Gabatarwa
Al-Fazaaree, daya ne daga cikin sahabban Manzon Allah (tsira da
amincin Allah su kara tabbata a gare shi), watarana ya dawo gida sai ya samu
matarsa ta haifa masa jariri baki sitik!
Nan take hankalinsa ya tashi. Domin
balarabe ne shi, farin balarabe kuwa.
Haka ma matarsa. Amma ta yaya aka
yi ta haifa masa jariri baki sitik? Nan
take ya nannade wannan jariri a zanen gayo, ya kama hanya sai wajen Manzon
Allah (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi). Yana zuwa ya tarar da shi cikin sahabbansa
kamar galibin lokuta. Yana isowa wajensa
bayan ya masa sallama, sai ya nuna wa Manzon Allah wannan jariri, ya ce:
"Dubi abin da ta haifa mini."
Sai Manzon Allah (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) ya
fahimci inda ya dosa nan take. Sai ya ce
masa: "Kana da rakuma?" Sai ya ce: "Eh, ina da su." Sai Manzon Allah ya sake ce masa: "Meye
launinsu?" Sai ya ce: "Jajaye
ne." Sai Manzon Allah ya sake ce
masa: "Babu wani mai launin baki-baki daga cikinsu?" Sai wannan
balarabe ya ce: "Akwai," sai
Manzon Allah ya sake tambayarsa: "Daga ina ya samo wannan launi (bayan
iyayensa jajaye ne)?" Sai Al-Fazaaree
ya ce: "Watakila wata jijiyar (dabi'ar) halitta ce ya jawo (daga
kakanninsa)." Sai Manzon Allah ya
ce: "Haka shi ma wannan, ta yiwu
wata jijiya ce ya jawo (daga kakanninsa)."
Watarana Manzon Allah (tsira da amincin Allah su kara tabbata a
gare shi) yana zaune sai ga wani daga cikin mutanen Madina ya riko matarsa,
rike da jariri baki sitik su ma, a kidime.
Suna zuwa wajensa sai mutumin ya ce: "Ga abin da ta
haifa." Sai matar ta yi caraf ta
ce: "Na rantse da Wanda ya aiko ka da gaskiya, a matsayin cikakkiyar
budurwa ya aure ni, kuma ban taba shigo da wani gidansa ya haye kan tabarmarsa
ba." Fadin haka ke da wuya sai
Manzon Allah (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) ya nuna cewa
lallai abin da ta fada gaskiya ne. Domin
daga ita har shi suna da dabi'un halitta wajen casa'in da tara ga kowanne, kuma
kowanne daga cikinsu na yaduwa cikin jikinta ne a lokacin saduwa, yana rokon
Allah da ya sa jaririn da za a haifa ya zo da kama irin nashi.
Ummu Sulaim ita ce mahaifiyar Anas dan Maalik (Allah kara musu
yarda). Watarana ta shigo inda Manzon
Allah (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) yake zaune tare da
sahabbansa, sai ta ce: "Ya Manzon Allah, hakika Allah ba ya kunyar bayyana
gaskiya. Shin, wanka ya wajaba ga mace
idan tayi mafarki (ana saduwa da ita)?"
Sai Manzon Allah nan take ya ce mata: "Na'ma, muddin ta ga ruwa."
(Ma'ana ruwan maniyya kenan). Nan take
sai Nana Aisha ta ce: "Shin mace ma na fitar da wani ruwa ne?" Sai Manzon Allah ya ji, kuma ya bata amsa da
cewa: "Kayya, Aisha! Ta yaya ake samun kamaiceceniya to, (tsakanin jariri
da iyayensa)?"
Daidai lokacin da Manzon Allah (tsira da amincin Allah su kara
tabbata a gare shi) ya shigo garin Madina lokacin hijira, sai Abdullahi ibn
Salaam, daya daga cikin manyan Malaman Yahudawan Madina ya je ya same shi, ya
ce masa: "Na zo ne in tambaye ka kan wasu abubuwa guda uku, wadanda babu
wanda ya sansu sai Annabi..." Daga cikin
tambayoyin da ya masa akwai neman sanin dalilin da ke sa jariri ke yin kama da
mahaifinsa ko mahaifiyarsa? Sai Manzon
Allah ya amsa masa cewa: "Idan ruwan (maniyyin) namiji ya riga na mace,
to, (jaririn) zai yi kama da mahaifinsa.
