Wednesday, February 13, 2013

Tsakanin Kwakwalwa da Zuciya...(7)



Matashiya
 
A makon jiya mun yi bayani kan yadda mahangar Malaman Musulunci suka sha bamban dangane da abin da ya shafi al'amuran zuciya da alakarta da "Hankali" da "Fahimta" da "Ruhi" da kuma "An-Nafs," wato "Zati" ko "Hakikanin" mutum kenan, wajen kokarin fahimtar yadda zuciya ke samar da tunani.  A karshe dai bayanai sun nuna mana cewa, yawan ambaton "zuciya" a cikin Kur'ani da Hadisai ingantattu, da yadda Malamai suka ta danganta tasirinta wajen tunani, na nuna lallai akwai wani sha'ani tattare da ita.  Duk da cewa malaman kimiyya a baya sun tabbatar kwakwalwar dan adam ce ke samar da tunani, amma ta la'akari da yadda nassoshin Kur'ani suka ta maimaita kalmar "zuciya" ta sa muka ce a yau za mu koma dakin binciken malaman kimiyyar wannan zamani, musamman daga shekaru 20 da suka wuce zuwa yanzu, mu ga ko sun gudanar da wani bincike kan matsayin zuciya dangane da tunani.  Domin, kamar yadda na sanar a kashi na 2, nassin Kur'ani ko Hadisi ba su canzawa dangane da abin da suke nuni zuwa gare shi, sai dai rashin dacewar mai bincike kan abin da suke tabbatarwa.  Idan suka ce abu kaza, kaza ne, to haka yake.  Idan mai bincike ya gano sai mu karbi bincikensa, idan ya gano sabanin abin da suka tabbatar, sai mu ajiye masa sakamakon bincikensa, mu ce masa: "Malam a dai koma dakin bincike, a hankali za a dace."  Domin wahayi ba ya canzawa, amma sakamakon duk wani mai bincike yana iya canzawa; dan adam ne shi; tara yake, bai cika goma ba.

Binciken Malaman Kimiyya Kan Zuciya

Malaman kimiyya sun gudanar da bincikensu na farko kan zuciya ne suna masu lura da matsayinta wajen famfon jini zuwa sassan jiki. Wannan mahangar bincikensu na farko kenan, wanda ya ta'allaka ne kacokan kan ayyukan zuciya na "zahiri" wadanda ake iya gani.  A marhala ta biyu, sadda aka fara samun yawaitan masu kamuwa da cututtukan zuciya masu alaka da tunani, sai suka sake komawa dakin bincike, inda suka sauya mahanga daga mahangar aikin famfon jini zuwa na fahimtar dalilin da ke haddasa kumburewarta, da kuma haddasa hauhauwan bugawan jini, wanda ke haddasa mutuwa nan take.  A nan ne suka gano mummunar tasirin yawan tunani, da bacin rai, da bakin ciki, wajen tauwaye wa zuciya karfin bugawarta da yin aiki yadda ya kamata.  To amma kuma, duk da wannan hobbasa da suka yi wajen gano haka, da kokarin samar da magunguna masu magance hauhawan jini wanda ke mummunan tasiri kan zuciya, yawan masu kamuwa da cututtuka masu alaka da zuciya bai ragu ba; sai ma karuwa yake yi a duk shekara, musamman a kasashen da suka ci gaba a fannin tattalin arzikin kasa da siyasa.  Sabanin yadda a baya tsofaffi ne galibi ke kamuwa da cututtuka masu alaka da zuciya, yanzu abin ya zama ruwan dare; daga samari zuwa 'yan mata, daga tsofaffi zuwa matasa, daga kasashe masu arziki zuwa kasahe masu fama da talauci. Kai, hatta likitoci sukan kamu da cututtuka masu alaka da zuciya.  Tirkashi!

Wannan lamari ne ya sake tilasta wa malaman kimiyya musamman masu lura da yadda zuciya ke gudanar da ayyukanta, da tasirin gazawarta wajen rage tagomashin rayuwa da tattalin arzikin kasa, suka sake komawa dakin bincike don gano hakikanin matsayin zuciya da alakarta da sauran bangororin jikin dan adam, musamman ma kwakwalwarsa.  Sanadiyyar wannan sabon tsarin bincike da aka faro tun shekarar 1983 ne aka fahimci abubuwa da dama kan alakar da ke tsakanin zuciya da sauran bangarorin jiki, musamman ma kwakwalwa.  Wannan sakamakon bincike da ake kan yi ne na kalato mana a yau, don mu samu wata sabuwar mahanga kan lamarin, kafin yanke hukunci na karshe.

