Wednesday, February 13, 2013

Tsakanin Kwakwalwa da Zuciya...(5)



Mahangar Musulunci Kan Asalin Tunani

A yau cikin yardar Allah ga mu dauke da bayani kan mahangar Musulunci dangane da abin da ya shafi tunani; shin, daga zuci yake samuwa ko daga kwakwalwa?  A mukaddimar da muka gabatar kan nau'ukan ra'ayoyi dangane da haka, mun fahimci cewa, ta la'akari da ayoyin Kur'ani da wasu hadisai na Manzon Allah (tsira da aimincin Allah su kara tabbata a gare shi), tunani na samuwa ne daga zuci, sabanin abin da malaman kimiyya suke tabbatarwa a yanzu.  Amfanin wannan kasida ta yau shi ne tabbatar da hakan ta hanyar kawo nassoshin Kur'ani masu Magana kan hakan, da na hadisai.  Domin su ne bayanan da shakku ko kokwanto ba ya shiga cikinsu, saboda tabbacin da ke tattare da asalinsu.  Kuma tunda mai zancen shi ne ya halicci dan adam wanda muke Magana kan tsarin halittarsa, ashe kuwa babu wanda zai fahimtar damu gaskiyar abin da ya dangance shi sai Mahaliccinsa.  Bayan haka, za mu ji mahangar Malaman musulunci kan ma'anonin da suke baiwa wadannan ayoyi ko hadisai dangane da abin da muke nema na ma'ana a tare dasu.

Kalmar "Zuciya" a Nassin Kur'ani

Daga cikin gabobi ko sassan jikin dan adam, babu bangaren da Allah ya ambace shi karara, da sunaye daban-daban irin zuciyar dan adam.  Wannan a fili yake ga duk makarancin Kur'ani, masani. Shahararriyar kalma ita ce wacce a asali take nufin Kalmar zuciya karara, a harshen Larabci.  Wannan kalma ita ce: Al-Qalbu.  Allah ya kawo ta a sigar tilo, watau Al-Qalbu, ya kuma kawo ta a sigar jam'i, watau Al-Quloob.  Wannan ita ce Kalmar da tafi shahara cikin kalmomin da aka yi amfani da su wajen ambaton zuciyar dan adam; musulmi ne ko kafiri, Annabi ne ko wani gama-garin mutum.

Kalma ta biyu da Allah yayi amfani da ita don nufin zuciya ita ce kalmar: Al-Fu'aad.  Ita ma ta zo a sigar tilo, watau Al-Fu'aad, sannan ta zo a sigar jam'i, watau Al-Af'idah.  Wannan kalma ita ma ta dan shahara a cikin Kur'ani. Sai kalma ta uku, watau kalmar As-Sadr.  Kamar sauran kalmomin da suka gabace ta, ta zo a sigar tilo da jam'i ita ma.  Watau ko dai ta zo a As-Sadr, ko kuma ka ga tazo da suna As-Sudoor, watau jam'in Sadr kenan.  Asalin ma'anar Sadr na nufin "kirji" ne a harshen Larabci.  Amma saboda alakar da ke tsakanin kirji da zuciya, dangane da abin da Allah ke son tabbatar mana don mu fahimta a aya, shi yasa duk masu tafsiri ke hada alaka tsakaninsa da zuciya, amma sukan fassara kalmar ne da ma'anarta na asali (watau kirji). Domin kirji ne farfajiyar zuciya, kuma ganin cewa duk abin da ke cikin farfajiyar nan yana tasirantuwa da abin da ke ciki, kuma zuciya ce gabar da tafi tasiri cikin gabobin da ke cikin kirji (tun da a wasu ayoyin an ambace ta karara), sai malamai su dauka kai tsaye zuciya ake nufi.  Allah shi ne mafi sanin sirrin da ke cikin ma'anonin kalmominsa.
Wadannan kalmomi, a takaice, su ne ke ishara ga zuciya a cikin Kur'ani.  Sannan sun maimaitu a wurare da dama, wanda hakan ke nuna matukar muhimmancin zuciya ga dan adam wajen fahimta ko rashin fahimtar sakon shiriya da Allah ya aiko Manzonsa da shi.  Kafin mu yi nisa, mu fahimci cewa yawan ambaton abu, a tsarin zance, na nuna lallai akwai wani muhimmanci – na bayyane ko na boye – da wannan abin ya mallaka ko yake yi.