Idan kuma ruwan (maniyyin) macen ne ya riga na namijin, to, (jaririn)
zai yi kama da mahaifiyarsa." Daga
nan sai Abdullahi ibn Salaam ya ce: "Na shaida hakika babu abin bautawa a
bisa cancanta face Allah, kuma lallai kai Manzon Allah ne."
………………………………..
Daga cikin nau'ukan ilmin kimiyyar halitta da rai a duniyar yau,
akwai fannin da ke bincike kan dalilan samun kamaiceceniya tsakanin 'ya'ya da
iyayensu ko kakanninsu, na kusa ne ko na nesa.
Da kuma kamaiceceniya ta dabi'ar jiki, da dabi'ar tunani, da dabi'ar
juriya ko ragwanci, da dabi'ar kirar jiki, da dabi'ar tsawo da gajarta, da
dabi'ar zati ko mutuntaka, da dabi'ar sanyi ko zafin zuciya, da dabi'ar karfi
ko kudurar zuciya, da dabi'ar taushi ko kaushin hali da yanayi, da dabi'ar
bambancin launin fata, ko launin gashin kai, ko yanayin farata da dai sauransu. Har wa yau, me yasa wasu 'ya'ya ke gadon
cututtuka daga iyayensu? Me yasa wasu ke
yin kama da dangin iyayensu ba da asalin iyayensu ba? Me yasa ake haifan 'ya'ya masu dauke da
cututtukan da iyayensu ba su da su? Me
yasa musamman a yau likitoci da ma Malaman addinin musulunci ke shawartar
samari da 'yan mata masu niyyar aure da su je don gunadar da binciken jini da
kwayoyin halittar jikinsu kafin su yi aure?
Me yasa jaririn da ake haifa wani ke zuwa namiji, wani kuma mace? Dukkan wadannan nau'ukan al'amuran halitta
ana binciken yanayinsu ne karkashin wani sabon fannin ilmin likitanci mai suna "Genetics",
ko "Heredity" ko kuma "Genetic Inheritance", a
turancin kimiyyar halitta da rai.
Hadisin farko da ke sama Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi,
tare da sauran malaman sunan, wato Abu Daud, da Tirmidhi, da Nasaa'i, da Ibn
Majah. Hadisi ne ingantacce. Hadisi na
biyu kuma mursal ne, ba hadisi bane ingantacce, amma ma'anar da ke
cikinsa daya ne da wanda ke cikin hadisin da ya gabace shi. Wato hadisin farko ya karfafe shi wajen
ma'ana kenan. Hadisi na uku ingantacce
ne, domin Muslim ne ya ruwaito shi. Sai
hadisi na hudu, wato hadisin Abdullahi ibn Salaam, shi ma ingantacce ne, domin
Bukhaari ne ya ruwaito shi. Dukkan al'amuran halitta da ke dunkule cikin
wadannan hadisai da suka zo a sama, abubuwa ne masu ban mamaki da suka faru, wadanda
a lokacin faruwarsu babu wanda zai iya gudanar da wani bincike a likitance don
gano sababin faruwarsu, sai dai kawai a yi imani. Amma a yau Allah ya kawo mu lokaci da zamani
mai cike da yalwa wajen samuwar kayayyaki da fasahar binciken kimiyya da
likitanci, cikin sauki. Ganin irin
tasirin da wannan tsarin bincike ke yi a sauran kasashen Turai na yau, musamman
kasar Amurka, yasa na ga dacewar gudanar da bincike na musamman don kosar da
masu karatu, da yardar Allah, dangane da wannan sabon fannin bincike, duk da
cewa dadadden ilmi ne. Amma Malaman
kimiyyar zamani basu fara gudanar da bincike a cikinsa ba sai cikin shekarar
1981.