Gamammiyar Alakar Sadarwar Jiki

Abu na farko da aka tabbatar shi ne, akwai gamammiyar alakar sadarwa tsakanin dukkan bangarorin jikin dan adam.  Ma'ana, dukkan gabobin jiki suna tarayya da juna wajen musayar bayanai a yayin gudanar da ayyukansu.  Daga kwayoyin halittar jiki da ke kaikomo a tsakaninsu (Cells), zuwa sinadaran Hormones da ke samuwa a cikin jiki masu kai-komo a tsakanin bangarorin jiki, duk bincike ya nuna suna dauke ne da bayanai daga wannan bangare zuwa wannan bangare. Wadanda suka fara gano wannan daga cikin masana su ne Dakta Gary E. Schwartz da Dakta Linda Russek ta hanyar wata ka'idar kimiyya mai suna "Dynamic Systems Memory Theory."  Daga cikin sakamakon binciken da wannan ka'ida ya hankado shi ne, da "Hankali", da "Fahimta", da "Irada", dukkansu sinadaran makamashin jiki ne masu samuwa ta hanyar musayar bayanai da bangarorin jiki ke yi.  Bayan Dakta Gary da Linda da suka tabbatar da wannan ta hanyar bincikensu, har wa yau akwai karin tabbaci da aka samu cikin binciken da Dakta Rollin McCraty da tawagarsa suka tabbatar su ma. 

Tasirin Zuciya a Jiki

Abu na biyu da aka sake tabbatarwa shi ne, Zuciya ce ke lura da kuma gyatta dukkan yanayin jikin dan adam; daga kwakwalwa har zuwa yatsun kafafunsa.  Domin ita ce kamar babbar na'urar samar da makamshin lantarki zuwa sauran sasannin jiki.  A binciken su Dakta Gary Schwartz, sun  nuna cewa: "Zuciya ce mabubbugar farko wajen samar da sinadarai da makamashin bayanai a jikin dan adam."  An kuma tabbatar da cewa, a duk bugawar zuciya wajen fanfon jini, wannan bugu kan samar da sinadaran lantarki sama da Watt 2, wanda zai iya haska karamin kwai na wutar lantarki.  Kuma zuciya ce ke aikin rarraba bayanai daga wannan bangare zuwa wancan, sannan ta karbo daga wani bangare zuwa wani. Duk bangaren da bai samu karban bayanai yadda ya kamata tsakaninsa da zuciya ba, to, ba zai iya gudanar da aikinsa yadda ya kamata ba, kuma wannan zai yi tasiri matuka wajen rage masa tagomashin rayuwa, musamman ta bangaren farin ciki da lumana.  Wannan na kunshe ne cikin ka'idar da suke kira: "Psychophysiological Coherence", wacce ke tabbatar da cewa, dan adam na samun kansa a halin "Cikakkiyar natsuwa" ne idan dukkan bangarorin jikinsa suna fahimtar sakon da zuciya ke aika musu ba tare da wata matsala ba. Bayan Dakta Gary, har wa yau an samu tabbaci daga binciken da Cibiyar Gudanar da Bincike kan Aikin Zuciya mai suna HeartMath Institute da ke kasar Amurka ta gudanar, karkashin Dakta Rollin McCraty.

Sadarwa Tsakanin Zuciya da Bangarorin Jiki

Abu na uku da aka sake tabbatarwa karara shi ne, akwai hanyoyi guda hudu da zuciya ke amfani da su wajen aiwatar da sadarwa zuwa sauran sasannin jiki. A cikin sakamakon bincikensu mai shafuka 103, Dakta Rollin McCraty da abokan bincikensa sun zayyana wadannan hanyoyi guda hudu a karkashin babi mai take: "System Dynamics: Centrality of the Heart in the Psychophysiological Network."  Hanyar farko ita ce ta hanyar jijiyoyin sadarwa da take dauke dasu, watau "Neurons", wadanda ke aikin musayar bayanai tsakanin zuciya da sauran bangarorin jiki, musamman ma kwakwalwa.  Sai hanya ta biyu wacce ta kunshi aiwatar da sadarwa ta hanyar sinadarai masu suna "Hormones."  Su sinadaran "Hormones" wasu nau'ukan sinadarai ne da bangarorin jiki ke samar da su, kuma suna dauke ne da bayanan sadarwa daga wanda ya samar da su zuwa bangaren da ake son su isar da sakon gare shi.  Zuciya kan samar da wadannan nau'ukan sinadarai masu dimbin yawa, kuma ta hanyarsu ne take aikawa da sakonni ga sauran bangarorin jiki.  Hanya ta uku ita ce ta amfani da sautin bugun zuciya da ke samuwa a duk lokacin da jini ya shigo ko yake fita daga zuciyar.  Shi kanshi wannan sautin bugun zuciya, wanda suka kira: "Pressure and Sound Waves" an lura cewa akwai bayanai na sadarwa da ke dauke a cikinsa, wanda bangarorin jiki ne kadai ke iya fahimta tare da sarrafa su.  Sai hanya ta karshe, wato ta hanyar sinadaran maganadisu, ko "Electromagnetic Field" a harshen malaman kimiyya.  Wannan hanya ta karshe na daga cikin abubuwa masu ban al'ajabi da zuciya ke samar da su.  Yanayi ne mai dauke da bayanai cikin sinadaran maganadisu, wanda ke bulbulowa daga zuciya, ya game sauran sasannin jiki daga ciki, sannan ya game muhallin da mai zuciyar yake.