Nau'ukan Zukata da Dabi'unsu

Kafin mu yi bayani kan na'ukan zuciya, yana da kyau mu yi bayani kan dabi'un zuciya.  Da farko dai, zuciya abu ne guda daya, watau dunkulen nama da ke bangaren kirjin dan adam na hagu, wacce ke aikin famfon jini, kamar yadda bayanai suka gabata.  Kuma, kamar yadda Allah ya fada cikin Kur'ani, bai taba halittar wani dan adam da zuciya guda biyu a kijinsa ba.  Wannan sunna ce wacce ya tsara wa kansa, cewa kowane dan adam zuciya daya ake halittarsa da ita.  Daga cikin dabi'un zuci da muka sani a al'adance, akwai ji irin na tausayi, da so, da kauna. Wadannan su ne manyan dabi'un da a al'adance muke danganta su ga zuciya.  Hatta masana fannin kimiyya da wannan suka san zuciya, duk da cewa ko a kimiyyance ba za su iya nuna alamar da ke nuna samuwar soyayya da kauna da suke danganta su gare ta ba (tunda ba abubuwa bane da ake iya ganinsu); sabanin hujjar da suke da ita kan kwakwalwa.

A daya bangagren kuma, Musulunci ya sanar da mu kari a kan wasu halayyar da muka sani dangane da zuciya.  Wadannan sun hada da: imani, da kafirci, da munafunci, da tunani, da fahimta, da rashin fahimta, da karbar gaskiya, da kin gaskiya, da shiriya, da karkata, da sabo, da niyya, da tsarkakuwa, da baci ko dauda, da karamci, da fushi, da rashin damuwa, da tsoro, da damuwa, da bakin ciki, da shakka, da kokwanta, da keta, da tawaye, da nadama, da tabbaci, da rashin tabbaci, da jiji-da-kai, da kishi, da kuma girman kai.  Wadannan su ne yanayi da dabi'un zuciya, kamar yadda nassoshin Kur'ani da hadisai ke nunawa.  Shi yasa suka kasa nau'ukan zukata zuwa kashi biyu; da zuciya lafiyayya ko kubutacciya daga kowane irin cuta, wacce ke dauke da farin ciki, da kwanciyar hankali, da imani, da gaskiya, da mika lamura zuwa ga Allah, da kuma zuciya mara lafiya, wacce ke dauke da cututtuka irinsu kafirci, da bidi'a, da shakka kan sakon Allah, da kokwanto, da girman kai, da zalunci, da yawan sabo, da sauran matsaloli makamantansu. Wannan rabe-rabe ne da malaman Musulunci suka yi, dangane da bayanan da suka zo cikin ayoyin Kur'ani da hadisan Manzon Allah (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) ingantattu.

Dangane da bayanan da suka gabata, idan muka yi dubi sai mu ga cewa a zahirin lafazi da yanayi, wannan zuciyar da muke dauke da ita a kirjinmu na bukatar karin bayani kan ayyukan da take yi.  Domin abin da muka sani kawai shi ne, tana aikin rarraba jini ne a jikin dan adam, wanda hakan ke taimakawa wajen tabbatar da rayuwarsa.  Wannan ta sa ra'ayoyin malaman musulunci suka sha bamban wajen ma'anar kalmar "Al-Qalbu" ko "Al-Fu'aad" a cikin Kur'ani mai girma.  Shin, akwai wata zuciya ce tattare da asalin zuciyarmu wacce ke gudanar da wadannan ayyuka amma ba a ganinta, ko kuma ita din ce ke dukkan ayyukan, a bisa kudura da ganin damar Ubangiji? Ko kuma dai kawai anyi amfani da kalmar ne don nufin wani abu daban, watau Majaaz kenan?

ABU RAIHAAN, MUHAMMAD IBN AHMAD AL-BAIROONEE (973 – 1048 MILAD) (2)

