da kwakwalwa kai tsaye
shi ne wanda Roger Sperry ya gudanar kan tsarin gudanarwar kwakwalwa, tsakanin
bangaren hagu da bangaren dama. Ya fitar
da sakamakon bincike ne da ke nuna cewa, mutane sun sha bamban wajen tunani ne
saboda irin bangaren da suke tunani da shi daga kwakwalwarsu. A karshen bincikensa ya tabbatar da cewa,
bangaren kwakwalwar dan adam na hagu shi ne wanda ke taimaka wa dan adam tunani
ta hanyar dabi'a. Ma'ana, dukkan abin da
dan adam ya ci karo da shi na bayanai ko gwagwarmayar rayuwa, yakan sarrafa
bayanan ne a tsarin da Allah ya halicce shi da ita na tunani, don fitar da
sakamako. Misali, idan mutum ya fito
daga gidansa, ya baro iyalinsa a ciki, yana fitowa sai ya ci karo da babban
amininsa da ya saba zuwa gidansa, suna gaisawa sai abokinsa yace ya zo ne su
gaisa da iyalinsa, abin da wannan mutum zai ayyana kawai shi ne, gaisuwa ce ta
yau da kullum. Ba wata damuwa.
Amma bangaren kwakwalwa na dama kuma shi ne ke taimakawa wajen tara
bayanai, da irin yanayin da abubuwa ke faruwa, da dalilan da suka sa su faruwa,
kafin fitar da hukunci kan wani abin da ya faru a lokacin Magana. A misalin da muka kawo a sama, mai tunani da
bangaren damansa ba zai amince cewa gaisuwa ce kadai ta kawo wannan abokin nasa
ba. Har sai ya yi la'akari da irin
lokacin da abokinsa ya zo (da safe ko da rana ko da yamma ko da dare?), da irin
yanayin da yazo a ciki (farin ciki ko bakin ciki?), da irin yanayin da alakarsu
ta abota take ciki (suna cikin shiri ne ko bayan sun bata?), sannan zai yanke
hukunci ko gaisuwar ta Allah-da-Annabi ce ko kuma da wata a kasa.
A takaice dai, an gudanar da bincike da dama kan kwakwalwar dan
adam, kuma ana kai. Ba don komai ba sai
don irin muhimmancin da ke tattare da wannan gaba na jikinsa. A gaba mai karatu zai ga bayanai kan abin da
ya shafi zuciya da kwakwalwar dan adam. A ci gaba da kasancewa tare da mu.
Allah ya saka da Alkhairi. Baban Sadiq
ReplyDeleteMasha Allah
ReplyDeleteALLAH yakara ilimi me albarka
ReplyDelete