Wednesday, February 13, 2013

Tsakanin Kwakwalwa d Zuciya...(4)



Yadda Tunani ke Samuwa, A Kimiyyance

A yau muna dauke ne da bayanai kan binciken malaman kimiyyar zamani, da sakamakon da suka samu da a cewarsu lallai tunani na samuwa ne daga kwakwalwar  dan adam.  Wannan shi ne ra'ayin malaman kimiyyar zamani.  Shi ya sa ma daya daga cikinsu mai suna Albert Einstein yake cewa: "Wannan duniyar da muke zama a cikinta mun kera ta ne ta hanyar tunaninmu; don haka babu yadda za a yi ta sake canzawa sai mun canza tunaninmu."  Wannan kalma ta tunani da ya ambata yana ishara ne ga tunanin da ke darsuwa ko samuwa daga kwakwalwa, kamar yadda sakamakon bincikensu ya nuna musu.  Sai dai kuma, da duk da wannan sakamako da suka fitar, har yanzu suna ganin cewa babu bangaren jiki mai wuyar sha'ani wajen fahimta irin kwakwalwar dan adam.  Domin duk tsawon zamani da duniya ta dauka ana gudanar da bincike kan yadda tsari da kintsin kwakwalwa yake, har yanzu abin da aka gano a ilimance dangane da kwakwalwa da irin yadda yake gudanar da aikinsa, bai wuce kashi 5 ba cikin 100. 

Daga cikin bangarorin da fahimtar tsarinsu da yadda suke samuwa yafi komai wahala, akwai tsarin tunani, da kuma yadda "hankali" ke samuwa a tare da mutum.  Shin, daga kwakwalwa yake ko daga ina?  Shi kanshi wannan wani bincike ne mai zaman kansa.  Domin idan ka bude kwakwalwar dan adam, kamar yadda bayani ya gabata a kasida ta biyu, ba abin da za ka gani sai tarin jijiya da yadi, da hanyoyin jini, da kuma romon kwakwalwa, watau Brain Protein.  Amma kuma, a cewarsu, wadannan bangarori ne ke samar da ji, da gani, da dandano, da tabawa, da fahimta, da hardace abubuwa, da yanke hukunci kan wasu ra'ayoyi biyu, da dai sauransu.  Babu wanda ya fito fili ya bayyana irin sarkakiyar da ke dauke cikin kwakwalwa irin wani masanin kimiyya mai suna Gottfried Leibniz.  Ya nuna cewa babu abu mafi wahalar fahimta irin yadda tunani da fahimta ke samuwa daga kwakwalwar dan adam, musamman ganin cewa ba wani girma bane da shi, sannan idan ka bude ciki in ban da yadi da jijiyoyi da romon kwakwalwa babu abin da za ka gani.  Har ya ba da misali da babban injin da ke sarrafa na'urar makamashin iska, watau Windmill.  Yace idan ka bude ciki babu abin da za ka gani sai karafa; wani akan wani, ko wani na juya wani.  Wannan zance nashi ya shahara a tsakanin masana, har a karshe ake mata lakabi da: Leibniz Mill. 
  
Bangarori Masu Alaka da Tunani

Kafin mu yi nisa, kwakwalwa na da bangarori daban-daban.  Amma a jimlace malaman kimiyya kan kasa kwakwalwa ne zuwa gida biyu.  Da bangaren dama wanda suke kira Right Hemisphere. Sai bangaren hagu da suke kira Left Hemisphere.  Bincike ya tabbatar da cewa jijiyoyin da suka taso daga kwayoyin idanun dan adam suna like ne a kwakwalwa.  Jijiyoyin idon bangaren hagu na like ne da bangaren kwakwalwa na dama.  Su kuma jijiyoyin idanu na dama suna like ne da bangaren kwakwalwa na hagu.  Bayan haka, bincike ya nuna cewa bangaren kwakwalwar dan adam ta dama, ita ce ke sarrafa bangaren jikinsa na hagu.   Bangaren kwakwalwarsa ta hagu kuma ke sarrafa bangaren jikinsa na dama. 

Bangaren kwakwalwa mai lura da tsarin tunani da fahimtar yanayi da yanke hukunci, shi ne bangaren da ke gab da goshi, wanda malaman kimiyya ke kira Cerebral Cortex.  Daga cikin wannan bangare akwai tsagin da ake kira Frontal Cortex, wanda ke da alaka da wani gungun tsarin da ke lura da sha'awa, da sinsino, da fahimta, da tunani, da barci, da jin zafi, da jin dadi, da gamsuwa, da jima'i, da sauran al'amuran da suke da alaka da dabi'ar jiki.  Wannan gungu na tsarin kwakwalwa shi ake kira da suna The Limbic System, kuma yana shimfide ne a kasa daga ciki, ya kuma bazu zuwa bangaren kwakwalwa na hagu da dama, da bangaren goshin dan adam.  Daga cikin bangarorin wannan gungu na Limbic da ke lura da dabi'a, bangaren Frontal Cortex ne ke lura da tsarin tunani sakakke, watau Abstract Thoughts.  Shi ne ke lura da karfin tunani kuma mai sa a iya yanke hukunci, ko daukan zabi a tsakanin nau'uka ko jinsin abubuwa guda biyu.

