Rabe-raben Fannin Dabi'u da Siffofin Halitta
Kamar sauran fannonin ilimi da muke dasu a yau, Malamai sun kasa
wannan fanni na binciken dabi'u da siffofin halitta zuwa kashi hudu. Sun yi hakan ne ta la'akari da fadinsa,
saboda fanni ne mai fadi sosai, musamman a wannan zamani mai dauke da ci gaba a
fannin kimiyya da kere-kere, wanda kuma ya dada taimakawa wajen kawo irin ci
gaban da ba a samu ba cikin shekaru 100 da suka gabata. Dalili na biyu kuma shi ne, saboda sawwake
tsarin daukan ilimin da kuma gudanar da bincike a cikinsa don fa'idantar da
al'umma. Dalili na uku kuma shi ne, don bambance asalin wannan fanni, da irin
nau'in binciken da ya gudana a zamani ko marhala ta farko, da irin binciken da
yake gudana a wannan zamani ko marhala da muke ciki. Wannan shi zai taimaka wa malaman tarihi kan
tsarin bincike a fannin dabi'u da siffofin halitta, don bambacewa tsakanin abin
da aka yi a baya da wanda ake yi a halin yanzu.
Ga takaitaccen bayani nan kan kowanne daga cikin wadannan rabe-rabe guda
hudu da ake dasu a halin yanzu.
Fannin 'Yan Mazan Jiya
Wannan shi ne bangaren binciken ilimin dabi'u da siffofin halitta
mai lura da asalin fannin baki daya. Shi
ne bangaren da ke lura da dukkan al'amuran da suka faru a marhala ta farko,
kamar yadda bayanai suka gabata a sashen baya.
Kuma shi ne bangaren da dukkan malamai suka yarda ya fi sauran inganci
dangane da asali da kuma tasirinsa.
Wannan reshe ne ke bincike kan siffofin halitta na bayyane, wato Phenotype,
da yadda kwayoyi halitta ke hayayyafa a tsakaninsu, wato Cell Division, don
haifar da gadon dabi'u da siffofin halitta daga iyaye zuwa 'ya'ya ko
zuriyarsu. Daga cikin abin da wannan
reshe na ilimi ya gano har wa yau, akwai dalilan da ke sa a samu bambancin
jinsi wajen haihuwa sanadiyyar wasu dalilai na zahiri, kamar yanayin mahalli da
tsarin jima'i a tsakanin jinsi biyu, da dai sauransu.
A wannan fanni ne aka gano tasirin mahalli wajen samar da jinsin
halitta. Misali, dabbobi irin su Kada,
da Kunkuru, duk an gano cewa irin mahallin da suke yin kwai a cikinsa ne ke
tabbatar da samuwar namiji za a haifa ko mace.
Sabanin jinsin dan adam, wanda hakan ke samuwa sanadiyyar dalilan dabi'ar
halitta na boye da ke can cikin Madaukan Dabi'ar Halitta (Chromosome). Bayan 'yan adam hatta dabbobi da shuke-shuke,
ta sanadiyyar wannan fanni ne aka gano irin tasirin mahalli da dabi'un halittar
da ke cikin kwayar halittarsu wajen samar da yabanya, ko yawan hayayyafa da dai
sauransu.
A wannan reshe ne har wa yau ake gudanar da bincike kan dalilan da
ke haddasa samuwar cututtuka daga iyaye zuwa 'ya'yansu, sanadiyyar bambanci ko
tangardar da ake samu a tsakanin sinadaran dabi'un halitta. Wannan fanni ne ke tabbatar da tsarin gadon
dabi'u da siffofin halitta a zahiri, watau Genetic Inheritance kenan. Kuma shi ne fannin farko da ake takama da shi
a duniya baki daya. Dukkan sauran
fannonin suna dogaro ne a gare shi wajen gina abin da suke gudanar da bincike a
kansa. Shi yasa hatta a Jami'o'in da
suke karantar da fannin Gadon Dabi'u da Siffofin Halitta (Genetics), wannan shi
ne reshen farko da ake fara karantar da dalibai kafin a haura zuwa wani reshe
da ke dogaro kan tsarin binciken kimiyya da fasahar zamani.