Wannan kasida za ta gudanar da bincike ne kan asali da dalilan da
ke haddasa wadancan al'amura. Da farko
bayanai za su zo kan ma'anonin kalmomin turanci masu alaka da wannan bincike,
wadanda mai karatu zai ta cin karo dasu a halin karatunsa. Sannan bayanai kan "Kwayar Halitta"
ko "Tubalin Halitta", watau "Cell" su biyo baya. A nan ne za mu fahimci tsarin wannan sinadari
mai matukar muhimmanci, da yanayinsa, da muhallinsa, da adadinsa, da kuma
abubuwan da ke kunshe a cikinsa, musamman irinsu "Tantanin Kwayar Kalitta"
ko ganuwarta, watau "Cell Membrane", da "Ruwan Rayuwa",
watau "Cytoplasm", da kuma "Asalin Sinadarin Halitta",
watau "Nucleus." A cikin
sinadarin halitta ne al'amuran da suka shafi bincikenmu suke kunshe.
Abu na farko shi ne "Madarar Bayanan Dabi'ar Halitta,"
wato "DNA" ko "Deoxyribonucleic Acid", a warware. Sai kuma babbar kundi, wato "Ma'adanar
Bayanan Dabi'ar Halitta," ko "Chromosome" a turance. Bayan mun yi bayani kan wannan babban kundi,
sai mu zarce kan sauran abubuwan da ke da alaka da wannan babban kundi mai dauke
da dukkan bayanai kan dabi'un da 'ya'ya ke gadonsu daga iyayensu, irinsu
"Dabi'ar Halitta," wato "Gene". Da "Dabi'ar Halitta ta Musamman,"
wato "Allele." Sai kuma "Kebantacciyar
Dabi'ar Halitta," wato "Trait" ko "Genetic Trait",
wadda ita kuma ta kasu kashi biyu ne; akwai "Dabi'a Mafi Rinjaye,"
wato "Dominant Trait," da kuma "Dabi'a Nakasasshiya," wato
"Recessive Trait."
Wadannan su ne damuwanmu cikin binciken baki daya. Kuma Fannin gudanar da bincike kansu shi ake
kira "Genetics." "Nau'in
Dabi'ar Halittar" mutum kuma shi ake kira "Genotype". Wannan wani abu ne da ba a iya gani, kamar
yadda bayanai za su nuna mana nan kusa. Amma "Nau'in Dabi'ar Halitta na
Zahiri" (irinsu kama, da launin jiki, da launin idanu, da tsawo da
sauransu) shi ake kira "Phenotype."
"Gadon Dabi'ar Halitta" daga iyaye ko kakanni kuma, shi ake
kira "Heredity" ko "Genetic Inheritance." Dan adam ba ya rayuwa sai da matsaloli na
abin da ya shafi lafiyar jiki. Wannan
ka'ida ce gamammiya da Allah ya sunnata wa dan adam, hatta kan abin da ya shafi
"Gadon Dabi'ar Halitta" akwai shi.
Idan aka samu matsala wajen gadon wata dabi'a ta halitta, har abin yayi
mummanar tasiri ga rayuwar mai gadon, a kimiyyance an samu abin da ake kira "Genetic
Disorder" kenan. To, shi dan adam a
duk sadda ya samu kansa cikin matsala, duk tsawon zamani, sai yayi kokarin
neman magani; ta hanyar halal ko ta hanyar haram. Ya danganci irin tarbiyya ko lalurar da ya
samu kansa a ciki. Don haka,
"Fannin Ilmin Magance Tangardar Dabi'ar Halitta" shi ake kira
"Genetic Engineering." A
karshe wannan kasida za ta dubi hukuncin halacci ko haramci a Musulunci,
dangane da abin da ya shafi tsarin da Malaman Kimiyyar likitanci ke bi a yau,
wajen gyara dabi'ar halittar da ta samu tangarda, sanadiyyar nakasu daga dayan
iyayen mai gado.
Wadannan su ne shahararrun kalmomin da mai karatu zai ta cin karo
dasu. A sashen da ke tafe cikakken
bayani zai zo kan kowannensu, don a fahimci abin da kowanne yake nufi.
No comments:
Post a Comment