Bayan ya kwashe 'yan shekaru yana wannan aiki ne ya zarce kasar Indiya daga can, lokacin da Sarki Mahmood ya ci daular Hindu (Indiya) da yaki. Ya kasance tare da shi a can, kuma a wannan lokaci ne ya rubuta shahararren littafin nan nasa mai suna Kitaabu Taareekh al-Hind (Littafin Tarihin Hind).  Duk da cewa wannan littafi ne na tarihi kamar yadda sunansa ke nunawa, amma a cike yake da nau'ukan ilmin kimiyya da fasaha da na sararin samaniya. 
Littattafan da Ya Rubuta
Abu Raihaan ya rubuta littattafai masu dimbin yawa. Malaman da suka rubuta tarihinsa sun yi sabani kan yawan wadannan littattafai na shi.  Sai dai adadi mafi karanci da suka bayar shi ne 146.  Daga cikin wannan adadi ko abin da ya wuce haka, kashi 65 duk a kan ilmin kimiyyar duniya ne (Astronomy), da fannin lissafi (Mathematics), da fannin lissafi na musamman kan ilmin kasa (Mathematical Geography), da fannin magunguna (Pharmacology), da fannin likitanci (Medicine) da dai sauransu.  Ya samu daman rubutu a wadannan fannoni ne musamman saboda baiwar da Allah ya masa na son ilmi da kuma sanin harsunan duniyar wancan lokaci da yawa da yayi.  Domin bayan harshen garinsu mai suna korasmiya, ya gwanance a harshen Farisanci (Persian), da larabci, da Sanskrit, da Turkanci, da yaren Girka, da Hibru, da kuma Siriyananci. 
Da wannan ya samu daman kalato ilmin kimiyya da ke makare wajen malaman kasar Hindu, da Girka, da sauran al'ummomin da yake iya magana da harshensu.  Bai tsaya wajen kalatowa kadai ba, ya yi geji a tsakaninsu, inda ya watsar da na watsarwa; musamman wadanda suka saba wa ka'idar musulunci.  Misali, ya fafata da Shehin malamin nan mai suna Ibn Sina, kan abin da ya shafi dogaro da kuma yarda da ka'idojin malaman Falsafar daular Girka, wadanda Ibn Sina ke bi sau da kafa.  Ba komai ya kawo haka ba sai don galibin sakamakon bincikensu na kimiyya a cakude yake da akidunsu na maguzanci.
Har zuwa yau duniyar kimiyyar sararin samaniya na tinkaho da Abu Raihaan.  Domin ta dalilin bayanan da ya tara kan yanayin Wata da alakarsa da Rana a lokacin da dayansu yake husufi ne, a yau aka gano tsarin gudanuwar Wata wajen tafiya (watau Moon Acceleration), abin da Dunthorne ya tabbatar a shekarar 1749.  Bayan haka, har zuwa yau ana amfani da bayanansa kan binciken da ya gudanar dangane da halittun da ke sararin samaniya – Rana, da Wata, da Taurari da yanayin gudanuwarsu.  Har wa yau Abu Raihaan babban malami ne kan abin da ya shafi ilmin zanen taswira, watau Cartography.  Domin yana cikin wadanda ake dogaro da zanensu kan Tsohuwar Taswirar Duniya (watau Old Global Map).
Daga cikin manyan littattafansa akwai babban littafinsa kan tsarin tunani da al'adun mutanen daular Hindu mai suna Tahqeequ Maa Lil Hind Min Muqawwilatin Fil 'Aqli, Ma'aqoolatan am Marzoolatan, wanda a harshen Turanci ake kira Indica.  Littafi ne da ke bayanin dabi'u da al'adu da kuma addinan mutanen kasar Indiya.  Sai kuma wani littafi mai suna Kitaabut tafheem Li-awaa'il Sinaa'atit tanjeem, wanda a harshen Turanci ake kira The Book of Instruction in the Elements of the Art of Astrology.  Littafi ne da ke bayanin hakikanin ilmin taurari. A cikin littafin ne Abu Raihaan ya bambance tsakanin ilimi kan taurari da rayuwarsu, da yanayinsu, da tasirinsu a sararin samaniya, duk a kimiyyance, da kuma ilimin taurari da bokaye ke amfani da shi wajen ikirarin sanin gaibu, ko wani mummunan lamari da ake tunanin zai faru idan tauraruwa kaza ta bullo a misali.  Nau'in ilimin taurari na farko, a cewarsa, shi ne abin da ya kamata a koya kuma a karantar da al'umma, saboda alakarsa da addini kai tsaye.  Amma nau'in ilimin taurari na biyu, shedanci ne, kuma musulunci bai yarda da shi ba. Domin taurari halittun Allah ne kamar sauran halittu, ba su da wani tasiri na musamman a bisa karankansu dangane da canza rayuwar mutane wajen samu ko rashi, wajen amfani da ko cutarwa.