A wani gwajin bincike da Dakta Gary da abokiyar aikinsa Linda suka gudanar, inda aka gwama kwayoyin halittar zuciya (Heart Cells) guda biyu na mutane daban-daban a mahalli daya, sakamakon bincike ya tabbatar da samuwar wani "gamammen tsarin musayar bayanai" da ya shiga tsakaninsu da hanyar sinadaran magadisu.  Wannan mahallin sinadarin maganadisu da zuciya ke fitarwa asalinsa daga kwayoyin halittu ne da ke cikin zuciyar, watau "Heart Cells".  Su wadannan kwayoyin halitta na zuciya, bincike ya nuna cewa a duk sadda zuciya ta buga, wannan bugu kan haifar da makamashin maganadisu da karfinsa zai iya haska dan karamin kwan lantarki.  Bayan haka, akwai na'urar gwajin zuciya mai suna "Electrocardiogram" (ECG), wadda ke dauke da wayoyi masu sinsino sinadaran lantarki ko maganadisu daga zuciya, don gano yanayin da zuciya ke ciki, da tsarin bugawarta, da kuma yanayin lafiyarta.  Galibi akan dora wadannan wayoyi ne a kan kirji da hakarkarin mara lafiya don fahimtar hakan. Daga baya aka gano ta hanyar bincike da gwaji, cewa a duk inda aka dora su a jikin mutum, na'urar na iya sinsino sinadaran lantarki da maganadisu daga zuciyarsa, saboda gamewarsu; abin da ke nuna karfin tasirin wannan yanayi na zuciya. 

Kari a kan haka, bincike na baya-bayan nan kuma ya sake tabbatar da cewa, idan mutum na kwance ko yana zaune, na'urar ECG  na iya daukan hoton zuciyarsa da tazarar kafa uku daga inda yake, ba tare da an manna masa wayoyinta a jikinsa ba don darsano sinadaran lantarki da na maganadisu.  Wannan ke nuna cewa lallai karfin tasirin zuciya a jikin dan adam ya shallake na kwakwalwa nesa ba kusa ba.  Domin na'urar "Electroencephalogram" (EEG) da ake amfani da ita wajen gwajin yanayin kwakwalwa, dole sai an manna wayoyinta a kai da goshin mara lafiya sannan ake hango yanayin bugawa da aikinta.  Amma na zuciya kuwa, ko da tazarar kafa uku ne daga inda mara lafiya yake ana iya daukan hoto da ganin yanayin da zuciyarsa ke aiki.  Wannan na yiwuwa ne sanadiyyar wannan sinadaran maganadisu da zuciya ke fitarwa, daga cikinta har zuwa waje, wanda malaman kimiyya suka ce yana game mahallin da tazararsa ya kai nisan kafa biyar. 

A wani binciken da Cibiyar HeartMath da ke jihar Kalfoniya na kasar Amurka ta gudanar, ya tabbata cewa ta hanyar wannan sinadaran maganadisu mai gamewa, zuciyar dan adam ta kan fahimci hali da yanayin mahallin da take ciki nan take, domin bincike ya nuna cewa ta wannan hanya zukata kan aiwatar da sadarwa a tsakaninsu, ba tare da an yi magana ko jin wani sauti ko kallon wani abu ba.  Shi yasa da zarar ka shiga unguwa ko gari ko wani wurin da babu zaman lafiya, nan take za ka sha jinin jikinka, saboda sadarwa da zukata ke yi a tsakaninsu. Wanda ya fara aiwatar da bincike a kan haka shi ne Karl Pribam, ta hanyar wata ka'idar kimiyya da ya kira: "Spetral Domain."  A karshe, sakamakon binciken Cibiyar HeartMath ya tabbatar da cewa: yawan damuwa, da bacin rai, da tashin hankali, da bakin ciki, suna rage karfin sadarwar zuciya, da rage tagomashin garkuwar jiki, sannan su rage karfin bugun zuciya wajen aika jini da kashi 5 zuwa 7.  A yayin da farin ciki, da kauna, da yafiya, da godiya suke kara karfin maganadisun lantarkin sadarwar zuciya, da sinadaran "Hormones" masu aikawa da sakonnin bayanai daga zuciya zuwa sauran bangarorin jiki, da kara wa garkuwan jiki (musamman sinadaran "White blood cells") karfi, don ba jiki kariya daga warakar cututtukar sankara da sauransu.

A mako mai zuwa in Allah ya yarda, za mu kawo bayanai masu nuna alakar da ke tsakanin zuciya da kwakwalwa ta bangaren sadarwa, daga nan za mu yi hukuncin karshe kan asalin tunani.  A ci gaba da kasancewa tare da mu.

No comments:

Post a Comment