Amma kafin haka ya samu a wannan bangare na Frontal Cortex, sai ya samu bayanai kan abin da ya danganci nau'in tunanin da zai yi.  Wadannan bayanai kuwa suna samuwa ne ta hanyar kwayoyin halittar kwakwalwa, watau Brain Cells, masu dauke da sakonnin sadarwa ta hanyar maganadisun lantarki da ke samuwa a jijiyoyinsu da ake kira Glia a kimiyyance.  Wannan jijiya ta Glia ce ke dauko bayanai daga jijiyoyin da suka fito daga idanu (wajen gani), da wadanda suka fito daga kunnuwa (wajen ji), da wadanda suka fito daga harshe (wajen dandano), da wadanda suka fito daga hanci (wajen shaka), sai wadanda suka fito daga fatar jiki (wajen fahimtar suka, ko yanka, ko duka, ko duk wani abin da ya taba jikin da adam).   Wadannan su ne kafofin samar da bayanai guda biyar da ke jikin dan adam. 

Da zarar bangaren Glia ta tattaro wadannan bayanai, sai ta hada kai da jijiyoyin sadarwar kwakwalwa, watau Neurons, da kuma sinadaran Hormones.  Nan take sai su sana'anta wadannan bayanai da suka taro don samar da tunani da ji irin na zuci (watau Emotions), kamar yadda Mark Treadwell, wani masanin kimiyya dan kasar New Zealand ya tabbatar.  Idan bayanan masu alaka da zartar da hukuncin wani aiki ne na gabar jiki a aikace, nan tace sai jijiyoyin bangaren sadarwar jiki (watau Motor Neurons) su zaburar da su wajen aikatawa.  In kuka ne, nan take sai dan adam ya kece da kuka.  In dariya ne, ko bakin ciki ko annashuwa, duk nan take suke samuwa. Wannan nau'in tunani wanda ke samuwa ba tare da son dan adam ko yardarsa ba, shi yafi yawa daga cikin nau'ukan tunani da adam ke yinsu a kullum.

Malaman kimiyya sun kiyasta cewa a cikin duk dakika guda, kwakwalwar dan adam kan taro bayanai sama da miliyan biyu ta wadannan hanyoyin samar da bayanai biyar.  Daga cikin miliyan biyu din nan, kashi biyar cikin dari ne kadai dan adam ke iya sarrafa su don yin tunani da nufinsa.  Amma duk sauran na tafiya ne wajen tunani irin na dabi'a, wadanda Allah ya tsara halittarsa a kansu. Ire-iren wadannan tunani ma dan adam ba ya sanin ya yi su.  Saboda tsarin da suke gudana, da saurin gudanuwarsu.  Misali, irin waige, da motsa yatsun hannu, da bita idanu, da hadiye yawu, da neman abinci idan yunwa ta karato, ko neman ruwan sha idan kishirya ta koro shi.  Dukkan wadannan abubuwa suna bukatar tunani kafin yinsu.  Amma da yawan lokuta dan adam ba ya taba tuna cewa ga lokacin da ya yanke shawarar aikata su kafin suka faru.  Sai dai yace kawai yayi su lokaci kaza.  Wasu ma ba ya iya tuna ya gudanar da su.  To amma, ta yaya malaman kimiyya suka gano wadannan al'amura?

Tsarin Bincike Don Tabbatar da Tunani

Akwai hanyoyi uku da malaman kimiyya suka bi ko suke bi a halin yanzu wajen fahimtar tsarin tunani da duk wani abin da ya shafi gudanuwar kwakwalwar dan adam.  Hanya ta farko ita ce ta hanyar amfani da kwakwalwar wasu halittu masu kama da na dan adam, irinsu Birai, da Gwaggon biri da sauransu.  Suna yin haka ne saboda akwai kamaiceceniya tsakaninsu, duk da cewa kwakwalwar dan adam ta bambanta nesa ba kusa ba da na wadannan halittu.  Sukan fahimci wasu abubuwa ta hanyar wannan kamaiceceniya dake tsakaninsu. 

Hanya ta biyu ita ce idan hadari ya faru wanda ya shafi kwakwalwar dan adam.  Misali idan ya samu buguwa a wani bangare na kansa har abin ya kai ga kwakwalwa.  Da zarar ya warke sai su rika lura da shi, idan aka ga ya kasa magana, ko ya kasa hankaltar yanayin da yake ciki – ya zama wani sususu misali – ko ya kasa ji, ko ya kasa tuno wasu abubuwa da ya sani a baya, sai su fahimci cewa lallai wannan bangaren da ya samu buguwa ne ke da alhakin sarrafa abin da ya rasa na kudura a matsayinsa na cikakken dan adam. Sukan nuna wannan hatta a fina-finansu.  Misali, akwai wani fim mai suna The Bourne Identity, a cike  yake da irin wannan yanayi na bincike.

Sai hanya ta uku, watau hanyar binciken zamani kenan, wanda ya kunshi amfani da na'urorin sadarwa masu sinsino ko gano ko dauko hoton yanayin da kwakwalwa ke gudanuwa a wani lokaci na musamman.  Daga cikin irin wadannan na'urori akwai na'urar Electroencophalography (EEG), wacce ake amfani da ita wajen gano yanayin harbawan sinadaran lantarki (Electrical Impulses) da shawaginsu a kwakwalwar dan adam.  Sai na'ura ta biyu mai suna Magnetoencephalography (MEG), wacce ke darsano sinadaran maganadisun kwakwalwa, watau karfinsa wajen jawo ko sinsino yanayin da yake ciki.  Wadannan sinadaran maganadisu su ake kira Brain Magnetic Field. 

Wadannan, a takaice, su ne hanyoyin da masana ke bi wajen gudanar da bincike kan abin da ya shafi kwakwalwar dan adam. Da wannan, kamar yadda bayani ya gabata a baya, suke tabbatar da cewa lallai tunani na samuwa ne daga kwakwalwar dan adam.  A mako mai zuwa za mu tattauna kan nassoshin Kur'ani da abin da suke tabbatarwa wajen samuwar tunani ga dan adam. A ci gaba da kasancewa tare da mu.

No comments:

Post a Comment