Littafi na gaba shi ne Al-aathaarul Baaqiyah, anil Quroonil Khaaliyah, littafin da ke bayani kan tarihin al'ummomin da suka gabata, da irin tasirin da suka yi cikin abin da suka bari na kimiyya a duniya.  A cikin littafin yana kokarin gwama tsakanin al'ummomin da suka gabata ne, da irin tasirin da suka yi wajen barin wani abu da ake dogaro da shi na kimiyya.  Kamar irin fasaharsu wajen gano shigan wata, da karewarsa, da amfani da taurari wajen gano bigiren wasu garuwa ko kasashe.  A takaice dai littafi ne na tarihi, wanda ke cakude da ilimin sararin samaniya, da lissafi, da kuma tarihin al'ummomin da suka shige.  Sai kuma littafi mai suna: Qaanoonul Mas'oodi.  Littafi ne na kamus kan abin da ya shafi kalmomi na musamman, da fannoni na musamman, da malamai shahararru kan ilimin Sararin samaniya, da lissafi, da ilimin kasa, da fasahar gine-gine.  Ya sadaukar da littafin ne ga daya daga cikin 'ya'yan Sarki Mahmood Al-Ghaznawi, mai suna Mas'ood.  Turawa kan kira littafin da suna: The Mas'udi Canon.
Sai littafi na gaba mai suna: At-tafheem Li Sinaa'tit Tanjeem.  Littafi ne mai dauke da tambayoyi da amsa kan ilimin taurari da bambance-bambancen da ke tsakanin nau'ukan ilimin taurari kamar yadda bayani ya gabata a baya, da ilimin lissafi, da ilimin sararin samaniya.  Ya rubuta shi da Larabci, sannan ya juya shi zuwa harshen Farisanci. Sai littafi da ya rubuta kan sinadaran da ke karkashin kasa wadanda Allah ya tanada wa bayinsa mai suna: Al-Jamaahir fee Ma'arifatil Jawaahir.  A harshen Turanci ana kiransa Gems.  Ya sadaukar da wannan littafi ne ga daya daga cikin 'ya'yan Mas'ud mai suna Mawdood. Sai kuma littattafan da ya rubuta na tarihin garin Khawaarizm, da tarihin Mahmud Al-Ghaznawi da mahaifinsa, da kuma fasahar gano bigire a duniya  mai suna Astrolobe da ya kera, sai littattafan da ya rubuta kan ilimin magunguna da harkar likitanci.
Dukkan wannan kokari da yayi suna nuna tsananin kwazonsa ne wajen tabbatar da ilimi, da son ciyar da al'umma gaba, da kuma karfin imani da sakamakon da Allah ya tanada wa masu ayyuka kyawawa.  Kamar sauran mutane masu numfashi, Abu Raihaan bai dawwama ba a duniya shi ma. A karshe Allah ya karbi rayuwarsa.  Bari in barku da daya daga cikin manyan abokan karatunsa mai suna Abul Hasan 'Ali bn 'Eesa, wanda ya zanta da shi cikin numfashinsa na karshe.  Ga abin da yake cewa:
“Na ziyarci Abu Raihaan a lokacin da yake fama da cutar ajali.  Ina shiga inda yake, nan take na gane cewa lallai ya kusa barin wannan duniya.   A cikin wannan hali ne yake sanar da ni cewa, a haduwarmu ta karshe lokacin da muke tattaunawa kan wata mas’ala da ta shafi rabon gado, akwai wani abu da na fada, wanda daga baya ya gane cewa kuskure ne.  Nan take sai na tausaya masa, har na ke ce masa ai yanzu ba lokacin da ya kamata a tattauna batu irin wannan bane; musamman ganin halin da yake ciki na rashin lafiya.  Sai ya ce mini, “Ai ni tuni na san zan bar wannan duniya, amma kuma ba ka ganin ya dace a ce in fahimci wannan mas’alar, da a ce na mutu da jahilcinta?”  Daga nan sai na maimaito masa abin da na fada, sannan ya fara mini bayani dalla-dalla.  Muna gama wannan tattaunawa da shi, sai na tashi na fita.  Fita na ke da wuya, sai na fara jin kururuwa, daga nan na fahimci cewa lallai ya rasu.  Rayuka masu daraja irin wadannan ne ke kasancewa cikin karfi da kuzari har zuwa numfashinsu na karshe.”

Abu Raihaan al-Bairooni ya rasu ne ranar 13 ga watan Disamba ta shekarar 1048 miladiyya, daidai da shekara ta 387 kenan bayan Hijira, yana dan shekaru 75.  Allah gafarta masa, ya kuma sanya Aljanna makomarsa da mu baki daya.

 

No comments:

Post a Comment