Idan muka yi la'akari da hadisan da muka kawo a baya, inda Manzon
Allah ke tabbatar da bambancin launin jiki, da bambancin jinsi wajen saduwa
tsakanin namiji da mace, za mu fahimci cewa duk sun kunshi abubuwan da wannan
reshe ne ke bincike a kansu. Haka
sakamakon binciken babban masanin kimiyyar nan mai suna Gregor Johann Mendel
dan kasar Jamus da bayani ya zo kansa a baya, inda ya tabbatar da samuwar gadon
dabi'u da siffofin halitta a tsakanin kwayoyin halittar shuke-shuke da mutane,
duk yana dogaro ne kan wannan reshe.
Haka sauran ra'ayoyin magabata kan fannin kimiyya da suka zo kafin
rubutun tarihi, duk da cewa wasunsu a cike suke da kurakurai, amma galibi
bayanansu na ishara ne zuwa ga abin da wannan reshe ke karantarwa. Don haka ake kiran wannan reshe da suna
"Classical Genetics" a Turance, watau "Fannin Ra'ayin Mazan
Jiya." Wasu sunayen da ake
kiransa
da su sun hada da "Mendelian Genetics" da kuma "Transmission
Genetics."
Fannin Sinadaran Dabi'ar Halitta
Fanni na biyu shi ne wanda ke dogaro kai tsaye ga tsarin bincike
kan yanayin sinadaran dabi'ar halitta, watau "Molecules." Abu na farko da wannan reshe ke bincike kansa
shi ne asalin "Dabi'ar Halitta" (Genes) da ke cikin kwayar halittar
kowace rai. Aikin wannan fanni ne gudanar
da bincike kansa, da yanayinsa, da tsarinsa.
Shi yasa wasu ke danganta wannan reshe da ga tsarin binciken dabi'ar
halitta na zamani, wato kishiyar reshen da ya gabata kenan.
Bayan asalin dabi'ar halitta, wannan reshe na gudanar da bincike
kan Ma'adanar Bayanan Dabi'ar (DNA), da Sinadaran Kara Kuzari da ke cikin
kwayar halitta (Cell Protein), wadanda ke sana'anta kowane kwayar dabi'a da
siffar halitta a cikin kowane mai rai.
Wannan reshe ne ke bayanin yadda dan adam ke samuwa daga kwayar halitta
(Cell) zuwa yadda yake a halin yanzu.
Reshen ne ke lura da tsarin gudanuwar jijiyoyi da kiftawar idanu da kuma
dabi'ar jure cututtuka, duk a mahangar dabi'ar halitta.
Daga cikin aikin wannan reshe har wa yau akwai bincike kan yadda
dabi'un halitta ke bayyana kansu da siffofinsu ga kowace halitta, watau
"Genes Expression." Sannan
yana bincken dalilan samuwar cututtuka irinsu Sankara (Cancer) ta hanyar
gamayyar dabi'un halitta, da yadda ake magance mantsalolin tangardar dabi'ar halitta
(Genes Therapy) da kuma kwaskwariman dabi'ar halitta ta hanyar kimiyya da
fasahar zamani (Genetic Engineering).
Wannan reshe, a takaice, shi ake kira "Molecular
Genetics" saboda tsananin dogaronsa kan asalin sinadaran da ke samar da
dabi'un halitta, da kuma amfani da tsari ko hanyoyin binciken zamani don
tantance al'amuran da suka danganci fannin baki daya.
Fannin Bambancin Dabi'u
Reshe na uku shi ne fannin Bambancin Dabi'u. Wannan fanni ko reshe yana bincike ne kan
bambance-bambancen da ake samu tsakanin nau'ukan halittu sanadiyyar
kebantuwarsu, ko yanayin mahallinsu, ko yanayin jima'i a tsakanin jinsinsu, ko
kuma dabi'un rayuwarsu. Ba nan kadai ba,
fannin na lura da wadannan abubuwa ne tare da karkasa nau'ukan da suka danganci
junansu a mahangar binciken ilimin dabi'un halitta.
Wannan reshe ne ke taimakawa wajen gano kamaiceceniya tsakanin
nau'ukan dabi'un halittar mutane ko dabbobi, da yadda za a samar da magungunu
ko hanyoyin waraka a likitance, don magance sauyin dabi'un halitta (Gene
Mutation) da ke faruwa ko samuwa a cikin Ma'adanar Dabi'ar Halitta, wato
DNA. Bayan gano wadannan
bambance-bambance, sai a rarraba su rukuni-rukuni, don tantance abin da ke hada
alaka a tsakaninsu. Idan aka samu wasu
matsaloli da suka danganci kebantuwarsu, sai a yi tunanin yadda za a samar da
waraka.
Don tabbatar da fahimta a kwakwalwar mai karatu, sun kawo misali da
daya daga cikin dabbobin dajin Afirka mai da aka si sani da suna
"Cheetah", wacce Allah ya hore mata kudurar gaugawa, da zafin nama,
da juriyar gudu na tsawon lokaci, da kaifin basira wajen fahimtar abin da zai
cutar da ita. Da malaman ilimin dabi'a
da siffofin halitta suka gudanar da wani bincike na musamman kan Dabi'ar
Halittar wannan dabba don fahimtar abin da ke kebance ta daga sauran dabbobi
masu dabi'a irin nata. Sakamakon
binciken ya nuna cewa jinsin wannan dabba ta "Cheetah" dabi'un
halittarsu duka iri daya ne. Sabanin
sauran dabbobi da ake samun bambancin dabi'un halitta a tsakanin jinsi
daya. Da wannan malaman ilimin fannin
dabi'ar halitta suka tabbatar da cewa akwai barazanar karewa da ke fuskantar
jinsin wannan dabba. Suka ce da zarar an
samu wata cuta wacce ke iya kashe su nan take, ba za a iya samun hanyar ceto
jinsin nasu daga karewa ba. Saboda babu
inda za a samu dabi'ar halitta irin tasu da za ta dace da dabi'unsu na zafin
nama, da kuzari, da kuru, da kaifin basira wajen kaucewa daga abokin gaba,
sannan da hikimar nemo abinci da sauransu.
Wannan fanni dai a yanzu shi ake kira da suna "Population
Genetics."
Fannin Alaka Tsakanin Dabi'ar Halitta da Siffofi
Wannan shi ne fanni ko reshe na karshe, wanda aikinsa shi ne
gudanar da bincike kan alakar da ke tsakanin dabi'ar halitta (Genes) da kuma
siffofin halitta na bayyane. A wannan
fanni ne ake fahimtar da alakar da ke tsakanin siffar halitta – misali, saurin
tafiya ga mutane, ko dabar iya nemo inda abu yake ga karnuka, ko yawan kwai ga
tsuntsaye da jinsinsu, ko kuma dabi'ar yawan yado da yabanya ga shuke-shuke ko
tsirrai da bishiyoyi. Wadannan dukkansu
dabi'u ne da siffofin halitta da suke kebance wasu jinsin halittu, ta wannan reshe
ake gano alakar da ke tsakanin wadannan dabi'u na halitta da siffofinsu.
Masana a wannan fanni ko reshe ne amfani ne da ka'idar
"Quantitative Trait Loci", wato "TQL" a gajarce. Da wannan ka'ida ne suke amfani wajen
fahimtar wannan alaka, musamman wajen gano yabanya a shuke-shuke da bishiyoyi,
da kuma yawan 'ya'ya ko ingancin rayuwa ga dabbobi. Wannan fanni shi ake kira "Quantitative
Genetics," kuma fanni ne mai cike da sarkakiyar lissafi da hasashe a fannin
kimiyyar lissafi.
No comments:
Post a Comment